Chapter 003
Tambarin Shahara Part 1 Complete Hausa Novel · about 11 min read
Mai_Dambu
*Wannan shafin kune masu sharing Ministan sharholiya tana mika muku godiya
a cigaba da Sharholiya kawai da shagali, Masu Comments mu ha
u next in sha Allah*
"Muje kin ji Hanjina shi yasa kullum nake miki Addu'oin Allah ya tabbatar da auren ku da Yazidulle" wani irin takaici ne ya kuma turnike Hajnah wato ita dai Dadah bata da wani buri na kuntattawa duniyar ta kamar ta hadata da wancan banzan, cikin zubar hawaye na cire hannunta tana kuka. "Wallahi bana son shi." Sake Dadah tayi da baki tana kallonta kafin ta ce mata. "Ungo naki, ban da shashanci namiji irin Yazidulle wacce mace ce zata ki shi? Yaron nan ga nutsawa ga ilimin addini, idan yana karatu ke kyace malam ne daga lahira ya dawo domin muryan shi sak da malam, gaki takwara Halimatu sadiyah kin ga babu me cewa wani abu, don Allah ki gayawa Yazidulle yayi wani abu naje Gombe" jin kiran Sallah yasa Dadah tayi shiru amma ba dan ranta yaso ba.
Imam Omar Hassan Sheikh, su din asalin
asar Nijeriya ce, kasuwanci da yawon adawa ya kawo Sheikh Hassan kasar Afrika ta arewa, har ya kafa zuri'ar shi amma asalin shi fulanin Gombe ne. Yana da matar shi Halimatu wacce aka yi musu auren zumunta, domin familyn su haka suke auren zumunta. Akwai kannen Imam mata biyu da suke can, Sayyadah Karimah wacce suke kiranta Umma Babba ita ce Mahaifiyar Yazidu, sai Sayyadah Hashimah, Yar ta Babban dan Imam Omar Hassan Sheikh zai aura. Daga can za a kawo ta Nuwanda.
Ganin yadda suke wata
asa yasa suka yanke hukuncin yin hadin zumunta da Yaran su, tun tsoho Sheikh Hassan yana raye shi da dan uwan shi, kuma cikin ikon Allah zaman yana daurewa domin ana zaman lafiya. Ita kanta Mamu Mahaifiyar su Hajnah ita ce karama a dakin su Baban Yazidu babban malami ne a garin gombe. Tunda Yazid ya ga Hajnah ya fada wani irin kaunarta, kamar zai yi hauka. Yayan shi Nurain yana nan a nan Nuwanda ana yake aikin banki kuma yana koyarwa a islamiyya,shi za a hada shi da Jadwah itama tana da wanda take so amma aka fi karfin ta, domin abu ne da ya shafi iyayen da kakanin. Nanah Babban dan Sayyadah Hashimah Hameem yana zaune a kasar Yemen, a can yake aiki ana shirin idan za ayi bikin su zai dawo karshen shekarar nan in sha Allah.
Imam Omar Hassan Sheikh yana da yara bakwai. Maza hudu mata uku.
Abubakar
Umar
Nanah Fatimah
Jadwa Hawwa'u
Hajna
Usaimin
Asad
Asad shi ne karamin su, duk yaran gidan Hajnah ita ce baka asalin baka, domin cewa suke mata sanjota aka yi a asibiti. Domin iyayenta farare ne sosai, sai haka yasa take jin ba dadi a cikin gidan, amma wani ikon Allah mahaifinsu da Mahaifiyar su kaunarta suke kamar su bada rayuwar su domin ita, haka yasa ta taso a sakalce amma tana da tsiwa domin masifaffiya ce, bata da tsoro sam duk abin da zaka ga taji tsoro a kai tow lallai abin tsoro ne, a lokacin da Mahaifin Yazid ya tuntubi Imam akanta, sai da ya rasa inda zai saka ran shi domin duk ta rigasu samun miji, koda ya gaya mata fashewa tayi da kuka ta ce mishi.
"Abeey don ina baka shi yasa zaka aurar da ni ko? Shi kenan." Ta mike zata fita ya ce mata. "Uwata zauna, ai da saura yanzu kike 15yrs zan barki kema ki samu damar fahimtar shi, idan kuma kina da wani abu sai ki fada."
"Abeey nifa bana son shi " zuba mata ido yayi, domin yana hango yarinta ce a lokacin don Allah ya ce mata. "Shi kenan ba zan mikk dole ba." Amma bawai ya bata damar ta zabi wani da kanta bane ya fada mata ne kafin lokacin da zata mallaki hankalin kanta ta sun fahimci juna da Yazid, tun daga ranar ta ce bata kuma zuwa Nigeria domin ba zata sake dauko damuwa ba.
Yanzu haka auren Abubakar da Umar da za ayi nan da wata biyu, a can Gombe ne za a daura za a kawo matan nan,.ana fara magana ta ce wallahi bata zuwa Allah ya kai su lafiya.
Hajiya shafa'atu Mahaifiyar su, tana da hakuri da son zaman lafiya, domin kuwa ita kanta tana da wanda taso a wajen family din su,.aka bada ita ga Imam kuma tayi hakuri ta zauna ba zaka tab'a cewa ba ita bace. Ita kanta tana
arin tankwara Yaranta suyi biyayya domin samun da cewa duniya da lahira.Daga Nanah har Jadwa karatun nurse suke, domin Imam ya ce nan ya dace da duk wata ya mace, amma Hajnah
arin ta yasa shi nima mata jami'ar da yake aikin koyar anan Nuwanda da wannan Yaran suka fahimci girman kaunar da yake mata. Su kan su yan uwan suna sonta halinta ya ja mata domin Hajnah bata da kintsi a gida, amma a waje, wata irin boss ce da bata daukar reni, idan ka ganta cikin hijab har da nikab. Amma a gida sai an sakata kuka, Domin ko Asad da ya
e auta bai kaita shagwab'a ba, uwa uba tana fama da wani irin cutar mura, wanda idan ya tashi kamar zata mutu, wannan yasa yan gidansu suke d'aga mata kafa bata aikin kome sai na wanka kamar agwagwa. Dake tasan laluranta ko ruwan sama bata yarda ta shiga, wani irin kulawa da kaunarta yake, domin ko tana aji idan lokacin shan maganinta yayi da kansa yake zuwa ya bata magani, haka yasa kowa ya gane irin kaunar da yake mata,.a yanzu haka tana aji daya na jami'a idan take karantar magani wato phamcy.
Bayan sun idar da sallah Dadah ta kalle ta, cikin niman su zauna lafiya ta ce mata.
"Halimatu wai ni kan me yasa." Kallon Dadah tayi kafin ta ce mata. "Kai Dadah meye kuma?" "A'a wai dama zan tambaye ki ne, ko Nurain yana zuwa wurin yar uwarki kwana biyu bai kawo min goro ba ne." Tasan Dadah da shegen son gulma, Dan haka ta gatsine fuska ta ce mata. "Ni bana son kwadayi wanda Abeey ya kawo ina kuma kika kai? Wallahi ki raba Kanki da cin goro da nama" tura baki tayi tana hararan Hajnah. "Hanjina bana son bakin ciki da mugun rowa,shima namar dan daukar alhakin rai hanawa zaki yi a kawo min, Hanjina duk cikin gidan nan waye nake nunawa so irinki da zaki ci amanata." " Ba wani amanarki da naci Dadah asalima kece kika ci amanata domin haka kawai kika kai ni aka hada ni da wani me dogon wuya can kamar lema, ayi mutum babu kulawa babu wata soyayya sai tsabar wa'azi, sai kace a kan shi aka fara da'awa "
Sake baki Dada tayi tana kallon ta,.kafin ta ce mata. "Hanjina!" Dadah ta fada tana salati tare da kiran sunanta. "Hanjina ba dai zagin shi zaki yi ba?" Tura baki tayi tana fa
in. "Huhunki dai Dadah wallahi sam kin cuce ni, ki san yadda zaki lalata shirin da kika kulla domin kika sake aka yi auren nan gawata za a kai gidan shi, karshe na zama fatalwa na hanaki barci mu tafi kabarina tare" "innalillahi wa'inna illahi raju'un, shafa'atu!!!" Dada ta fita waje tana ihu da kuka, duk yadda aka yi Hajnah ta fusata Dadah domin yadda ta fita zani a hannu da hijab a dokin wuyar zai fahimtar da kai a birkice take. Mamu tana lazumi taji muryan Dadah, ita kuwa oganniyar tana can daki zaune, tayi fuskar tana s
han fura da nama.
Da gudu Nanah ta fito tana kallon Dadah, da ta fyace majina da habbar zaninta tana fa
in. "Duk yadda aka yi Hanjina Aljanun fitsara ya shige ta, wai yau ni hanjina take cewa zata zama fatalwa ta ja ni kabarinta, haka bai mata ba sai da tace naci amanarta na shiga uku na lalace, ina zan kai rayuwata. Ni Hanjina take cewa na zama maciyar amana, kaf gidan nan waye ya san cewa tana shan kankara? Waye ya san cewa idan ana ruwan sama tana shiga tayi wanka, waye ya san cewa tana sace min kudina, kai haka bai isa ba sai da ta kai duk wata idan Imamu ya bani kudi wallahi tare muke rabawa, duk abin da na samu tare muke ci, ko kwanakin baya da kawayenta suka zo, ashe bashin kudi ta ci ta saya yi abu suka biyo ta amsa Allah yasa ina da shi na biya mata Asadu na tab'a baka labarin nan?" Cikin matukar tausayawa suka girgiza kai, fyace majina tayi tana fa
in. "Amma ban tab'a gayawa kowa abin da yarinyar nan take min ba wai ni ce naci amanarta." "Kema Dadah madalla nan muka zo ki bamu aron kudi har da rantse mana baki da shi, bamu san me muka miki ba kika tsane mu baki da abar kauna sai hanjinki, madalla gara da kuka yi fada yau mun ganku a rana" inji Nanah ta fada tana barin falon, Dariya Jadwah tayi tana fa
in. "Wannan fadar cikin gida ne, me karatu muje tambaya na gaba. " Ta fada tana kyalkyalewa da dariya, fitowar Mamu da ta gama jin rigimar Dadah da Hajnah ta cewa Asad. "Ubana kira min hamshakiya mandiya naji uban da yaci amanarta " da gudu ya nufi dakin Dadah. Ita kuma ta cigaba da bawa Dadah hakuri. Share kwalla tayi tana fa
in, "baki ga Kalwa dariya take min ba, ta maishe ni mahaukaciya." Daukar pillow Mamu tayi ta makawa Jadwah wacce ranta ya gama
aci da kiranta Kalwa, lokacin da Hajnah ta fito falo, kallon kallo aka yi a tsakanin ta da Dadah domin bata san me ya faru ba.
"Waye kika ce yaci amanarki?" Mamu ta tambaye ta, "innalillahi wa'inna illahi raju'un, Dadah dama kawo karata zaki yi? Lallai ma shi kenan." Ta fada idanunta yana kawo kwalla, "Hajnah wallahi zan sab'a miki, kar ki sake na mare ki zaki ji a jikin ki fa, wato har kankara kike sha? Shi yasa ciwon ki baya wuyar tashi " gallawa Dadah harara tayi. "Ai shafa'atu har madarata da milo na yarinyar nan kwabawa take ta saka a firij yayi sanyi ta sha ban tab'a gayawa kowa ba, ina gaya miki namar layyata ta bara yarinyar nan tass ta rabewa kawayenta sai dan dambun da ta bar min a kasar kwano ai ban gaya miki ba. Wai domin ina sonta." Wani irin kallo tayiwa Dadah ta hadiye maganar ta. "Yanzu don Allah na tambaye ki? Kina tsoron Allah?" Kuka ne ya kwace mata tana kallon Dadah cikin shashekar kuka ta ce. "Am sorry Mamu!" Ta juya zuwa dakin Dadah,.ta kwaso kayanta kaf, ta wuce dakin su ta zuba a drowa tana kuka. Dama sun saba fadar su, amma kuma yadda za a dawo a shirya yafi fadar tashin hankali. Kallon Mamu Dadah tayi cikin jin haushi ta ce mata. "Amma wallahi shafa'atu baki da hali, yanzu ke da zaki taya ni lallabata kece kika kuma tunzura min ita, yanzu don Allah waye zai kula da ni idan lokacin sallah dare na yayi? Fisabilillahi idan baki son zamana da Hanjina ai ba zaki fito min ta nan ba, yanzu ko Imamu ba zai iya tankwaro min Hali dubu, gaskiya baki da kirki." Ta mike tana masifa kamar ba ita ce ta kawo karar ba, ita kan ta Mamu sai da tayi danasanin shiga fadar Dadah da Hajnah, kuma tasan karshen haushinta za aji tunda Abeey ya daina shiga fadar ya samu salama, da duk wannan korafin Washi za akaiwa. Ta kuma san fushin Hajnah bazata sauko nan kusa ba. Haka Dadah tayi ta sintiri ita kuwa Oganniyar tana gama shirya kanta, ta kwanta abinta tana duba handout dinta, sai kwafa take yadda Dadah ta ha
a mata husuma shigowa Jadwa tayi tana fa
in. "Mutum da mugun halin shi, kamar siffar shi." "Thank God ba ni nayi kaina ba, balle a goranta min. Wallahi Addah Jadwa ba tsoronko nake ji ba, idan kika kuma gaya min magana sai na miki shegen duka." Dama haka Jadwah take bata da karfi sai bakin tsiya, sannan yadda take kishi da Hajnah kamar zata yanka ta ta boye wukar tsabar kishi. Nanah najin su ganin Nanah tana dakin yasa ta ce. "Kambu idan ban ballaki ba, ke ni sa'arki ce?" "Jadwah bana son fitina ki kyale ta, idan kika bari ciwon ta ya tashi keda Abeey bana son fadar rashin gaskiya.". "kema tsoronta kike ji? Tow wallahi ba zan tab'a jin tsoron kanwar baya na ba. Domin kin ga ana fifitaki ai ba fin mu kika yi ba, da baki kamar zunubi" kallonta Hajnah tayi sannan ta ce mata. "Ih na yarda duk abinda kika so ki ce, hassadar ki ya kashe ki, duk da ni baka ce kamar zunubi Alhamdulillahi bana yiwa kowa bakin ciki, keda hassadar ki ta kasa boyewa a zuciyarki ko zaki mutu haka zaki ganni ki bar ni domin babu yadda kika iya da ni. Wacce bata rike girmanta ba." Kamar da gaske tayi kan Hajnah, zata dake ta, ita kuwa ta shake ta, tana jan numfashi, saboda
acin ran da ta shiga. "Addah Nanah kinga zata suma." Numfashinta ya shiga hawa da sauka. "Mamu!!" Nanah ta kira sunanta da
arfi, tana banbare Jadwah a hannun Hajnah...
_Yau dai Dadah da Kawarta sun yi fa
kuma ba mamaki shiga tsakanin su Kalwa Tayi_
#Tambarinshahara
#Mafialovestory
#Minitansharholiya
#Mai_Dambu
[2/26, 7:24 PM] MINISTAN SHARHOLIYA: TAMBARIN SHAHARA... (FREE BOOK)
Mafia Romance story.