← Book details Tambarin Shahara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 16 OF 22

Chapter 016

Tambarin Shahara Part 1 Complete Hausa Novel · about 12 min read

"Allah ya shirya mana ke, amma kiyi a hankali ba kowa ake ja a kasa ba Baby" Murmushi tayi tana jefa grape bakinta, "ki gane Addah Nanah abin a jini na yake, ba kowa yake iya tsayawa ya nemi yayi min kaud'i ba." Dariya Nanah tayi domin ita kan halin Hajnah na masifar burgeta tsokanarta a cikin gida ne, amma a waje shegen kamun kai ne da ita, domin bata magana kuma bata shiga abin da babu ruwanta. "Bari naje dakin Mamu" "ok" a da can tasan tare zasu tafi, amma a yanzu sai ta ga sam ba haka ba ne, ita dai Nanah bata ce kome ba, ta fita koda ta shiga dakin Mamu, ta same ta tana gyara wardrobe dinta ne. "Mamu ina Jadwah da ta bar ki da aiki?" Murmushi tayi tana fa
in. "Tana wurin Kulsum. Dama Hajnah ce me taya ni, tun abin da ya faru a bikin ku ta yanke kafarta da shigowa dakina, tsakanina da ita gaisuwa." Kura mata idanu tayi kafin ta amshi kayan ya cigaba da shiryawa, "ban ga laifin ta ba wallahi domin duk dan halak yasan darajar kan shi, ke da Jadwah da yan uwanki, kuka sakata a gaba domin fitina da tashin hankali, Mamu ko nice wallahi tunda bake kika haife ni ba, ba zan kuma saka kaina cikin al'amarin ki ba, kin gane kuma kin san Hajnah tana da zuciya ko baka wulakantata ba, tana iya kokarin ta kame kanta, Mamu nasan dalilin da yasa kike gudun Hajnah, ki gane babu wanda ya wuce kaddarar shi, Halimah ita din Yar da Abeey yake masifar kauna ce, da ace akwai wani abu bayan kaunar, da kin hango haka a cikin kwayar idanun shi, tunda ita din yanzu tana matsayin mace cikakkiyar budurwa da take da ikon sarrafa kanta da kimarta, she's Abeey beloved daughter, ba a shedan maza amma ni na sheda mahaifina baya cikin masu ha'inci da son zuciya, mutumin kirki ne da baya hango kome sai adalci, shi kansa ba zai tab'a amfani da haka wurin yin gaban kansa, koda babu alakar riko tow a wannan age na Abeey bana tunanin zai ga wata mace da gashi kamar yadda ya auro ki har ya aure ta domin da zai yi haka tun ganiyar kuruciyar shi zai yi, soyayyar da yake gwadawa Hajnah kiyi nazari soyayyar Uwarta ce, tunda ke da Kanki kika ce, ita ce macen da yaso iyakar rayuwar shi. Kafin wannan abin ya faru, ki kula Mamu yanzu mu zamu fara rayuwa, ke kika ce min namiji ba a bude mishi idanu da wani hauka da sunan kishi. Karki koya mishi soyayyar ta domin shi jagoranci zuciyar shi da cutar daku baki daya, tana da nata rayuwar shima yana da nashi, idan har kika sake wani abu ya faru, zai iya koraki ya ri
e Yar rikon shi, at this point kin zalinci rayuwarta domin ko ni bana fatan kasancewa da sa'an shi, don Allah ki dakatar da Jadwah da yan uwan ki, ina tunatar da ke ne a matsayin Yarki abokiyar shawaran ki, kar ki saka mishi abin da bai da niyyar haka." Suna wannan maganar Abeey yana tsaye a bakin kofar shiga dakin ta, jikin shi a mace ya juya zuwa dakin sa. Shekaru goma sha takwas baya.
Ya fito daga masallaci, bayan sallah isha. Dauke yake da lema,.yana sauri domin ana ruwan sama kasancewar lokacin ruwa ne sosai dan ana watan Agusta ne, a bakin kofar gidan sa ya hangota tsaye, duk da ruwan da ake bai hanata tsayawa a cikin ruwan ba. Duk da akwai haske ga kuma walkiya, haka yasa shi kara haska torchlight din shi, fuskar a kumbure. Idanunta daya ya rufe sakamakon jin ciwon da tayi. "Aminatu kece a wannan daren ina Nasir?" Hawaye ya zubo mata ta mika mishi jaririyar da take dauke da shi. "Gashi nan, ya zabi hanyar da ba zata bulle mishi ba, ya ciyar da mu da haram ya shayar da damu da haram, ina tsoron kar hakkin jini ya bibiyeta. Ban san yadda zan maka bayani ba, amma qaddara ta riga fata Yamma kayi hakuri gata sunan Dadahna na saka, kace ta yafe min" "tow wai duk meye haka?" "Ba zaka gane ba, ga wannan littafin naga ana ruwa ne, ka ajiye mata, don Allah kar ka ga wani abu bayan haka kace zaka shiga, ka janye tunaninta daga duniyar da muke ciki, wasu mafarkan suna cika, amma wancan azzalumin yayi nasara raba ni da abin da nake so, don Allah ka nisanta ta kamar yadda Allah ya nisanta fir'aunan da rahamar shi, ka barratatta kamar yadda ya barrata hamana daga jin kanshi, bata kome ban da abin da take so, na roke abu daya ya rage min shi ne wannan takardun ba mamaki wata rana zata bukaci sanin wacece ita." "Aminatu!" "Shiiiiii, ka kaiwa Dadah ita don Allah kar ka tambaye ni ina Nasir, yayi abin da yake so na biyewa son zuciyar shi da kwadayin duniya, Allah ya nuna mishi ikon shi. Zan tafi" ta mika mishi wata karamar jaka, "wannan da gumina ba tara su saboda ita, domin bana son ta tashi a gorance please ka kula min da little Dadah, ka sa mata soyayyar dadah da naka, kamar yadda ban yi maraici ba, don Allah kar ka barta tayi maraici itama. Ka nema min yafiyar Dadah" daga haka ta wuce wurin motar da tazo da shi, tana kuka har ta fita a estate din. Lokacin da ya shiga cikin gidan, ya samu sabon tashin hankali Mamu itama haihuwa tazo mata, ajiye Babyn yayi a wurin Dadah ya ce mata yana zuwa. Koda suka tafi asibiti Mamu sai da ta kwashe awa biyar kafin ta haifi danta namiji sai dai sau daya yaron yayi kuka, ya koma haka ya sakata a cikin damuwa duk da a lokacin manyan Yaranta sun girma, Washi gari da yamma aka sallame su..
Ajiyar zuciya ya sauke sakamakon sallamar Hajnah, kura mata idanu yayi bakin shi yayi nauyi, waving din shi tayi tana fa
in. "Abeey meye ke damun ka?" Dan karamin tsaki yayi, ta shigo ta zauna a kan stool din dakin shi. Abin har mamaki ya
e bashi idan tana wani abu a fisge kamar ta da Mahaifiyarta yana fitowa, idan ya cire hasken fatar da ta rasa na Uwarta. "Abeey batun komawa Hostel din fa?" "Ba zaki koma hostel ba" "haba Abeey don Allah?" Wayar shi ce tayi kara, ya dauka. "Dr Jamil ya kwana biyu?" "Alhamdulillahi, Imam na kasa gane kan Najlah ina son turota wurin Hajnah su cigaba da karatun tare, Dr Kabir ya ce Kamnah zata dawo itama. Imam bayan tafiyarka abubuwan babu dad'i, shi yasa zamu turo su nan su ci-gaba da karatu yaran mu yan mata basu da tsaro, V.C ya bawa Mafia damar suyi yadda suke so, don Allah ka taimaka mu turo su." Sosa goshinsa yayi yana fa
in. "Abin da nake gudu kenan, tow ba damuwa ka turo su zan samu malaman department din su ayi magana, su zo akan lokaci " inji Abeey, "mun gode sosai Imam ka yafe mana da rashin girmama maganar ka" "ba kome " ya fada yana kaf
eta da idanu. "Tow Abeey me kace?" Hararan ta yayi yana fa
in. "Najlah zasu zo, sai ku nutsu bana son shiririta " "in sha Allah " fita tayi tana murna, abin da ya ki kenan, amma baki daya Malaman suka ki fahimtar asalima asibitin AJ shi ne babban matsalar Nuwanda amma an tula musu kudi an basu kome, ga rayuwar Yaran mutane tana cikin matsala. Tun ba yau ba ya samu labarin haka ta hannu babban dalibin shi Abu Jafar, bai yi mamaki ba, sai dai har ga Allah ya tsani AJ har cikin ran shi a kasa da wata hudu sun lalata Nuwanda babu me ikon magana.
Mafia City.
Dragon castle town
Tunda Duah ta nime kashe kanta, yasa aka rufe ta a daki domin yadda ya tsani alakarta da AJ kamar yadda ya tsani mutuwar shi. Shiga dakin yayi ya zauna a bakin gadon. Tunda abin ya faru yasa ake danna mata alluran barci. Bude idanu tayi ta zuba mishi. "Ina son AJ" "Duah idan har AJ ne sai dai ki mutu, soyayyar ku ba zata amfane ni da kome ba, sai ma tashin hankali. Ni gawar shi nake son gani, don haka ki cire AJ a ranki, zan zab'a miki wanda ya dace dake" "A'a Papa shi nake so" "kina hauka ne? AJ ya san waye ni, ba zai duba al'amarin da yake tsakanin ku ba, bindiga zai saka a goshina ya zazzaga min albarushi, idan baki sani ba AJ yasan waye ni, tabbas mutuwata ba zata yi kokarin daukata a gaban shi ba, sai bayan idanun shi domin ba zai bari na mutu ta sauki ba ba tare da ya wulakantani. Duk inda aka kafa wata gidauniya tow harkan Arziki ake tunanin ya habb'aka ba sharri ba. Nasara a jinin su take, daukaka da shahara jinin gidan su ce, shi yasa ake kiransu da Nasara ki manta da AJ zan nima miki wani wanda ya fi shi a kome" yana gama fadar haka ya juya ya fita yana tsaki domin baya kaunar tuna kome, abin da aka yi shi sama da shekaru saba'in ya dawo ai wallahi AJ binne shi zai yi da ran sa, har gara su Mr Gayu.
----
A bangaren shi sai da ya gama bibiyar kome, sannan ya saka aka mai dawa Najlah Account dinta. Inda yayi tracking number ta, domin yana son yasan inda Hajnah take, yaji dadin daukar fansar shi.
Kusan mako biyu kenan yana bibiyar motsin Najlah, babu wani labari. A gajiye ya fito daga shi sai singlet da gajeren wando. Idanun shi ne ya sauka akan JB da ya
e cin abincin. "Tuzuru" JB ya kira shi da sabon suna. "Dan iska nayi kewar ka shi ne nazo ganinka, nayi maka bazata" daukar goran ruwa yayi ya nufi kusa da JB ya zauna. "Karya kake ba shi ya kawo ka ba" ya fada yana daura bakin goran a bakin shi. "Yes dan iska kai likita ne fa, amma idanunka baya tab'a kawo maka ciwon mutum sai wani abu na daban." Shiru suka yi, can JB ya ce mishi. "AJ meke faruwa a nuwanda?" "Kamar ya?" "Asibitin ka yana shirin zama na Mahaukata ne? AJ abin da yake faruwa yan matan makarantar basu tsira ba, domin ana lalata musu yara, matasan su an fara amfani da su wurin sayar musu da kwayoyi, AJ Imran memorial hospital yana shirin gurbatta wasu abubuwan da garin tayi imani da shi. Nazo na gaya maka ka takawa su Father birki domin wallahi Allah ba zai barka ba." Daga haka ya saka kai ya wuce dakin shi. Shima dakin shi ya koma ya dauki wayar shi. Sai da ya kunna tabar shi ya mata zuka daya kafin ya kashe daidai kiran shi ya shiga."waye ya bada umarnin sayar da kwayoyi a Nuwanda?" "A'a king bamu sani ba." "Awa biyu na baku gani nan zuwa" "tow king"
*
Mr Paul yana tattaunawa da wasu bakin shi, bai san lokacin da ya mike ba. Domin yau kusan sati biyu kenan yana son ganin AJ amma dan banza yaki yarda su ha
u. Da ya takura mishi da aika cewa yayi a gaya musu baya son ganin fuskar wani kare, wannan abin ya mishi ciwo haka suka zauna jiran tsammanin kira daga gare shi. Don haka a gaggauce ya shiga kiran yan kungiyar yana gaya musu ga AJ nan zuwa, kafin ka ce me sun hadu. Alhaji Barraq ne bai zo da wuri ba. Koda suka hadu Mr Paul ya zuba musu idanu. Kafin ya ce. "Waye yake wani kasuwanci a Nuwanda?" "Adil ne" Alhaji Barraq Bukar ya bashi amsa, "akan me? " Mr Paul ya tambaye shi, "Yana son..." "Amma me AJ ya ce mana?" "Kaga Paul mu na yaran AJ ba ne, da zai na juya mu son ran shi." "Dama ina zan haifi dabbobi irin ku, kuma zan gwadawa d'anka abin da ba zai manta da shi ba. " Ya fada yana zama a kujeran shi. Yana zama JB da wasu manyan guard din AJ suka shigo da Adil. Wani irin karfe AJ ya dauka, ya kalli Adil wanda ya ci dukaea hannu JB kafin. Suka kawo shi.
Duke kafar shi yayi sai da ya durkusa a gaban AJ, shi kuwa ya saka kafar shi ya daura a kafad'ar Adil, yana bubuga karfen a kasa. "nace kar a shiga garin nuwanda ni burin mahaifina zan cika ko?" "Ih King" "da Izinin waye wannan dan shegiyar ya shiga Nuwanda?" "Ayi hakuri a yafe mishi." "Ba zan yafe masa ba " zubewa Alhaji Barraq Bukar yayi ya fashe da kuka, "kayi hakuri don Allah, kar ka kashe min Yarona" "waye Allah?" Ya tambaye shi, dafa shi JB yayi yana fa
in."ka kyale shi tunda ya ha
a ka da Allah" "waye shi?" Girgiza kai yayi sannan ya ce. "ka kyale shi zaka san waye Allah" cikin fushi ya juya karfen ya make Adil da shi ya fadi sumamme. Sannan ya juya yana kallon su. "Ku wanke garin kafin nan da wata shida, shima Mayor idan muka yi ido biyu da shi sai ya gayawa yan garin su." Sannan ya fita tare da JB. _Jahili wanda bai san waye Allah ba_ dafe goshinsa yayi a bakinta ya fara jin sunan Allah. Yana jin ana fadin God ko lokacin da yake zuwa sallah juma'a a sati bai tab'a mai da hankalin shi akan kalmar Allahu Akbar sai yau ya fahimci hakan.
Kwantar mishi da kujeran motar JB yayi suka nufi gida.
Lagos
Kwana biyu kenan Mamu taga gano Hajnah so take ta nisanci gidan, domin a bakin Abeey ta samu labarin zuwan su Najlah amma bata kawo zasu koma hostel da zama ba ne, sai yanzu da taga tana ta ha
a kayanta. Shigowa dakin tayi ta same ta, tana saka kayan ta cikin suitcase babba. "Halimah wato baki dauke ni a uwa ba ko? Tunda su Nanah suka tafi baki son zaman gidan nan me nayi miki don Allah?" "Wallahi baki min kome ba, kawai nafi son karatu ne a can din, in sha Allah zan dawo gida idan weekend yayi." Daga haka bata kuma magana ba, baki daya Mamu ta rasa wani irin taurin kai ne da ita, gashi a idanun kamar me hakuri amma a zahirin gaskiya zurfin cikin ta yasa bata da hakurin wani ya mata wani abu, ta kyale shi kuma ko jiya da yamma tana jin Jadwah tana zaginta bata kula ta ba, har ce mata take me zubin karuwai, bata da aiki sai na karkad'a jiki, ita kuwa ta gayawa Jadwah maganar da yasa ta fusata. "Oh Ashe dai ina da sexy body, tow na gode sosai, ke kuma muciya da zani, sai ayi hakuri domin kiwon ka banza ne, duk namijin da ya kwasa domin zai kare yana bautawa kashi da rai jijiya da bala'i....
#Mai_Dambu
[2/26, 7:24 PM] MINISTAN SHARHOLIYA: TAMBARIN SHAHARA... (FREE BOOK)
Mafia Romance story.
*Mai_Dambu*
Chapter 16 · 0% Book details