← Book details Tambarin Shahara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 10 OF 22

Chapter 010

Tambarin Shahara Part 1 Complete Hausa Novel · about 15 min read

Mai_Dambu
Wanka yayi ya shiga wani daki, yana me kunna wutar dakin hoton Mahaifin shi, wanda ya ke tsakiyar wani black board, a hankali ya zuwa hoton Mahaifiyar shi idanu, yana kewar su sosai. Irin kewar da iya su ne zasu taimaka mishi idan yana cikin damuwa, mik'awa yayi ya fita daga dakin, ya koma dakin shi ya kwanta. Kasa barci yayi duk juyin da zai yi Hajnah ce a cikin kwakwalwar shi, baki daya yarinyar ta goge mishi
urar kan shi. Tashi yayi ya zauna yana tunanin yadda zai mata rashin mutunci. Har kusan asuba yana zaune, kafin can wani idea ta fado mishi. Kafin gari ya shirya kome yadda zai tafi mishi.
----
A bangaren JB ganin tunda aka samu wata guda, AJ bai yi wani yunkurin ba, yasa shi janye masu bibiyar al'amarin Hajnah. Yasa shi sallamar su, domin shima bai da wani lokacin kan shi.
***
Nuwanda
Yau kwana biyu kenan da dawowar ta, bata san meke faruwa ba, amma ta fahimci ana boye mata abu. Daga ita har aminiyar sirri, kallon Dadah tayi sannan ta ce mata. "Dadahna don Allah meke faruwa a gidan nan?" Murza radio kachbo Dadah tayi ta kalle ta shekeke. "Hala kin ajiye ni nayi ta tattaro miki duk wata gulmar da aka yi ne? " Ta fada rai a b'ace, dake itama Hanjinta tana niman rigima ne sai cewa tayi. "Ko daya yau zan koma dakin mu da kwana, domin yana da labarin cewa rundunar yan mafiya da fatalwar su zasu zo, mu kwana lafiya domin gara na mutu cikin yan uwana da na mutu kusa da tsohuwar da ba zata kare min mutuwa ba." Sake baki Dadah tayi cikin tsannanin mamaki wato har a shirya mugun abu a gidan nan a rufeta ba dan hanjina ta gaya mata ba, babu me gaya mata rundunar Mafiya da fatalwar su zasu zo. "Hanjina a ina kika samu labarin?" Tura baki tayi zata fita ta riko hannunta. "Zauna kawar arzikn a ina kika samu labarin nan?" Nan fa yan matancin ya motsa ta shiga jan wani class wa Dadah, tana wani fisga. Ita nan dole jan aji take, bude adaka Dadah tayi ta dauko wani labceccen sarkan zinarinta. "Hanjina ko bayan raina wannan abin wuyar mallakarki ce" sai duk Dadah ta bata tausayi, rufe yar akwatin gold din tayi, tana girgiza mata kai. "A'a Dadah, kar ki min haka, wallahi wasa nake miki. Ina sonki sosai ba zaki bar ni ba. Dama naga gidan kamar ana abu a kasa kasa ne shi yasa na tambaye ki, ko kin sani" idanunta ya cika da kwalla. Wani irin ja fuskar Dadah yayi kafin ta mike, tana fa
in. "Cin amanar mu suke tunda baki sani ba, nima kuma ban sani ba. Biri yayi kama da dan mutum." Fita Dadah tayi da akwatin gold din tana kallon su Nurain da Abubakar da suke falon. "Ungo nako! Ina Imamu da shafa'atu?" Fitowa Mamuh tayi tana kallon ta, "ina Imamu nace?" "Yana wurin karatu yau ai karshen mako" shiru tayi tasan idan ta tambaya ba zasu bata amsa ba, kawai sai tayi decided mikawa Hajnah box din gold din tayi tana fa
in. "Ko bayan raina naki ne" babu wanda yayi gigin magana, domin tsoron abin da zai faru. "Dadah ai ba ita
aya ba ce jikar ki muma ai jikokin ki ne" inji Jadwah "Ih na san da haka, ta saka idan Allah ya nufa bikinta da Yazidulle" "Tab ai kuwa yadda idanun shi ya makance da soyayyar balarabiyar saudiya yaushe zai kalli wata me baki da bakin jini, ki tambayi Abeey sati me zuwa za su tafi nima mishi auren Kulsum " dama inda Dadah take bu
atar ji kenan, kuma ta zunguro haka. "Kai haba shi ne Sayyadah Karimah bata gaya min ba? Wato har ni, zan hada su lalata min? Ina nan ina tausar yarinya suna can suna hangen wasu. Allah ya basu hakuri, ke kuma Hanjina in sha Allah zai zo nan da kan shi kamar tukunyar bammi." Da gaske abin ya daki zuciyar Hajnah, amma idan baka san halinta ba, ba zaka dauka taji haushin labarin ba, tsaki ta ja, tana fa
in. "Yo ai Dadah kece kika dami kanki da Yazidulle, tow gashi ya watsa miki kasa, dama ni tuntuni baya son shi. Kece kika nace kamar talauci, gara haka kowa ma ya gani, nice da riba ga dhama, bana son shi ga zukekken sarka " ta juya abinta zuwa dakin Dadah, tana shiga ta wuce ban daki, ta fashe da kuka. Irin kuka me cin rai din nan, domin kuwa abin da ciwo. Yadda take kuka zaka dauka hundred percent son shi take, sai da tayi kuka ya ishe ta, ta koma daki ta kwanta ko abincin dare bata ci ba, ai kuwa sun sha tijaran Dadah duk da Abeey ya mata bayanin cewa ai zai auri Hajnah daga baya tunda akwai maganar su a kasa, kuma za a hada bikin ne baki
aya. Ita kuma Hajnah tunda tana karatu daga baya za ayi. Gefe guda gani suke ai Hajnah bata wani girma har can da za ayi wani rigima akanta bane, shi yasa abi ya kwantar da hankalin Dadah domin tace ko a kafa sai ta tafi gombe.
Washi gari da hantsi Hajnah da su Hamma Umar da Usaimin da Asad, suka nufi Super market, jikinta a mace ga wani kasala da take ji, domin ta tashi da period sai abin ya zame mata biyu, haka suka tafi a cikin motar ya Umar, tana gaba Usaimin da Asad suna baya, hira suke sosai. Domin akwai fahimta sosai tsakaninsu. Har suka isa,
ashin Mall din akwai parking lot, sai ku shiga wurin zaku ajiye motar ku, sannan ku wuce wata karamar corridon da zai kai ku wurin elevator, haka suka wuce tana fa
in. "Hamma idan muka dawo bikin ku, ni daya ne zan rage sai su Usaimin." "Ih hanjin Dadah, daga ke Sai Dadah kuci drama dinku babu me sani. Amma zamu yi missing Dramatic dinku" dariya tayi tana fa
in. "Ai idan ina son Dadah ta nutsu, shi ne na ambaci fatalwa tuni zaka ji labarin wasiyya ya tashi" dariya suke har cikin mall
in. Suna shiga cikin suka fara abin da y kawo su shafa aljuhun shi yayi yaji babu card din shi. "Kinga ga key mota dauko min katina yana cikin motar a wajen Aljuhun driba,kiyi sauri." "Tow" ta fada, tare da fita da gudu suka cigaba da sayayyar su. Koda ta fito wurin motar ta nufa babu kowa. Tsigar jikinta ne ya mike alamar ta razana da shirun wurin bakinta dauke da addu'a ta nufi motar Umar, ta bude motar zata dauki key aka ce mata "excuse me ?" Juyawa tayi ta zuba mishi idanu, ba iya shi daya ba, har da wasu kartin maza ne, sake katin tayi a hankali jikinta yana daukar wani azzaben rawa, ta juya zata gudu, sai ji tayi an shaka mata abu a fuskarta. Lakwas jikinta yayi, suka dauke ta tare da kaita wata jaguars din da suka tawo da shi, suka sakata. Daidai isowar Hamma Umar wurin. Bai kawo ita suka dauka ba, sai da suka bar wurin da gudu ba dan ya kauce ba, sai sun take mishi kafa, hango motar shi yayi a bude ga katin, a inda motar ta tsaya yaga warin takalminta, "Kai!!!" Ya fada da
arfi tare da bin bayan motar da gudu, amma ina sun yi nisa, wayar shi ya ciro tare da kiran Abubakar da Nurain, ya gaya musu, akan lokaci suka iso tare da niman Abeey. Lokacin yana tare da Majalisar malaman addinin Musulunci na Nuwanda suna tattaunawa akan abin da ya shafi taron wa'azi da za ayi na kasa. Suka kira shi bai dauka ba, tura mishi sako Abubakar yayi. "Ku gafarce ni, akwai abin da ya taso daga cikin gidana, zan tafi". "tow ba damuwa" suka mishi uzuri. Ya fita, kiran su yayi ya ce musu. "Kar ku sake ku saka jami'an tsaro a maganar, babu damuwa gani nan zuwa" akan lokaci ya isa mall
in, aka tafi har dakin da Cctv yake sai da Hamma Umar ya nuna takardan aikin shi. Abin mamaki babu rahoton daukar wannan lokacin, haka suka gama wahalar su, suka fito. Hankalin su a tashe.
"Ko lambar motar baka rike ba?" Shiru yayi yana kurawa wurin idanu, kafin ya juya da sauri ya kira wani abokin shi ya tura mishi bayanin motar amma bai rike number ba.
Can kuwa abokin ya turo mishi da sakon. "Motar ta Mayor ce, kuma tana under Tambarin shahara ne." Juyawa yayi ya kalli Abeey bakin shi na rawa ya ce. "Meye hadin Hajnah da tambarin shahara?" Rintsa idanu yayi yana dafe kirjin shi. "Muje gida" ya iya furtawa, "ku bar maganar a tsakanin mu, ita kuma a gayawa Shafa'atu tana gidan Dr Jamil" haka suka isa gida zuciyar su babu dad'i.
-----
Lokacin da suka dauke ta, sai da suka tabbatar da an goge daukar Camera din parking lot din, sannan suka wuce da ita airport, saka ta suka yi a cikin suitcase babba, suka rufe aka wuce da ita cikin jirgin da zai wuce mafia City. Koda jirgin y isa dama iya ita aka zo dauka. Domin jet din AJ ne, kai tsaye suna isowa aka wuce da ita Dasuka town.
Yana can wurin Karanukan shi suka wuce da ita a cikin akwatin har dakin shi, sannan suka bude akwatin suka cirota tare da ajiye saman kujera, sai da suka daure hannunta da kafarta suka fita daga dakin, kafin James ya nufi wurin da yake ya gaya mishi, sun iso. Hannu ya d'aga musu sannan ya cigaba da abin da yake. Sai da ya gaji sannan ya nufi cikin gidan yayi wanka, ya shirya cikin wasu fararren kayan, rigar kirjinta a bude. Daukar kofin da ya cika da ruwan sanyi yayi ya watsa mata a fuskar ta, wani irin ajiyar zuciya ta sauke, kanta yana wani irin juyawa. "
Innalillahi wa inna alaihil raji'un allahumma ajirni fii musibati wa'akhlifni khairan minha." Kura mata idanu yayi yana jin wasu irin surutai. Tab'e baki yayi ya cigaba da abin da yake. D'ago kai tayi tana kallon inda take. Kafin Idanunta ya sauka a bayan shi, a ina tasan wannan ma? Kamar yasan tunanin haka take ya juya yana kallonta atishawa tayi, da karfi sannan ta kuma yi tana tasbihi. Kallon cikin idanun shi tayi, takaici yasa ta jan tsaki, ta fara kokarin kunce hannunta da yake baya. Mamaki abin ya bashi domin ya zata shi ne uban marasa mutunci, sai ya lura akwai wacce rashin mutuncin a jininta yake. Kamar shi zata jawa tsaki? Takowa yayi ya nufi inda take ya ja hijab dinta baya, "uban waye ya tsaya miki?" Kura mishi Idanu tayi sannan ta tattaro yawun bakinta ta watsa mishi akan kyakyawar fuskar shi, bai san lokacin da ya kifa mata mari ba, yana dukar iska domin baya jin ya isa ko ya cika namiji da zai mare ta. Faduwa tayi daga kujeran kashin hannunta yayi
ara, ajiyar zuciya ta sauke dan azaba, dawo da ita yayi. Tare da shake ta. "Sake min wuya ragon maza, mazan kwarai a titi da wurin niman abinci suke faffatawa domin niman abincin da zasu ri
e iyalin su, kai kuwa ka zauna kana niman hanyar cin zarafin mutane, jahili irin ka haushin maka magana nake." Dai dai lokacin da ta kunce daurin hannunta, ta tallafo hannun da take da yakinin ya samu matsala. Ta ajiye shi a kan cinyar ta, sannan ta lallube wayar ta da yake cikin wandon ta, domin riga da wando ta saka. Miss call ta gani yana tsaye ta kira Abeey. "Halimah" wani irin kuka ne yazo mata, amma hakuri da juriya da son nunawa AJ bai isa ya mata kome ba ta ce. "Abeey kar ku saka hukuma domin yan jarida zasu iya samun wani abu, kayi kamar babu abin da ya faru shi kuma wanda ya dauke ni zai dawo da ni gida. Ka cewa Dadah gani nan.." kwace wayar yayi ya ce. "Sheikh idan na gama yadda naso zan dawo maka da gawarta. " Sannan ya cilla mata wayar kan cinyar ta. "Abeey kar ka damu, ka yarda Allah yana tare da mu" ta kashe wayar ta ce mishi. "Kai Alade zo nan, danta mace mara daraja, anya kuwa aure ya samar da kai?" Sake kwalbar wine din yayi da
asa, ya tawo a fusace, ya shaketa tare da yaga hijab dinta. Hannunta me lafiyar ta kai ta shiga dukar shi, tare da kai mishi cizo ta ki ina. Kuma tana ihu, sake ta yayi dan bai iyawa da jaraba. Ya shiga kunce kafarta _Anys aure ya samar da kai?_ wannan kalmar tayi mishi zafi, daukar ta yayi ya watsata saman gado, "A'a ba aure ya samar da ni ba, idan kika ji yadda nake zaki gane" ya fada yana hakin takaici. "Ba zaka iya kome ba, ragon maza ba zaka iya min kome ba, kai ko hawa kaina ba zaka iya ba, domin mu tsarkakkakun yara ne da aka samar da mu ta kyakyawar makoma, kai idan har Omar Hassan Sheikh bai kebe da yar kowa ba, Abubakar Omar Hassan Sheikh bai yi tunanin taba kanwar wani ba, Umar Omar Hassan Sheikh bai tab'a yayar wani ba, banza irin ka zai tab'a ni ne? Kai jahili ne, mahaukaci, wawa mara hankali. Ka mai dani inda ka
auko ni" wani irin yanayi yaji ya rufe shi me kama da zazza
in. Sauka yayi daga gadon, ya shiga jan wuyar hijab dinta, ya fito da ita ta kitchen ya kai ta wurin Karanukan shi ya bude su. Tabbas ya nuna mata shi mahaukaci ne a cikin Mahaukata, domin wani irin fincikar kayan jikinta da fatarta suke tana kuka da kiran sunan Allah. Ko tausayin ta bai ji ba, Allah da ikon shi sai ga JB, ganin yadda suke yaga kayan jikin mace bai kawo Hajnah ba ce, sai da ya daka musu tsawa, suka koma suna gurnani, ko yatsar hannunta ba iya motsawa domin sun ji mata ciwo sosai. Zuwa yayi ya d'agota."Hajnah Imam" ya juya a fusace, yana kallon yadda AJ yake shafa wuyar Karanukan shi. "AJ me ta maka?" "Kanwar Ubanka ce?" "Ya ishe ka haka, banza jahili" ya fara kokarin daukar ta. "Dan Ubanka tunda ba kai ka kawo ta ba, ajiye min ita" ya fada cikin isa da iko. "Idan naki fa" "zan kashe ta" ya furta bayan ya Ciro bindigar ya daura a kanta, yasan tunda ya fadi haka zai aikata. Ajiye ta yayi, cikin fushi ya buge hannun AJ, abin da basu tab'a ba, wato dambe sosai suka shiga bawa hammata isa, sai da Mss Yunah ta iso, ta raba su. Ganin Hajnah a kwance ta umarci JB ya dauke ta. "Na rantse ya tab'a ta sai na kashe ta" "Tow sai ka
auke ta" "ba zan dauke ta ba" ya fada yana wuce su, dole ta nimo masu tayata aikin gidan suka shiga da ita, JB ya kira family doctor din su, yazo ya mata duk wani abin da take bukata na kulawa, sannan ya tafi.
----
A can gida kuwa hankalin su ya tashi musamman Dadah, domin jikinta ya bata Hanjinta ba lafiya, haka suka wuni har dare. Abeey yake basu labarin sunyi waya,. A garin surutu Usaimin ya gayawa Mamu. Aikuwa daren babu wanda ya rintsa, Abeey ya musu bayani, amma basu fahimta ba, Dadah har da sumanta."idan aka bar maganar nan ta fita, mutuncin ta ne zai zube a bar maganar a cikin gidan zata dawo in sha Allah" amma ina tuni Jadwah ta watsa labarin a grp din su na family tsabar cutar da kai cewa tayi tabi saurayi yawo. Ita
aya ta fita zakka. Wannan abun yayiwa Nana ciwo, shi yasa da ta rufeta da duka kamar zata kashe ta. Sai da aka kwace ta. "karya nayi? Saurayi ta bi, ku fito ku gaya mana Hajnah ba jinin ku ba ne kuke boye mana, domin rufa mata asiri mu zata tona mana, kuma ku ajiye sai ta kawo muku shege har cikin gidan nan." "Allah ya mai da miki kaidinki kanki" Mamu ta fada tana rufe ta da duka, cikin takaici Nurain ya ce. "Na zata kina da hankali, ashe baki da shi Kawu kayi hakuri ba zan iya auren Jadwah ba Wallahi matar rufin asiri nake nima ba wacce zata zauna tana cutar da wasu dan kanta ba"
Wannan tashin hankalin yasa Dadah faduwa ragas. Dole suka nufi asibiti da ita. Ita kuma Jadwah aka barta a can gidan ba kowa a dakin.

***
Wurin asuba ta farka jikinta ko ina yana ciwo, da taimakon Mss Yunah tayi wanka, ta sauya pad, ta bata wani doguwar riga ta saka, ta fita ta kawo mata ruwan zafi tea me kauri, ta bata da magani ta sha, "Madam ina wayata?" Tashi tayi ta kawo mata, amsa tayi ta shiga kunawa fuskar wayar ta lalace. "Madam zan iya samun wayar ki" "Ba zata bada ba" "idan ta bayar ka amshe kazami dabba" da yasan meye yasa ta mishi wannan zagin ba zai sake ya nufota ba, cikin fushi ya nufota ai kuwa ya watsa mishi ruwan zafin tea din a kirjin shi, ware idanu yayi a kanta."idan ka yi yunkurin tab'a ni, zan nakasaka." Ta fada cikin rashin mutunci, kaf rayuwar shi bai tab'a ganin mace mara kunya irin ta ba. Me zai mata ya wuce. Yaga rigar yayi fatar tayi jajjur. "3-1" ta furta, tana murmushi. Ganin yadda jikin Mss Yunah yake rawa, yasa ta cigaba da cewa. "Manta da sakarai bani wayarki" fuuuu ya fita, ita kuwa Mss Yunah ta ta bata wayar, ta cire layinta, wurin karfe shida ta kira Abeey. "Abeey! Yasu Mamu da Dadah?" "Suna lafiya, wani hali kike ciki" "Alhamdulillahi sai na zo kawai, amma kawai sai nazo in sha Allah zanyi dhur a gida da yardan Allah" "Allah ya kare min ke" "Amin Ya Allah" kashe wayar tayi ta cire layin, wurin karfe takwas Jb ya zo gidan. Inda suka fara sa'in'sa. Fitowa tayi tana kallon JB. Mika mata hijab yayi ya ce mata. "Muje na kai ki gida" juyawa tayi ta kalli AJ, "in sha Allah sai barci ya gaggare ka. Sai kayi kukan da ka samu" sannan suka fita. Tunda suka shiga motar JB yake bata hakuri. "Kar ki ga laifin shi, bai san kwab'a ba, haka ya tashi da tsananin son kai da girman kai, na jinjina miki tun haduwar farko, kiyi hakuri" "Ba kome" ta fada tana share kwalla, "Shine shugaban tambarin shahara. " Da wani irin tsoro ta kalle shi bakinta yana rawa ta ce" Shugaban Mafia na ilahirin City din nan" "Yes Ajwaad Imran Nasara" ya bata amsa, dole ya haukace, wayyo Allah, wallahi ta zata ko shima wani kusa ne a mafia ashe shi din ne valcano, tasan wallahi ba zai rabu da ita ba, sai ma sabon shiri da zai yi...
Shegyada a faranti kin zata hi din, banza ne a banza tow ki ji da kyau muna sabon shiri akan ki da shugaban munafukai ko ba kome kin daku kare masu yi yadda suke so
Mtsew.
#Mai_Dambu
[2/26, 7:24 PM] MINISTAN SHARHOLIYA: TAMBARIN SHAHARA... (FREE BOOK)
Mafia Romance story.
Chapter 10 · 0% Book details