Chapter 011
Tambarin Shahara Part 1 Complete Hausa Novel · about 18 min read
Mai_Dambu
*Wannan pagen na kune*
Sister Sa'adatu Ambassador
Sister Bilqisu
Yar London
Aunty Binta Niger
Ummu baanat
Sister Amina Aliyu
Maryam Bin Muhammad
My Fatima Tambry
Oum Sultan
Mum Anam
Aunty Jamcy
_Duk cikin wadannan mutanen mutum daya muke party daya da ita Sister Maryam Bin Muhammad, ita ce bata yarda da wulakancin da akewa AJ ba, ni Ministan Sharholiya nayi alwadai da masu farin cikin abin da Hanjin Dadah take wa AJ ba da saka hannun mu wannan ta'asar ke faruwa ba, kuma duk wanda yaga zai iya goyan bayan ta, ya je da halin shi. Allah sarki My King AJ poor guy like you wata yar mitsitsiyar yarinya tana juya ka....Bunch of Love
"Yanzu kafin mu isa Nuwanda zai kai awa nawa?" Juyawa yayi ya kalleta kafin ya sake murmushi ya ce mata. "Nan da awa daya zaki isa gida" saka hannu yayi a aljuhun motar shi ya ciro kwalin waya, iphone XR ya ajiye mata a gefenta. "Me zan yi da shi?" "Wayarki da ta fashe" "No need. Ai idan aka gani a hannu na ba zasu tab'a yarda sace ni wancan bunsurun yayi ba, kawai ka rike abin ka za a gyara min ba hannuna" wani irin burge shi tayi, wow ya fada yana dukar kan motar, "Baby girl, kika ce ba zaki amsa ba" dan murmushi tayi sannan ta ce mishi. "Idan na amsa some people zasu yi tunanin i sold my pride" sake baki yayi, yana kallon ta har, "like how?" "Ih mana, wasu zasu yi tunanin wani abu na bada aka bani waya irin shi. Don Allah ka bar shi na yafe." "Kina gudun rumors din mutane ne?" Gyada kai tayi tana fa
in. "Da kuma mutuncin gidan mu" haka suka isa airport, da kan shi ya rakata har zuwa Nuwanda, suna isa motar Mayor tana zuwa daukar su, "A cikin su zaki gane wanda ya dauke ki?" Kallon su yayi kafin Idanunta ya sauka akan mutumin karshe ta ce mishi. "Wancan ne" basu rabuwa da makamai a mota ko a jikin su. Ita kanta bata kawo wani abu zai yi ba, sai dai yana zuwa inda yake, ya yanke suka mishi wuka a gefen cikin shi. "Wannan ya zama warning ko waye ya tura ku, daukar ta ku nuna mishi na hana" "Ok sir " "ku wuce da shi asibiti " a tsorace ta kalle shi. "Kar ki damu warning nayi mishi, ba iya ke ba kowa ba daga yau zasu kare ki. Baza su kuma miki kome ba." Gyada kai tayi tana bin bayan shi suka shiga motar, har gida JB ya kaita, lokacin duk Yayunta maza suna waje zasu tafi asibiti su duba Dadah, aka yi horn. Bude kofar aka yi hancin RR ya tura cikin gidan wato Rolls Royce wraith ya shiga cikin gidan. "Na gode" ta fada tana kallon shi. "Ba zan manta alkhairin ka ba, na gode sosai." Fitowa tayi shima ya fito, yana kallon yadda yayunta suka mishi caaa da idanun, sun zata shine AJ. "Hajnah!" Hawaye ne ya zubo mata. "Yes Hamma" ta karasa wurin su, ganin yadda fuskarta ya kwarjane yasa su kallon shi. "Shi ne?" "A'a" aka basu amsa daga baya. "Mr Jabir" Abeey ya kira sunan shi. Mikawa Abeey hannu yayi suka gaisa, sannan ya ce mishi. "Ayi hakuri na dawo da ita, haka ba zai kuma faruwa ba" murmushi Abeey yayi sannan ya ce mishi. "Mun barwa Allah" ya fada yana yana kallon Hajnah. Cikin gidan suka shiga har da JB suka karrama shi, sannan a lokacin ya kara basu hakuri, da ya mike zai fita ne Hajnah ta ce mishi. "Na gode sosai, Allah ya bika maka bukatar ka na alkhairi, ba dan kai ba da jiya ba mamaki bana raye" "ba kome Big girl" haka suka rako shi, har ya shiga motar ya fito da ledar maganinta da kwalin wayar ya mikawa Hamma Nurain, sannan suka fita. Sai bayan fitar shi ne ta koma falo ta cire hijab dinta, "Innalillahi wa'inna illahi raju'un, me ya same ki" cikin juriya ta fara basu labarin abin da ya faru, ko kafin ta kawo karshe kuka take sosai, "Abeey karanuka ya turo min har cikina sun ji min ciwo, Abeey Allah ya isa mana" yadda take kuka ba zaka dauka ba zata yi ba a gaban AJ. "Allahummah Amin, tashi muje asibiti" haka ta.mike suka tafi asibitin a dakin Dadah aka kwantar da ita, aka shiga bata treatment sosai, hannun kuwa sun ga bai da matsala, don haka suka daura kula da ita, "sannu Hanjina, hmmm kice kin ga mala'ikan mutuwa da idanunki? Kai yaron nan anyi dan banza ya rasa wanda zai buwaya sai ke, dan banza mara mutunci da zan gan shi sai na mishi dukan Kawo wuka" murmushi tayi kawai ita ta san abin da take ji, domin bata jin ko mutuwa tayi zata yafe mishi, sai ta saka shi yaji ciwon da take ji.
JB bai bar Nuwanda ba, sai da ya tafi har gidan Mayor, suka yi uwar watse da shi kafin ya gargade shi akan Sheikh, kafin ya bar Nuwanda. Koda ya isa Mafia City bai koma gidan shi ba, gidan AJ ya wuce ya same shi. Yana can swimming pool, yana kwance cikin ruwa. Sai da ya bata kusan awa guda kafin AJ ya fito sanye da yar boxes, ya dauki bathtube ya saka yana me
aukar por larranga Galanes ya kunna yama zuka a hankali. "Baka kyauta ba, yarinyar nan tayi karama da
aukar tashin hankali, please take it easy mana." Idan kayan wurin sun tanka AJ ya tanka haka JB ya karaci surutun shi ya gama ya bar wurin tari bai hada su ba, dama tun kafin ya iso, Mayor ya kira shi ya gaya masa abin da ya faru, shi yasa ya kuma jin kaf duniya bai da makiyi irin Jb domin yana cin amanar shi a bayan fage. Abraham kuwa baya ma kasar ya koma laa vages yana musu aiki. Sai da ya gama shirmen shi ya nufi cikin gidan shi, Duah ya samu a falon tana kallon kofar da zai shigo, ya hangota tsaf ya dauke kai abin shi, "Hey King " banza yayi da ita har ya haura sama, duk iskancinta bata son ta bata rawanta da tsalle. Dakin shi ya shiga tare da rufe kofar. Yana kallon kujeran da aka zaunar da ita. Tsaki yayi ya wuce closet din shi ya saka kaya, kafin ya dawo inda kujeran yake, cikin fusata ya kaiwa kujeran naushi da kafa, (Allah ya so babu Hajnah
) ya wuce abin shi yana huci tare da harara kamar Hajnah ce zaune a wurin.
Barci ne yayi gaba da shi, ai kuwa kamar jira ake ya fara barci, sai ga Hajnah tana mishi wannan kallon renin, cikin fushi ya shiga kai mata naushi tana kaucewa. Abin haushi yana mafarkin yana ihun zai kashe ta, bitch. Buga kofar dakin shi aka fara yasa shi bude idanun shi da suke sara mishi. "Waye?" Ya dakawa me buga mishi kofa tsawa. "King Duah ce na ji kana ihu ne" "Ki b'ace min da gani" ya fada a fada ce. Haka ta bar kofar tana jin haushin kanta. Barin gidan tayi bayan awa guda ya fito zai fita ya hadu da Imtisal. Shiga motar shi yayi ya bar ta a gidan, can tambarin shahara ya wuce, ya nufi office din shi, jikin su Mr Paul na rawa suka bi bayan shi, yana shiga ta fara musu sign kamar yadda suka bukata, yana gamawa ya mike bai basu fuskar mishi magana ba, suma dake mutanen banza ne, babu wanda ya iya mishi magana. Duk yadda yaso ya samu nutsuwar zuciya ina ya kasa samu, domin baki daya Hajnah ta zame mishi bala'i duk inda ya nufa ita yake gani da wannan kallon banza. Haka yayi ta ha
a kashi a cikin City kowa sai da ya kama kanshi. Abin da bai tab'a yi ba, shi ne drunk yau sai da ya shiga wani club ya saka aka sallami kowa, sannan ya zauna yayi ta tulawa cikin shi manyan brand na giya, kiran JB yayi yana dauka ya ce mishi. "Na rantse idan na kama Yar Sheikh sai na bata mamaki, sai na lalata mata suna daga ita har Ubanta" "AJ, why? Me yasa tuntuni baka sha wani abu ba sai yanzu? Kana ina yanzu?" "Ina... ina" ya kashe wayar shi, yana me cigaba da shan giyar shi, bayan wani lokaci Jb ya sami inda yake yana zuwa ya dauke shi zuwa wurin motar shi. "Ni yarinyar nan zata kira Alade jaki dabba, ni ta ce ba aure ya samar da ni ba. JB waye ya tab'a maka wannan tozarcin? King like Me the great Mafia King, sai na kashe yar banza na mata yankan rago " na koya mata hankali yadda zata rinka tunawa da ni har abada. "Idan bata tuna da kai ba, ai kai zaka tuna da ita tunda gashi ta hanaka barci" "hey " ya fada yana me kifa kanshi yana kallon kasa. "Jabir zanci ubanka"."na nawa kuma ai ni bani da lokacin ka, idan ka ishe ni da Iskanci Hajnah zan dauko ta gyara maka sittings dan iskan karya" kallon JB yayi sannan ya fashe da dariya. "Kasan cewa tayi na mai da ita inda na dauko ta." Maida kanshi yayi ya fara barci. "She too young da na gyara mata zama da my mysterious big." "Dan iska har da cin yaran mutane da ka fara yasa ka haukace, ka zata matan kowacce sakarya ce da zaka mata barazana da kayan haushin ka. Ita wannan na musamman ne." Haka suka isa Swan town. Ya fito da shi ya kai shi har dakin shi. Har da rashin zama cikin mutane yasa shi banzan tunani domin da yana cikin su ba zai yi tunanin kome a ran shi ba. Haka ya kai shi dakin shi da yake gyare.
****
Two weeks later.
Kamar babu abin da ya faru, har su Hajnah sun koma school, sai hannunta da yake dan ciwo amma da sauki kamar ba ita. Shiri take, Jadwah ta shigo dakin Dadah zata dauki abu, ganin tsohuwar wayarta a saman bedside din Dadah tayi, ga sabon wayar a kunne. "Hmmm! Kice kin yi tsada irin wannan wayar haka? Nawa aka sayi pride dinki da har kika amshi Iphone XR?" Kallon juna suka yi, kafin Hajnah ta ce mata. "Daidai da girman naki yan mata, yadda kika sayar da naki haka na sayar da nawa" juyawa tayi ta kalli Hajnah. "Kar ki min rashin kunya da sharri" "kamar yadda kike burin yi min sharri haka nima nake baki shawara kar ki fara." "Ballagaza karuwa" "Eh na yarda kenan ai dukkan mu halin mu daya" "kutmar Uba" sanin Hajnah hannunta yana ciwo yasa ta tunkare ta da nufin fada, ita kuwa Allah yasa bata yi rashin lafiya da zaka mata Iskanci ba, ai kuwa suka kama dambe, sosai in Allah ta bawa Hajnah sa'a ta bukat da kasa tayi ta dukanta, ihunta ya koro Dadah da take jin shi a ban dakin. "Gurje mata baki yar banza mara kunya, fashe mata baki mata baki yar banza ne kama da sauro" ai kuwa kamar ta zuga Hajnah ta cigaba da dukanta. Har su Mamu suka shigo d'aga Hajnah tayi ta kifawa Jadwah mari. "Samun wurin ki yayi yawa, kyale ki da muke yayi yawa, kin sakata a gaba. Kin hanata sakat me ta miki? Me Hajnah ta tsare miki? " "Mamu duk abin da ta min baki gani ba, sai Laifina? Mamu me yasa baku kaunar mu sai Hajnah? Idan ba budurcinta ta sayar ba a ina ta samu wayar dubu dari biyar da wani abu?karya nayi an fake da cewa an sace ta, ta bawa wani gardi kanta." Rufeta da duka Abubakar yayi da suka shigo dakin, sosai yana kallo da ita, ita kuwa Hajnah tana zaune a bakin gadon Dadah, hawaye na zuba mata, kuka take ta rasa me tayiwa yar Uwarta ta tsane ta haka? Bayan haka ita kanta sai da Abeey ya amshi wayar ta karba, amma ba da son zuciyar take rike da wayar ba.
...... Ban daki ta shiga ta wanke Idanunta, ta nufi waje ta hada tea ta sha, sannan ta tafi school. Haka suka cigaba da karatu lafiya lafiya, a wannan semester din zasu tawo gombe bikin su Hamma Umar, yasa ta koma school da zama. Duk da gidan babu dad'i amma tafi son zaman makarantar sama da gidan su. Hankalin ta kwance ta manta da AJ. Ana saura kwana uku zasu fara jarabawa, aka tawo binciken Abeey, wai ana zargin shi. Da dillancin miyagun kwayoyi, wannan abin ya kad'a alumma musamman masu ganin shi da mutunci, har office din shi na islamiyya sai da aka samu hodar iblis, da gidan shi da motar shi da Office din aikin shi. Da zunzurutun kudi masu masifar yawa, Mutanen da aka kama suka kira sunan Sheikh. Lokacin da abin ya faru ko waje basu fita, kowannen su tashin hankali yake fuskanta, illa Usaimin da Asad ake kaiwa makaranta. Abin haushi basu ajiye shi a wuri da iyalin shi zasu same shi ba, dauke shi suka yi daga garin. Idan kaga Hajnah zaka dauka ita
aya ya haifa domin ta fisu hauka da shiga tashin hankali. Amma idan ba ka zauna da ita ba, sai ka dauka abin bai dame ta ba. Ranar da ta shiga makaranta, dakyar aka barta ta shiga jarabawa. Shima tana fitowa sai nunata ake da yatsa. Haka ta fito Najlah da Kamnah suka zo zasu wuce suka ganta tsaye bakin titih, tsayawa suka yi suka dauke ta zasu tafi gida. Har suka iso gida bata ce musu kalla ba. "Hajnah!" "Hmm! Kiyi hakuri" "ba kome" haka suka tafi ta shiga cikin gidan, ta samu kowa jigum jigum, wuce su tayi zuwa daki Dadah ta ce mata. "Hanjina anya ba dan mafiyan da ya dauke ji bane ya dauke su ba kuwa? Domin an je daukar Usaimin da Asad basu makaranta" gabanta ne yayi mugun faduwa. Kamar zata kifa ta juya tana kallon Mamu da casbi yake hannunta. Hawaye yana zuba mata, a hankali ta juya tare da shigewa
akinta su. Wayarta ta ciri taga miss call rututu da bakon Number. Dauka number da aka fi kira tayi ta kira.
"Sheikh Daughter, Asad zo ga Didinku" "don't dare touch my brothers, uban me kake bukata?" "Oh kin manta Babanki yana hannuna? Ko kin manta kannen ki ne, well bude email dinki ki gansu, dan na fahimci dakikancin ki ya hanaki bude Whatsapp." Jikinta yana rawa ta kunna data, sannan ta shiga Email din ta, hoton su Usaimin ne tare da wasu irin dabbobi, suna ihu. Kiran shi tayi ta ce. "Kai ka zata tsoronka muje ji? Ka dawo min da Yaran nan da awa daya, idan ba haka ba. Wallahi kayi asarar Hospital dinka idan kana ganin karya ne the golden time zai fara. "
Abin dariya ya bashi, yarinyar nan tana shirin bashi mamaki, kashe wayar tayi ta shiga ban daki tayi alola ta zo ta tadda sallah. Sai da tayi la'asar sannan ya dauki Alkur'ani ta fara karatu, minti Talatin ya wuce, arba'in da wani abu ya tawo ya wuce. Da minti hamsin da biyar ta ji muryan su Usaimin suna ihu sun dawo. Rufe Alqur'ani tayi, ta fashe da kuka. Cikin tsananin damuwa, bata yi kome ba kuma bata da nufin kome, ta dauki Alqur'anin ne domin ya zama gatan su. Shigowa dakin Asad yayi dauke da wani kwali ya mika mata. "Inji Uncle wai a baki wannan"
"Thank you" ya furta tana share kwalla. Dauka tayi tana me budewa.
*Zan sake Babanki, sai kin fito idanun duniya kun bani hakuri ke da shi, gobe za a bude hospital dina, ki tabbatar kin zo wurin kiyi magana da media press" murmushi tayi sannan ta ce. "Lallai kai Jahili ne" ta ajiye kome, bata kuma ji zata yi abin da ya ce din ba domin baya cikin tsarin ta. sai dai kuma ita zata saka shi ya kunyata a gaban idanun duniya da jama'an da ya tara.
Shigowa Mamu tai, sannan ta zauna a gefenta. "Asad ya ce kin san wanda ya dauke su." Dauke kai tayi tana wasa da zoben hannun ta. "Hajnah ba zaki gaya min ba ne?" "Abeey ya kwabe ni da na gaya muku kome, tow me zan gaya miki? Nace miki suna son abeey ya saka hannu domin lalata garin nan ne yaki suke mana bita da kulle? Mamu Abeey yana nan lafiya, ki yarda da ni ko rigar jikin shi ba zata kwarje ba. In sha Allah " "Allah ya miki albarka " "Amin" ta fada tana dauke kanta, bata son kallon Mamu. Washi gari ta shiga school. Kiri-kiri aka hanata shiga jarabawa, haka ta juya ta bar makarantar. A bakin get ta hadu da JB, bai san abinda yake faruwa ba, ita kuma sai ta nuna babu kome suka gaisa a mutunci ya nime ya kawo ta gida taki, haka ya kyale ta duk abinda suke akan idanun AJ yana kallon su daga sama.
Wato duk halin da ake ciki ba zaka rasa wani na nishadi ba, tunda ta dawo take kwance, shigowa Dadah tayi tana kallon yadda ta rame kamar ba ita ba.
"Hanjina! Su Yan mafiya basu shan jinin tsofi ne?" Yadda tayi maganar yasa Hajnah bude idanun ta, kafin ta zauna, murmushi tayi sannan ta ce mata. " Yo me zasu yi da jininki?" "Wai so nake su bani Imamu na," yadda tayi maganar zaka fahimci tayi kewar
anta. "In sha Allah zai dawo kinji Dadah na" "Tow Hanjina na gaji da garin nan zamu koma gombe ko?" Gyada mata kai
tayi, domin tunda tayi missing exam take da yakinin ta gama karatun boko a Nuwanda duk lalacewar masa tafi kashin shanu, gara su koma tushen su. Wayarta ne yayi kara, dauka tayi ta saka a kunne. "Beb we are ready" murmushi tayi ta kashe wayar ta fara kokarin cire kayan jikinta. "Hanjina wai ya naga nonuwarki kamar sun rame?" Cak ta tsaya da cire kayan, tana bin Dadah da idanu. "Kinga Dadah bana son irin haka wani rama nono suka yi?" "Oho dai amma dai ga alamu nonuwarki sun rame, idan kin dawo zan saka a dama miki kunun alkama da hulba, ina dalili yarinya kina mace cif a ga nonuwa kamar kuma kirjin bera, dube cinyarki wai yaushe kika yi jinya haka?" Ganin Dadah ba fahimta zata yi na ta shige ban daki. Ita kuwa Dadah fita daga dakin tayi ta nufi Mamu. "Shafa'atu! " Sam bata damu da su Hamma Umar da suke falon ba, ta zauna tana fa
in. "Shafa'atu, baki ga yadda yarinyar nan ta lalace ba? Kin ga yadda yan nonuwarta suka koma kamar me kirgan dangi, cinyoyinta kuwa kamar na fara, don Allah dama mata kunun alkama da hulba a saka madara ta sha. Ina dalili yarinya me kyan sura ta koma kamar an bawa maye ajiyarta, ko da yake tunda dan mafiyan nan ya dauke Hanjina ta daina gaba ta daina baya, in sha Allah zan hada mata maganin mayu" Usaimin da yake gefe ya ce mata. "Dadah keda labarin fatalwa yake hanaki barci shi ne zaki hada mata maganin Mayu? Hmmm baki tab'a ganin Uncle AJ ba ne, baki san waye Uncle AJ ba ne, idan kika ganshi sau daya ko hmm, sai kinyi fitsari, domin shi da lion yake wasa, don haka ki daina kiran maganin mayu, cilla mu yasa aka yi akan kada, suna wasan banza damu." Ya fada idanun shi yana cika da kwalla. Da sauri ta fito sanye da hijab da safa, har kasa. "Mamu ki min Addu'a Allah ya bani sa'a" "Allah ya dawo da ke lafiya" har ta isa bakin kofa, Hamma Abubakar ya ce mata, "ina zaki da maraici?" A razane ta juya tana inda-inda. "Muna da " "Ke tafi kyale dan banza idan da shi aka cunawa zaki da yanzu muna zaman makokin shi." Inji Dadah. Ta zabga mishi harara, tana kallon shi. "Dan nima har yau hannun da bata warke daga karayan da karannunkar wancan dan mafiyan ya mata ba, ai Hanjina ba karamar jaruma ba ce, lokacin ina yan matancina, ai buga yan mata nake da kasa." "Gashi kuma sai fatalwa take saka ki shiga ban daki kina zawo" inji Asad, "kai Asadu ka fita idanuna, dan kaniyar ka, lokacin ko malam sai da yayi da gaske kafin ya aure ni, domin Allah ya nufa a mace zan zo, da a namiji nazo ba makawa da sai n zama yar dambe." Ta fada tana mikewa, jiya ba yau ba, tana tafiya tana basu labarin kuruciyar ta, tow haka ma Hajnah take itama.
An bude asibitin da la'asar, itama ta samu shiga da get pass dinta, sai da ta bari an cika makil, ana ta liyafa. Daga sama suka jiyo muryanta cikin tausassan kalamai. "Ina muku murna da bude asibitin Imran Nasara memorial hospital, sai dai takaitaccen tarihin bude asibitin da filin da mammallakin filin ya kasance Malam Chindo me lambu ne," ga hoton shi. Dauke wuta aka yi hoton dattijon nan ya bayyana.
"A da wannan filin noma ake rani da damina, Malam Chindo yana bawa mutane suna biyan shi taro sisi, kunga filin girman heka dubu daya da dari tara ne, wanda ya dauke asibitin baki daya. Da wannan filin ya ke ciyar da marayun jikokin shi. Amma dare daya aka kwace filin. Koda yayi magana sai aka yanke wuyar shi yadda zai magana. Bayan yana ji yana gani dole ya tura jikokin shi cirani, yana da inda zai ci abinci an kwace ba saya aka yi ba." Wani irin gumi ne yake karyowa AJ, wato duk inda aka saka mace tow wallahi tafi shaidanan bala'i yanzu lokaci guda ta ruguza mishi kome na shi. Ji yayi kan shi yayi wani irin girma, baki daya tunanin shi ta tsaya cak. Kallonta yake idanun shi cike da mamaki da kuma kwallan bakin ciki. "Ana haka Professor Karib yayi magana domin shiga hakkin Dan Adam, sai labarin hatsarin shi aka ji, daga karshe Imam Omar Hassan Sheikh, Mahaifina dole ya hakura da maganar ya zubawa sarautar Allah idanu, amma wancan mara kunyar sai da ya shigo rayuwar shi. Kaji tow na gaya maka da kyau, yaki da faffutukar yancin wasu a jinin mu yake, na baka awa ashirin da hudu, ka sake min mahaifina ko kuma na sake faifen videon abin da yake tsakanin mu, na...." Ajiye abin maganar tayi ta tako gaban shi. "Matashi kudi da zama wani abu ba haka kawai Allah yake bawa mutum ba, zab'en ku yake domin ku zama sanyi ga alumma. Da alamu baka san kome ba, sai hauka idan ka gama kazo na kai ka ajiye daya na islamiyya ka fara koya daga kasa, kasan Allah sai ka faka Iskanci da hujja.ko fir'aunan yasan Allah, dan haka nan da biyar da kwata, mahaifina ya iso gida lafiya idan ya kai biyar da rabi. Da kai da karannunkar ka sai na watsa fuskar ku a social media, yadda ka lalata min kome nawa ina shirye na hanaka barci kowani each second sai na zama kamar numfashin ka, sai sautin agogo ya zama shi yake jagorancin bugun zuciyar ka, kafin nan suna na ya zama shi ne saukar numfashin ka tik-tik-tik"
(Allah yana gani ta fara bani haushi
#Mai_Dambu.
[2/26, 7:24 PM] MINISTAN SHARHOLIYA: TAMBARIN SHAHARA... (FREE BOOK)
Mafia Romance story.