← Book details Tambarin Shahara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 13 OF 22

Chapter 013

Tambarin Shahara Part 1 Complete Hausa Novel · about 10 min read

Shigowar wasu daga cikin yan uwan Mamu, yasa Hajnah ta koma jikin Addah Nanah, tana zare idanu mika mata abincin tayi su Sayyadah zasu bar falon Abeey ya shigo, gaisawa da Jajje suka mishi hankalin shi yana kan Hajnah da take rab'e jikin Nana, "Hajnah!" Ya kira sunanta cikin kulawa, "Na'am" "ta so muje ai baki sake ba a nan" ya fada yana kallon ta. Kana ganin yadda yake kallonta da kulawa zaka fahimci ba karamin kauna ba ce a tsakanin su, da sauri ta mike tana
aukar plate da cup din kunun suka fita, a tare sai lokacin ya bawa Sayyadah Karimah good attention din shi, Hajnah tana bayan su har wani bangare na gidan. Tashi Nana tayi ta wuce dakinsu. Tana shiga ta samu Hajnah ta gyara ko ina tsaf, sannan ta shiga ban daki tayi uzurinta. "Yanzu Shafa'atu haka zaman kun yake da Yarki?" Inji wata wacce da alamu yayar Mamu ce dan ga kamar su nan a fili. "Addah Yaha, kar ki yi mamaki domin tun lokacin sunan Asad na fahimci bauta take daga baya sakamakon ya zo mata a matsayin
addara, Allah na tuba ba zan yi goyon dan masara ba." Shiru Mamu tayi tana jin yadda suke ta magana akan Hajnah, can kuwa sai gata ta shigo dauke da laptop din Abeey, tana murmushi. "Mamu kiga gidan da zamu zauna a lekki " ta ajiye mata laptop din, karfi da yaji take danne b'acin ranta, tana yake kallon Hajnah take tana kuma kare mata kallo. "Mamu kin ga dakin Abeey, kin ga naki a kusa da nashi a sama kuke,.sai na mu ni da su Addah Nanah, nan nasu Usaimin ne. Sai wancan dakin extra room ne, part ne ta waje ina ga domin su Hamma aka ajiye ko baki, Mamu kin ga kome" a gundire ta ce mata. "Ya isa na gani " ita bata kawo kome a ranta ba, ta washe baki tana fa
in. "Mamu" "Hanjina!!!" Dadah ta shiga Kwala mata kira, da sauri ta fita tana fa
in. "Na'am Dadah" "Zo muje ki ga abin da aka kawo min " tuni suka wuce dakin Dadah, fura ce da gasashen nama, kura mata idanu Dadah, share kwalla tayi a fakaice tana fa
in. "Ya Allah kai ka fimu sanin dai-dai " "kin ce wani abu ne?" "A'a Hanjina." "Na'am Dadah." "Kiyi hakuri da duk abin da zaki gani ko zaki ji, wannan ba kome ba ne sai tsarin
addara, duk wanda kika gani Allah ya san abin da ya shirya mishi, kowanne bawa baya mutuwa sai ya cinye arzikn shi, don haka babu wanda ya isa ya ce yasan abinda gobe zata bayar sai Abin da Allah ya tsara. Kiyi hakuri" "kai Dadah sai kace zaki mutu? In sha Allah ba zaki mutu ba yanzu, sai kin ga Yarana kin goya su" "in sha Allah zan yi fatar haka " a can kuwa Yan uwan Mamu, sai zugata suke, suna wasu irin surutai da yasa baki daya Mamu komawa upside-down, baki daya ta kasa fahimtar kome, sai yamma gidan yayi sau
in Jama'a, Shigowa Nurain yayi ya hango Hajnah tana ta fama da laptop
inta, kallonta yayi a nutse yarinyar bata da kaud'i ko rawan kai da iyayi irin na Jadwah. She always cool, "Yan mata!" Juyawa tayi tana murmushi. "Hamma" zama yayi kusa da ita yana kallon yadda take ta aiki babu ji babu gani. "Hmm ke daya ne?" "Ih suna cikin gida, suna aiki kuma kaga akwai
ura." "Gaskiya kan amma kuma" d'ago kai tayi ta cikin Medical glass ta ce" me?" "A'a" shigowar Nanah da Jadwah, yasa ta bin su da idanu. "Hamma Nurain kana nan ne?" "Yes " Nana ta tambaye shi, hararan Hajnah Jadwah tayi tana fa
in. "A haka mutum zai kare " "like you" ta bata amsa, a fusace tawo kanta. Ajiye laptop din Hajnah tayi, tana fa
in. "Wallahi kika min iskanci mugun duka zan miki, jaka jahila kawai, ban da bakin ciki baki ajiye kome ba, shi yasa gaji nan kullum kamar abin da ake bawa kaji baki gaba baki baya, tsabar bakin ciki da hassada." "Ni kika zaga?" "An zage ki" ta bata amsa, ganin haka yasa ta juya ta fita, sai gasu tare da Mamu. "Ke Halima Jadwah sa'arki ce?" "Amma Mamu meye na mata zata na bina da mugun nufi? Naga dai ban tsare mata kome ba, daga sun zo ta ga Hamma Nurain anan kawai ta fara gaya min magana, " "Ta gaya miki, wallahi zan sab'a miki bar ganin Dadah tana daure miki gindi zan saka ta miki abin zai baki mamaki " kallon Mamu tayi baki daya yau ta rikide mata kamar ba Mamu da ta sani ba. Sai fada take, kamar ta samu wani mugun abu a tare da Hajnah. Bata kuma magana ba, ta fita ita kan Nanah ko sau dari zasu yi bata shiga, domin tasan a yan tsakanin nan Mamu tana son sauya halinta akan Jadwah wanda karshe haka koma baya ne. Haka shima Nurain yaki magana,.har Mamu ta gama ta fita.
Tashi tayi ta koma dakin su, ta kwanta, da ta gaji ta tattara kayanta zuwa dakin Dadah, dama can nan ne wurin zamanta, bata gayawa Dadah abin da yake faruwa ba, amma itama tasan matukar ba barin gombe aka yi da Hajnah ba, ba zata tab'a samun sukuni ba, domin yan uwan Shafa'atu basu da hankali ko ka
an kuwa. Satin su uku suka tattara suka bar gombe bayan an saka bikin su Nanah da su Abubakar da Umar, Nurain kan kiri-kiri ya fasa auren Jadwah inda ya ce baya yi, ba zai auri mace ta nuna ta fi karfin shi ba, kuma babu wanda yayi mishi dole, domin gani suke kamar daga baya zai dawo tunda shi yayi niyya.
***
Nuwanda.
Shiru yayi yana me kallon JB da hankalin shi yake kan Tap, "kit-kit" a zabure ya juya yana kallon agogon, cikin takaici ya dauki glass cup ya jife agogon a take ya fashe. Domin baki daya shi a yanzu agogo d'aga mishi hankali yake, kar'ar fashewar Abu Jb yayi yaji ya juya yana kallon shi. "Me aka maka?" Bakin halin ya motsa har zai yi magana sai ya fasa ya cigaba da kallon gefen shi. Seriously AJ ya sauya domin kuwa tun barin su Hajnah nuwanda ya sauya sosai, sai dai shegen girman kai ya hana shi magana, ko asibiti ya tafi baya aikin kome, sai jarabar bakin rai, a wannan lokacin Duah bin shi take tana wulakantata, haka Imtisal zata fara bin shi JB ya kore ta. Ba zata raba musu zumunci ba, domin AJ baya sonta kuma baya jin zai sota.
"Man!" Sai a lokacin ya d'ago kai ya dubi Jb. "Meke damun ka?" Kallon juna suka yi kafin ya dauke kai yana fa
in. "Babu kome" kallon agogon hannun shi JB yayi ya mike abin shi, domin lokacin sallah isha yayi. Yana kallon shi har yayi alola ya fito ya gabatar da sallah, ko a jikin shi. Shima kuma Jb bai mishi magana ba, domin yana ganin akwai lokuta da dole shi da kan shi zai magantu ko ya bukaci sanin Allah, shi kuma ya mai da hankalin shi ne kan ibada da kuma sanin hakikanin meye addinin musulunci, shi yasa idan ya zauna yana bibiyar rubuce-rubucen manyan malaman Musulunci, musamman wanda Dr Zakir Naik yayi, da kuma Imam mufti Menk. Sai abin ya zo mishi da sauki sosai ya kuma makale a jikin AJ. Haka yasa baya shiga wasu dirty Mind ko wani abu mara kyau, duk kwalaben giyar gidan ya kwashe ya watsar. Ya kuma watsar da bin mata ba sosai ba. "Malam ni fa zan tafi niman abinda zanci." Dauke kai yayi kamar ba da shi JB yake ba. "Dan iska" Jb ya fada yana nufar hanyar fita, gani yayi shima ya mike ya biyo bayan shi, tsaki yayi cikin takaici kafin ya juya ya fita yana bin bayan shi. A mota ma sai da suka raba halin su domin baki daya JB ya rasa wani irin Iskanci AJ yake ji, sun saba idan suka shiga mota matukar tare zasu fita gaba suke zama dayan su yana driving. Amma yau da suka shiga motar baya ya koma tare da zuba kafar shi a daidai wuyar Jb. "Dan Ubanka ni bawan ka ne?" Shiru yayi mishi, "banza dan iska idan wani abu kake ji a ranka, ka fito ka fada ba wai ka zauna kana cin magani ba." Haka Jb yayi ta bala'i da kananun magana amma AJ bai kula shi ba. Har suka isa wurin cin abincin. Kin fita yayi yana daga cikin motar. Har Jb ya ci Abincin ya mishi oda yana zaune, baki daya takaici yake jin yadda ya samu labarin JB yana behind din Hajnah da familyn ta, babban burin shi a karasa bincika mishi inda take, idan ya kama ta sai yai slide da namanta yayi Choping din shi into thousand pieces yadda zai bawa Karanukan shi su cinye. Abin har mamaki yake ji yadda JB ya ce Mishi ta mutu bayan tana raye, familyn ta suna raye. A lokacin da Jb ya shigo ya ajiye mishi odar suka dauki hanya. Sai da ya sha jinin jikin shi, amma sai ya share domin shi kan shi idan ya ce zai yi magana zuciyar shi a kusa take. Suna isa gidan suka samu motar members na Tambarin shahara. A hankali ya fito yana tafiya, Jb yana dauke da abincin. Har cikin gidan, yana shiga ya kalle su. Mikewa suka yi tare da gaishe shi take wani tsinannen girman kai ya shige shi, yana kallon shi like wani abu. Zama yayi ya daura daya akan daya yana me kallon su. "Mun zo ne akan kasa mana hannu saura watanin biyar zaben kasar nan kuma muna da wasu daga cikin members na tambarin shahara da muke son su amshi madafin iko. " Suka jibge shi wasu takardu. "Akwai containers na kudi suna kan hanya." Lumshe idanun shi yayi. _Da alamu baka tab'a zaman islamiyya ba, ka zo zan saka ka._ bude idanun shi yayi sunyi jajjur ya kai hannu ya aljuhun shi ya ciro por larranga, zai kunna wani tsoho ya kunna mishi. "Ina son ku nimo min inda Imam Omar Hassan Sheikh yake, da wannan tsageran yar shi, ku tattara kayan ku iya abinda nake bukata kenan na baku nan da wata uku. Kafin zaben zan saka muku hannu idan kuka samo min details din su." Murmushin mugunta JB yayi yana kallon ikon Allah, bari ya ga waye yake da zarran nimo Hajnah da Ubanta. "King idan da hali ka hakura da yarinyar nan domin zata iya" wani irin duba yayiwa Mr Gayu, kafin ya tsayar da idanun shi kan Mr Paul. "Ba zaka nimo ta ba" "King ko gawarta kake bukata zan nimo maka ita a fadin duniyar nan, Kai Jabir na baka wuka da nama ka nimo mana inda take" murmushi AJ yayi sannan ya ce. "Ba sai kun ba shi ba. Ku nime wani ku ba shi." "King Jabir zai samu kome akan lokaci " "Ok" mikewa suka yi cikin girmamawa suka gaishe shi sannan suka mishi sallama. Suna fita Jb ya ajiye mishi abincin shi ya wuce abin shi. "Ai nasan kana Behind din Halima " Cak JB ya tsaya. "Sai dai matukar na gama da ita sai ka karasa. Amma sai na lalata mata abin da take takama da shi" juyawa JB yayi yana dariya. "Wallahi bana shakkar mutuwa akan Halima sai dai ka sani ko gashin kanta ba zaka iya kusanta ba, nasan inda take amma ba zan tab'a gaya maka ba, ba zan tab'a barin ka isa gare ta ba. Domin tayi maka nisa har abada."
"JB" "Ajwaad " a fusace suka fuskanci juna suna huci. "Sonta kake?" Murmushin takaici Jb yayi ya ce mishi"idan ina son ta zaka dakatar da zuciyata ne? Ko zaka hana ni son abu me nagarta da kyau ne?" Zabga mishi naushi AJ yayi. Cikin wani irin fushi."Ni zaka gayawa kyanta da Nagartatta? Ni King Ajwaad Imran Nasara". "So what? Ita din bata yi kama da hakan ba ne? Dolo su zasu bika ni ba zan bika ba, tun daga ranar da ta mare ka na daina ganin ka da mutunci domin yar yarinya karama ta share maka duk wani Haukar ka" Cak ya kurawa fuskar JB idanu .....
Uzuri sai a hankali.....
#Mai_Dambu
[2/26, 7:24 PM] MINISTAN SHARHOLIYA: TAMBARIN SHAHARA... (FREE BOOK)
Mafia Romance story.
Chapter 13 · 0% Book details