← Book details Tambarin Shahara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 19 OF 22

Chapter 019

Tambarin Shahara Part 1 Complete Hausa Novel · about 10 min read

Sake baki tayi tana kallon shi, juyawa tayi ta kalli Abeey ya tambaye ta da kai, girgiza mishi kai tai alamar bata san kome ba. Shiru yayi but akwai wani abu, don Allah yadda Rafiq yake bada hakuri sai abin ya bashi mamaki, gyada kai yayi ya ce mishi. "Ya wuce" anan aka sassanta amma uban shi bai so ba, ya kalli Hajnah cikin takaici ya ce mata. "Zaki gani" riko hannun Uban yayi yana fa
in. "A'a akwai fadar da ko baka ce zaka yi ba, Allah ya maka kar ka fara fadar da aljanu domin babu riba." "Aljani ne ya dake ka saboda ita?" "Dady ban gaya maka." "Tow kuwa babu me tab'a mutuncina ko na Yarana na kyale shi. Dan haka zata biya kai ma Imam zaku gani" ya fita yana masifa. Duk yadda yaron yaso Uban ya gane Hajnah tana da wani a bayanta yaki fada yake ba a isa ba, ba kuma za a tab'a mishi kimar shi ya kyale ba. Haka suka wuce unguwar su da yake ikoyi cikin fushi, "Dad listen to me, yarinyar nan ba ta da laifi" "kasan waye ni? Kasan me na taka? Wani yazo ya dake ka ya maka karaya biyu saboda ita, zan saka a dauko min ita kayi yadda kake so da ita." "No need Dad yarinyar nan bala'i ce ni naga abin da na gani" kifa mishi mari yayi, yana nuna mishi yatsa. "Be careful dole ka koya mata hankali" gyada kai yayi dan Uban bai tab'a dukar shi ba, sai yau a rayuwar shi. Alhaji Kayode haifaffen garin Osun ne, amma girman lagos, cikakken dan daba ne wanda yake under wata kungiyar yan daban garin lagos, ya shahara a duniyar dabanci, kuma gefe guda yana sana'ar safarar mata da maza tare Yara, gefe guda yana kasuwancin sayar da kwayoyi da makamai sannan yana shirya fashi da makami. Mutum ne ma tsananin sa'a da albarka, Yaran shi uku ne Rafiq shi ne babba, sai Ganiyah tana south Carolina tana karatu, sai Femi tana tare da Mahaifayar ta da suka rabu da Alhaji Kayode. A duniya baya kaunar laifin Yaran shi, musamman Rafiq kowa a cikin garin yasan Rafiq, musamman da yake yana yawan tabargaza a cikin gari,da wasu abubuwan, Alhaji Kayode yana da wani abu daya idan ka tab'a dan shi matukar namiji ne b'atar da kai ake, idan kuma mace ce sawa yake a dauko yarinyar a mata alluran kwayoyi, Rafiq yayi ta kwanciya da Yarinyar har sai ya gamsu ya huce haushin sa, sannan ya saka a kashe yarinyar me Sa'a ce za a wurga da ita ta rayu idan bata yi Sa'a ba ta zama shekakkiya. Kuma babu abin da ya tunzura zuciyar shi kamar ganin yadda yadda Rafiq yake rokon Hajnah. Zubewa a kujerar falon yayi tare da dafe goshin sa. "Kaji me nace?" Shigowar sako ne ya katse amsar da zai bawa Uban, ya duba wayar shi. *Da fatan kayi abin da na ce domin naga tana murmushi, na san waye ubanka da abin da zai iya aikatawa. Ganiyah tana south Carolina ko? Ga Femi take ko? Ka cewa baban ka kar ya sake ya sha ruwan da za a ba shi idan ya fita taron su na anjima domin nasan waye shi. Well bye* "Dad ni na yafe, ka kyale yarinyar nan, idan ba haka ba mutuwa zaka yi gashi ya turo min sako har da abin da zai faru da kai an jima" "shake ka da yayi yasa kana shirin zaucewa." Uban ya fada yana barin falon, ya shiga yayi wanka sannan ta shirya ya nufi wurin taron shi. Yana shiga abin da ya fara kokarin yi shi ne tura wasu manyan yaran shi izuwa makarantar su Hajnah domin farautar rayuwar ta. Ko ta halin k'ak'a ko ba yau ba, a cigaba da farautar rayuwar ta kawai. Kayan shaye-shaye aka kawo mishi, maganar Rafiq ya fado mishi yaki sha, ba wai dan ya tsorata ba, sai dan ya yarda da zancen dan shi.
--
Kallonta Abeey yayi yana fa
in. "Halimah anya zan iya barin ki, ki gama karatu ban miki aure ba? Har ga Allah na fara jin tsoron kar wani abu ya cutar dake, baki daya rayuwar ki kamar irin nasu ne, nasabar ki da matsalolin ki irin" "suwaye Abeey?" Murmushin karfin hali yayi ya ce, "mutanen kirki, ki wuce aji ban da wasa ki kula da Azkar." "Tow Abeey in sha Allah " a bangaren AJ kuwa, kamar mayen karfe haka yake kokarin shiga rayuwar ta, so yake kome nata ya zama ya sani, karfi da yaji yayi ya bin duk wani sawunta. kama daga yawan wayar da take, mu'amalar ta da kowa, da kawayen ta.
Bayan sati biyu, yau sun taso da wuri ta shiga wurin Abeey ya bata kudi zata sayan abinda bata da shi ita da su Najlah, haka suka fita tare. Mr Wale ya dauke su zuwa supermarket, suna isa wurin suka fito. Kafin ta rufe kofar su, sai tashin harbi suke ji. Haka yasa aka shiga guje-guje. Kafin tayi wani yunkuri sai ji tayi an saka mata bindiga a wuyarta, ta tab'a ganin bindiga a wurin shi amma bai yi approach
inta da shi ba, kafin ta yi magana sai ji tayi an wurgata cikin mota. Ihu ta fara tana buga glass. Suka wuce da ita da mugun gudu.
Warehouse din Alhaji Kayode suka kaita, tare da fito da ita, suka watsata a gaban Alhaji Kayode. Tana ganin shi ta ja da baya, wani irin kuka ya zo mata, wannan wacce irin masifa ce? Kallonta yayi kafin ya kalli yaran a hankali ya ce musu. "Ku mai da ita inda kuka dauko ta, Yarinya kiyi hakuri ba zan kuma shiga tarihin rayuwar ki ba, nayi kuskure babba da na saka a ka kawo min ke, ku mai da ita." Haka suja fita da ita tana kuka. Kiran shi AJ yayi sannan ya ce mishi. "Good boy zan baka kyauta na musamman, ba zan raba ka da kome ba amma zan rabaka da abin da yasa kake Iskanci tab'a wannan Yarinyar gara ka tashi unguwa guda domin tsakanina da ita bana bu
atar wani dan banza ya shiga". Ya katse kiran, zuwa Mr Tanimu yayi ya mika mishi wani kofi da madara a cikin shi. "Waye shi?" "Uban ubanka ne, hatsabibi maganin kananun kwari, shaidani me maganin yan iska, shi din ba Lucifer ba ne, but is the king of demons, ka fahimta" jikin shi yana rawa ya karbi kofin ya sha yana zubda kwalla, a hankali ya fara kakari. "Ita kanta rayuwa tana tasiri ne ga wanda ya isa, karka dauki nauyin kasadar da ba zaka iya ba. Bai kashe ka ba amma ya bar ka da wahala likitan
walwar uban uban Mahaukata." Mr Tanimu ya fada bayan ya gama abin da zai yi ya futa daga warehouse din.
A gaban shi yake a durkushe, shi kuma ya juya mishi baya, kuka yake yana fa
in."kayi hakuri na so fahimtar da shi bai yarda ba. Kayi hakuri ba zai kuma ba." D'aga mishi hannu yayi. "Bai mutu ba, ga na bar shi ba zai rayu lafiya ba ne you can go ahead domin nima mishi magana". Ya fada yana harde hannu a kirjin shi. A duk lokacin da ya tuna irin marin da ta kafkkafat mishi ji yake like ya shiga garin lagos ya tashi kowa. Tsaki yayi yana kallon waje, har Rafiq ya fita.
-- A bakin Supermarket din da suka dauke ta nan suka ajiye ta, sannan suka tafi da gudu Najlah ta zo ta rungume ta, jikin ta ya mutu kamar an zare mata laka, "ina Abeeyna?" "Wallahi mun manta sao dai security din nan suka kira yan sanda, gasu nan" a hankali take tafiya, sai ta taka kafarta sai kuma taji zata fadi riketa suka yi. "Yarinya wai ke aka sace?" Gyada kai tayi, "ina iyayen ki" wayarta ta laluba ta kira Abeey, ai cikin abin da bai wuce minti Talatin ba ya iso, daga nan suka wuce station, duk yadda suka so ayi bincike domin abin sai da aka hada da
angaren masu laifukan fyade da sauran su, ban da kuka babu abin take, taki kuma magana dole aka sallame su, suka fito yana cikin motar shi yana kallon yadda ta kifa kanta tana wani irin kuka. Har ta kusa da motar shi suka tawo sauke glass din yayi yana jin yadda take shashekar kuka, iyakar rayuwar shi wannan itace ranar da yaji wani abu ya buge zuciyar shi, kuka take sosai yana kuma bin su da idanun har aka sata a mota, fuskar nan tayi fayau, saman idanunta sun kumbara, bude idanun ta tayi ta kalli Abeey ta ce mishi. "Na gaji gara na mutu na huta." Buge mata baki Abeey yayi yana hararanta, cikin sabon sakalci ta kuma ware baki tana ihu, kuka sosai take tana ihu, abin mamaki ya bashi yana kallon yadda take kuka. D'aga glass din motar yayi ya danna horn me kafirin kara, wanda ya janyo hankulan su, a hankali ta leka shi, zare madubin idanun shi yayi iya kwayar idanun shi ta gani, da suka yi jajjur. Sannan ya rufe glass din, cak kome na kanta ya daina lissafi domin wallahi ita kanta bata san wani irin tashin hankali take ciki ba, dan haka ta kuma rushewa da kuka, domin make mata baki da Abeey yayi. Kafin su isa gida zazza
i ya rufeta, haka suka isa har falon Mamu, da ta samu Nurain tare da Umar da kuma Hajiya Dadah. Ganin Dadah yasa ta karasawa cinyarta tana kuka. "Ni wallahi gara na mutu" "innalillahi wa'inna illahi raju'un, Uban me aka miki? Wani dan banzan ne ya baki labarin mutuwa da har kike sha'awar mutuwa kunga wannan me idanu kamar na tsitaka ko? Me aka miki" zama Abeey yayi yana fa
in. "Dadah Halimah bata da hankali ban san yaushe zata yi hankali ba, aurar da ita zan yi." "Ai da an huta tunda dan banzan yaron nan ya ci amanar mu, sai gashi da kafaffuwa kamar na shanshani wai ya dawo a bashi ita sai kace ta zama haja" "Najlah wuce da ita daki" "tow" ta amsa, haka suka mike zuwa daki, sai da Abeey yayi shiru kafin ya labarta musu abin da yake faruwa, shiru falon yayi kafin ya ce musu. "ina ganin tunda Abubakar bai da matsala zan bashi aurenta koda daga baya ne ayi bikin " "Wallahi ba zai ba, matukar nice na haife shi, ba zai auri Yarinyar da take bin maza suna yawo da ita kamar kayan wanki a yanzu meye Hajnah bata sani ba. Wallahi ba dai Yarana ba." Abin sai ya bawa Abeey tsoro da mamaki, yana kallon ta. "Shafa'atu kina da hankali?" Dadah ta tambaye ta, " baki daya abin ya bawa Kowa mamaki. "Abeey ka bani damar aurenta" inji Nurain, kallon shi Mamu tayi tana fa
in. "Bayan akwai maganar ka da Jadwah? Sannan da munafunci kace zaka auri Hajnah, Gaskiya Allah sai ya saka min wallahi Aminatu ta zama annoba a cikin zuri'a ta. Amma ku rubuta ku ajiye in sha Allah Hajnah ba zata tab'a aure ba, balle ta ji dadin auren da ni ake zancen " "Shafa'atu ba zaki kuma maimaita kuskuren da kika yi ba a baya, idan na kyale ki saboda Yaran wannan karon wallahi ba zan kyale ki ba, zan nuna miki cewa ni ce nan na haifi Imanu shege ka fasa." Inji Dadah da ta fusata ainun. "Hahaha akan shegiya mara uba kike magana? Akan yarinyar da Uwarta ta samota ta hanyar zina, Alhamdulillahi ai ko domin dawainiyar da nayi da Yar da Uwarta ta gudu duniya domin abun kunya a sassauta min, Waye Uban Halimah? Waye Uban ta gata nan a tsaye? Ki tambaye su Waye Ubanki? Me yasa Uwarki ta gudu ta bar ki? Koda yake karuwanci a jinin ki yake, Uwarki watsar da darajar gidan su tai ta bi namiji yawon bari...... *Nima daga yau zan tafi hutun zabe sai kuma Allah ya kai mu bayan za
e. Idan kuma Allah ya kawo min sauki wasu abubuwan shi kenan sai bayan sallah in sha Allah bye Na gode sosai*
#Mai_Dambu
[2/26, 7:24 PM] MINISTAN SHARHOLIYA: TAMBARIN SHAHARA... (FREE BOOK)
Mafia Romance story.
*Mai_Dambu*
Chapter 19 · 0% Book details