← Book details Tambarin Shahara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 21 OF 22

Chapter 021

Tambarin Shahara Part 1 Complete Hausa Novel · about 14 min read

Mamu
Kiran Addah Yaha tayi tana fa
in. "Addah Yaha wallahi na gaji, daga Dadah har Imamu kamar su cinye ta, wai yanzu halin da ake ciki Zunurain ne yake son a bashi Auren Yarinyar nan? Ina ciki daya da Ubanshi. Bayan ga maganar shi da Jadwah" "tun farko ke ce kika sake,.kika amshe rikon Yar Aminatu ko wadanda suke ciki daya da Aminatu basu karbi rikon yarta ba, balle ke ai sun gama rena ki, taya haka ba zai faru ba, kar ki sake ko Yayanki a lika musu aurenta, shi kuma Imamu ki tsaya kai.da fata sai ta bar miki gidan ki." Inji Addah Yaha. "Gida kan ai bata cikin shi wani ya kama mata, kamar yadda ya kamawa Uwarta a lokacin zamanta a Nuwanda." "Kai amma zuri'ar Gambo Sheikh masifa ce sun fitar da masifar da su kansu kunyar haka suke, ki ga bikin da aka yi wai dan kar su hadu da ita babu wanda yazo bikin sai aika kawai suka yi. Wai suna gudun abin kunya, Allah ka tsinewa Aminatu albarka,." "Amin Addah Yaha." Haka ta gama daura ta akan keken bera sannan suka rabu.
----
Wai meke faruwa ne a zuri'ar Sheikh.
Asalin sunan ya samo ne daga Sheikh Muhammad Sudan. Malami ne kuma kusan bafulatani yake gauraye da Larabawa, yake yawon almajiranci, wanda ya zo ya yadda zango a unguwar jeka da fari na garin gombe.
Sheikh Muhammad Sudan yana da mata daya, da yan uwan shi biyu Dalhat da Zubair. Kuma suma duk manyan malamai ne suna Sudan din, shi ne kawai ya fito duniya karatu da niman ilimi, duk da gogagge ne a ilimin addini da haka bai hana shi niman na zamani ba, yana da mace daya da Yara biyar. Hassan da Hussaini sai Gambo, sai Harisah da Dayyiba. Kasancewar yana garin Gombe yan uwan shi zubair da Dalhat suka tawo tun daga can suka nimawa Yaran su auren Harisah da Dayyiba, su kuma Hassan da Hussaini da Gambo aka basu auren yaran su na can Sudan din. Halimah wacce ita ce babba a gidan wato Dadah kenan, ita ce matar Hassan wanda shima ya gaji mahaifin shi ya tafi yawon niman ilimi da yad'a shi, inda ya tafi da Dadah, Matar Husaini Zulaikha, suna zaune a garin gombe,sai Mariyah matar gambo, mace me zafin kishi, cikin su daya da Dadah kasancewar Yaran Zubairu ne. Ita kuma Zulaikha yar Dalhat ce.
Haka suka taso da mugun riko da zumunci, kuma suka yi alkawarin inganta dangantakar juna har ga Yaran su. Domin akwai dan uwansu Gaddafi wanda aka nime aka rasa kasancewar uwar shi yar asalin yankin sudan ta kudu ce, Mahaifin su ya aure ta, haka yasa aka yi ta samun rikici da rashin zaman lafiya, gashi Allah yayiwa Mahaifin su Sheikh Muhammad Sudan arzikn, dare daya aka nime Gaddafi aka rasa, domin shi yaki karatun addini, sai rashin ji da fita, kuma abin haushin da ya tashi tafiya ya kwashi dukiyar uban kaf ya gudu da shi, dama yana yawan tabargazan shi. Don haka mahaifin su yayi mishi Addu'a, Allah ya shirya shi amma yaje duniya ce kamar yadda ya saka shi tashin hankali Ubangiji ya saka mishi, domin koda dukiyar al'umma a cikin tashi haka suka rasa kome nasu. Shi yasa suka yi alkawarin basu kuma auren bare domin tsoron mugun iri.
Wannan al'amarin ya faru da Gambo, domin kuwa fadawa soyayya yayi da wata yar Fulanin Akko, domin yana shiga kasuwar kauye cikin kasuwa. Duk da gargadin da aka musu, amma haka ya kafe kai da fata, ya auro Sa'adatu, wacce Mariyah kamar zata yi hauka, Sa'adatu yarinya ce karama domin bata wuce shekaru goma sha hu
u ba, aka yi auren gata kyakyawar gaske, jajjur kamar zuri'ar Sheikh domin suma haka suke yan sirara kyawawan gaske. Hakuri da juriya, kawaici da kamala yasa Sa'adatu tayi karko a cikin gidan, domin kuwa tasha azaba a hannu Mariyah da
anta, gashi Allah sai bai bata haihuwa ba, sai da ta shafe shekaru goma sha biyar, kafin Allah ya bata Haihuwar Aminatu wacce ta zo akan goshin ajalin, domin cikin sai da ya kwanta na tsawon shekaru uku, kafin Allah ya nufa ta haife ta. taci bakar wahala a hannun Mariyah domin sai an kwantar sai an tayar. Lokacin Sheikh Hussain shi ne ya tsaya akan ta, tunda iyayen su duk sun rasu, yaki a maida ita gida, shi kuma Gambo tsoron fitinar Mariyah yasa shi kasa kome, kwananta arba'in da haihuwa ta ce ga garin ku, kaf cikin zuri'ar Sheikh da Dadah kawai suka shaku wacce ita ce ta saka mata suna Dadah, lokacin da labarin yazo Dadah tayi kuka domin tasan Sa'adatu ta sha azaba a hannun kanwar ta. Gashi ta samu sakon cewa don Allah dadah ta rike mata Yarinyar da ta haifa, Mariyah tace ba zata rike ta ba. Haka Mariyah da Zulaikha suka hade kai suna ta gunaguni, dan ma dai Dadah yar bala'i ce fada ne da ita kamar wuta, idan ta fara kowa samun kam shi yake da shiru. Aminatu ta taso a hannun Dadah, wani ikon Allah. Yaran Dadah uku nan biyu Sayyadah Karimah da Sayyadah Hashimah a Gombe aka aurar da su, yayinda Imamu aka hada shi aure da Yar gidan Hussaini Sheikh, domin Yaran Gambo Sheikh duk mata ne, Allah bai bashi haihuwar maza ba, har ya koma ga Allah. Sai dai Yaran shi Jamilah da Jalilah suna aure a sudan, yaran dangi ne shi yasa aka aura musu Yan uwan su na dangi. Lokacin da aka fara zancen auren Imanu da Shafa'atu a take Mamu ta ce musu Imamu mata biyu zai zauna da su. Nan aka mata caaa. Sai dai idan bata son zumunci. Ita kuma ta kafe akan haka, su kuma suka kafe. Sai dai ta bari guda Aminatu kamar wacce aka saka mata hannu taki gaba taki baya, har aka yi bikin Mamu ta haifi Abubakar Aminatu babu karen da ya fito yana sonta, Mamu ta kuma haihuwar Umar, takwaran Imamu. A lokacin ne wani aiki ya ha
a Aminatu da Imamu, wanda kusan a tare suke fita domin duk cikin Yaran familyn Sheikh ita ce wacce ta hada degree biyu a fannin likitanci kwararriyar likita ce na fitar hankali. Wannan fitar da suke lokacin Addah Yaha tazo Nuwanda. Yasa take ganin ai Imamu da Aminatu soyayya suke. A lokacin ko kai mace idan ka zauna da Aminatu sai ka fa
a soyayyar ta, domin ta iya salo da jan hankali. Idan tana magana sai ka rantse da Allah irin kwararriyar karuwa ce me lasisi, gashi ba zaka tab'a gane fushi da fara'arta ba, domin ta iya tafiyar da kowa, gata da hakuri da juriya kamar mahaifiyarta. A da basu da wani kusanci da Imamu sai dai ayi tattaunawa a wurin dadah wani lokaci kuma idan halin ya motsa bata iya d'aga kai ta kalle shi. Sai a fitar su, da ya janyo hankalin shi ta bangaren da bai tab'a zata ba, Aminatu ba shigar banza take ba, asalima irin shigar gidan su take da tarbiyyar Dadah take aiki. Sai dai magana da hira, ga uwa Uba shagwab'a kamar yar mage, idan tana tare da Dadah tow kanta yana cinyar Dadah. Domin wallahi ko mage albarka. A hankali Imamu ya kasa hakuri da kusancinsa da ita kai tsaye ya gaya mata yana son aurenta dariya tai mishi irin me sanyin nan sannan ta ce mishi. "Ka makaro wallahi" "kina da wanda kike so ne?" "Nop kawai abin ne can sense." Wasa wasa maganar ta fara girma, inda har Dadah ta ja maganar har Sudan. Wayyo Allah ina wutar da za'a jefa Aminatu, bala'i tun daga Sudan har Gombe, kiri-kiri Baffa Dalhat ya ce matukar sai Imamu ya auri Aminatu tow ya sake mishi jikar shi. Wannan abin yayiwa kowa zafi, amma kuma kasancewar Mamu ta samu daurin gindi ta fara wani mahaukacin kishi, tare da attempting kashe Aminatu tare da dukar ta, har da mata tsirara. Abin da yayi mata zafi kenan ta bar gidan, Dakyar Imamu ya samota a wani unguwar mata masu zaman kansu, duk da ba wai tana dabi'ar su ba ce, Dadah tazo har wurin akan taxo su koma gida, amma fir taki dole Imamu ya nima mata gida haya, ta zauna duk da haka Mamu bata kyale ta ba har nan take biyo ta tayi mata cin mutuncin a gaban jama'a. Bakin ciki yasa Aminatu ta bar Nuwanda zuwa Yolbe, acan ta cigaba da aikinta Imamu yana zuwa sosai domin kamar Jaraba sonta yake, amma taki fir. A wani zuwan shi ne ya same ta da wasu baki maza, falonta kaca-kaca da kayan asibiti. Tana kokarin ceto rayuwar mutumin..gashi wasu masu
auke da bindiga sun zagaye ta. Haka tana kuka tana aikin har Imamu yazo ya tafi bata samu nutsuwa ba. Domin a ranar yaso matuka ya tafi da ita amma taki bata son tashin hankali. Kwanan mutumin biyar yan Uwanshi suka zo daukar shi, bayan sun mata gargadin matukar tayi magana zasu kashe ta. Haka yasa tayi shiru domin ta lura mara lafiyar wani irin gata ya
e da shi. Bayan tafiyar su kuwa rayuwarta, ta shiga garari yau yan sanda gobe yan daba. Kuma aka hanata tafiya. Wani dare tana kwance kusan wata uku da faruwar haka, kamar yadda suka zo gidan cikin dare haka yau mutumin yazo mata cikin dare. Tsabar kidima da gigita, haka suka same ta. a gigice a wannan lokacin mutumin sai da ya kusan mata fyade amma yadda ta cure wuri guda tana kuka tare da cewa "don Allah kar ku lalata min rayuwata, na fito daga babban gida ne mutuncin gidan mu zai zube." Zama yayi a gaban ta yana tattara gashin da ya watse a fuskarta da jiknta ya ce. "Idan na aure ki zaki mallaka min surar nan? Tunda ba zaki bar ni na huta da shi ba, wancan ranar ina cikin halin jinya ne likita amma na yaba dake, kuma daga yau babu me kuma zuwa inda nake. Babana da Yana zasu baki kome matukar zaki mallaka min Kanki" babu yadda ta iya tare da niman su kyaleta haka ya Amince, tun daga ranar kuwa ta samu salama babu me zuwa inda take kai ita kanta bata da sukunin yawo cikin yanci sai da yan rakiya, wasika ta turawa Imamu na maganganu masu muhimmanci da kamun rai. Yazo har Yolbe yaga mutumin wanda yana ganin shi a zahiri ya ce mata"kiyi hakuri amma wannan bai dace dake ba, daga inda ya fito a kwai matsala" "tow ya kake so nayi? Shi yafi da cewa kawai" domin ita a lokacin bata san waye shi din ba, shi kuma Imamu daga ganin shi yasan waye shi " duk da yaki nuna mata waye shi amma yaki, da kanta tazo har wurin Dadah ta gabatar da Nasir, itama Dadah bata da zabi, ta tura su Gombe abin tausayi babu wanda ya shiga al'amarin, ita nan ta nufi har Sudan suka ki da kuka suka dawo abin ya mata ciwo, dole ta nime dangin mahaifiyar, sune suka mata gata kuma suka bata abin da tazo da shi. Aka daura mata aure suka bar kasar baki daya. Ita da Imamu suna zumunci sosai, daga baya Nasir ya shiga tsakanin su domin tun daga daren da yayi da ita, yasa yake jin zai bada rayuwar shi domin kare nata, domin wani mugun sonta yake kamar ya cinyeta. Haka Yayanshi da Matar shi da Yaronsu. Sune dangin Aminatu. Fitinar Nasir da yawan takalo rigima yasa suka yi ta samun matsala, daga nan bayan mutuwar Matar wanshi. Lokacin suka so rabuwa wanda ya janyo Nasir rabuwa da dan uwansa. Yayan kamar zai yi hauka domin tun bayan mutuwar mahaifin su, bai da wanda ya zarta nasir domin Nasir wani bangare ne na rayuwar shi. Haka suka koma Peru da zama a can tasamu cikin Hajnah, wanda tasha matukar wahala. Sai dai tun da ta samu cikin bala'i da masifa tsakanin wa da kani ya kunno kai, lallai dan uwan shi ya dawo, ita kuma ta yi al
awarin matukar ya koma wancan dattin ya nemi wata ba ita ba. Wata rana tana kwance da tsohon cikinta, Nasir ya shigo mata a gigice bayan ya shige daki can ya hado kayan ta da takardun ta baki daya ya ce mata. "Ina son ki ina son rayuwa da ke, amma na za
i Yayana sama da kome, kiyi hakuri zan dawo gare ki idan har muka daidaita" eh tasan yana son Yayan shi kamar zai mutu, domin bayan barin su wurin wan shi sai da yayi jinya, wani irin kaunar juna suke kamar ba maza ba, amma akanta ya bijirewa duniyar shi da daular shi da kome na shi. Kuma tasan halin da ya shiga bayan rabuwa da dan uwan shi, yasan yasa ta kasa dakatar da shi. Sai dai kafin su rabu da ce mishi. "Nasan kana komawa gare shi komawa ruwa zaka yi zaka ci gaba da wanka cikin datti da zunubi, ba zan ce kar ka tafi ba, amma ka sani kana tafiya ba zaka kuma samun kusanci da ni tare da abin cikina ba, har abada Nasir kayi min dole na zauna da kai, amma ka bani farin cikin da rasa har abada, a wannan situations ina bukatar ka, amma ka tsallake zaka tafi ka bar ni bayan kasan bani da kowa bayan kai da abin cikina. Zan tafi zan tafi kuma zan nisanta abin cikina da kai har abada, ni kaina xan nisanta kaina da shi domin ya taso cikin kyakyawar alumma.
addara tace rayuwa cikin al'ummar da bata damu da kome ba sai son kai bayan ni ban yi kome ba, ban yi zunubin kome ba,
addara ta hada ni da kowa kaje amma zan fada maka abin da nasan kai va haka ba ne, ka aure ni ne domin sha'awar kanka baka san meye soyayya da kauna ba, a halin da nake ciki ika bukatar abokin tarayya ta hanyar aure, yasa na amshe ka. Ba wai dan ka cancanci zama abokin rayuwata ba, sai dai daga lokacin da na zauna da kai na fahimci kai ne
addara ta mafi girma. Na fara sonka ba tare da na sani ba. Nasir ka tafi na gode " ta ha
a kayan ta baki daya ta ma riga shi barin gidan, damuwa da kunci yasa haihuwa ya taso mata, dan dole ta nime taimakawar asibitin da take aiki domin ta haihu, Allah da ikon shi ta haihu lafiya ta samu y'a mace, kuka tayi sosai tsoronta daya kar ta mutu yarinyar ta shiga gararin rayuwa, kwananta biyu taki bawa Yarinyar nono, wanda haka ysa ta bata madara. Sannan ta nufi Nuwanda duk da jegon da take yi,domin a lokacin ta gama yanke hukuncin nisanta kanta da Yarinyar ta zauna a hannu Imamu da Dadah yadda zata samu nagartacce rayuwa, zamanta a hannunta ba zata iya samun kulawar da ya dace ba. Lokacin da ta isa Nuwanda a tashar jirgin sama aka bata wani sako.
*Nasan nayi laifi amma a halin da nake ciki kece kawai hanyar da zaki iya tsira idan na rayu zan gaya miki waye Nasir da duniyar da yake wanka da shi. Ina sonki tun ranar da kika iya tsayawa domin ceton rayuwata. Ban san sunan da kika zab'a mata ba, but i'm glad da kin sauka lafiya. Sorry to say. Ina farin cikin da duk abin da kika yanke domin nasan zata zama mafi alkhairi a cikin Zuri'ar mu, Ina kaunarki ke da abin da ita. Zan bawa rayuwarki da nata wani irin kulawa. Sai dai akwai abu daya matukar jini na yake yawo a jikin ta zata kasance daban da sauran koda ta zama shiryayya sama da mu. In sha Allah tsoro da fargaba ba zai tab'a zama a zuciyarta ba. Ki saka mata suna me ma'ana wanda zai bita har karshen rayuwar ta. A duk inda nake matukar ma rayu na tsira zan cigaba da bibiyar al'amarin ta. Ina sonki wife ina son Baby girl. Idan mun hadu zan yi fatan na samar mata wasu kannen domin ina ji xan yi nisan kwana zan rayu kodan ke. Kafin nan sai naga bayan wanda yake da hannu ruguza mana rayuwa.*
........... Yours Nasir...... I love you..
Hawaye ne ya zubo mata, domin ta fahimci ba zai tab'a dawowa a gare ta ba, tunda yana can ya zabi wanka da datti. Da rayuwar su. Har gidan Imamu ta isa, kasancewar abinda Mamu tayi mata yasa bata fara shiga cikin gidan ba, ta zauna sai da Imamu ya fito daga masalaci ta mika mishi yar, bayan ta tafi washi gari aka kawo musu kayanta ta rasu ko gawarta ma ba a samu ba, sun yi hatsari a babban gadar Nuwanda da wasu takardun ta masu muhimmanci yasa aka gane sunanta Aminatu Gambo Sheikh. Dangin sun yi watsi da ita, sun manta ita, asalima yarta gudunta suke. Itama Mamu koda ta haihu Babyn babu rai Imamu yaso ta rike Hajnah taki fir, Dadah ta rike Hajnah da kome yarinyar sai Allah ya saka mata wani irin hakuri kamar kakarta, duk da tana da yawan zolaya, Hajnah ta taso cikin tsana da tsangwama, amma naci da shakuwa yasa babu yadda Mamu ta iya da ita, domin ta masifar shigewa jikin Mamu, duk yadda Mamu take kinta haka ta hakura domin Nanah ma itama sonta take, Imamu bai ta
a banban ta su ba. Tana da mugun
walwar
aukar karatu. Duk Yaran Imamu suna da shekaru goma sha shida suke sauka, ita kuwa tsabar naci a shekaru goma sha biyu ta sauke tarti. Tana cika sha biyar ta sauke hadda, gashi Imamu sonta yake sama da Yaran shi baki daya tausayi take bashi domin kaddaran iyayen ta. Tun tana yarinya take fama da cutar mura. Shi yasa ba'a son shigar ta cikin ruwan sama ko wani abu. Wannan shi ne abin da ya faru.
..........
A dawo labari.
*Hey masu bukatar a magana labarin kafin Azumi, so kuke na harhada na gama ne? Nifa labarin nan wallahi bayan sallah albarka in sha Allah. So labarina part part ne ko da bibiyu zan baku dole ayi min hakuri domin bana jin zan iya gama shi nan kusa don Allah a daina cewa a wuce wurin kawai kome dan a hankali ne.*
[2/26, 7:24 PM] MINISTAN SHARHOLIYA: TAMBARIN SHAHARA... (FREE BOOK)
Mafia Romance story.
*Mai_Dambu*
Chapter 21 · 0% Book details