← Book details Tambarin Shahara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 14 OF 22

Chapter 014

Tambarin Shahara Part 1 Complete Hausa Novel · about 10 min read

A hankali ya zare hannun shi daga kwalar Jb, idanun shi na cika da kwalla. "Jabir ni ka zaga?" "Na zage ka akan Halima zan kashe ko da Ubana ne" abin mamaki wai kura a rumbu, kasa magana yayi zuciyar shi tana wani irin bugawa. "Ni ka zaga?" Murmushin takaici yayi wanda yayi sanadin zubar kwalla daga idanun shi. Tun bayan mutuwar mahaifin shi, sannan ya kalli Jb. "Ban waye zan rantse da shi b
a, amma tabbas nayi maka alkawarin sai na nimo ta kuma na mallaketa ni daya koda zan zama zero point ne. Kuma akan idanun ka" sannan ya share fuskar shi ya wuce har ya nufi hanyar dakin shi ya ce " kar na fito na ganka a cikin gidana" "mtseeeeeew" Jabir ya mishi tsaki, har ga Allah babu wani abu a tsakanin shi da Hajnah iya abin da yake yana yi ne don AJ. ya fahimci ba kome kake da iko akan shi. Ya kuma fahimci Hajnah ita
aya ce zata iya saita abokin shi,.shi yasa shima yake amfani da kausassan kalmai domin ya tunzira shi, yasan bakar zuciyar shi koda ya nime ta zai yi wuya ya saukar da kai, zunzurutun girman kai irin na shi,.amma idan ya hadu da ita zata iya biyar da shi. Dan haka cikin d'ago murya ya ce " Nima ina da Gadon Abba Imran dan Uban mutum zama kuma yanzu na fara, sai na auro Hajnah muci uwar Sabada akan idanun mutu, zamu yi ta having affairs daga kofar dakin mutum har dakin mu zamu shiga kai har gadon mutum zan ci mata ta." Bude kofar dakin shi yayi ya ce. "Dan Ubanka sai na yanke maka gabanka dan iska tsinanne". "oho dai kafin lokacin, na zuba mata yarana hudu ta haifa min idan kayi dace akwai Y'a mace zamu yi tunanin baka ita amma kasan dai ka wuce lokacin tuzuranci sai dai mu nima maka bazawara ka fara da ita dan kar first night ka yaga min Baby girl dina " daga saman ya wurgo mishi takalmi, ya kauce yana murmushi, "Kai bakar mace duniya ce, kai da iya mata biyu ka ci zauna na baka labarin wata yar ebonyi da naci, wallahi kana buga musu wuta suna tsiyayyar ruwan dad'i " "sai naci mutuncinka shege dan iska" ai kuwa ya mannawa AJ hauka, kamar zai fita hankalin shi, gashi bai iya shiga tashin hankalin ba. "Daga kai har Halima ranar daurin auren ku zan kashe ku" "kaga kuwa sai a buga mu a jarida mun ajiye record mun mutu ranar auren mu" gajiya yayi da magana ya koma dakin shi bai kuma fitowa ba, dan ya fahimci Jb so yake ya ga bayan shi. Yana shiga daki kuwa kwanciyar shi yayi yana haki zaka rantse da Allah wani abin Arziki yayi nan kuwa yar sa'in'san da yayi ce ta saukar mishi da gajiya, tsabar lalaci da iyayi.
---
Ikko ikon Allah.
Abeey da Hajnah suke fita school, Adda nanah da Jadwah a tare, sai a sauke Asad da Usaimin a makarantar su, duk da Dadah bata nan, sai dai kullum suna waya, da Hajnah, sai dai a bangaren Mamu ne, a hankali ta fara janye Hajnah a jikinta, kiri-kiri zata nuna Yaran ne ita kuma bare, haka yasa Nanah gulmatawa Abeey, sai yayi kamar bai san da zancen ba, ya zuba mata idanu. Iskancin Jadwah karuwa ya cigaba da yi domin tana da me daure mata gindi. Shi yasa kullum sai ta takalo Hajnah da magana, haka yasa idan Hajnah taci da zuci suyi fa
a, har da dambe dan ta gaji.
Yau ta kama asabar, suna kwance dan niman fada, Jadwah ta dibo ruwan sanyi sai da tazo inda Hajnah take, ta sake kofin ruwan haka ya bata mata wurin kwanciyar da sauri ta farka ta ce mata. "Wai me yasa kike min haka ne?" "Anyi gidan Ubana ne, idan kin yi zuciya ki nime gidan Ubanki" maganar ya masifar daurewa Hajnah kai,.cikin fushi ta ce mata. "Bani da wanda yafi Abeey domin nima gudan jinin shi ce. Idan kika kuma watsa min ruwan sanyi wallahi sai na karya hannunki" "kut lallai ma, tow bari na gani" ta kuma tafi kawo ruwan sanyi, ita kuwa Hajnah ta zaro wayar chajin laptop
inta, gashi dama Nanah bata dakin tana kitchen, a fusace Jadwah ta shiga kitchen din tana gayawa Mamu abin da Hajnah ta mata. Ita kuwa ta ce mata" wai Hajnah nan tsoronta kike ji? Da zaki lallasa min ita ba" "Amma Mamu abin da kuke wallahi bai dace ba, meye Hajnah ta miki? Haka kawai kin biyewa mutane da Jadwah kina kuntatta mata sai kace baki san halin Jadwah da Hajnah ba, fisabilillahi idan har zaki iya yarinyar da kika rike haka wacce bata san kowa ba sai ke da Abeey wallahi Jadwah ba zata auru ba, shi halacci haifar mutum ake da shi, ba daga sama yake tsintar shi ba, ke kuwa kin ga ai yadda Nurain ya ce ba zai aure ki ba, ki saka idanu bakin lalata soyayyar Yazid da Hajnah ba, wallahi muna nan daku Allah ya bamu lafiya a wannan duniyar me cike da al'ajabi kayi abin alkhairi ya aka cika balle kayi na banza, ke Uwa ce idan kika kuntatta mata akan mu zai kare matukar zuciyarta me kyau ne. Wallahi rayuwar ba a bakin kome yake ba, yau gare ka gobe ga wani ka." wannan maganar da Adda Nanah tayi ya kashe jikin Mamu. Sai kuma ta rasa gane me take shirin aikatawa, fuuuu Jadwah ta fita zuwa dakin da niyyar dukar Hajnah. Ai kuwa Allah ya bawa Hajnah sa'a, ta tsulla mata bulalar sau biyu, ta fito tana ihu kamar ranta zai fita, abin da ya fito da Abeey kenan. "Subhanalillahi lafiya?" "Wayyo Allah Abeey Hajnah zata kashe ni, duka na tayi da wayar laptop." Kura mata idanu yayi kafin ya kira Hajnah. "Na'am Abeey" "me ta miki?" "Abeey ruwa ta watsa min a wurin da nake kwance kuma ruwan sanyi, da na mata magana a madadin ta saurare ni, sai ta hau zagina. Tare da cewa zata kuma kawo ruwan ta watsa min" "kul na kuma jin kin daki Babba kin ji, ki zo ki gaya min bana son daukar doka a hannu. Jeki dakin ki." Ya juya kan Mamu da take tsaye ita da Jadwah, ya ce mata. "Ina sane da abin da yake faruwa ina da abin da ya sha kaina ne, wallahi idan Jadwah bata fita harkan Hajnah ba, na rantse da Allah sai na bada sadakarta babu sadaki idan kina ganin karya ne Allah Ubangiji yasa ta kawo min karar ta, kuma ban damu ba koda tsoho ne dan shekaru dari zan bashi aurenta Billahi azim." Yana fadar haka ya juya ya bar falon. "Kin ga ki kyale Hajnah bana son fitina." "Mamu ta sanadinta fa Nurainya fasa aurena, fisabilillahi wallahi kawai ta bar mana gidan nan, domin ina ji anan gaba sai ta raba mu da Abeey" ta fada tana kuka. A can daki ma Hajnah kuka take tana jin wani irin kewa a zagaye da ita, kewar Dadah take ji tasan da tana nan da haka bai faru ba, koda aka gama abin karyawa bata fita ba, Nanah ce ta kawo mata. Ita kanta Nanah tana girmama hakurina Hajnah. Ranar monday kuwa zasu tafi makaranta, tana zaune a gefen Abeey ta ce mishi. "Don Allah Abeey ina niman Alfarma ne?" "Me kike so?" Ya zuba mata ido. "Ina son komawa Hostel da zama ne" a hankali ya zuba mata ido, "me yasa?" "Kawai nafi son can ne da gidan." "Zan duba" har suka isa bata kuma magana ba, sai dai kuma yanayinta zai nuna maka akwai damu da kunci dan ma tana da kokari. Haka yanayin ya cigaba da tafiya, har suka samu hutu wanda yayi daidai da gama karatun Nanah na nursing, dake ana bikin zasu tafi Yemen a can zata yi duk wani abin da ya da ce. Daga can lagos Abeey ya warewa Mamu da Yaranshi kudi suka tafi Dubai, a can suka hado kayan dakin da na kitchen. Duk da tsakaninta da Addah Nanah akwai fahimta, kusan a tare suka zabi kayan da zata yi fitar bikin da shi, itama kuma Nanah ta zab'a mata, idan ka gansu a tare sai sun baka sha'awa, ban da Bindin Mamu tana tare da Mamu tare da kai gulmar kome aka yi, Idanunta na kai. Satin su biyu suka wuce gombe daga can, inda aka fara shagalin biki. Bikin ya kasu biyu ne wasu sun tafi Saudiya daurin auren Yazid, tun ranar Laraba, za a daura ranar juma'a za su tawo da amaryan, su kuma nan za a daura auren ranar asabar, domin za a yi bikin al'ada anan shi yasa ana daura aure a can basu zauna ba, suka juyo har da Amaryan.
A cikin gidan gani da tayi yaran familyn suna wani ja baya da ita, yasa taki shiga wurinsu ta zauna da Amarya, kome tare suke, bayan daurin aure, walima aka yi gagarumin a cikin gidan, dukkan su yan matan har da Hajnah liffaya suka saka dakyar aka mata Kwalliyar kawayen amarya, shima sai mita take fuskar ta tayi nauyi. Ana cikin walimar mutanen Saudiya suka iso, ba abi ta kansu ba domin akwai liyafa da dadre, haka aka yi nasiha me shiga jiki. Sannan aka raba kayan biki. Dayawan abokan angon Nanah Hameem sun bukaci alaka da Hajnah amma fir taki basu fuska.
Da dare kuwa,.amare hudu ne. Nana da Hanifah matar Abubakar, sai Ikilima matar Umar, sai Kulsum matar Yazid. Lokacin da aka fara musu Kwalliya, Addah Nanah tura Hajnah tayi bayan an gama mata. "Kin ga kar ki min irin na
azun don Allah just light makeup" ta fada kamar zata yi kuka. Ai kuwa haka ta mata light me daukar hankali, a dakin Dadah ta koma ta shirya tsaf ta dauko dham dinta, ta daura a wuyarta. Sannan ta nufi wurin su tana nishi da kyar da kyar ita ta saka rigar da ya kamata, gashi wani shegen
inki aka mata gaban rigar net ce, kana iya hango White bra dinta, kugunta ya fito daidai matashiyar budurwa, tana shiga dakin sai kallo ya dawo kanta, daukar net tayi ta rufe kirjinta. Me makeup din ta ce mata. "Ina ma da kema amarya ce" murmushi tayi tana dariya, sannan ta ce mata. "Bikina sati daya za a dauka ana yi. Idan aka fara ranar monday sai next Monday a gama, domin za ayi billionaires wedding ne.lolz" ta fada tana dariya. "Please idan lokacin yayi karki manta da ni, zan miki makeup din bikin baki
aya" dariya Hajnah da Nana suka yi, matar ta cigaba da gyara mata zaman mayafin, Jadwah ana can wurin Kulsum ana baza iyayi. Ita nan ta kure a daka, sai da suka fito filin da za ayi liyafar. Idanunta ya dauka akan Hajnah, da mutane suke ta binta da waya ana
aukar ta hoto, dayawan samarin familyn Sheikh sai yanzu suka san ashe mace ce cikin manyan hijabs da Jalbab, da abaya domin kayanta duk sun fi karfin ta. Tayi ta yawo cikin kayan kenan. Haka yasa samari suka mata caaa. Babu wanda ya kuma gigicewa da yanayin da ya gani kamar Yazid, binta yake da wani irin bala'in feelings wanda bai san lokacin da ya taso mishi ba, abin baki daya ya tsaya mishi a rai, kallon Kulsum yake ashe kyal-kyal banza ya bi. Idanun shi kur akan yan matasan kirjinta da suka sha bra pushup, kugun nan kuwa rigar ta zauna das. Tana taku cikin nutsuwa da kamala. Ga wani shu'umin murmushin da take. Arees kanin shi ne da suke ciki daya, ya tawo gefenta yana tsokanar ta. "Yan mata kin ga muje gaban Dadah ayi magana kin ji" "nifa ka kyale ni bana son auren dangi." "Wayyo Flower kina son bin ra'ayin Nurain ne, wallahi ina son ki" "sai kayi kuma, amma babu zancen soyayyar family." Ta nime wuri ta zauna tana kallon yadda ake harkar bikin. Idan ran Yazid yayi dubu sai ya
aci ainun. Sai yanzu yake danasanin kin hakura ya jira ta. Haka aka yi ta hidimar biki har aka zo acin abinci, dake wurin ya kacame da hayaniya wani baya jin wani, suna magana da Arees. Taji an damki hannunta aka shiga janta har cikin gidan ya kaita falon Baban shi ya watsar da ita. "Na kuma ganinki a wurin bikin nan sai na cire miki hayakin da yake yawo a kanki. Kin yi tsirara da sunan kwalliya kina washewa mutane baki."
Team Yazid
Team JB
Team Hanjin Dadah
Team King Ajwaad......
A tsakaninsu dole a cire da waye za a buga wasan....
#Mai_Dambu
[2/26, 7:24 PM] MINISTAN SHARHOLIYA: TAMBARIN SHAHARA... (FREE BOOK)
Mafia Romance story.
*Mai_Dambu*
*Barka da warhaka daga Ministan sharholiya
a daina zare min idanu firgitani kuke
20 read more a sha karatu lafiya Barka da Jumma'a*
Chapter 14 · 0% Book details