← Book details Tambarin Shahara Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
CHAPTER 20 OF 22

Chapter 020

Tambarin Shahara Part 1 Complete Hausa Novel · about 14 min read

This page is for you Miss Ango
Wani irin abu take ji take wani abu yana yawo a cikin kanta, "wuuuuu" rike Kamnah tayi da ta rikota zuwa waje, dan ta nace sai ta fito. Bude idanu tayi. "Bin Ubanki tayi bariki" daga nan bata kuma wanin sauran kalman da suka fito bakin Mamu ba. "Shafa'atu!" Abeey ya daka mata tsawa. Dariya Mamu tayi tana fa
in. "Uwarta ta hana ni sukuni da gidan Aurena how dare zan dauki iskancin yarta? Idan kuma auren Yar zaka yi Bismillah Omar Hassan Sheikh, na dama gane take takenka, da ka bi uwar baka samu ba shi ne bari ka bi yar tow wallahi ko zan yi yawo tsirara sai na wulakantata." Ta juya zata bar falon. "Ba sai kin yi yawo tsirara ba, in sha Allah idan ina raye sai na baki mamaki, da Izinin n Ubangiji. " Cak mamu ta tsaya tana kallon Dadah, "tow shi kenan inda ba a kasa nan ake gardaman kokuwa." Ta wuce
akinta wani irin kunya ce ta kama Umar da Nurain. Baki daya sun rasa meke damun Mamu. "Abeey Hajnah she is collapse fa" ta fada tana d'ago Hajnah amma ina ta tafi kasa. Sai aka rasa da Nurain da Abeey waye ya isa wurin, wani irin janye hannu Nurain yayi sakamakon daukar da Abeey ya mata, suka fita da gudu da ita. Fashewa da kuka Dadah tayi cikin tashin hankali me aka yi aka yi Shafa'atu, a wancan karon ma abin da ya faru kenan, har Aminatu tayi zuciya ta bar gidan. Duk da tana da wanda take amma kuma ta hakura ta amshi zab'a mata Imamu da aka yi. Har gombe aka yi rigimar da ta kusan fasa kan yan uwa, karshe abin bai yiwa kowa dadi ba. "Allah kar ka kuma maimaita abin da ya faru. Amma in sha Allah sai na nunawa shafa'atu ni ba kanwar lasa ba ce, dama irin zaman da suke da Yarinyar nan kenan? Ban sani ba."
Tunda suka bar wurin ya kifa kansa a jikin motar yana jin sautin kukanta, baki daya
walwar shi ta fara wani irin yamutsin da bai san meye makomarsa ba. Kafin kace me kan shi ya dauki wani irin zafi, kiran JB yayi. "Boy are you ok? Domin jikina yana bani kana da matsala" "i need you less than 24hrs" "Ok my king I'm in my way" katse kiran yayi, dakyar ya iya sarrafa kan shi har ya kawo gida. Wayar shi ce tayi
ara. "Sir wani abu ya faru a gidan mota biyu ya fita daga cikin gidan, sun nufi wani asibiti da yake kasar layin gidan, and nayi kokarin bin su naga yarinyar ce aka kawo."
"Shit! Ok samaul" katse kiran yayi ya nufi ban daki wanka yayi, ya jima a cikin ruwan dumi meke faruwa da ita? Me yasa ta shiga wani hali? Yana fitowa ya nufi wurin wayar shi. Dauka yayi ya kira Mr Tanimu. "Ka kira Samual" "An gama my King " ya katse kiran. Shiryawa yayi cikin kananun kaya, black jeans and red shirt, me guntun hannu, daukar facecap yayi ya saka sannan ya dauki wata jack me hula ya daura bayan ya saka facemask, gaban madubi ya nufa ya dauki wani karamin box ya bude device system ne, sai da ya kalla sosai kafin ya sauke ajiyar zuciya. "I need to know what happening with her" haka ya fita bayan ya dauki wayar shi. Yana sauka Mss Yunah ta ce mishi. "Ga Abincin" girgiza mata kai yayi ya nufi hanyar waje. A bakin kofar ya sami Mr Tanimu. "Sir na kira me asibitin na mishi magana." Gyada kai yayi ya shiga motar ya zauna, jin sheshekar kukanta, kawai tadda mishi tsigar jikin shi yake, bai tab'a zata zai ji babu dad'i ganin hawayenta ba. Kukanta wani irin tasiri ne da shi. Haka suka cigaba da tafiya har asibitin, kusan me asibitin ne da kan shi ya tare shi, har Office din shi. "Dr ai Mr Tanimu ya gaya min zaka yi aiki da mu na while time, sir da zaka zauna a cikin asibitin zan yi alfahari da haka, Sir" "A wani daki aka kwantar da Halimah Sheikh?" "Ok sir kana bukatar wani abu ne?" Cire facemask din shi yayi ya mishi wani irin kallo. "I'm so sorry" da sauri ya fita ya nufi ER. ya samu likitoci suna fama da ceto rayuwar ta. Ajiyar zuciya yayi ya juya zuwa office din. "Sir ana faman ceto rayuwarta domin ta shiga" "Bani labcoat." Mika mishi yayi da duk wani abin da ake bukata. "Kasan me? Ka ja bakin ka kayi shiru" Mr Tanimu ya gayawa mutumin. "An gama" fita yayi yana tafiya kamar ba zai taka kasa ba. Har ya isa bakin dakin yana kallon yadda suka d'aga hankalin su. Shiga dakin yayi ya jingina da kofar daidai lokacin da wani likita yake kokarin saka hannun shi a sama kirjinta. "Enough!" Ya daka musu tsawa, juyawa suka yi suna kallon shi. "Waye kai?" A hankali ya taka yana kallonta. Bai basu amsa ba, ya saka safar hannu, ya nufi inda likitan yake ya ture shi. Sannan ya shiga danna kirjinta. " Ai kusan aikinku?" Yana fadar haka suka shiga shirin kota kwana, yana gama danna kirjinta cardiac output aka shiga amfani da shi, a duk lokacin da ya danna kirjinta su kuma sai su saka mata abin, haka zata yi kamar zata tashi, ga computer din da alamar vital pulse
inta yana kasa, gefe guda numfashinta shima sauka yake, a karon farko da yayi fatan wani ya rayu ko ma yaya, sake danna kirjinta yayi cikin sarewa daga zata rayu ko zata tafi, domin number vital pulse
inta 18/6 ne, numfashinta yana kan 10/.0. "Allah idan da har tayi imani da kai ka dawo mata da rayuwarta" ya cire hannun shi suka saka.mata abin "Ahhhhhh!" "Din-din-din" computer ya fara kara al'amar kome yana dawowa dai-dai, hawaye ya zubo a gefen idanunta na hagu. Nan nurse da Drs suka shiga kokarin taimaka mata, kafin aka makala mata abin numfashin da zasu bar mata, suka gyara. zasu fita ganin har lokacin rubutu yake akan wani takarda, sai da yaga fitar su, ya duba aljuhun shi ya cire device din ya zare zoben hannun ta, ya balle ball din kai, ya saka abin sannan ya mai da mata, yana cikin gyara mata Abeey ya shigo, da sauri ya mai da facemask din shi, ya gama abin da zai yi ya fita. Office din MD ya nufa ya zauna yana sauke ajiyar zuciya. A ran shi yake tambyar kan shi, me ya haifar mata da arresting? Lokaci guda zuciyarta tana shirin bugawa? Tsaki yayi, sannan ya cire safar hannu ya daura a saman table din MD, kafin ya tashi yana kallon Mr Tanimu. "An gama sai mun kuma shigowa amma a canja mata daki VIP room" suka fita tare. Zama Abeey yayi yana kallonta ya kasa tantance wani irin yanayi yake ciki ne, shigowa Nurain yayi shima. Kallon juna suka yi kafin Abeey ya ce mishi. "Ka je ka tawo da Dadah da Najlah " "ok" ya furta idanun shi yana kan Hajnah da take barcin wahala. Yau ya kara jin kaunarta da begenta sama da yadda yake ji a baya, tausayinta yana kara karya mishi zuciya. Haka ya fita shi kan Abeey bai san me zai ce ba, amma tabbas yana cikin damuwa. Shafa'atu ta bashi mamaki wallahi. Can kuwa sai ga su har da Kamnah tun bayan fitar su Dadah taso Umar ya kawo ta, Uwar shi ta ce wallahi ya sake ya kaita sai ta tsine mishi, Dadah tayi kuka ba ka
an ba, taji ciwon abin da Shafa'atu tayi, tana zaune sai ga Nurain. A bakin kofar fita suka hadu da Jadwah wacce bata san me ya faru ba, ta shigo gidan. Duk da tasan yana gari amma kuma ba ta kawo kome a ranta ba. Ko kallo bata ishe shi ba. Haka suka tafi.
Har suka isa asibitin AJ yana cikin motar kamar mayye gani yake matukar ya bar asibitin Hajnah zata mutu, shi yasa yake zaune a cikin motar. Har dare yana wurin a zaune. Su Abeey suka tafi masalaci. Kuma har lokacin babu wanda ya ga yazo domin su. "Ga card a kawo abinci da abin da ake bukata" "ok My King" ya fita a motar, yana kallon agogon hannun shi har aka fito sallah isha, kafin Abeey da Nurain suka fito basu koma asibitin ba, suka fita kowanne su a mota. Can sai ga Mr Tanimu ya dawo dauke da kayayyaki har da wasu mutane biyu suka rike mishi, ER ya nufa dakyar ya gano dakin su, domin an kaita Ward. Wanda yasan shi yayi magana, ya rigada yasan abin da AJ yake so, ko magana yayi kafin ya kai aya yasan manufar abin. Haka suka shiga dakin, juyawa Dadah tayi tana kallon su. "Sannu Hajiya, abinci ne muke rabawa muka kawo nan dakin" "mun gode" ta furta tana share kwallan da yake zubo mata. Suka amsa ba iya abinci bane har da flast kayan tea, da duk wani abin da zasu bukata. Ga wasu green card na get well soon. Suka ajiye suka fita a cikin kayan suka ga karamar cattle. Can aka sake buga musu kofa drinks ne da wasu tarkacen. Aka shigo da shi abin sai ya fara ba su mamaki. Amma kuma basu yi mamaki ba dan dama ana samun masu rabon abubuwa haka. Wani leda na eatry Kamnah ta gani ta bude takeaway ne da abinci me zafi, kusan leda uku ne iri daya, turawa dadah tayi. "Dadah kici abinci" "ba zan iya ci ba, kamla bana jin yunwa Hanjina zata mutu" "in sha Allah ba zata mutu ba." Daukar roba daya suka yi ita da Najlah domin rabon su da abinci tun rana suka fara ci. Dakyar dadah taci tuwon shinkafa miyar kuka, yaji manshanu asalin girkin yan mali, sai wani irin kamshi miyar ga rabin kaza da aka saka a kowani roba. Sai da suka ci sosai, sannan suka dawo hankalin su. Lokacin da suka gama suna gyara kayan Nurain ya shigo shima da nashi kayan shi. "Sannu da dawowa, yanzu wasu yan albarka suka kawo mana.." Dadah ta fada, tana kara mishi bayani. Bayi mamaki ba amma kuma ya zai yi da abincin da yazo da shi. Dole haka suka bude yar karamar firj din dakin suka ajiye kome, sun tab'a hira kafin ya bukaci Kamnah tazo su tafi. Haka kuwa ya faru, "Hamma zan dauki abincin na tafi da shi kaga situation din gidan bai zama dole na samu abinci ba." Lumshe idanun shi yayi domin komawarsu ba karamin al'amari aka yi Abeey da Mamu ba, idan yake kokarin
alle igiyar auren su ita kuma ta kafe kai da fata idan ya sake ta sai ta zama ajalin Hajnah. Dole aka shiga tsakanin su, domin yayi mugu mugun fushi abin ka da me hakuri. Daukar wanda ya kawo tayi suka fita. Tare da yiwa Dadah da Najlah sai da safe. Koda suka shiga mota basu yi magana ba, suka isa gidan. Wucewa dakin su tayi ta kwanta. Ta dan bude abincin tayi wanka ta kwanta.
Washi gari sai da ta ci abincin, a falo suka hadu da Abeey ta gaishe shi. "Kuna da class ko?" "Eh" "muje sai na dauki Najlah ku tafi ku shirya, zuwa an jima sai a azo a dauke ku, make sure kun tawo mata da kaya. Muje kar ku mara gashi sai na nime inda zaku samu Breakfast." "Ok" haka suka fita, sai da ya tsaya nima musu abin karyawa, suka nufi asibitin. Koda suka je basu gaya mishi abin da aka kawo ba, kawai dai sun sha tea, kwai da sausage stew sai chips. Yasan Nurain zai kawo shima tea ya sha suka wuce gidan su da Makarantar suka shirya sannan suka shiga motar oga wale ya kai su makarantar. Sosai suke kewar Hajnah,
Barci yake sosai duk da dakin akwai duhu, amma zaka iya hango shi kwance kamar wani mage, AJ yana son barci musamman da ya kwana yana nazarin maganar su Dadah da su Najlah domin suma basu yi barci ba. A yadda yaji suna fa
in Mamu ce ko wacece bata kyauta ba yaji ran shi ya
aci. Jan labulen dakin JB yayi wanda ya iso da safe misalin
arfe goma. AJ ya gayawa Tanimu JB yana hanya. Shi yasa shi kuma ya nufi airport jiran shi. Kallon shi AJ yayi yadda yake ta barci, samun cinyar shi yayi ya sake mishi duka. "Kai dai dan iska ne" ya furta yana kare hasken rana da yake cika mishi idanu. "AJ wake up" "mtsew" ya ja tsaki yana jan mayafin shi. "Allah ya baki lafiya Hanjina" yaji computer din shi ya fada, "Allah ya d'aga kafadar ki" dafe goshin sa yayi. "Sai da ka nimo yar mutane? Me ka mata?" "Mtseeeeeew Ubanka na mata" "zaka aikata" JB ya furta yana nufar ban dakin AJ, sai da yayi wanka ya fito a hankali yana kallon shi. Ganin yadda ya tashi daga shi sai buster men pant, yasa shi dauke kai . "Banza karuwa" "kai ma haka ai" JB ya bashi amsa. "Jakar ya bude ya ciro abin sallah. Sai da ya fara gabatar da da Isha da ya rasa kafin ya gabatar da Asuba, yana zaune yana addu'a. AJ sai kallon shi yake cikin mamaki. Yadda ya iya tsayar da kome yake wannan abin, shi rabon shi da zuwa ko sallah juma'ar ma manta yaushe tsaki yayi ya wuce ban daki yayi wanka ya fito shiryawa yayi sanye da kaftani Mint green sai riga brown ya gyara sumar shi. Kafin ya fito JB ya rigar shi fita a wurin cikin abinci ya same shi. "Me za a saka maka?" "Moringa tea with honey." ya fada tana kallon JB da ya
e cin abincin shi kamar bai san da zaman shi ba. "Dan Ubanka idan ka gama ka koma inda ka fito" ya fada yana yatsina face, kamar ya ga kashi. "Ai naga wurin zama
an Ubanka ba zan tafi ko kofa ta kashi ba." Ya cika bakin shi da Chips. "Good morning My King" jinjina kai yayi yana jiran karin bayani."Sir jikin da sauki amma bata farka ba, har yanzu" jinjina kai yayi yana kurb'an tea. "Sir maganar asibitin da zaka bude nan an samu wani gida amma gaskiya yayi kudi dayawa, a kusa da unguwar da take ne" "A biya price din" JB ya fada, dan yasan mutumin shi ya tsani ace za ayi ta ciniki, yakance idan akwai ayi kawai. Sai da suka gama sannan ya suka wuce studio da JB, table tennis ne a dakin. Suka fara bugawa, cikin halin shi kamar bai son ya fadi matsalar shi amma kuma ya kasa daidaita yadda zai yi bayanin. " Idan na fahimta ka hadu da ita ta kuma kafta maka mari ko wannan karon ba zan lamunta ba, kar ta ganka jibgegge ta dauka baby boy bai da me rama mishi." "Kai dai a cikin yan iska kai ne karshe ko?" Ya tambayi JB. "Tow me zan iya maka banza ka dauko ni tun daga las Vega sannan kana kashe ni da silent mood ubanka ne ya ajiye ni na maka hidima na mutu da mugun halin ka?" Murmushin karfin hali yayi ya cigaba da buga kwallon.
"Ajwaad!" D'ago kai yayi yana few seconds kafin ya buga kwallon. Rike kwallon JB yayi ya ce mishi. "Meye matsalar ka?" "I feel guilty " gyara tsayuwar shi yayi yana kallon shi. "Do you like her?" Wani irin shan kamshi yayi yana huhhura hanci kafin ya ce. "No ba wannan a ra'ayina " "ok shi ne kake jin damuwa?" JB ya fada yana ji kamar ya rufe AJ da duka, domin ya fara kulewa da iskancin AJ. "I want girl in my side" "bura Ubanka banza dan iska" ya ajiye abin game din zai fita yana kananun magana"shege ka kira ni ne ka gaya min kana son ta a gefenka? Aiyuka masu muhimmanci na tsalleke saboda kai amma dake kai haifaffen mara mutunci ne zaka gaya min kana son ta zauna a gefen ka? Shege dan iska " "ta samu matsalar heart attack ne " juyawa JB yayi yana kallon shi, "like how? Anyone harm her? Ko tana da wani matsala ne a gefe" zama yayi jagwab kamar wanda aka zare mishi laka. "Yes shi ne abin da ban fahimta ba" "but babu wani hanya da za ayi iya niman mafita ?" JB ya tambaye shi. Tab'e baki yayi yana gyara zaman shi. " Bani da wani abun da zan iya asalima ba zan iya cewa ga abin da ya faru ba." Shiru yayi yana kallon tv, kafin ya dauki apple a falon ya fara ci. Can kamar wanda aka mintsine shi ya fara bayanin abin da ya faru. Shiru suka. "Kasan i'm here ne domin take revenge so idan na." "Naci uwar revenge da gudu ba wando, dan iska revenge taci uwar Uwarta, AJ idan zaka bar all your destination ka tawo yes we need Halimah more than you expected, kana bukatar ta ne na fansar ka kazo dauka ba, soyayyar ta ce twins marin da ka sha " "Ni ne nake son ta? Lallai ko mata sun kare ba zan kalleta a mace, beside bana jin any feel akan ta is better for you ka iya harshen ka. Kasan who i'm the king how ocean and desert zasu hadu. " "Idan Ubangiji yaso ha
awa sai yayi iko akan lamarin shi so ka daina mamaki." Mtseeeeeew AJ ya ja tsaki. Sanin babu hanyar da JB zai kuna shi sama da zolaya ya ce mishi. "Ok tunda baka sonta why not ka tsaya min na nime aurenta?" Cak AJ ya tsayar da taunar da yake. "Ina ga a tsinannu kai ne jagoran su ko? Dan Ubanka idan ka fasa auren ta shege kake." "Ai ina gaya maka bakar mace siririya yar doguwa me manyan kayan aiki duniya ce, sun fi sauran mata daukar daka " bai san lokacin da ya rarrumi wuka zai yi kan JB da shi ba, "dan iska kana sonta me yasa kaji haushina?"
Tsaki yayi ya fita daga falon ya nufi bayan gidan shi da Jb yana zolayar shi.
[2/26, 7:24 PM] MINISTAN SHARHOLIYA: TAMBARIN SHAHARA... (FREE BOOK)
Mafia Romance story.
*Mai_Dambu*
Chapter 20 · 0% Book details