Chapter 18
Tambarin Shahara Part 1 Complete Hausa Novel · about 13 min read
Jan hular kanta tayi tana kallon waje, a hankali ta mike ta kwanta a gefen Kamnah, "ke jeki gadon ki mana" "ban yi niyya ba, anan zan kwanta." "Najlah zo ki taya ta kwana" "ke ja can hotter guys nake gani a Pinterest don haka ku kare kalau." Najlah ta fada tana juya musu ba, "Egiya aikin ke nan kallon maza" leko da kanta tayi daga sama, ta ce musu. "Idan ban kalli maza ba, mata zan kalla banzaye." Ta diro a gadon tare da kunna wuta, cire top din rigar barcinta tayi tana fa
in. "Dan Uban mutum ina zan kai wannan kayan? Ko akwai wacce zata cinye ni ne?" Kamar munafukai suka cure wuri guda, suna girgiza mata kai. "Ku bar ni na kalli maza, ko ba kome kun saya min lemon tsami idan na tadda tarzoma kun matsa ku bani, munafukan banza" gyada mata kai suka yi ta koma sama abinta, bayan ta banka musu harara. Domin ita daya ta san yadda take kallon su, har ta kwanta sannan ta leko. "Anya babu mata maza a cikin ku?" "Ko daya mu dai ba jarababbu ba ne." Kamnah ta bata amsa tana jan bargonta. "Ke Haj koma wurin kwanciyar ki don Allah wallahi bana iya kwanciya da wani kusa dani" sauka Hajnah tayi ta koma wurin kwanciyar ta, domin bata da bakin magana. "Iskanci duk ranar da aka kai ki gidan Mijinki haka zaki ce mishi ya sauka baki iya barci da wani? Allah ya yaye miki, ai ni tun kafin a kaini zan gaya mishi ni fa a jikin shi nake son kwana ba a katifa.." "don Allah kiyi hakuri kin ji wallahi ilimin mu bai kai babin da kike kawowa ba, don Allah ki raba mu da aljanu domin suna son zantuttukar batsa" "ke don girman Allah?" Tsaki Hajnah ta ja, domin tasan halin Najlah Allah ya daura mata tsoron aljanu, kamar Dadah da zancen fatalwa. Jan bargo tayi tare da kashe wayar hannunta.
Karfe biyu na dare, kowa na barci amma ban da Hajnah da ta farka zaune tana kallon wayarta, wani mafarki tayi tana gudu cikin ruwan jini, wasu mutane dauke da makamai suna bin ta. Gudu take suna bin ta, har zuwa wani katon gida. Shiga cikin gidan tayi ta wuce saman gidan tana shiga ta samu wasu mutane kwance suma cikin jini male-male, juyawa tayi ta hango Abeey shima jinin yake zubdawa bai mata magana ba ya riko hannunta suka shiga gudu a cikin gidan, har ya kaita wani kofa juyawar da zata yi ta ga ashe ba Abeey ba ne wata mata ce, wurgata cikin wani irin daki me duhu tayi ta farka. Shi ne tafarka take haki, ban daki ta wuce tayi alola ta fito ta shimfida abin sallah, ta tadda ikama, har kusan uku ta koma ta kwanta. Sai biyar na Asuba Najlah ta tashe ta ganinta a kan abin sallah yasa suka fahimci tayi sallah, da sauri ta mike ta nufi ban daki ta kuma alola ta fito, sallah tayi tana azkar suka fita falo. Daga dakin take jiyo ihun su, suna hira girgiza kai tayi aikin kenan idan zasu hadu tow ba ruwan su. Wanka ta shiga ta zauna a cikin ruwan dumi tana kara nazarin mafarkinta da ya kashe mata jiki baki
aya tow wacece matar nan? Meye hadinta da ita? Su kuma sauran mutanen meye ya ha
a su? Jinin da ta gani fa? Ganin bata da me bata amsa yasa ta mike a hankali ta cigaba da wankar ta, tana idarwa ta fito a hankali ta same su, suma sun yi wanka suna shirin su ne. "Me ke damunki Halimah?" Murmushin karfin hali tayi tana fa
in. "Kawai jiya na dan yi mafarki ne, amma ba damuwa" ta wuce wurin kayan kwalliyar da suka jera tun jiya, suka shirya tsaf domin suna da class 9am, abincin ta tsakura ka
an, sannan ta mike tana kallon su. "Hanjin Dadah, mu barwa matar da zata so mana aikin ko?" "Eh mu bar mata sai ku kulle store da kome frij ma ku rufe ku tawo da keys din ba, zan tsaya a labrary, sai kun tawo" ta fada zata fita. "A'a ko tsaya mu tafi kawai" Najlah ta fada, haka suka hada kome, sai ga matar ma da yar ta karama bayarabiya ce, suka gaisa sannan ta ce musu . "Nice zan na muku aiki" "ok akwai kome dakunan mun gyara falo ne da wanke wanke, akwai sauran abinci ki bawa Baby" inji Kamnah ta fada cikin girmamawa, tana shafa kan Babyn. Suka mika mata key daya suka tafi da saurin inda suka gaya mata koda zata zo ta samu basu gida tayi aiki kawai, ta amsa tana godiya. Fita suka yi waje suka samu mutumin da zai kai su makaranta, fitowa yayi ya gaisu, Najlah ta shiga gaba bayan sun amsa, Hajnah da Kamnah a baya sai hira suke jifa jifa, har zuwa inda zai ajiye su. "Madam ga wayana ka bani Number ka" "ok" Hajnah ta fa
a tana amsar wayar shi ta saka Numberta ta kira layin, yana shiga ta mika mishi ta ce mishi. "Halimah Sheikh " sannan ta kalle shi"Mr Wale " "Ok idan aka tashi zamu
ira ka" "tow Madam " ya koma motar suka wuce abin su. Har labrary suka shiga, anan suka rage sauran lokacin karatun su. Tara da minti goma suka nufi class, suna shiga suka zauna a wuri guda. Sai kallon su ake domin idan ka cire Hajnah da take an santa Kamnah da Najlah baki ne. Don haka suka cigaba da zama suna hira sama sama. Har malami ya shigo ya gama musu karatu. Bayan fitar shi ne suka fito, suka nufi wurin cin abinci ruwa suka sha kawai, suka wuce masallacin makarantar anan suka yi sallah sannan, suka dan yi karatu kafin suka fito daga masallacin suka nufi aji. A hanyar komawar su ne, suka hadu da wasu gang na tsagerun makarantar, basu kula su ba suka wuce abin su. Domin sun ga basu ta kansu. Amma kuma suna ganin yadda suka wuce yasa gang din suka biyo bayan su da nufin tsokana don sun saka Hijab, haka suka ta bin su har cikin ajin su. Sai dai har suka shiga babu wanda ya iya musu magana domin Yaran yayan manyan ne, sai yadda suka yi da mutane. "Hajnah ki kira Abeey tsoro nake ji" inji Kamnah tana rike hannun Hajnah. "Ko na kira Abeey babu abin da zasu yi, yaran manyan ne, kuma
arku dauka karatu suke kawai niman magana ce irin ta su. Idan bamu kula su ba, haka zasu gama haukar su ta fi" da wannan yanayin suka samu nutsuwa. Tunda suka fara bin su, Hajnah bata kula ba, sai da shugaban Gang din me suna Rafiq, ya tawo zai dauki littafin ta, d'ago kai tayi ta kura mishi Idanu tayi. "Kasan me? Ka fice mana daga class, idan ka sake muka tsaya a gaban jama'a ba zai maka kyau ba." "Uban waye ya tsaya miki?" Kallon shi tayi, tana tuna in da taji makamancin kalmar. "Allah" kwashewa da dariya suka yi, suna haja Abeey ya shigo, ganin yadda ya shigo da wasu malamai yasa Rafiq juyawa yana fa
in. "Gaskiya yarinyar nan zazzafa ce." Ya juya ya fita. "Abeey" murmushi yayi sannan ya ce" ina ce baku yi rigima ba?" "A'a'wallahi " "shi kenan " ya juya suka fita. Baki daya bai da nutsuwa ba zai iya tashin hankali ba, ya baro wani ya zo ya samu wani kuma abin takaicin akan Hajnah. Sai da ya koma office din shi. _Don Allah ka nisantatta daga kowacce irin matsala_ tow me yasa fitinannun maza suke bibiyar ta? Ya rasa gane kan wannan yanayin baki daya. Bayan sun taso sai da suka bi office din shi suka mishi sallama, suka nufo gida.
***
Tafiyar kwana goma suka shigo cikin garin Lagos, a inda ake sauke kayan da aka shigo da shi daga
asashen duniya suka sauka, idanun shi sanye yake da black glass, yana sanye da katon jackit. A hankali yake takawa, guard din shi ya hango suka karaso da sauri suka amshi kayan hannun shi, sannan suka nufi motar da suka zo da su unguwar da suka sayi gida Victoria island. Kome na gidan an shirya yadda zai rayu cikin farin ciki da aminci, yana shiga cikin gidan da Mss Yunah suka hadu. "Son ka iso?" "Hm" ya fada yana haurawa sama, haka suka bishi sama. Sai da yayi wanka ya huta yayi bushe bushensa, sannan ya sauko kasa cikin kayan shan iska yana kallon waje ta barandar baya, yana iya hango yadda ruwa yake. Mutum sai kace kifi domin yana masifar kaunar ruwa. Sai da yasha karar sigar uku, sannan ya nufi dinning room, ya zauna ya fara cin abinci a yangance kamar baya jin yunwa, kafin ya sha ruwa ya mike. Zai iya gudun kowa a duniya ban da Jabir. Shiga dakin shi yayi ya hada kome sannan ya kira JB. "Dan kutmar Uba nasan AJ ba zai mutu ta sauki ba, kana ina?" "Hmm! Ka yarda na mutu kawai, zan iya mutuwa a ko ina amma ba zan iya mutuwa a bayan ka ko akan idanun ka ba." " Na sani shi yasa gani nan na kafe kai da fata ka mutu tsinanne mara mutuncin, duk inda kake zan biyo ka ba zan iya rayuwa babu abokin fada ba, kana iya?" "Idanu zasu yi yawa akan ka, so ka bari sai an kwana biyu zan turo maka da yadda zaka " "muna tuntubar juna don Allah AJ" "Hmmmm, shi kenan zan cika alkawarin" kashe wayar yayi kasancewar ta internet ya kira duk bala'in mutum dole haka zai hakura.
A can mafia City kuwa bayan an fitar da sanarwar mutuwar AJ, kafin kasa da awa ashirin da hudu, duk wani members na tambarin shahara ya bayyana, hatta Abraham da yake kuka riris, JB dama bai yarda ba, kawai yasan AJ gudu yayi wurin Hajnah. Yadda yake kuka zaka rantse da Allah domin mutuwar yake kuka nan kuwa sai ya fashe da kuka sai ya koma gefe ya fashe da dariya, kuma abin takaici shi suka daura a binciken gawar AJ, dan haka ya saka kudi ya sayi likitocin da kowa a cikin kwana uku kacal sakamakon mutuwarsa ya bazu a duniya, kafin kace me an kame duk gidajen shi ana bincike wanda aka bawa binciken kuwa Abraham ne, kewar abokin shi yasa ya kasa hakuri yayi binciken haka dai aka yi kome biri-biri. Mr Paul kamar zai yi bindiga tsabar rashin hankali domin kuwa ya gama saka rai a wannan lokacin AJ zai saka musu hannu akan zaben da za ayi dan banzan yaro ya mutu. B
aki daya sai yake jin zafin AJ akan mutuwar shi don ma an samu gawar shi ta kone murus. Iya binciken da suka yi babu wata wacce AJ yayi mu'alama da ita. Sannan wani abin burgewa yadda JB yake ya zake yana kuka kamar da gaske mutuwa aka.musu bayan kwana goma da mutuwar ne ya tattara ya fara kokarin komawa Las Vegas.
Duah kuwa ruwa aka yi ta saka mata, domin suma take, daga Morocco Imtisal ma tasha kuka kamar me, amma shiga damuwar da Duah tayi ya fi na kowa domin bata ci bata sha, haka yasa ta bar
asar itama, domin ba zata iya zama babu AJ ba.
***
Lagos
Mika mishi tap yayi hoton Hajnah Sheikh ya bayyana, kallon ta yake tana sanye da nikab, sai kwayar idanunta. Murmushin mugunta yayi yana fa
in. "I catch you Gurl"
"Sir a dauko ta ne?" "Barta" ya furta yana nufar sama, daki ya shiga ya kwanta barci yake ji. Sosai yayi barci abin shi,
Two weeks
Yau sai karfe biyu zasu shiga cikin class, don haka ta musu abinci, tuwo da miyar alayahu. Ta malmala sannan ta fito ganin suna gyaran falo ta ce musu. "Bebs food is ready." Ta nufi daki, wanka tayi tana fitowa ta saka doguwar rigar na lace green, sai Hijab dinta cream cheese. Shafa aud tayi ta nufi wurin su. Abinci suka tana fa
in. "Mu shiga makarantar da wuri, " "tow" bayan sun gama suka fito. Mr Wale ya fita da su, a kusa da department din su ne ya tsaya, suka fito da sauri suka fito daga motar zasu nufi class. Rafiq da gang din shi suka sha gaban su. "Yan mata yau babu class sai dai shagali" rab'ewa ta gefen shi suka yi zasu wuce yayi caraf ya riko hannun Hajnah. "Sake min hannuna" "idan ban sake ba fa?" "Zan baka maka, sake min hannuna" kokarin fisgota yake ya ha
a da jikin shi, su kan su basu san daga inda ya fito ba, sai dai yadda yazo ba tare da sanin su ba, ya shake wuyar Rafiq yafi kome basu tsoro, musamman yadda suka cure wuri guda tsabar tsoro da tashin hankali. Riko hannun shi yayi ya murd'a sai da kashin hannun ya karye. Ai da gudu sauran abokan shi suka ware, sake karya hannun yayi. "Ka kyale shi don Allah zai mutu" duk da idanun shi na cikin bakin madubi bai hana ya kalle ta a fusace ba, ganin yadda baka ganin har kwayar idanun shi yasa ta ja da baya cikin tsoro. Hatta fuskar shi facemask ne. Haka yasa dole suka watse da gudu suma. "Ka sake ka kuma bin inuwar ka sai ya yanke wuyar ka" ya wurga shi can yayi tafiyar shi. Wani shegen tsoro da kunya yasa shi suma. Shi kuwa wurin
atuwar Bike din shi ya hau ya tashe ta da wani jahilin gudu ya juya ya fice a makarantar. Yadda yake gudu zaka rantse garin Lagos zai bari, yana isa unguwar kafin ya isa gidan shi, an bude kofar. Shiga yayi ya cire facemask din shi ya je da niyyar fansa, jahilin yaron nan ya riko hannunta. Ko kashe Bike din bai yi ba ya sauka ya wuce cikin gidan. Shi dayan shi ya shiga naushi da kwallo da kayan da suke falon. (Dan banza me egen tabara " sai da ya gama barnar shi ya wuce abin shi ya kwanta. Bai fito ba sai dare dan haka yana fitowa ya sa lallai a nimo mishi wani team da suke bada horo na musamman ga matasa, yana haurawa sama kuwa Mr Tanimu amintaccen Yaron shi. Ya shiga niman irin wannan office din, Washi gari kuwa sai ga shugaban
ungiyar. Yazo har gida domin al'amarin kudi na gwamna masu gidan rana, aka kawo mishi wasu kartin maza bodyguard ya mika musu hoton Hajnah. "24hrs idanun ku a kanta da motsinta. Idan ta kama hatta wanda zai kusance ku san waye. " "Ok sir" daga haka ya juya ya bar falon, wani karamin jaka Mr Tanimu ya mikawa ogan su, ya fita yana godiya. Ya cire musu wani abu, sannan suka shiga binciken inda take gidansu makarantar su. Da kawayenta.
Ita bata sani ba, AJ yana can yana shirin kafa mata tsiya. Tunda ta koma gida bki daya abin ya ki barin kanta, "Hajnah waye mutumin da ya karya hannun Rafiq?" "Wallahi ban sani ba" ta fada kamar zata yi kuka."Gaskiya abin da ban tsoro" inji Kamnah, "bari wallahi sai da naji kamar zan yi fitsari. " Haka suka kwanta da abin a ransu. Washi gari a cikin makarantar sai kallon su ake al'amarin yana shirin zafaffa. Har hall aka zo kiran ta, haka ta fita ta je office din shugaban makarantar ga Abeey ga mahaifin Rafiq. "Halimah Sheikh waye kika kira ya karya hannun shi?" "Sir ban san shi ba, nima ganin shi nayi kawai na rantse da Allah" shiru Office din yayi Rafiq yana son magana amma tsoro ya hana shi magana, domin ko
azun AJ yazo har dakin da yake da shigar likita ya ce mishi. "Ka sake bakinka yayi magana sai na maka Alluran da ba zaka kuma moruwa ba, kana da wani issues ne a makarantar ne?" Ya ce "A'a sir" "tow kar na kuma ganin ka idan ba haka ba,
walwar ka da kake dura mata kwaya zan birkita yadda ba zaka tab'a farin ciki ba har abada ka fahimci ne, kuma ka bata hakuri na gaya maka." Kamar wanda ya ya farka daga barci ya zube a gaban Hajnah "don Allah ki yafe min daga yau ba zan kuma shigowa ba, ina rokon ki da Allah ki yafe min " baki daya sai ta shiga rud'ani kafin tayi magana Ya ce musu. "Ni na tsokano shi, nayi mishi sata ne, shi ne ya biyo NI yaga ina rashin da'a ga mace ya hukunta ni daga yau ba zan kuma zuwa nan ba ayi hakuri a yafe min... *Wuya kashin kota*
#Mai_Dambu
[2/26, 7:24 PM] MINISTAN SHARHOLIYA: https://www.wattpad.com/1318190644?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Mai_Dambu&wp_originator=tlX9murA8aOHPUMQF%2BX3szwBUbcfB2OZ7QdWaOSJo8YC52FiWCR11mCiq9NfX2c3LxAyvYWdLLzwNcpPdb68AgJ8fGB7fpjIYnTWrqz868MSvNlo2YCmgCNCyalA5ThH
TAMBARIN SHAHARA... (FREE BOOK)
Mafia Romance story.
*Mai_Dambu*