← Book details Matar Mustapha Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 28

Sashe 9

Matar Mustapha Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sosai SEEYA ta ci abincin,ta na ci su na hira ita da Kakarta wacce lokaci guda ta ji ta shiga ranta kuma ta sake da ita.
"Hajiya ki kira mini Yayana" SEEYA ta faɗa cike da yarinta.
"Wane Yayan ki?"
"Mustapha !" Ta bata amsa ,Hajiya ta yi dariya ta ce "ai banda lambar shi" SEEYA ta ɓata rai ta yi shiru,sam zuciyarta babu daɗi muryar Mustapha kawai ta ke son ji sai dai babu hali.

A ɓangaren Mustapha kuwa ya na fita direct gidan mota ya nufa,ya yanki tikiti.Ya kuma yi sa'a akwai motar da za ta tashi,Zinder suka fara tsayawa kafin su ci gaba da tafiya.
Kwanan shi biyu a hanya kafin ya isa Tilliya.

"Idona ke mini gizau ko dai gaske Mustapha soja nake gani?" Umar ya yi tambayar ya na mitsike ido.
Wata bangaza Mustapha ya yi masa ya ce "ban hanya na wuce in ka gama shirmen sai ka same ni" da sauri Umar ya sha gaban shi ya ce "don Allah kar ka shiga na kawo wata Baby ne"
Mustapha ya tsaya cak ya na kallon shi,Umar ya ɗan shafa gefen wuyansa ya ce "yi haƙuri yanzu zan sallame ta ba jimawa za mu yi ba" ya na gama faɗa ya shige ɗakin haɗi da dantse ƙofar.

Mustapha ya haɗiye wasu yawun takaici kafin ya gyara tsayuwa ƙiƙam ya na sauraren duk abin suke wanda hakan ya jefa shi cikin wani halin.Sai yanzu yake takaicin fushin da ya yi ya baro SEEYA ,ya bugi ƙofar da ƙarfi ya na duka cikin iska.

Tsawon lokaci kafin Umar ya buɗe ƙofar,wata ƴar matashiyar budurwa ta fito sai faman gyara hullar gashin doki take.Tsabar haushi Mustapha bai san lokacin da ya kai mata wani kutufo ba,ta saki ƙara haɗi da rugawa da gudu.
Umar ya ce "Ni ya kamata ka daka ba ita ba,tun da ni na kawo ta"
"Ja bani wuri na wuce" ya faɗa cikin muryarsa ta basawa,Umar ya taɓe baki kafin ya ɗan ja baya.

Mustapha ya shiga ɗaki ya ajiye jakar shi sannan ya faɗa toilet,shower ya sakar ma kansa idonsa na hango masa Baby SEEYA .Wata irin kewarta ya ke ji kamar zai mutu,gefe guda kuma buƙatuwar shi na sake bijiro mishi .Ba don ya san illar masturbation ba to da babu abin da zai hana shi aikata hakan,ya yi saurin kawar da tunanin gefe ya fito ya na shaye jikinsa da ƙaramin towel.

"Ga abinci nan na kawo maka"Umar ya faɗa ya na mai zama bakin gadon shi.Ci kan ka Mustapha bai ce ba har ya gama kimtsawa zai fita Umar ya yi saurin tashi ya na cewa "don Allah ka yi haƙuri ba zan sake ba" ya faɗa ya na mai riƙo hannun shi.

Mustapha ya ce "sake mini hannu zan fita"
"Zuwa ina? Yanzu fa ka zo ka na buƙatar hutawa"
"Na yi da kai na gaji? Dallah malam cika ni" ya yi maganar cikin ɗaga murya haɗi da fizge hannun shi.

Umar ya ƙara shan gaban shi ya ce "haba dogon namiji angon SEEYA yi haƙuri mana" ambaton sunanta ya saka shi jin wani sanyi ya ratsa shi,ya ja ajiyar zuciya ya ce " Umar amma dai ka san wannan abin da ka ke yi bai dace ba ko? Yanzu in ƙanwar ka ce aka yi ma haka za ka ji daɗi?" Ya girgiza kai ya ce "a'a ba zan ji daɗi ba gaskiya, ka yi haƙuri na yi ma alƙawari daga yau ban sake wa"
Mustapha ya ɗan ture shi cikin wasa ya ce "dallah can kullum ai haka ka ke faɗa,amma bai hana gobe ka rakito wata"
Umar ya sheƙe da dariya ya ce "don Allah ni dai zo ka ci abinci ka bani labarin SEEYA ,ya aka yi ba ka zo da ita ba?" Mustapha ya je ya zauna ya fara cin abincin, sannan ya fara baiwa Umar labarin komi.

"Madallah tun da ta fara jinin al'ada yanzu za ka ga ta fara haɓaka kamar fulawa,ka san da zarar mata sun fara wannan abu shike nan za su fara girma kamar gingiya"

"Mtsw! Matsalata da kai kenan kai komi ka sani akan Mace ,wlh matar ka ta shiga uku har na fara tausayinta" Mustapha ya faɗa ya na kai loma baki .
"Hhhh! Wlh SEEYA ce abar tausayi,yi tunani fa ta na ƙwailarta duk ka susuce ina da ta girma? Kuma ga shi ba ka taɓa wannan lamari ba.Cabbb za mu sha kallo,wa ya ga Mustapha da SEEYA a ɗaki guda hhh tsiya na san da safe sai na je na yi mata allura"
Mustapha ya kai masa duka a baya ya na cewa "mugu! Wa zai kira ka? Ni? Tabbb! Allah ya tsare ni da yin shubka a gaban idon maƙiyi"

"Ni ne maƙiyin ?"
"Ah to saboda Allah Umar in na kira ka don yi ma SEEYA allura ai na shiga tara ba uku ba,na san har sai ta yi haihuwar farko ba ka bar mini iskanci ba"

"A'a abokina ba zan yi ba! Sai dai fa ina shaida ma muddin ka jima ƴar mutane ciwo bayan na ɗinke ta zan mayar da ita gun Inna ne"
Mustapha ya ɗauki kofi ya buga masa ya ce "lalle ba ka da kunya matar tawa za ka yi ma ɗinki?"
"Mi ya ke? Ai matar aboki matar ka ce..." Da sauri Mustapha ya ce "ba da ni za a yi wannan iskanci ba ka ji,mu canza hira kar ka sa zuciyata ta hau na buge ka"
"Hhh! Sarkin ƴan kishi! To yanzu ita Seeyar na can Gidan Rumji?"
Sai da ya ja wani numfashi sannan ya bashi amsa da"eh ta na can tun ranar da na baro gidan"
"Fatan dai ka faɗa ma su Hashim komi kafin ka tafo?"
"Eh na shaida masu,don shi ya gaya mini ma an kai SEEYA"
"To madallah bari na je can cikin compagnie na dawo" Umar ya faɗa ya na tashi.
Mustapha ya ce "to kar dai ka gaya ma Oga zuwana"
"Kawai haka nan sai na faɗa masa?"
"Eh don na san ka da mugun ɗumi abin da ba a tambaye ka ba ma faɗi ka ke,in ka fara zuba kamar ƴaƴan kanya"

"Na dai ji ! Ai an fi son mutum wayayye ba baƙauye ba kullum fuska a murtuƙe" Umar ya faɗa ya na mai ficewa, Mustapha ya yi murmushi kawai.

★Sati guda cicif da zuwan SEEYA gidan.A wannan ƴan kwanakin ta fahimci kowa na gidan,Rahamu ita ce babba sai kuma mai bi mata Aminu wanda ke da mata uku da ƴaƴa barkatai.Tun daga matan har Ƴaƴansu babu mai son SEEYA,wanda ƙiyayyar ta samo asali ne daga uba mahaifi gare ta Lawali wanda ya kasance Autan Hajiya a yanzu tun bayan rasuwar ƙanen shi.

SEEYA na wanke kwanuka ya shigo,murya na ɗan rawa ta ce "ina wuni Ya Abdul?" Bai amsa ba sai mugun kallo da ya jefe ta da shi ya wuce ɗakin mahaifiyar shi.
Idonta ya ciko da ƙwalla,Allah na gani sam zaman gidan ya ishe ta.
Murya Baba Malam ta ji,da sauri ta miƙe cike da murna ta tarbe shi.
Har cikin ɗakin Hajiya Habsu suka shiga,bayan sun zauna ne Baba Malam ke cewa "dama takardun SEEYA ne,tun da a nan za ta ci gaba da zama shi ne na kawo sai ayi mata gyara ta ci gaba da yin karatu a nan"

Gaban SEEYA ya faɗi,ita da ke tunanin in zai koma ya tafi da ita amma ya kawo zancen zamanta a nan na dindindin.
Shaaa hawaye suka zubo mata "Baba ni ban san kowa ba a nan" ta faɗa kuka na kubce mata, Baba Malam ya yi murmushi ya ce "da sannu duk za ki san su"

Aminu Hajiya ta baiwa takardun ya je ya kai makaranta,kwana biyu da yin haka SEEYA ta fara zuwa makarantar wacce ta kasance ta gwamnati.
Can ƙarshen aji ta zauna ta wani rakuɓe,sautin murya ta ji an ce "sannu ƴan mata" ta ɗago ta kalli mai maganar.Matashiyar budurwa ce ƴar kimanin shekaru goma sha biyar.
Ta ci gaba da cewa" sunana Maimunatu ke fa?" Ta bata amsa da "Shamseeya amma ana ce mini SEEYA"
"Waooo! Suna mai daɗi,kin ga taso mu koma can gaba ya fi" ba tare da ta musa ba ta tashi.

Maimunatu irin yaran nan ne masu shegen wayo da kuma rawa kai, sannan ba ta da wuya sabo wannan ya saka ta yi ta ba SEEYA labari har ta saki jiki da ita.
Ashe unguwar su guda,kawai dai da ƴar tazara ne tsakani.Bayan sun taso daga makaranta su ka kamo hanya su na tafe su na hira har aka kawo gidan su Hajiya , SEEYA ta ce "kin ga gidan mu nan" Maimunatu ta ce "ok to in an jima zan zo na kawo miki goron aurena na manta ban faɗa miki ba an kusa bikina" SEEYA ta waro ido da mamaki can kuma ta ɗan yi tsallen murna wanda ya sa har hijabinta ɗagewa sama,Abdul da ke bakin ƙofa ya ce "kam bala'i dube mini yarinya da manyan mazaunai" har wani lashe baki yake.
SEEYA ta zo wucewa ya tare hanya haɗi da game girar ƙasa da ta bisa.....
[10/11 08:51] MRS SADAUKI: *MATAR MUSTAPHA*
LOVE STORY

```MRS SADAUKI```💫 ✍️

DEDICATED to MY SADAUKI🫡

FCWA ☀️
_________

*Ku yi following channel ɗina domin samun book ɗin nan daga farko dama wasu littattafai*
9

Abdul ya ƙanƙance ido ya na kallon SEEYA wacce tuni jikinta ya ɗau rawa don ba ƙaramin mugun tsoron shi take ba.
Har zai kai hannu jikinta ko mi ya tuna? Oho! Kawai sai ya saki murmushi ya bata hanya ta wuce.
Ita kanta ta yi mamaki,har sai da ta waiwayo shi ta ga har yanzu bai ɗauke idonsa a kanta ba.Ta na shiga ɗaki ta ajiye bag ɗin ta,Hajiya ta ce "ƴan makaranta a zo a bani labarin yadda ranar farkon ki ta kasance" SEEYA ta yi murmushi ta ce "komi daidai har na yi Ƙawa Maimunatu,ta na da kirki sosai sannan ƴar nan unguwar ce can gaba kaɗan da nan"
Chapter 9 · 0% Book details