← Book details Matar Mustapha Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 28

Sashe 17

Matar Mustapha Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sake da baki Abba ke kallona kafin ya ce “wane irin sassan jiki kuma? Ciwon ciki ne fa ya kashe shi ko?”

Ni ma da mamakin na dube shi,kafin na yi wa kaina tambayar ‘ kenan shi Abba bai ga gawar Joy an cire mata ido ba?’ amma don sake tabbatarwa haka na buƙaci mu koma can mutuware.

Da muka je muka shiga ciki na buɗe gawar Joy tare da tsure Abba da ido kafin na ce “ka gani ko?”

“Me?” ya tambaye ni,“ba ka ga komai ba?” na tambaye shi ni ma.Ya ce “ka ga David mu je gida” ba tare da na ce komai ba na rufe gawar muka fito.Ko da muka dawo gida mun tarar da Joyel na yin kuka kamar ranta zai fita ,tana ganina ta zo ta faɗa jikina.Ban iya rarrashinta ba kawai na bar ta tana ta yin kukan har ta gaji don kanta ta je ta zube kan tabarma.Mutane sai shigowa suke yi suna taya mu jaje har cikin dare kuwa,sai da daren ya tsananta sannan ƙafa ta ɗaga.Na je na rufe ɗaki tare da shiga ɗakinsu Ummah na yi zaune kamar yadda su ma ɗin suke zaune in aka cire Joyel da ke bacci.

So nake mu haɗa ido da Ummah amma ta ƙi yarda da hakan,da na gaji don kaina na miƙe na fita.Sai da na watsa ruwa na ɗan ji sanyi kafin na shige ɗakina,bayan na rufe ƙofa na ɗauko littafin sirri na ajiye kan table.

A hankali ya soma buɗe kansa har aka zo a page ɗin da na tsaya,idona ya sauka kan rubutun da ya shafi nasabata.

“BABU WANDA ZAI IYA MALLAKAR LITTAFIN NAN SAI SARKI KO KUMA MAI SHIRIN ZAMA SARKI! DOMIN SANIN DALILI KA BUƊE PAGE TA GABA” shi ne abin da yake a rubuce, wannan karon da kaina na buɗe page ɗin ta gaba sai dai wayam take babu rubutun komai a cikinta haushi na ji kawai na rufe shi na mayar.

Na ja tsuki kafin na kwanta ina shirin lumshe idona na soma jin yanayin iskan ɗakin na canzawa.A nan take na fahimci ta zo,babu jimawa kuwa na soma jin ana shafar jikina tare da sarrafa ni kafin ta mu'amulance ni bayan nan sai na ji wata irin gajiya da ciwon jiki amma ban iya ko da motsi ba ne a haka bacci ya ɗauke ni.

Wannan karon a wata unguwar nakassu duniyar mafarkin tawa ta kai ni,ko ta ina makafi ne da kurame da guragu da duk wata irin nakasa.Cike da ƙyanƙyami nake ratsa wurin wanda yake cike da datti da ƙanzata iri-iri,daga bayana na ji an dafa ni.Na juyo da sauri nan na yi arba da wata yarinya wacce ba za ta wuce shekara goma ba a duniya ,fara ce tasss ban taɓa ganin mutum mai irin farinta ba.Gashin kanta kuma wani iri ne kamar na gingiya,idanuwanta blue ne masu ɗan girma duk da kuwa yadda take ta ƙoƙarin ƙanƙantar da su,laɓanta jajaye ne sirara.

“Ina ne nan?” na tambaye ta.

“Daular Alfanso !” ta bani amsa tare da miƙo mini wani ɗan itaciya wanda shi ma ban taɓa ganinsa ba,hannunta na bi da kallo wanda yake da datti duk laka ta ɓata shi .Na girgiza mata kai na ce “a'a ban ci”

“Ka karɓa dai za ka ji daɗinsa” ta faɗa tana yi mini dariya wacce ta bank damar ganin haƙoranta waɗanda suka sha banban da na mutane don kuwa ba farare ba ne a'a kamar chocolat haka suke da duhu amma wani abin mamaki sosai suka yi mata kyau ƙila don saboda kalar fatarta.Na kai hannu kenan zan karɓa na ji muryar Ummah “Davido?” kamar tsawa haka na ji sautin,da mugun sauri na tashi ina ware ido a kallon farko sai na ga Ummah da wata siffa kanta kamar na Tinkiya amma da na murje idona sai na ga ta dawo normal.

Kafin na kai ga cewa wani abu ta ce “ka tashi ka yi mini rakiya can mutuware ina son ganin gawar ɗana kafin a rufe shi”

Na ce “an samo kuɗin bikin jana'izar ne? ”

“Ka same ni a ƙofar gida” ta faɗa tare da ficewa,a dole na fita na yi wanka na zo na shirya.Sai da na shiga ɗakinsu,a zaune na hango Joyel ta rakuɓe kamar wata marainiya,tausayinta ne na ji ya ratsa ni amma ban iya yi mata magana ba na fice na samu Ummah a ƙofar gida.Gaishe ta na yi amma ba ta amsa ba,taxi na samo mana muka shiga.Har muka isa babu wanda ya yi magana,sai da na nuna takardar shaida sannan aka buɗe mana mutuwaren.Wani irin iska ne mai haɗe da hucin ruhika ya tarbe mu,da sauri muka kalli juna ni da Ummah kafin kuma mu ida shiga.

Gawar Joy na nuna mata,ta buɗe tana shafar fuskarsa.A yanayinta kawai na fahimci ita idonta suna gane mata abin da ni ma na gani a tattare da gawar saɓanin Abba.

“Je ka biya kuɗin wanka a zo a yi masa mu wuce da shi,ba zan bari ya ƙara kwana ɗaya ba a nan” Ummah ta faɗa .

Na ce “akwatin gawa fa? Ina za a samu?”

“Ka yi abin da na ce” ta faɗa cikin ƙaraji,wani irin tsoron Ummah ne na ji ya ɗarsar mini a ƙahon zuciya wanda ban taɓa jin makamancinsa ba,da sauri kuwa na je na nemi mai gadi na sanar da shi tare kuma da biyan kuɗi.

Wani matashin saurayi ne aka turo domin yi masa wankan,Ummah ta fita yayin da ni kuma na tsaya.Almakashi yasa ya yage suturar Joy sannan ya luluɓa masa wani zanen,ya ɗago da niyyar yi mini magana sai kuma na ga ya yi shiru tare da kafe ni da ido har sai da na tsargu na ce “Me?”

“Babu komai! Ammm.. na ce ka taɓa ganin an yi wankan gawa irin wannan ko kuwa yau ne farko?” ya faɗa .

Na ce “ban gane irin wannan ba?”

Sai da ya sake dubana da kyau kafin ya ce “kar ka nuna kamar ba ka san abin da nake nufi ba, alhalin ga alamun baiwar da ke tattare da kai nan a bayyane”

Na ja ajiyar zuciya don na fahimci abin da yake nufi, wannan yasa na basa amsar tambayar tasa na ce “yau ne farko”

Ina faɗar haka sai ya miƙo mini auduga ya ce “ka cusa wannan a ƙofofin hancinka ” na dube shi har zan yi tambaya amma kuma sai na karɓa tare da yin yadda ya ce ɗin ,yana fara zuba ruwa a gawar Joy sai na ga gawar ta yi motsi.Murya na ɗan rawa na ce “kamar fa ya motsa” ya ce “ba kama ba ce motsin ne ya yi” sai kuma ya ci gaba da yin wankan,can sai ga gawar Joy ta tashi zaune kan ƙugunsa.Matashin sai ya ciro wani abu daga aljihunsa ya shayar da Joy,nan take sai ya soma aman wani baƙin abu ana cikin haka sai kuwa wasu baƙaƙen inuwoyi suka fara bayyana a cikin gidan gawar.....
[10/11 19:33] MRS SADAUKI: *INUWAR ALJAN*👻

```LoVe aNd HoRrOr story```👽

By
Chamsiya Laouali Rabo
{MRS SADAUKI💫✍️}

*SADAUKARWA:* Ga Rachida Mamar ƴan biyu, alherin Allah ya luluɓe ki . Ubangijin rahama ya kula da lamurranki👏🏻

*FCWA*☀️

________________________

03

Yadda baƙaƙen inuwoyin suka zagaye wurin shi ya haifar da dissashewar ƙwan lantarkin mutuwaren.A daidai wannan lokacin ne matashin mai wankan gawa wanda har zuwa yanzu ban san sunansa ba ya soma yin magana.

“Kar ku yi kuskuren taɓa patient ɗina,kun yi naku aikin kun kashe shi yanzu kuma ku bari na yi nawa aikin” ya faɗa cikin muryar gargaɗi.Sai kuma na ga duk sun nutsu sun bar motsi,wani abu ya ƙara cirowa daga aljihu ya shafa a goshin Joy nan take gurbin idonsa wanda babu komai a ciki ya soma ɓulɓulowa da jini can sai ga dukkan idanuwansa biyu sun dawo.Kamar yadda mutum mai rai ke kallo haka Joy ya dube ni da idonsa kafin ya yi baya ya kwanta ya lumshe ido,gefen wuyansa wanda yake a ɓurme nan ma sai da ya zuba maganin da ban san na mine ne ba shi ma ya dawo daidai .

Inuwoyin da suka kawo mana caffa? Tuni sun ɓace kamar walƙiya.Na ja ajiyar zuciya na dubi matashin na ce “kana da baiwa ! Haifarka aka yi da ita ?”

“Sunana Nelson ɗa ga Sarkin yaƙin Daular Uganda ” ya bani amsar da ba ita na tambaye shi ba yana mai ci gaba da gyara gawar Joy har ya kammala.

Ƙofa aka buɗe,mai gadi ne da wani suka shigo suka kawo akwatin gawa sai muka haɗu mu duka huɗun muka saka gawar a ciki. Tare da fito da ita aka saka a mota,Ummah na duba sai na ga tana kallon Nelson na ɗan matsa kusa da ita na ce “ko kin san shi ne?”

“Mutane na can gida suna jiranmu mu je” shi ne abin da ta faɗa tare da yin gaba,na juya na kalli Nelson wanda shi ma na ga yana kallon Ummah wani iri.Na ce “na gode ” ya jinjina kai.Sai na wuce na shiga mota,kusa da ita na zauna kafin na ce “a ina kika samu kuɗi?”

Ko kallona ba ta yi ba,a haka muka ƙarasa gida.Tun da muka shigo layinmu na soma jin ƙarar sautin ganguna ana kiɗe-kiɗe,muna isa aka zo aka sauke gawa aka ajiye ta a wurin da aka yi mata tanadi aka ci gaba da yin kiɗa da rawa da waƙe-waƙe.

Hannuwana na harɗe ina kallon akwatin da ke ɗauke da Joy,duk wasu tsoffin moments ɗinmu ne suka ta kawowa ƙwaƙwalwata ziyara ina tuna yadda yake mugun sona da girmama ni.Wasu hawaye masu ɗumi ne suka zubo mini,daga bayana na ji muryar Isa yana cewa “David ashe rasuwa ƙanenmu ya yi? To Allah ya jiƙansa ya yi masa gafara,yanzun nan muka dawo daga wurin interview tun jiya da muka tafi”
Na ida juyowa ina kallonsu,tsabar yadda hankalina ya ɗan gushe sam ban san mene ne shi Abdul ke faɗa ba kawai dai na ga bakinsa na yin motsi.
Chapter 17 · 0% Book details