← Book details Matar Mustapha Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 28

Sashe 27

Matar Mustapha Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Idon Dadda suna fitar da wasu ruwan hawaye ta ce “asalinki shalele zo mu je” sai ta ƙara janta suka fara ratsa ruwan har suka je tsakiya .Wasu mata ne suka fara yin da'ira suna fitowa daga ƙasan ruwan suna zagaye su.

A tsorace IZZATU ta riƙe Dadda gam,ɗaya daga cikin matan ce ta matso tana cewa “kar ki ji tsoro ƴata,ba ki zo nan don a cutar da ke ba sai don nuna miki hanyar da ya kamata ki ɗauka sannan kuma mu buɗe miki taurarinki” sai ta kamo hannun Izzatun nan take ruwan suka yi wani irin juyawa kamar walƙiya suna fitar da wani irin sautin wuluuuk.Jiri ne ya soma ɗibar ta,ganinta ya dinga dissashewa , kunnuwanta suka fara jiyo mata waƙe-waƙen kwaɗo,wani ɓangaren kuma dariyar mutane ce ke fitowa daga can nesa da su garwaye da maganganun wasu mutanen daban suna magana kamar a lokaci guda.Can kuma komai ya tsaya cak,tunaninta ya yi duhu,igiyar da ke saita numfashinta ta katse.Ba ta ƙara sanin abin da ya faru ba sai tashi ta yi ta ganta kwance a kan gadonta wanda aka yi masa ƙawa da manyan kyandir sun zagaye shi suna ci da wuta.Izzatu ta yunƙura za ta miƙe ta ji wani abu mai taushi da santsi a cikin tafin hannunta,tana buɗewa ta ga wani jibgegen Kwaɗo ne kore sharrr da shi ya zubo mata manyan idonsa....

*Da zarar na saki last free page shikenan book ya dawo 500 ,don haka wanda ke buƙatar discount ya yi niyya ya yi payment 300 Via* 2670215530
ZULFAU YAHAYA
Ecobank DM +27795045822

🚫Ga détail nan na bada Please ki tura kawai kai tsaye ki bani shaidar biya ta WhatsApp, yan Nijar carte Moov ko airtel ta 300f
[10/11 19:33] MRS SADAUKI: *INUWAR ALJAN*👻

```LoVe aNd HoRrOr story```👽

By
Chamsiya Laouali Rabo
{MRS SADAUKI💫✍️}

*SADAUKARWA:* Ga Rachida Mamar ƴan biyu, alherin Allah ya luluɓe ki . Ubangijin rahama ya kula da lamurranki👏🏻

*FCWA*☀️

________________________

10

Wani irin matsanancin dokawa ƙirjinta ya yi,kamar kuma wacce aka yi wa dole ta ƙi jefar da Kwaɗon sai ma kallonsa da take yi ita ma kamar yadda ya zuba mata manyan idonsa.

“Barka da safiya Queen!” ta ji wata siririyar murya irin ta maza,bakinsa ta ƙure da duba sai ta fahimci yana motsi kuma daga nan ne maganar ta fito.

“Kar ki ji tsoro ni ne abokin ɗebe miki kewa ” ya sake faɗa .

Ba tare da ta buɗe baki ba ta jefo masa tambaya ta idonta na tsakiyar goshi “wane ne kai? Mene ne haɗina da kai? Mafarki nake yi ko gaske?”

Tana gama jero tambayoyin ya yi tsul ya sauka daga cikin tafin hannunta ya sauka kan ƙirjinta,kamar wani mutum haka ya ɗora tannuwansa kan haɓarta kafin ya ce “na kasance tsawon ƙarni biyu da wasu ƴan shekaru ina wanzuwa a wannan doron duniyar ta bil'adama,ba don komai ba sai don yi wa masu jinin prophecy jagora zuwa tsoffin asirai da wasu ɗaiɗaikun musulmi suka yi amfani da su waɗanda suka sha banban da sauran waɗanda ki ka sani.Ba mafarki ki ke yi ba,a zahiri ne ki ke tare da protector ɗinki,babbar alaƙata da ke ita ce jagora” yana gama faɗar haka ya wani turo bakinsa gaba sannan ya tsirta mata yawunsa masu yauƙi,da wani mugun sauri ta rufe ido tana mai yin wata irin ƙara saboda zafi da raɗaɗin abin da ta ji ya game mata fuskar kamar wuta. A hankali fuskarta ta soma canza launi tana rikiɗa zuwa kore kamar dai jikin kwaɗo,tsawon lokaci kafin ta dawo normal .

Ta buɗe idonta tana mai jan numfashin wahala kafin ta tashi zaune, wannan karon kuma cike da murna ta ɗauko Kwaɗon ta ɗora a tafin hannunta kiss ta yi masa a goshi kafin ta sauka ta ɗauko ƴar ƙaramar jakarta wacce a duk inda za ta je tana maƙale da abarta a ciki ta jefa shi kafin ta shiga wanka.Sai bayan ta fito ta yi sallah tana tsaka da shirya wa Dadda ta shigo hannunta riƙe da ganyen bishiyar floris.

“Daga ina haka tun da safe?” Izzatu ta tambaya tana mai saka doguwar riga.
Dadda ta ce “ke ya kamata na tambaya ina zuwa da farar safiya?”

“Na warware zan koma bakin aikina,saura ke ki faɗa mini ina ki ka je?”

Dadda ta ɗan ja baki kafin ta ce “dajin tsira na je,ungo wannan itaciyar sirri ce ki dinga tafasa ta kina zuba ruwan a cikin shayin Yarima ”

Wani kallo Izzatu ta soma yi mata,Dadda ta dungure mata kai ta ce “yana da muhimmancin ne a rayuwarsa kin ga ke ma in kina so za ki iya sha”

Izzatu ta turo baki kafin a shagwaɓe ta ce “shi ne tun can ba ki taɓa bani ba sai yanzu da Yarima ya zo? To na ƙi na sha ɗin shi kaɗai zan saka ma tun da kin fi sonsa fiye da ni ”

Dadda ta yi ɗan murmushi kafin ta ce “haba shalelena!” Izzatu ta mayar mata da martani kafin ta fice,tana tafe tana rangaji har ta isa sashen Yarima.

Falonsa ta soma sharewa ta goge ta saka turare sannan ta shiga kitchen ta soma haɗa masa breakfast kamar yadda aka ɗora mata nauyin dukkan abin da ya shafe shi.Tana aiki tana karatun Alkur'ani cikin taushin murya da daɗin amo.

★YARIMA

Bayan na gama bincike akan babyn littafin sirri ban samu komai ba haka na kwanta lamo ina tunanin abubuwan da suka ƙunshi rayuwata a haka bacci mai ya ɗauke ni ban shirya ba sai kuma na tsinci kaina a wata duniyar wacce ba ta bil'adama ba.

A gaban idona babyn littafin sirri ta fito ta daga cikin page ɗin ta zo ta yi tsaye a gabana,a hankali take daɗa girma har ta zama matashiyar budurwa sai dai baƙin dogon gashin kanta ya rufe mata fuska hakan ya hana ni ganin ainahin face ɗin nata .Wasu fitinanun kayan bacci ne a jikinta waɗanda suka fallasa ni'imar da baiwar da Allah ya zuba mata.Cikin abin da bai fi minti biyu ba casbin hankalina ya katse ,nutsuwata ta gushe jikina na ɗan rawa na jawo ta gare ni ta faɗo kan ƙirjina ina shirin yaye gashin gaban goshinta ɗakin ya ɗauki duhu sai hannuwanta da na ji suna yawo a duk illahirin jikina.Cike da tsimin abin da ban taɓa jinsa ba a siffar normal ni ma na dinga mayar mata da martani har ta kai na kusance ta.Ba wai iya cikin baccin ba ne na samu gamsuwa a'a har a zahiri ina jin daɗin mu'amulantar juna da muka yi.

Ina gama samun kaina na farka daga baccin,da baiwa Izzatu na ci karo ta juya kenan za ta fita da sauri duk illahirin jikinta kuma rawa yake.Da na dubi jikina sai na ga ko albarkar blanket ɗin rufa babu,ƙila kuma ta ga yanayina ya canza ne a yayin da nake bacci.Ko kaɗan ban yi ƙoƙarin tsayar da ita ba,tana fita na miƙe cike da ƙyanƙyami ina jan tsuki na shiga toilet na cire kayan jikina na yi wanka na ɗauro towel na fito.

Gaban makeken madubina na yi tsaye wanda aka cika da mayukan gyaran fata da Kuma turaruruka.Ina tsane jikina ina kuma kallon siffata ta madubin,duk da ina baƙi amma ina da kyau da kuma nagartar da duk wata ƴa mace za ta so mijinta ya kasance da ita.Amma duk da haka wani irin tsoro ne nake ji kar na je wa da EZRA da buƙatata amma ta watsa mini ƙasa a ido duba da yadda na hango zallar ƙiyayyata a ƙwayar idonta.Na ja dogon numfashi kafin na soma shafa mai da turare,bayan na gama na je gaban drower na zaɓi kayan da zan saka da kaina saɓanin kullum baiwa Izzatu ce ke fitar mini da su.Ina gama kimtsawa na fita falo,can rakuɓe jikin kitchen na hange ta tana magana ita ɗaya don babu kowa kusa da ita.Ba tare da na ɗauke idona a kanta ba na je na yi zaune,sai kuma a lokacin ta farga da wanzuwata.Ta sunne kai ƙasa kafin ta fara takowa inda nake,ta ɗan tsaya nesa da ni kaɗan kafin ta ce “barka da fitowa ranka shi daɗe ”

“Sunana David in kuma ba za ki iya faɗa ba kawai ki ce Yarima ” na faɗa ina mai kallon yatsun ƙafafuwanta,wani irin yarrr na ji sakamakon ganin wani sirri a tattare da baiwa wanda ba kowacce mace ke da shi ba.

“To yallaɓai!” ta furta tare da juyawa ta shiga kitchen na bi bayanta da kallo a zuci ina cewa ‘bawan da zai samu wannan baiwar ya ji daɗinsa ya samu macen zinare ’

Ba ta wani jima ba ta fito hannunta riƙe da babban faranti,akan table ɗin gabana ta dire shi kafin ta soma haɗa mini shayi mai kyau sai dai aka samu akasi wajen rawar jikinta shayin ya zube mini a ƙirji.Ido kawai na rumtse yayin da kuma nake jin shashekar kukanta haɗi da hannunta yana goge mini rigar.

Cikin kiɗima da tsantsar tashin hankali take cewa “yi haƙuri don Allah, wallahi ba da niyya na yi ba.Hankalina ne ba ya jikina amma na yi maka alƙawarin ba zan sake aikata wannan kuskuren ba,don Allah kar ka hukunta ni ”

Ba tare da na buɗe idona ba na ji wani sashe na zuciyata na bani wata shawara da ta dace da halin da nake ciki ,ba tare da wani dogon tunani ba na buɗe ido ina mai haɗe rai na yi mata wata uwar tsawa wacce ta saka ta yin baya ta faɗi ƙasa kanta ya bugu a jikin table nan take kuma jini ya soma yi mata zuba.

Ba tare da ɓata lokaci ba ta ɓare baki ta shiga yin kuka,wanda zan ce shi ne raunina a game da ita don duk lokacin da na ganta cikin yanayin nan tana tuna mini ne da Joyel.

A hankali na sauko na soma ƙoƙarin tsaya da jinin ,sai dai ɗan kusanci da na samu da ita yasa na soma jin wata irin kasala na rufe ni.Na ɗan ja baya kaɗan na ce “je ki toilet ki wanke kayanki duk sun ɓace da jini,ki kuma wanke jikinki ”
Chapter 27 · 0% Book details