Sashe 15
Matar Mustapha Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Da turanci suka gaishe ni na amsa musu ni ma da turancin,Joy ya ci gaba da yin magana don yana ɗaya daga cikin abin da yake yi mini wani sa'in yayi mini magana da turanci kasancewar tawa makarantar ba ta yi nisa ba na fita.Amma wani abin mamaki sai na samu kaina da iya turancin, Joy ya ce “amma Yaya ya aka yi ka iya turanci haka?” shiru na yi ina kallonsa,ni ma ban sani ba amma sai na share na miƙa musu kuɗin da za su ci abinci na fice.
Direct inda muke haɗuwa ni da abokaina na tafi,duk sun hallara kuwa da alamu ni suke jira.Hannu na basu duk muka gaisa kafin na samu wuri na zauna a daidai tsakiyarsu wanda kuma kusan kullum muddin za mu haɗu ni a tsakiya nake zama ,in suna son tsokanata suna cewa ni ne shugabansu.
“Yau dai in mun tafi aiki sai dare na dawo saboda ina son kuɗi sosai zan fara tara kuɗin aurena ” Isa ya faɗa yana wani jan gemu.
Abdul ya karɓe da “ai kuwa kamar ka shiga zuciyata ni ma haka na yi tunani ya kamata a ce mun fara tara kuɗin aure tun yanzu kafin ƙarshen shekara ta zo tun da layi ya kawo kanmu”
Isa ya ce “a'a yanzu fa layinsu David ne masu shekara ashirin da biyar”
“To ai ba wani girme mana ya yi ba kawai ƴan watanni ne”
Da na ga za su ɓata mini lokaci na miƙe na tsaye na ce “ko za mu iya tafiya?” duk suka miƙe suna dariya kafin mu tafi can wurin aikinmu na dako.A nan ɗin ma wani abin mamaki ya faru da ni,a yayin da abokaina ke ta aiki tuƙuru don samun kuɗi masu yawa ni kuma kamar wani shashasha haka na samu wani lungu na ɓingire ina bacci wanda ban san dalili ba.Sai yamma lis na farka,duk wata kasala ce nake ji ta rufe ni amma a haka na samu ruwa na wanke fuskata.
“Ina ka tafi tun ɗazu?” Isa ne ya yi mini tambayar ,yayin da kuma Abdul ke tsaye yana kallona.Dakyar na buɗe baki na ce “ina can kwance ina bacci tun safe”
“Amma kuma babu inda ba mu duba ba kuma har can ɗin mun je ba mu ganka ba” cewar Abdul yana mai ci gaba da tsure ni da ido .Shiru na yi don ban san taƙamaimai abin da zan ce ba,Isa ya ja ajiyar zuciya ya ce “tashi mu ƙarasa aikin to” haka na miƙe muka yi aikin a tare da aka zo raba kuɗi nasu sun ninka nawa biyar amma da yake abokan ƙwarai gare ni sai suka ƙara mini cikin nasu kafin mu koma.
Ina shiga gida da Ummah na fara cin karo,lissafin bashin da ta ciyo mini ta soma yi mini daga ƙarshe ta tara hannunta alamun na bata kuɗin.Hannu na saka aljihu na ciro dukkan kuɗin na miƙa mata,har zan tafi amma wani abu ya ja hankalina.Zanen kunamar da ke hannun Ummah na ga yana motsi har da wani buɗe baki kunamar take yi,cak na tsaya ina mai ci gaba da kallon zanen yayin da ita kuma Ummah ke ƙirga kuɗin.
“Lafiya me aka yi kake kallona?” ta tambaya,ba tare da na bata amsa ba na wuce ɗakina.Tsaye na yi bakin ƙofa na riƙe ƙugu tare da yi wa kaina tambaya “wai shin meke faruwa da ni ne? Ko na haukace ne? ” tamkar bugawar guduma haka na ji kunnuwana sun bada wani sauti duummm! Sai kuma na ji tamkar ana kiran sunana a wani wurin da ni kaina ban san ina ne ba.Kamar zararre haka na fito,a lokacin tuni gari ya ƙara yin duhu .Tafiya kawai nake yi ba tare da na san inda zan je ba,har yanzu kuma ina jin sautin nan na kamar ana kiran sunana.A haka na yi nisa sosai a tafiya har na iso cikin wani wuri mai ciyayi da kuma dogayen bishiyoyi,haka nake ratsa wa ta cikinsu ba tare da wani tunani ba a haka har na iso gaban wani kabari.Haske na ga yana ɓulɓulowa ta cikinsa,ina zube gwiwaina ƙasa muka samu contact da ƙasar wurin sai yanayin tafiyar kaɗawar iska ya canza,ƙamshi wurin ya ɗauki yanayin damshi kamar irin an yi ruwa an ɗauke.A kan kabarin wasu irin ƙananun baƙaƙen duwatsu ne a zube kamar shara,sai kuma wani farin kyandir daga tsakiya wanda ya fara ci da wuta da kansa,wani irin abu nake ji kamar ana fizgo ruhina tamkar dai akwai wani ɓoyayyen ruhi da ke jawo ni izuwa gare shi.Ba tare da tunanin komai ba na soma ture ƙasar kabarin ina buɗe shi,sama da minti talatin na ɗauka kafin yi nasarar buɗe shi duka.Wani ƙyalle ne na ci karo da shi a shimfiɗe a samansa wani ƙaton littafi ne akai,an yi masa cover da wata fatar dabba tamkar mai motsin rai,a ƙasa an yi wani rubutu wanda ba da Yaren da na taɓa ji ko gani ba ne,amma sai na ji rubutun da kansa yana yi mini magana.
Ina sa hannu na ɗauki littafin sai wani irin shock ya ziyarci yatsun hannuna suka fitar da wani hasken wuta irin kamar waya ta ƙone.Bishiyoyin da ke zagaye da ni ne suka soma yin wata irin rawa har kana jin suna kai wa juna karo,yayin da kuma wani huci wanda kana ji ba na bil'adama ba ne ya soma karo da juna yana fitar da wani iska da ya saka furanni faɗowa suna mutuwa murus.Page ɗin farko na buɗe,nan take na soma jin ana yi mini wankin ido na soma gane-gane ina ganin abubuwan da suka faru lokacin baya a cikin littafin tamkar an kunna tv.Abubuwa ne waɗanda hankali ba zai ɗauka ba,mata da maza suna bayar da jininsu domin ƙaddamar da yarjejeniyar a tsakaninsu da Aljanai ,lamarin da muke ta tunanin tatsuniya ce ashe gaske ne an yi su a ƙarnin baya .Littafin na riƙe a hannuna yayin da kuma kukan ƙananun yaran da aka sayar da ruhikansu ko kuma aka bayar da jininsu matsayin hadaya na ta kawowa dodon kunnena farmaki,gefe guda kuma dubban ahali ne tsundum cikin rayuwar ƙunci saboda tun kakanni da iyaye sun yi harƙalla da Aljanu a yanzu kuma suna biyan bashin ƙarfin ikon da aka basu.
Duk page ɗin da zan buɗa tana ɗauke da wani baƙin sirri da ya gabata.Na ga ahali da dama waɗanda suka yi ƙaurin suna a zube gaban baƙaƙen ruhikan da ido bai isa ya gani ba amma sun yi harƙalla da su don samun dauɗar duniya ko iko.Wata page ɗin kuma magana take yi kan ƙungiyoyin asiri waɗanda aka ƙulla ta hanyar jini da kuma sassan jikin ɗan Adam ,yayin da kuma wata ke magana kan mutanen da aka jefa wa ƙunci a zukata ta hanyar tsafi wasu kuma an haukata su ,yayin da wasu aka ɓatar da su daga duniyar bil'adama zuwa ta ruhaniya saboda sun gwada tonawa azzalumai asiri.
Numfashina ne na ji yana son ɗaukewa,littafin kamar yana son koyar da ni,ya canza tunanina,ko kuma ya gwada imanina.Ji na yi ruhina yana kimsa mini wasu kalamai,yana cika mini ƙwaƙwalwata da ilimin da aka yi hani,a kuma wannan lokacin ne na ji wani irin tsoro mai tsanani ya ya daskarar da ni,sai kuma idona suka ci karo da wani rubutun da aka yi da manyan harufa.
“DUK WANDA YA TAƁA WANNAN LITTAFI SHI NE SHAIDAR INUWARMU.WANDA YA KARANTA SHI KUMA YA ZAMA *INUWAR ALJAN*” kalmar ƙarshe ta inuwar aljan wacce rubutunta yake da jan jini na ƙara maimaita a zuci,sai kuma na fahimci cewa wannan littafi ba wai iya kundi ne mai ɗauke da sirri ba,a'a shi kansa yana rayuwa ne yana tattare da motsin rai.Yana ankare da ni tun tuni,ko kuma dai yana amayar da wani sirrina da nake ɗauke da shi tun tuni.Ji nake ana kallona,ana ankare da ni ana kuma gwada ni da kuma tsare ni da ido waɗanda ba a iya gani.A nan take kuma na fahimci wani abu ,na canza har abada kuma ba zan dawo yadda nake ba tun farko .......
[10/11 19:33] MRS SADAUKI: *INUWAR ALJAN*👻
```LoVe aNd HoRrOr story```👽
By
Chamsiya Laouali Rabo
{MRS SADAUKI💫✍️}
*SADAUKARWA:* Ga Rachida Mamar ƴan biyu, alherin Allah ya luluɓe ki . Ubangijin rahama ya kula da lamurranki👏🏻
*FCWA*☀️
________________________
02
Banda wani zaɓi wanda ya wuce na taho gida da wannan littafin sirrin wanda nake jinsa tamkar wani jigo na rayuwata.Wuri mai kyau na yi masa a cikin akwatin kayana na ajiye shi,abincin dare sam ban ma yi tunanin ci ba don dama duk wunin yau ba zan ce ga abin da na ci ba.
A wannan daren sam ban yi baccin kirki ba,da zarar na samu na ɗan tsunduma cikin bacci sai na soma ganin baƙaƙen inuwoyi masu jajayen idanuwa suna ambaton sunana suna kuma nuna mini yadda ake gudanar da baƙin tsafi da wasu dangin asirai.Yadda ake yin hadaya da jinin bil'adama,da kuma yadda ake ƙulla harƙalla tsakanin jinsi biyu.Cikin firgici na farka jikina duk ya jiƙe da gumi,idona kan littafin da na ɓoye a cikin kayana ya sauka amma a yanzu kan table na gansa kuma a buɗe.Da na ɗauke shi sai na ga sak irin abin da na gani cikin mafarki ne,wato ya buɗe kansa da kansa yana karanto mini labarin da ke ƙumshe a ciki ne.Waje na fita na yi rame can bayan ɗaki na binne shi da tunanin hakan shi ne kawai mafita,ina komawa ɗaki na sake tarar da littafin ya buɗe shafi na gaba.Zaman ƴan bori na yi tare da yin tagumi,wata murya na ji tana cewa “littafi ya zaɓi wanda zai karanta shi,tun da kuma ya zaɓe ka to har abada ba zai taɓa barinka ba” kamar wani mahaukaci haka na matsa kusa da shi na ce “to na ji ni ne ka zaɓa amma sai ka bari har lokacin da na buƙaci karanta ka ni ne da kaina zan ɗauko ka na karanta don haka yanzu ka koma ma'ajiyarka ta farko” abin mamaki ina gama rufe bakina na ga ya ɓata kamar walƙiya yayin da kuma jakar kayana ta yi wani motsi tana rawa alamun dai ya shiga ciki ya zauna.