← Book details Matar Mustapha Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 28

Sashe 19

Matar Mustapha Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin rigar rashin mutumcin da na aro na yaɓawa kaina na ce “ku sanar da ni abin da Joyel ke yi a wannan gidan tare da ku”

Cikin rikicewar tunani Abdul ya fara yi mini bayani daki-daki,“ka yi haƙuri David wallahi su pasto ne suka saka mu wannan aikin,su ne suka yi mana alƙawarin bamu aikin gwamnati da kuma arziki mai ɗumbin yawa muddin za mu kashe Joy bayan mun aiwatar da abin da suka ce sai kuma suka bamu maganin da za mu zuba a cikin akwatin gawar amma ka hana faruwar haka shi ne kuma suka buƙaci mu kawo Joyel ”

Zuciyata na tafasa na ce “ita kuma me za ku yi mata?”

“Budurcinta kawai za mu cire” ya bani amsa .

Na maimaita kalmar kawai a zuci kafin na ƙure Abdul da rikitatun idona,ba tare da na furta komai ko wani motsi ba jikin Abdul ya soma yin rawa harshensa na zazzalowa kafin kuma ya yanke ya faɗi kamar yadda ake datsa nama to haka wata ƙara ta ziyarci wurin harshen Abdul na guntsirewa ƙasa ya faɗi.

Isa ya saki wani mahaukacin ciwo kafin ya soma suratai na alamun hauka ya aure shi.Wani irin daɗi ne na ji a raina ganin ya haukace,ɗayan kuma na nakasa shi.Kan kafaɗata na saɓi Joyel na tashi sama cikin iska ,kamar leda haka nake shawagi a sama har na isa ƙofar gidanmu .
Ina tura ƙofa na ci karo da Ummah a tsaye tsakar gida tana yin tsafi ido rufe,jikinta babu kaya daga ita sai ɗaurin ƙirji na wani jan zane.A gabanta kuwa wata ƴar madaidaiciyar tukunyar ƙasa ce cike da ruwa,muna haɗa ido da ita ta yi saurin lumshe nata waɗanda suke a juye sak irin na tumakai.Ban ce mata komai ba na shiga ɗakinta na shimfiɗe Joyel ,ina nan tsaye na ji motsi bayana.

“Daga ina kuke? Me ya samu Joyel ɗin?” na ji muryar Ummah,share tambayoyin nata na yi na ce “ki zo ki taimaka mata ta farfaɗo” sai kuma na fice muna yi wa juna wani irin kallo.Ɗakina na shiga,kayan jikina da suka jiƙe na cire na rataye su jikin ƙarfen da nake aje sakale kaya.

Ba tare da na juya ba na yi wani furici nan take ƙofar ɗakin ta sakawa kanta sakata,na ja wani dogon numfashi kafin na buɗe akwati na ciro littafin sirri na ajiye kan teburi.Pages suka fara ƙarrr na buɗe kansu har suka tsaya a daidai farar page ɗin da babu komai a cikinta.Nan ne na ji wata murya cikin ƙwaƙwalwata na yi mini magana “jinin jikinka shi ne tawadar rubutu” ban ɓata lokaci ba kuwa na samu allurar da nake yin ɗinki na tsaki yatsana,jini ya soma ɓulɓulowa wani kare na ɗauka na rubuta sunan David Jakob amma sai ban ga komai ba.Iskan bakina na hura daidai saitin sunan Abba nan take ya goge na maye gurbinsa da na Alfanso nan take rubutu ya soma bayyana jikin takardar kamar ana ƙyanƙyasarsa.

Ina fara karanta farkon abin da ke rubuce kamar magic sai ga shi abin da na karanto ɗin ya soma bayyana a gare ni kamar na kunna magiji ko tv sai na soma ganin video ɗin shuɗaɗen zamanin da ya wuce na can wasu ƙarni da kuma na shekaru baya.

Wata Masarauta ce mai girma da tsari wacce ta dace da zaratan dakarun yaƙi.Wani sarki ne mai jini a jiki ya fito,kallo ɗaya za ka yi masa za ka fahimci shi da imani da tausayi sun yi hannun riga.Wata magana ce ya yi mai kama da raini da kuma cin fuska,“duk wani mai nakasa na ƙasar nan,daga yau ina mai bada umarni da ya koma can keɓaɓen wurin da na sa aka gina .Ban son ganin nakasshe ko ɗaya na yawo a doron masarautata, wannan shi ne adalcin da ƴata tilo ta yanke wanda ya saɓawa nawa wanda na faɗa a jiya na cewa za a kashe duk wani mai nakasa in kuma nan gaba aka haifo yaro da ita za mu sadaukar da shi matsayin hadaya ga ababen bautarmu masu inganta gobenmu ” Sarkin ya faɗa yana kallon wata matashiyar budurwa wacce ba kowa ce ba illa Ummana.Wani irin kafirin murmushi ta yi tana mai bai wa sojojin yaƙin damar aiwatar da abin da mahaifinta ya ce.

Daga can cikin duban al'ummar wani matashin gurgu ya matso a gaba cikin ɗaga murya ya ce “ya sarkinmu mai adalci a sake duba wannan hukunci,ta ya za a ce a mayar da mu bayan gari kamar dai wasu dabbobi? Shin nakasasshe shi ya halicci kansa?” yana gama rufe baki sai masu nakasa suka fara yin shewa haɗi da taɓa masa, wannan ba ƙaramin abu ba ne.Lamari ne mai nuni da cewa shi ɗin jarumi ne tun da har ya iya yin magana a gaban Sarkin da ba ka isa ka ɗaga kai ka kalle shi ba muddin ba shi ya lamunce da hakan ba.

Cike da takaici da baƙin cikin da ya rufe Sarki ya ɗaga hannu,nan take aka sauko da tutar rashin mutumci mai nuni da za a kashe matashin wanda ba kowa ne ba sai wannan mutumin nan da tsoho Jacki ya ce shi ne mahaifina.

Wasu dakaru biyu majiya ƙarfi suka zo suka ja matashi Alfanso suka tafi da shi,shi kuwa cike da ƙwarewa a aikinsa ya saka idonsa cikin na gimbiya Janaki ya jefa mata ƙwayar sonsa da kuma tausayinsa.Wani baƙin kurkuku ne aka tura Alfanso,yayin da kuma ta ɗaya gefen kuma sarki ya cika umarninsa aka soma kwashe nakassu aka kai su keɓaɓen wurin da ya yi musu tanadi.

Ina kawowa nan page ɗin ta ida sai na rufe littafin na mayar da shi ma'ajiyarsa,ina shirin fara tunani na soma jin yanayin kaɗawar iska na canzawa.Ko tantama babu ruhin matar nan wacce zan iya cewa matar da ta mayar da ni mijinta shi ne zai ziyarce ni.Ban yi ƙarya ba don kuwa kamar ƙyaftawar ido haka ta bayyana gabana,a madadin ta zo ta mu'amulance ni kamar yadda ta saba a'a yau tsaye ta yi muna kallon juna.

“Ban san ke wace ce ba,amma abu ɗaya na sani ba za ki taɓa yin nasarar hana zuciyata son albino girl ba” shi ne abin da na samu kaina da furtawa,furicin nawa ba ƙaramin harzuƙata ya yi ba sai na ga ta wani cije haƙora gashin kanta ya watse cikin iska yayin da fuskarta ta yi ja kamar wuta.

Wani irin tsalle ta yi ta faɗo jikina,babu ɓata lokaci ta soma yin abin da ya kawo ta.Sai da komai ya lafa sannan na samu hankalina ya dawo jikina,na ja wani dogon tsaki ina jin takaicin lamarin kafin na buɗe ƙofar ɗakina.Har zuwa yanzu ana ruwan sama,amma haka na fita na cika bokiti na yi wanka.Ina dawowa na tarar an canza mini zanen shimfiɗa,an kuma kunna turaren wuta sai dai ƙamshin ba irin na bil'adama ba ne.Ina jin motsin ruhinta a cikin ɗakin alamun ba ta tafi ba,yi na yi kamar ban fahimci komai ba na shirya cikin kaya marar nauyi na kwanta.Wata murya na ji ana rera waƙa mai bala'in daɗi,sai dai sam hatta waƙar tsohuwar yayi ce ta ƙarnin baya.Amma sosai nake jin daɗinta,ido na soma lumshewa a daidai nan ne na ji motsi a bayana da kuma yanayin nan in an kwanta gefenka sai dai ban iya yin komai ba saboda fin ƙarfin ruhina da aka yi.

A can ɓangaren Ummah kuwa David na barin ɗakin ta matsa kusan Joyel ta dafa kanta ta soma yi mata wasu surkulle tana jin ranta na azalzala saboda abin da bincikenta ya bada.Joyel ta ja wani dogon numfashi tana cewa “Yaya David me yasa ka kashe mutum? Wayyo ! Wayyo!” sai kuma ta buɗe idonta taram kan fuskar Ummah wacce take ta Tinkiya amma idon Joyel ba su isa su ga hakan ba kasancewarta normal mutum.

“Tashi ki sha magani” Ummah ta faɗa .

“Ina David Ummah?” Joyel ta tambaya.

“Yana ɗakinsa” ta bata amsa tana mai tashi ta shige uwar ɗaka.Wani irin motsi ne zuciyarta ke yi mata,ganin David a cikin yanayin ɓacin rai da kuma yadda zubin jarumtarsa ya bayyana yau a fili sai ta tuno da tsohon mikin da zuciyarta ke ɗauke da shi.A fili ta furta “ina sonka Alfanso” karaf a kunnen Abba wanda yake shigowa,cikin kaɗuwar zuciya ya ce “uban wane ne Alfanso?” Ummah ta juyo a firgice sai dai ko kafin ta kai ga yi masa bayani ya rufe ta da duka,tun tana kaucewa har ta soma mayar da martani,ran Abba ya ɓace sosai ya fito waje ya ɗauki wuƙa yana ɓaɓatu “wato ni za ki dinga cin amana kina bin mazan banza sai na kashe ki yau” ita ma Ummah fitowa ta yi waje, Abba ya je zai caka mata wuƙa amma ta juya tsinin wuƙar zuwa ga Abba ta hanyar furta kalmar tsafi.

Ihun Abba shi ya fito da ni daga cikin ɗakina,ban ida fita daga cikin mawuyacin hali ba na kuma shiga wani shock ɗin.Na ga lokacin da bakin Ummah ya motsa na kuma ji sarai abin da ta furta duk da kuwa kamar mai yin raɗa ta yi furicin.Babban tashin hankali a ciki kuma shi ne huda cikin Abba da wuƙar ta yi,nan take kuma jini ya soma yi masa zuba kafin ya faɗi warwas a ƙasa.

Shigowar maƙwabta kuma kamar ƙyaftawar ido ce,ni ma wani furicin na yi wanda ya fito tun daga ƙasan zuciyata sai ga ni kusan Abba hannuna riƙe da wuƙar da ke soke a cikinsa har zuwa yanzu.

Kururuwar Ummah cikin tashin hankali tana ambaton sunana shi ya ida jawo hankulan sauran maƙwabtan da ba su shigo ba.Raina ne nake jin yana ɓaci yayin da kunnuwana ke zuƙo mini munanan kalamai daga bakunan mutanen da suka shigo,babu jimawa kuma jiniyar motar ƴan sanda ta cika wurin.Sai da suka zo suka janye ni ne kawai na cire hannuna daga jikin wuƙar,tsakiyar ido na dubi Ummah ina yi mata wani kallo da ni kaina ban san ma'anarsa yayin da kuma ƴansanda suka maƙala mini ankwa suka fita da ni.
Chapter 19 · 0% Book details