← Book details Matar Mustapha Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 28

Sashe 6

Matar Mustapha Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tun da Inna ta yanke wannan hukunci ta kafe waje guda,a doli aka bar maganar sai dai ashe akwai jan aiki a gaba ana haka ɓulluwar ciki ya bayyana ga Zeinab.....
[09/11 08:35] MRS SADAUKI: *MATAR MUSTAPHA*
LOVE STORY

```MRS SADAUKI```💫 ✍️

DEDICATED to MY SADAUKI🫡

FCWA ☀️
_________

6

Zeinab tsugunne ta na sheƙa amai Mustapha na tsaye daga gefe riƙe da butar ruwa.Ta na gamawa ya miƙa mata ta wanke bakinta da fuskarta,shi kuma ya zuba ƙasa ya kwashe.

Cikin ɗaki ya tarar da ita a kwance ta na mayar da numfa,ya zauna kamar zai yi kuka ya ce "Momy mi za a dafa miki yau ?" Zeinab ta buɗe ido ta ce "ban cin komi goriba dai nake so bakina duk babu daɗi" da sauri ya tashi ya fice ya na tunanin inda zai samu goriba.

Kasuwar mata ya je sai dai sam mutumen da ke sayar da ita bai zo,nan aka yi masa kwantace bayan gidan Sarki.Keken haya ya samu ya je ya sayo ,da murna ya kawo mata nan ta shiga ci shi kuma ya na daga gefe.

Masifar Inna ce ta tabbatar masu da zuwan ta,Zeinab ta girgiza kai ta ce "sam Inna ta ƙi fahimta haihuwa ta Allah ce a doli so take sai Ya Usman ya ƙara aure ,daga Mamar ka ba ta sake haihuwa ba"
Mustapha ya ce "Momy ni ma ina son ganin ƙannaina,amma mace nake so zan rinƙa yi mata kitso da kwalliya" ya yi maganar ya na murmushi.

"To Allah sa in haifi macen"
Ya amsa da "Amen! In sha Allah ma mace ce,ai kullum sai na yi mafarkinta inda kin gan ta mai kyau,ina fatan dai kar ta yi rigima"
Zeinab ta ce "ai kuwa in ta biyo Kakarta za ta yi wuyar auruwa" kamar suɓutar baki Mustapha ya ce "ai ni ne mijin! Wlh Momy ba zan bari wani ya auri ƙanwata ba,ni zan aureta yadda zan kula da abata" mi Zeinab za ta yi banda dariya,can ta ce "to surukina Allah gwada mana wannan lokaci" ya amsa da "Amen saraku!"

Tun daga wannan ranar su ka canza ma junansu suna, Mustapha zai kirata da Saraku ita kuma ta ce Surukina.Wannan ya sa kowa ya san da labarin hirar da su ka.
A sannu a hankali cikin Zeinab ke girma wanda ke ƙarƙashin kulawar Mustapha,duk wani abun kwaɗayi da mai ciki ke so to shine zai nemo shi a haka har cikin ya shiga watan haihuwa.

"Saraku ga zuma na samo miki ki rinƙa sha,so nake ko da ake haifar matata ace ta zo da zaƙin murya" Mustapha ya faɗa ya na mai miƙa mata zuma a roba.
Ta karɓa ta na mai cewa "Mustapha ina tsoron na haifi namiji ka ce sai ya biya ka duk toshin da ka yi "
Ya ɗan sosa ƙeya ya ce "ai kuwa in namiji hummm! Na dai ƙyale ba zan ce komi ba" Hajara wato mahaifiyarsa ta shiga dariya kafin ta ce "in dai Mustapha ne har dukansa zai iya,kin san dama ba zuciyar tausayi ne da shi ba"
"To ai haka ake son namiji da jarumta" Zeinab ta mayar da martani,shi kuwa Mustapha Sarkin zuciya tuni ya game fuska.

"Surukina zube min ruwan wanka ka ji,kar ka sauri Mamar ka kishi ne take" Cewar Zeinab ta na mai buɗe robar zumar ta na sha.
Mustapha ya cika mata bokiti ya kai banɗaki,ya na gamawa ya fice ya nufi filin ƙwallonsu.

Zeinab na gama wanka kamar an ce lale maraba,naƙuda ta zo mata gadan-gadan.
Hajara ita ce ta kai ta asibiti,tsawon lokaci kafin nurse ta kawo albishirin ta haihu.
Mustapha na filin ƙwallo labari ya zo masa,jikinsa duk ƙasa haka ya nufo asibitin.
Kukan Babyn ya fara yi masa maraba wacce likitoci ke ta ƙoƙarin samun jijiyarta don yi mata allura.Ya yi tsaye ya na kallo,sai tsakarta ake da mugun sauri ya je ya ɗauke ta daga kan gadon ta kuwa tsagaita kukan.

"Likitoci ne ku ko kuma ƴan koyo?" Ya yi maganar cikin ɗaga murya kafin ya nufo Hajara wacce ke zaune kusa da gadon da Zeinab ke kwance.
"Allura za a yi mata ka bado ta" cewar nurse.
"Na ƙi na bayar ɗin,Maman ki na gani ana ta cin zallun Babyna shi ne ki ka yi zaune a nan?"
"Mustapha ka mayar da Babyn nan kar na saɓa ma,da ka shigo ko sallama ba ka yi ba.Wai ma wa ya gwada ma ɗakin da mu ke?"
"Daddy mana,ai na ga lokacin da ya fito zai shiga office..." Nurse ɗin ce ta katse shi "don Allah ka bado ta lokaci na tafiya za mu yi mata allurar nan kar aje a samu matsala" ya juyo ya yi mata wani mugun kallo,kafin ya yi magana Hajara ta karɓe Babyn ta mayar su ka ci gaba da sukarta har Allah yasa suka samu jijiyar.

Mustapha ya rumtse ido kukanta na sa zuciyarsa wani irin ƙunci.
Daddy ya shigo ya na cewa "na kira lambar Lawali da ya ɗauka na shaida masa haihuwar,amma ya ce shi ba zai zo ba Mustapha ya zaɓi sunan da za a saka" Hajara ta ce "amma sam bai kyauta ba,ta yaya za a yi ma mutum haihuwa ya ce ba zai zo ba?"
"Matsalar daga ƴan uwan shi ne,amma ya gane kuskuren shi kin san tun tuni ya nemi yafiya.Mustapha mu je ka bada suna" cewar Daddy ya na mai yin gaba,da murna ya take masa baya.

Mustapha zaune gaban Dr ya rasa sunan da zai zaɓa har Daddy ya yi fushi ya barsa nan.
"Likita a saka mata sunan Shamseeya" Dr ya yi murmushi ya na shirin rubuta wa Mustapha ya ce "ko zan iya rubuta wa da kaina"
"Babu matsala" Dr ya faɗa tare da miƙa masa abun rubutun ya rubuta.

Sai bayan ya dawo ne ya shaida ma Daddy sunan,shi kuma ya yi mata huɗuba.
Zeinab ta farka daga bacci,da sauri Mustapha ya sunne kai ganin ta na kallon shi wai kunyarta yake ji.
"Laaa ! Surukina wai har an fara jin kunyata?" Duk kowa na wajen dariya ya yi banda shi da ya game fuska.

Bayan an sallamo su ƴan Barka haka su ka rinƙa shigowa ganin Baby.
Sai ana gobe suna sannan Lawali ya zo shi da wani ƙanensa suka kawo rago da kuɗin da za ayi hidima.

"Na so ace kin koma ɗakin ki sai dai Allah bai nufa ba,amma ki sani ina son ki sosai"
"Na sani baban Shamseeya dangin ka ne ba su sona"
"Ina Mustapha?" Ya tambaye ta don kawar da zancen.
"Ya na nan waje shi da abokansa ko?"
"Ban gan shi ba ne"
"Bari na sa a kirawo shi" ta na gama faɗa ta fita can kuma ta dawo ta zauna .

"Saraku gani aka ce ki na nema..." Maganar ce ta maƙale masa ganin Lawali a gaban shi, Mustapha ya juya zai fita amma ya yi saurin tsayar da shi .
Yadda Lawalin ke yi masa magana cikin taushin murya ya saka Mustapha sakin jikin shi,bisanin su ɗan taɓa hira bayan tafiyar Mustaphan ne Zeinab ta baiwa Lawali labarin komi yadda ya yi ta kula da ita da kuma yadda ya ce ya na son aurenta,shi dai murmushi kawai yake.

Washegari
Aka zana suna,kafin kuma a watse aka sake yin wani zaman.Abu kamar wasa haka aka aka ɗaura aure tsakanin MUSTAPHA USMAN YAHAYA da jaririyar amaryarsa SHAMSEEYA LAWALI RABO .
Mutane da dama sun yi mamaki tare da al'ajabi,ganin wai yarinya ƴar kwana bakwai da haihuwa ce aka ɗaura ma aure.

Mustapha ya rungume surukinsa wanda ya cika masa burinsa."Babu komi Mustapha,zuciyata ta samu nutsuwa ko bayan raina na san na bar Ƴata gun da ba za taɓa yin kuka ba"
Duk kowa ya yi murnar hakan,don ba ƙaramin karamci ba ne wannan.

Washegarin buki aka yi ma Baby aski,nan fa Mustapha ya ɗora masifa don mi za a aske wa matar shi gashi.
"Wani zai fito ai ka yi haƙuri" Zeinab ta faɗa.
"Saboda Allah Momy hakan da ku ka yi kun gyara mini? Ni fa so nake na fara yi mata kitso,Maman Hajara da ke shafa ma kan Baby hoda ta ce "ai ba a ma gama ba sai an yi na arba'in"
"Wlh babu wanda zai taɓa mata kai" Mustapha ya faɗa a zuciye su kuma su na ta yi masa dariya.

A sannu a hankali haka rayuwa ke ta tafiya,shaƙuwa gami da so mai ƙarfi na ƙara shigar Mustapha yayin da lokaci guda ya yi mata sauyin suna daga Shamseeya zuwa *SEEYA* doli kowa ya bi hakan.
Dukan hankalinsa ya mayar da shi kan yarinyar,tun kafin lokacin fara cin abincin ta(wata shidda) ya yi Mustapha ya fara bata abubuwa wasu ta yi amai wasu kuma ta ci haka nan.
A haka har ta zo matakin yaye,a ranar ta yi rigima sosai ba ta jin rarrashin kowa sai na shi wannan dalilin yasa ta koma wajensa a can take kwana.

★Cikin gwaranci na wanda bai ida iya Hausa ba ta ke gaya mishi "Ande ta buge ni saboda Jafar"
Mustapha ya ƙanƙance ido tare da sukutar SEEYA wacce ta ke ƴar shekaru uku a duniya,sarai ya fahimci abin da ta ce hakan yasa ya kakaɓe mata kanta wanda ya yi ƙasa kafin ya wuce gidan maƙwabciyar tasu.

Su na shiga SEEYA ta nuna masa wani takalme tare da gaya masa yadda Ande ta buga mata shi a kai.Ido rufe ya shiga shamakinta,sai aka yi sa'a ya hangi Jafar zaune bisa pô ya na kashi,wani irin ball ya yi da shi ya bugi randar ruwa wacce sai da ta fashe ji kake kwatsaaaa.

Ande ta fito daga ɗaki kafin ta tambayi ba'asi Mustapha ya nuna ta da yatsa ya na cewa "daga yau sai yau,wlh in ki ka sake taɓa lafiyar Babyna kotu ce za ta raba mu" ya na gama faɗa ya fice.
Chapter 6 · 0% Book details