Sashe 26
Matar Mustapha Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
“Ga ni ranka shi daɗe ” ta furta cikin wata irin sanyin murya tana ƙanƙame jikinta da alamu kamar sanyi take ji,a hankali na soma takawa zuwa gare ta har na isa gabanta na tsaya.Ba tare da na ce mata komai ba na kai hannu zan cire bandejin sai dai ya ƙi fita ba tare da wani tunani ba na ja wuyan hijabinta baya kanta ya fito.Na ɗan ranƙwafa tare kai hannuwana baya ina kuma kallo na kwance ƙullin tare da cire ƙyallen duka.
“Buɗe idon na gani!” na furta cikin bayar da umarni,kai ta girgiza wanda ya bai wa baƙar sumar kanta damar motsawa.Zuciyata na ɗan dokawa na soma motsa bakina ina karanto wasu ɗalasima haɗi da hura mata iskan bakina a fuska.Babu shiri ta buɗe idon,sai dai a tashin farko sun canza daga na normal mutum saboda wata irin kalar haske da suke fitarwa.Ɗayan idon ya zama kamar hasken rana yayin da kuma ɗayan ya ɗauki siffar na mage yana fitar da wani blue haske.
A hankali kuma ta ƙara mayar da su ta rufe,da sauri ni kuma na sa hannu ina ƙoƙarin buɗe su sai ga Nelson ya turo ƙofa ya shigo.Cak ya yi tsaye yana kallon mu kafin yayi gyaran murya,baiwa Izzatu ta nufi ƙofa za ta fita amma na dakatar da ita “ke!” cak ta tsaya ba tare da juyo ba.
“Kina iya tafiya ke ɗaya ne ba tare da ƴar jagoro ba?” na tambaye ta ina kallon yadda hijabinta ke jan ƙasa.“Eh ranka shi daɗe zan iya”
“Okay!” na furta,tana fita Nelson ya matso yana cewa “meke tsakaninka da wannan baiwar? Ka rasa wacce za ka ƙulla alaƙa sai wacce ba ta da wasu taurari masu haske?”
Wani irin kallo na yi masa kafin na ce “na yi maka kama da wanda zai yi mu'amalar banza da mace ? Yawwa dama ina son yi maka wata magana,me yasa ka kusanci Nadiya sannan kuma ka kashe ta?”
Babu wata kunya Nelson ya bani amsa da “saboda ina son samun ƙarfin power,ita ɗin ƴa ce ga wani matsafi ya saka mata abubuwan tsafi sosai su ne na sace sai kuma aka samu akasi ajalinta ya yi”
Na taɓe baki kawai tare da komawa bakin window na yi tsaye.
“Yarima faɗa mini mana shin namiji ne kai?” na ji wata tambayar rainin hankali Nelson ya jefo mini.
A zuciye na ce “a'a mace ce ni ! Ai ka ɗan kwali a kaina”
Ya yi wata irin dariya sannan ya zo kusa da ni ya tsaya yana mai cewa “ba haka nake nufi ba,tambaya nake yi in ka taɓa jin feeling akan mace”
Da sauri na kalle shi ina jin bugun zuciyata na canza sheƙa,na haɗiye wasu yawu ina mai ci gaba da kallonsa.Yayin da shi kuma ya ɗora da cewa “kar ka ji kunyata,ni abokinka ne sannan kuma mataimakinka ban yi maka wannan tambayar don rainin wayo ba a'a sai don ina son isar maka da wani saƙo mai muhimmanci ”
“Wane irin saƙo?” na tambaye shi.
Ya ce “duk wanda ke ɗauke da rigar prophecy ana killace masa sha'awa har zuwa wani tsaunin nasara,ba zai kasance namiji ba har sai in ya haɗu da macen da ababen bauta suka zaɓa masa wacce ita kanta ba normal mutum ba ce tana ɗauke da wani muƙamin ƙarfin iko ne wanda zai taimaka maka ka tura motar burinka ga ci”
Na kawar da kai gefe ina mai cewa “sam ban fahimci abin da kake son faɗa ba”
Nelson ya ce “ka fahimta sarai Yarima kawai ba ka son sanar da ni amsar tambayata ta farko,sai dai ka sani nan kaɗan zan samo ta ba ni ɗaya ba har da mai girma sarki Alfanso ”
Na juyo da sauri ina kallonsa,ya jinjina kai yana mai ci gaba da cewa “a ranar da ka zo masarautar nan in ba ka manta ba ka suma,a lokacin ne kuma aka gudanar da bikin ƙaddamar da kai.Aka yi maka wankan ruwan tsafi wanda ba a samu damar yi maka shi ba lokacin da aka haife ka, sannan an yi maka sabon shayi wanda za a tabbatar da ingancinsa nan da kwana uku ”
“Shayi? Ni ɗin ne aka yi wa sabuwar kaciya? Hahaha” na yi wata irin dariya saboda maganar tasa ta fi kama da rainin wayo.
Ya ɗaga gira ya ce “tabbas an yi maka sabon shayi Yarima.Kuma ƴan matan lorori ne za su tabbatar in kai namiji ne ko kuwa dai...” mugun kallon da na watso masa ya saka shi yin shiru .
“Kana iya tafiya!” na furta ina jin wani nauyi a zuciyata.Nelson ya ɗan bubuga kafaɗata ya ce “ka huta lafiya sarkinmu na gobe” har zai fice na dakatar da shi ta hanyar cewa “an kawo iyalan wannan matsafin?”
“Matarsa na rufe a kurkuku ko ka manta? Sai ƴarsa ce kawai EZRA Albino girl ”
“A je a tawo da ita” na faɗa cikin bayar da umarni,ya ce “an gama” sai ya fice na bi bayansa da kallo ina maimaita kalaman da ya furta mini a game da nagartata ta ɗa namiji.In da akwai wacce zan gwada sanin ni ɗin a wane sahu nake cikin jerin maza to EZRA ce,yarinyar mafarkina matar da zuciyata ta zaɓa.
Ina nan a tsaye bakin window na tsinkayi Nelson shi da wasu dakarun sun haɗu wuri guda suna yin wasu alamo na tsafi,kafin ƙyaftawar ido suka ɓata cikin wata ƙura da ta turniƙe wurin ta haifar da guguwa.
Ba a kuma ɗauki lokaci ba suka bayyana suna riƙe da EZRA,sai ƙoƙarin ƙwacewa take .Nelson ya ɗago kansa saitin benen da nake,duk nisan tazararmu kuma bai hana mu ganin ƙwayar idon juna ba har muka yi magana irin tamu ta matsafa.
Cikin sauri na je ƙara kimtsawa na ɗora babbar rigar ƴaƴan sarakai kafin na fita.Ina tafe wasu ɓoyayyun ruhika na take mini sawu har na isa wani sashen sirri wanda aka ware domin ni,ban jima a cikinsa ba aka kawo mini EZRA hannuwanta ɗaure da kacocin tsafi waɗanda nata tsafin ya gagara ya kwance su.
A gabana suka gurfanar da ita kafin su fice su bar Nelson shi kaɗai yana kallona.
“Zan neme ka daga baya” na furta,ya jinjina kai kafin ya fice.
Na maida dukkan hankalina a kanta ina jin wutar sonta na ƙara ruruwa a birnin zuciyata.
“Mene ne sunanki?” na tambaye ta.
Cikin zafin kai na matsafiya ta ce “ka juya ƴaƴan wurinka domin samo sunan”
“Ni ba boka ba ne matsafi ne!” na bata amsa ina mai ɗauke ta da wani gigitacen mari wanda ainahinsa ba daga gare ni ya fito ba a'a kawai na samu kaina da yinsa ne.
Ta goge bakinta da ke fitar da jini kafin ta ɗago tana kallona da idon sharri,kunnuwanta kuma suna daɗa yin tsayi sosai har suna mai hudu dogon gashin kanta wanda yake kamar zaren kwakwa.
“Ki yi ƙoƙarin mayar da waɗannan siffofin naki kafin raina ya ƙara ɓaci na sauke miki waɗannan kunnuwan masu kamar na Zomo ” na furta tare da kallon tsakiyar idonta da nawa idon muguntar.
Ta saki wata razananiyar ƙara tana mai rumtse idonta gam,nan take kuma suka fara shatatar da jini.Rai a ɓace na ce “dakaru!” suka wani buɗo ƙofa da ƙarfi suka shigo,“ku ɗauke ta ku kai ta can inda aka ajiye mahaifinta ƙila in ta ga irin azabar da ake yi masa ta yi hankali ta saurare ni a nutse ” na furta cikin amon ɗaga murya.
Ƙiiii suka ja ta suka fice da ita,ni ma fita na yi na koma sashena na fiddo littafin sirrina.Hoton nan dai ne na ƴar babyn nan mai ɗauke da ƴar tsanar roba.Zama na gyara na soma gwada yin siddabaru don nuna mini abin da babyn ta zama a yanzu sai dai kashhh iya wani zane kawai na iya gani da ke manne gefen wuyanta.
★ BAIWA IZZATU
A daren ranar da ta ga Dadda da kan Saniya a wannan daren ne prophecy ɗinta ta soma.A washegari sam ba ta tada wa Dadda zancen ba ita kuma a nata ɓangaren sai ƙoƙarin ganin ta rufewa Izzatun idanuwanta take don kar ta ƙara yin tozali da Yarima David sai dai kuma aka samu akasi yau Yariman da kansa ya turo wata baiwa kan ta zo ta tafi da ita.Duk yadda Dadda ta so hana Izzatun tafiya amma kasa samun ƙwarin gwiwar yin haka ta yi a dole ta bar ta suka tafi.
Ita kuwa IZZATU banda bugawar zuci babu abin da take yi har lokacin da suka isa can ɗin.A sa'ilin da Yarima ya samu kusanci da ita sosai ji ta yi numfashinta na ƙoƙorin ɗaukewa,don haka ba ƙaramin jin daɗi ta yi ba da Nelson ya shigo ya same su wanda hakan yasa ta samu damar silalewa.
Tana tafe tana gwada buɗe idon nata amma ta kasa,yau ɗin ma ji ta yi wani abu na yi mata motsi a tsakiyar goshi kafin kuma ta samu damar ganin duk abin da ke gabanta.Sam ba ta yi tunanin idonta ne na uku ya buɗe ba,a haka ta ƙarasa gida tana buɗe ƙofa Dadda ta saki ƴar tukunyar ƙasar da ke hannunta tana mai kallon idon da ke tsakiyar goshin IZZATU wanda kuma da idon ne take kallonta.
“Dadda lafiya kika saki tukunya haka kamar kin ga aljana?” IZZATU ta tambaya.
Dadda ta haɗiye wasu yawu kafin ta zo da sauri kamar za ta faɗi ta kamo hannun Izzatun .Jikinta na ɗan rawa ta fiddo wani tandun kwalli cikin aljihun rigarta,ta shafa wa kanta sannan ita ma Izzatun ta shafa mata.Kamar ƙuda haka suka dawo ƴan ƙananu da su,Dadda ce ta kama hannun Izzatun suka shiga wannan tandun kwalli wanda ya kasance wata duniya ce ta daban da wasu al'ummar ke rayuwa a cikinsa.
IZZATU wacce take ganin komai kamar a mafarki ta soma ƙoƙarin toshe hancinta da yake shaƙo mata wani irin wari kamar na ruɓaɓen kifi,ga wani irin duhu da ya mamaye ko ina.A cikinsa Dadda ke ci gaba da jan hannunta suna tako cikin caɓo har suka isa wani tabkeken Teku sai duk suka ja suka tsaya.A wannan lokacin duka idanun IZZATU uku a buɗe suke,murya na ɗan rawa ta ce “Dadda ina ne nan kuma kika kawo ni?”