← Book details Matar Mustapha Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 28

Sashe 22

Matar Mustapha Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Darasi ya fara yana tambayoyi amma babu wanda ya sani sai EZRA,duk da ya ga tana ɗaga hannu amma ƙin saka ta yayi ya juya ya ci gaba da rubutunsa.

Koojal ta dubi littafinta irin wanda makafi ke aiki da shi mai kamar na'ura,shafa shi ta fara yi tana mai kallon rubutun sai ta ji tamkar wata murya na karanto mata abin da ke rubuce ba tare da ta san idanuwanta ke karatun ba.

“Koojal?” malamin ya kira sunanta,cikin sauri ta ce “na'am malam”

“In kin ga matsafi a gabanki mene ne farkon abin da za ki? Shin za ki guduwa ne ko yaya?” ita ce tambayar da malam ya jefo mata.

Koojal ta basa amsa da “zan gaishe shi cike da girmamawa saboda babu abin da ya fi burge ni a duniya kamar tsafi da matsafi”

Duk da ya ji haushin amsar haka ya ƙara jefo mata wata tambayar,“in ya yi ƙoƙarin cutar da ke fa wane mataki za ki ɗauka?”

“Zan karanto addu'o'in kongosa na neman kariya Yesu ya taimake ni ” ta basa amsa.Sai ya saki murmushin jin daɗi ya ce “ta ya ake gane matsafi? Ina tambaya ne ga duk ƴan aji”

Duk kowa shiru ya yi,can ya ci gaba da cewa “Maraton babban malamin Kiristanci ya ce duk wani matsafi ya tsani Bible da kuma Cross wannan ne yasa za ku ga da yawan mabiya addinin ke maƙale da Cross ko kuma ɗan ƙaramin icce mai hoton inda aka maƙala abin bauta Yesu Almasihu wannan babbar kariya ce.Sannan ya ƙara da cewa addu'ar Yesu Almasihu ka cece mu ta yi nauyi a bakin matsafi.Ku maimaita YESU KA CECE MU!” duk ƴan ajin suka furta amma banda EZRA sai kuma ya ci gaba da kawo wasu addu'o'in waɗanda suka saka kanta fara juyawa tana jin tamkar suna ƙona ta ne.

Daga nan inda take zaune ta soma jin jijiyoyin jikinta suna wata irin kumbura suna ƙara girma,ta ware idonta waɗanda hucin azabar halin da take ciki ne ya haddasa suka rine suka zama kamar nunannen tumatur.Kan malam Rohan ta sauke su wanda shi kuma tsabar kaɗuwa da ganin lukutar masifa ya soma yin fitsari a wando ji kake shaaa kamar raƙumi na fitsari.Duk ƴan aji suka sa dariya,babu wanda kuma ya lura da halin da EZRA take ciki in banda shi wanda ya yi sanadiyar shigarta.

Kamar wanda lantarki ya damƙe haka ya kasa yin motsi yana mai ci gaba da kallonta don dole don ita ce da kanta ta hana jijiyoyin jikinsa ci gaba da aiki.Cikin ƙaraji ta yi amfani da wata guragurbin murya mai matuƙar firgitarwa ta ce “wato so kake yi a lalle dole sai ka murƙushe baiwar tsafi da ke gudana a jinina da kuma ire-irena? Ka makaro domin kuwa na da ɗan lokaci tutar tsafi ce za ta dinga kaɗawa a kaf Daular Alfanso”

Malam Rohan wanda yake cikin halin ƙaƙanikayi ya soma motsa baki yana son yin magana amma babu dama,ta hanyar tunaninsa ta bankaɗo abin da ke ƙunshe a ruhinsa.“Duk yadda kike son cikar wannan buri naki har abada ba zai taɓa cika ba ƙasƙantaciyar matsafiya,ba tun yau ba na daɗe da fahimtar cewa laifin ƙazamai nakassu ire-irenki ne suka hassala gimbiya Janaki ta yanke wa iyayenmu hukuncin mayar da su a keɓaɓen wuri ”

Ambaton sunan gimbiya Janaki shi ya ƙara tunzura EZRA ,saboda duk wani mai rai da ke rayuwa a Daular Alfanso ya tsane ta saboda silarta ne suke a bayan gari ba tare da an basu damar cuɗanya da sauran al'ummar yankin Uganda ba .

Daidai saitin zuciyar malam Rohan EZRA ta aika masa da wata kibiyar tsafi ta cake shi nan take ya saki wata irin razananiyar ƙara wacce ta jawo hankulan mutane da dama ciki kuwa har da shugaban makaranta.
Duk students ɗin suka miƙe tsaye cike da tsoro ganin malaminsu yashe a ƙasa yana fitar da wani baƙin hayaƙi kamar tsohon batiri haka fatarsa ke zagwanyewa.Shigowar shugaban makaranta ya yi daidai da dawowar EZRA normal,ita ma sai ta miƙe tsaye kamar sauran ɗaliban tana waro idonta da suke sak irin na mage don ita madadin baƙi wani blue mai ratsin kore ke juya duniyar ganinta.

Kallon tsaf shugaban ya soma yi wa students yayin da sauran malaman da suka samu damar zuwa nan ɗin suka fara ƙoƙarin ceton ɗan uwansu sai dai sun kasa saboda lamari ne na tsafi.

“Kowa ya tafi gida an tashi!” shi ne kawai abin da ya faɗa kowa ya soma fita.EZRA na riƙe da hannun Koojal suka fito,direct kuma can wajen banɗakunan makaranta ta kai ta.

“Me za mu yi a nan?” Koojal ta tambaya,EZRA ta ƙara ƙanƙame ta sosai kafin ta ce “ki jira kaɗan yana zuwa” ko gama rufe bakinta ba ta yi ba kuwa sautin iskan fukafukinsa ya soma kawo musu farmaki.Kamar saukar jirgin sama haka Jemagen ya dira a gabansu,babba ne sosai don ya fi girman Giwa wannan ya tsoratar da Koojal ta ɓuya a bayan EZRA ita kuwa ce mata ta yi “kar ki ji tsoro mana,zo mu hau ya kai mu fadar Mermaid zan nuna miki abubuwan da ban taɓa faɗa miki su ba”

Koojal dai a tsorace ta yarda ta hau bayan Jemagen, EZRA ke gaba ita tana baya a haka ya tashi da su sama.Cikin abin da bai fi minti biyar ba ya kai su wata duniya wacce ba ta bil'adama ba.
Farkon wurin ya soma ne da wani abu mai kamar bakan Gizo,yayin da hotonsa yake kamar madubi.Sauka suka yi suka ratsa ƙofar,nan suka ɓulla a daidai wurin nan da suka zo ɗazu da Malama Sharly.

EZRA ta ce “nan ne tushenmu,ni ɗin jinsi biyu ce .Ba koyon tsafi na yi ba,haifata aka yi da shi sai dai ban taɓa sanin mene ne ba sai da Ummi ta ilmantar da ni.Wannan Jemagen da kika gani shi ne abin hawata,duk inda zan je muddin yana da nisa to da shi nake amfani”

Koojal ta ja ajiyar zuciya ta ce “amma ta ya aka kika san da zamansa?” kafin ta bata amsa wata kifanyar ruwa ta ɓullo ta cikin wani ɗan ƙaramin gurbin ruwa.Ta yi ihu ta ce “ EZRA???” ambaton sunan nata yasa ruwa suka dinga ɓulɓulowa ta ko ina kafin ƙyaftawar ido sai ga su a ƙasan ruwa.Ido Koojal ta buɗe tana kallon halittun ruwa,wasu rabi mutum rabi kifi ko kuma rabi mutum rabi maciji.Tsaye ta yi tana kallon ƙawarta wacce a duniya in aka cire iyayenta babu wacce take so bayan EZRA,yadda ta ga jelar kifi madadin ƙafafu yasa ta waro ido ta matsa da sauri don fargar da ƙawartata sai dai ita ma sai ta ashe ita ma ta zama Siren ɗin.Wani irin kuka ne ya zo mata ba ta shirya ba,wanda ya jawo hankalin EZRA da sauri ta zo ta kama hannunta.Kamar ƙyaftawar ido sai ga su wajen ruwa a saman wata ƙatuwar bishiya....

★ DAVIDO

Ruhina da ruhin Nelson ne suka ɗingiza esprit ɗinmu izuwa maƙabartar da aka binne ƙanena Joy.A tsaye suke suna ta shawarar yadda za su haƙo gawar Joy,na dubi Nelson kafin na ce “mene ne zan yi a yanzu?”

“Ka yi musu magana,ka kuma basu damar ganin ruhinka ” ya bani amsa,sai dai ko kaɗan wannan karon ban tambaye shi ƙarin bayani na game da yadda zan yi hakan ta tabbata.Ƙarasawa na yi na tsaya kai ga kabarin,abu na farko da na yi shi ne bayyana musu hasken ruhina.Sai duk suka ja baya,sai kuma na soma gaggaɓa dariya kafin na soma yi musu magana cikin gargaɗi “tona wannan kabarin shi ne babban kuskuren da za ku aikata a rayuwarku,ina mai baku shawara da ku juya ku koma inda kuka fito”

Ɗaya daga cikinsu wanda yake da ƙarfin hali sai cewa yayi “ba za mu taɓa matsawa daga nan ba sai mun tabbatar da abin da muke zargi,don haka kar ku wani ji tsoro ku tuna cewa littafin sirri ya fi komai muhimmanci a rayuwar kowanne daga cikinmu” ya yi furicin ne tare da duƙawa ya soma ture ƙasar kabarin.Kamar yadda ake ɓalle hannun ƴar tsanar roba haka na yi wa dukkan hannuwansa a lokaci guda suka fita suka yi sama.Cikin iya shege irin nawa na yi amfani da hannuwan na soma ɓalla musu maruka ji kake fauuu,tun suna daurewa har suka soma yin ihu sai dai babu damar guduwa na riƙe ƙafafun.

Koke-kokensu ya jawo hankalin mai gadin maƙabartar,shi kuma babu wani tunani ya kira jami'an tsaro.Ko da suka iso wurin tuni na canza musu kamanni.

“David? David?” na ji muryar Jami'i na tashe ne,dakyar na fizgo ruhina daga waccan duniyar na maido shi gangar jikina.Na ware ido dakyar na sune shi,da sauri na ga ya ɗan ja baya yana haɗiyar yawu.Duk da ban san dalili ba haka na ja fatun idona na rufe,kafin can ƙasan maƙoshi na ce “har gari ya waye ne?”

“Wai don Allah wane ne kai?” na ji ya yi mini wata tambayar rainin hankali sai ka ce ba shi ne ya je ya ɗauko ni ba.

Ni ma cikin rainin wayon na ce “David Jakob,Mama kuma ta ce Davido”

Ya ja dogon tsuki kafin ta bugi gefen cinyata ya ce “banza ba wannan nake nufi ba,a duniyar ruhaniya nake tambaya wane ne kai?”

Zumbur na miƙe tsaye ina mai yi masa wani kallo kafin ni ma na aiko masa da tawa tambayar“ wa ya aiko ka wurina ?” bai ce mini komai ba illa juya mini ƙeya da yayi ya fice.
Chapter 22 · 0% Book details