← Book details Matar Mustapha Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 28

Sashe 25

Matar Mustapha Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ko da dare yayi zama na musamman muka yi ni da sarki Alfanso wanda har zuwa wannan lokacin ban furta masa kalmar da ke nuni shi ne mahaifina ba.Bayan mun gama cin abinci muka tattauna game da abin da na gani a Masarauta kafin kuma mu yi sallama kowa ya tafi sashensa.

Cikin kayan bacci na alfarma na shirya ,na rage hasken ɗaki kafin na jawo littafin sirrina.A daidai page ɗin da na tsaya ya buɗe sannan ya ci gaba da nuno mini abubuwan da suka shuɗe.

Ta ƙarfin tsafi ne a wancan lokaci Alfanso ya jawo ragamar hankalin gimbiya Janaki ta zo har a nan cikin kurkuku ta kawo masa kanta ya yi tarayya da ita wacce ta sauya ƙaddararsu shi da ita.

Ina kawowa nan na yi wa littafin magana cikin sigar raɗa na ce “ka bani wani tarihin ban son wannan,in lokaci ya yi iyayena da kansu za su bani gwagwarmayar da suka sha” ai kuwa ina gama rufe bakina sai pages ɗin suka fara yin ƙarrrr suna ta gudu haɗi da buɗe kansu,har aka zo kan wata page mai ɗauke da wasu ahali.Uba mahaifi ,uwa da kuma wata ƴar babynsu a hannu ita ma tana riƙe da ƴar tsanar roba.

Na kai hannu na shafi hoton babyn,girrr na ji wani shock ya kama ni da sauri na rufe littafin ina jin kamar na taɓa jin makamancinsa abin da na ji sai dai ko da wasa ban kawo a kaina wai moments ɗinmu ne na ɗazu ni da baiwa Izzatu.

Ina shirin kwanciya bacci na soma jin yanayin iskan nan na kaɗawa,wato matar mafarkina ce za ta bayyana.Wani irin sanyi ne ya soma luluɓe ni yana saukar mini da kasala,idanuwana sun yi mini nauyin da yasa dole na soma rufe su a daidai kuma wannan lokacin ne ta bayyana a gare ni cikin shigar tsaraici.Tana shirin kai hannu jikina wani irin haske da ban san daga ina ya fito ba ya taso ya luluɓe ni tare da yi mini iyaka da ita.Na ja wani numfashin farin ciki kafin wani daddaɗan bacci ya ɗauke ni mai ɗauke da mafarkin prophecy ɗina wanda ababen bauta suka zaɓe ni matsayin wanda zai cika musu wani buri wanda tun lokacin baya suka fara gina shi.

★IZZATU

Ko da ta fita daga sashen Yarima David direct can ɓangarensu na bayi ta nufa.Tana shiga ta soma cire kayan jikinta ta jawo wani tsohon zane ta yi ɗaurin ƙirji kafin ta fara kiran sunan Kakarta “Dadda? Dadda?” daga can cikin wani ɗan ɗaki mai kamar akurkin kaji wata dattijuwa ta fito tana cewa “shalele har kin dawo?” da mugun sauri Izzatu ta ƙarasa wurinta tana cewa “kin ga Dadda ruwan wankin ƙafafun Yarima sun shigar mini ido kuma an zuba musu sanadarai dayawa”

Wani irin kallo ne Dadda ke yi wa Izzatun mai cike da tsoro,shakku da kuma zargi kafin can ta nisa ta ce “je ki kwanta kan gado na duba idon” ba tare da ta musa ba ta je ta kwanta ɗin,Dadda ta ɗauko wata ƴar ƙaramar fitilar hannu wacce a baɗininta wani busashen maciji ne da ya yi zamani wajen ƙarni uku.

Idon Izzatu ta soma dubawa bugun zuciyarta na sake tsananta tana jiye wa ƴar jikarta tsoron abin da tarihi ya tanadar mata.Yadda take gumi ya saka Izzatu cikin damuwa ta ce “Dadda ko dai makancewa zan yi ?”

Dadda ta ajiye fitilar tana mai cewa “a'a zan saka miki magani sai a ɗaure idon”

Izzatu ta ce “to bari na yi alwala tukun ” sai da ta je ta yi alwala ta dawo sannan Dadda ta saka mata maganin ta ɗaure idon sai ta zauna gefenta tana kallon face ɗinta sannan ta ce “ya yariman yake a zubin halitta? Ɗazu na ji gangami amma ban fita ba ballantana na gansa”

Izzatu ta saki wani murmushi wanda kana jin sautinsa za ka fahimci tun daga ƙasan zuciyarta yake,ta ce “dogo ne mai cikar zati,yana da manyan idanuwa da ɗan madaidaicin saje,fuskarsa babu walwala amma yana da kirki”

Dadda dai ido kawai ta tsura mata can ta miƙe ba tare da ta ce komai ba ta shiga haɗa wasu magunguna tana yi tana yin wasu siddabaru tana zuba wasu kalolin ruwa da aka tatso daga jikin wasu dabbobin masu dafi.

Bayan ta gama sai ta zuba maganin cikin kofi ta bai wa Izzatun da kanta,duk da babu daɗi haka ta daure ta sha.Magungunan sai suka saka ta bacci wanda hakan ya bai wa Dadda yin wani tsafi wanda ta jawo wasu tsoffin ruhika da zamaninsu ya shuɗe.Kamar wasu likitoci haka suka zagaye Izzatu kowanne yana nasa aikin sai dai sam sun ƙi yin nasara game da abin da suke buri a dole suka haƙura.

Lokacin sallar azahar na yi Izzatu ta farka ta je ta yi,haka ta wuni tana tunanin irin yadda Yarima David ya bushe mata ido ita ɗaya kuma sai ta yi ta murmushi a haka dare ya same ta.Bayan ta gama shafa'i da witiri sai ta yi zaune kan sallaya idonta na rufe da bandejin da Dadda ta saka mata.Tasbihi ne take ta jerowa haɗi da kirari ga Ubangijin talikai tana jin wata nutsuwa na ratsa ta,a daidai lokacin ne kuma aljanar Yarima David ta yi ƙoƙarin kusantarsa sai dai kash addu'ar kariya da neman Allah ya saka hannu a lamurran sarkin daularsu na gobe yasa ta kasa mu'amulantarsa.

A wannan daren sam Izzatu ba ta yi bacci ba,wani irin sabon yanayi take ji yana bijiro mata wanda ba taɓa sanin kanta da shi ba.A hankali ta tashi kamar makauniya ta soma yin lalube sai kuma wani abin mamaki sai ta ga wani haske ya fito mata a tsakiyar goshi wanda ke bata damar gani duk da idonta a rufe suke.Sam ko kaɗan tunaninta bai bata cewa ido uku ne gare ta ba,biyu na normal mutum ɗayan kuma wanda ababen bautar kakanni da iyayenta ne suka tsaga mata ita wacce za ta dinga bata damar ganin abin da mayafin sirri ya ɓoye.Cak ta yi tsaye tana kallon Dadda wacce ta sharar baccinta da gibjejen kanta irin na Saniya,yadda zuciyarta ta soma bugawa a tsiyace shi ya bai wa masu kula da idon goshin saurin rufe mata ita sai ta bar ganin komai.Ji ta yi wani abu ya matsar da ita shuuu ya kai ta dab da ɗan madaidaicin gadonta na itace,babu shiri ta kwanta tare da soma karanta “hasbunallahu wa ni'imal wakil!” cikin ikon Ubangiji ta samu salamar ruhi ta yi baccinta.

★A can ɓangaren EZRA kuwa duk da Yarima David ya bada umarnin a damƙo ahalin gidansu hakan bai sa dakaru sun rufe ta ba. Gida ta koma ta je ta yi tsaye gaban baƙar rijiyar tsafin da mahaifiyarta ta nuna mata ita da kuma yadda ake amfani da ita.Cikin ƙwarewa a wurin tsafi ta soma kiran baƙaƙen ruwan da ke kwance a rijiyar,nan suka fara yin zillo suna tumbatsa sai dai fa sam ta kasa taɓuka komai game da Yarima David saboda shi ne zaɓin ababen bautarsu.

Duk da haka EZRA ba ta karaya ba da dare ya yi sai da ta ƙara gwada sa'arta sai dai wannan karon garkuwar da ke bai wa Yarima kariya ta sha banban don kuwa wannan garkuwar hasken rahama ce .Cike da tsoro da firgici ta soma kiran ruhin Goggoji wato aljanarsu babu jimawa wata baƙar siffa marar kyawun gani ta fito daga can ƙasan rijiyar tana mai bata amsar abin da take son sanin cikin wata irin murya ce marar daɗin amo sannan a Yaren mutanen farko take cewa “garkuwar Yarima tana cikin Daular Alfanso,ba iya garkuwa ba ce ita ce sarauniyar gobe muddin ba ki yi wani abu ba to za ta hana ki cikar burinki da na mahaifiyarki”

Cikin ɓacin rai EZRA ta yi wani ihu wanda ya haifar da rikiɗewar harshenta ya koma wani baƙin maciji,idonta ma suka juye suka dawo wasu kore kafin ta fara aman furicin ɗaukar fansa tare da alwashin ko wace ce mai bai wa Yarima kariya ita ce za ta zamo ajalinta......

My book is only 500 via

2670215530
ZULFAU YAHAYA
Ecobank

DM +22795045822
[10/11 19:33] MRS SADAUKI: *INUWAR ALJAN*👻

```LoVe aNd HoRrOr story```👽

By
Chamsiya Laouali Rabo
{MRS SADAUKI💫✍️}

*SADAUKARWA:* Ga Rachida Mamar ƴan biyu, alherin Allah ya luluɓe ki . Ubangijin rahama ya kula da lamurranki👏🏻

*FCWA*☀️

________________________

BONUS

Daga yau Laraba bonus zai tsaya da zarar na saki page 10 to 500 ne,yanzu kuma bonus za ki tura 300 VIA 2670215530
ZULFAU YAHAYA
Ecobank DM +22795045822 .

09

#Yarima David

Tsawon kwana biyu ban saka baiwa Izzatu a idona ba,tun ranar da ta zo wanke mini ƙafafuwa sabulu ya shigar mata a ido.Duk yadda na so kuma na watsar da zancen nata sai na ji na kasa ina son jin labarinta.Yau rana ta uku kamar yadda na samu canjin wacce ke zuwa tana yin ayyukan da baiwa Izzatu ke yi,tana shigowa ta gaishe ni cike da ladabi tana shirin kwasar kayan wanki na ce “ina waccan baiwar?”

Ba tare da ta ɗago ba ta bani amsa da “ba ta da lafiya,idonta ya samu matsala ”

Haka kawai na ji ƙirjina ya buga,na ce “makancewa ta yi ko me?”

“Eh to hakan dai na ji ana faɗa amma ban tabbatar ba” ta bani amsa kanta na ƙasa har yanzu.

“Okay! Ki yi mata jagora zuwa nan ɗin” na faɗa cikin wata irin izza da ban san yaushe ta ratsa jinina ba.Sai da ta ɗan rusuna kafin ta ce “an gama ranka shi daɗe ” sai ta fice.

Bakin window na je na yi tsaye ina kallon yadda bayi ke ta kai komo a cikin katafariyar farfajiyar masarautar.Yadda nakasa ba ta hana wasu daga cikin bayin aiki ba shi ya fi komai burge ni,saboda ina son mutum mai jarumta.Ina nan tsaye na ji suna neman izini,ba tare da na juyo ba na ce “ku shigo!”

Da sauri kuma na lumshe ido jin amon muryartar na furta kalmomin amincin Ubangijinta a gare ni,duk da cewa ni ɗin ba musulmi ne ba amma na ji daɗin haka sosai.A hankali na juyo,idona suka yi tozali da ita tana sanye cikin wani pink ɗin hijabi har ƙasa idonta na naɗe da wani jan ƙyalle.Ɗayar baiwar na kalla,da mugun sauri ta fice har tana tuntuɓe.
Chapter 25 · 0% Book details