← Book details Matar Mustapha Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 28

Sashe 8

Matar Mustapha Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Laha ila! Mi nake gani? Daga cin abinci shine ku ka wani zo ku ka kwanta kamar an yi jeran kwanoni? Ke Shamseeya keee?" Inna ta faɗa ta na janye ta daga jikin Mustapha,ashe ita ma baccin ya ɗauke ta .
Cikin kukan shagwaɓa ta ce "Inna ki ƙyale ni" luuu ta koma ta sake komawa ta lafe bayan Mustapha wanda tuni shi ma ya farka sai dai ba zai iya tashi Inna ta gan shi cikin wannan yanayin ba.

Dukan tsiya Inna ta yi mata haɗi da jan SEEYA zuwa can tsakar gida.
Mustapha ya ce "kai wannan masifa da mi ta yi kama? Mutum da matar shi amma a hana shi ya huta!" Ya faɗa a bayyane kafin ya zura jallabiya ya je ya yi wanka.

Inna ta ƙasan ido take kallon shi ta na jan baki, Mustapha ya kimtsa kan shi sannan ya fito cikin shiri.
"Ina kuma za ka je da wannan jakar?" Inna ta tambaye.
"Madarumfa zan je na yi masu kwana biyu!" Ya bata amsa "ka kyauta kuwa Allah tsare hanya ka gaishe da mutan can"
"Za su ji! Ina SEEYA ?"
"Na aiketa,ai gwara ka yi sauri kar ta dawo ta hana ka zuwa" ya yi murmushi ya fice.

Tashar mota ya je ya shiga motar da za ta kai shi garin mahaifiyar shi wanda yake zuwa lokaci zuwa lokaci.
Sosai su ka yi murnar zuwan shi, musamman Kakar shi wacce ta haifi Hajara ita ma ta tsufa sosai fiye ma da Inna.
Sai da ya zaga garin sosai ya ga ƴan uwa,duk inda ya je sai an tada maganar mutuwar Mamarsa.

★Kwanan Mustapha biyu sannan ya dawo Maradi.
SEEYA ta juye kai kamar ba ta gan shi ba wai ita ala doli fushi take da shi.
"Babyna zo ki ga abin da na sayo miki" ya furta ya na sakin murmushi mai sauti,SEEYA ta maƙe kafaɗa ta ce "ban so ba tafiya ka yi ka bar ni ba?"
"Yi haƙuri mana ,ke da za mu je Tilliya mine ne kuma na fushi?" SEEYA na jin haka ta washe baki tare da nufar shi.
Inna ta girgiza kai ta ce "ƙuda wajen kwaɗayi dai yake mutuwa" SEEYA ta turo baki Mustapha ya ce "kar ki kula ta kishi ne take don nace ban son ta"

Da dare da Baba Malam ya zo ya ke shaida ma Mustapha yadda suka yi da dangin Baban SEEYA .
"Sun ce a basu nan da wata biyar,sannan su na buƙatar a kai masu Seeyar ta zauna can har ayi bikin"
Mustapha ya yi shiru can ya ce "amma Baba ba ka faɗa masu da ita zan je ba?"
"A'a ! Kai dai yanzu ayi yadda suka ce ɗin tun da Ƴar su ce,gobe in sha Allah zan kaita da kaina" Baba Malam ya faɗa ,jikin Mustapha duk sai ya yi sanyi.
Watanni biyar ɗin da aka ce sai ya ji su tamkar shekaru biyar ne,sai dai bai da wani zaɓi.
Tun da wuri ya shige ɗaki ya kwanta kamar wata kaza,idonsa ƙurrr akan ƙofar shigowa har ya gaji da jiranta can sai ga ta.

Inna sai masifa take ya na jin ta,da alamu ba da son ranta Seeyar ta zo gun shi ba.
Kusa da shi ta zauna ta na kallon shi kamar yadda shi ma idonsa ke kanta.
"Yayana don Allah gobe ka shirya sai mu tafi tare ka ji?" Ta yi maganar idonta na rau-rau.
Ya lumshe ido haɗi da jawota ta faɗa ƙirjin shi,cikin kunnenta ya raɗa mata "ki haƙuri ki je Babyna ai za mu haɗu,ni ma nan cike nake da zullumi don babu yadda zan yi ne" SEEYA ta ɗan janye daga jikinsa ta hanyar ɗago kanta ta na mai ɗora tafukan hannuwanta kan ƙirjin shi.

Ta na shirin yin magana ya juye da ita,sai ya zamana ta koma ƙansa shi.Shiru ta yi ta kasa cewa komi sai aikin kallonsa, Mustapha ya ɗan waiga ya kalli ƙofa ya ga ruf take da labule sannan ya yi ƙasa da kan shi wajen fuskarta ya kamo laɓanta ya fara sumbata.

SEEYA ta lumshe ido zuciyarta na bugawa, Allah na gani duk lokacin da yake mata irin wannan abun sai ta ji sam ba za ta iya kallon shi ba.
Sumba yake mata ta fitar hankali sai numfashi yake sauke wa kamar wanda ya yi tsere.Can ya tsaya,SEEYA ta buɗe ido ta na so ta tashi sai dai ya yi mata rumfa da ƙirjin shi duk da bai sakar mata nauyi ba.

"Je ki rufe ɗaki!" Ya fizgo furucin dakyar ya na mai mirgina wa gefe.Ba tare da wani tunani ba ta sauka ta rufe ɗakin,da hannu ya yi mata alama akan ta kashe hasken ɗakin.
"Yayana tsoro nake ji" ta furta ta na fiddo ido ,"babu abin da zai same ki ba ga ni ba? Kashe ki zo"
Ta kashe sannan ta nufi bakin gadon , Mustapha ya jawo ta ya jikinsa bayan ya cire mata doguwar rigar jikinta.
Jin ya na romance ɗin ta ya saka SEEYA firgita ,sosai take jin zafi ƴan ƙirgen dangin ta sun shiga hannun TUZURU (MRS SADAUKI) kuka ta fara yi mishi da sauri ya toshe bakin ta hanyar saka halshen shi bisanin ya haɗe bakin su.

Washegari
Kuka SEEYA ta ke kamar ranta zai fita yayin da Inna ke masifa ta na cewa "ai ga irinta nan ya yi mata fyaɗe jini ya ƙi tsayawa.Amma Mutapha ka ji kunya,ka kuma ci amanar da aka bar ma.Innalillahi wa'inna ileyhi raji'un! Yau ni na ga ta kaina! Ke kwanta in gani"

Mustapha na daga gefe,in ransa ya yi dubu to ya ɓace.Baba Malam kuwa matsowa ya yi kusa da shi ya ce "mi yasa ka kusance ta?" Mustapha ya haɗiye wasu yawu muƙut ya ce "Baba wlh ban yi mata komi ba"
"Au! Shi kuma jinin da yake mata zuba fa? Haihuwa ta yi komi?" Inna ta faɗa cikin masifa.
"Kin manta akwai jinin girma na haila?" Cewar Baba Malam,tsit Inna ta yi can kuma ta yi ma SEEYA dundu " shi ne dan uban ki ba za ki faɗa ba? Wannan shegen kukan da take duk ya ruɗa ni sam na manta"
Cikin zafin rai Mustapha ya shiga ɗaki ya gangame kayan shi cikin ƙatuwar jaka ta sojoji kafin ya fito tsakar gida.....
[09/11 15:33] MRS SADAUKI: *MATAR MUSTAPHA*
LOVE STORY

```MRS SADAUKI```💫 ✍️

DEDICATED to MY SADAUKI🫡

FCWA ☀️
_________

8

Daga can banɗaki yake jiyo yadda Inna ke yi ma SEEYA dundu haɗi da balbalin masifa,dama ransa a ɓace yake bai san lokacin da ya ƙarasa banɗakin ba.
Tamkar wata mai jego haka ya tarar ta na yi mata wanka,ita kuma SEEYA sai kuka take na jinin da ta gani ya na zuba a jikinta.

"Ya kamata dai daga yau kar ki ƙara yi mata wanka ki bari ta yi kayanta da kanta" Mustapha ya faɗa cikin dakakiyar murya.
Inna ta ɗago ta ce "to Ubana! " Tare da yi masa wani mugun kallo,cikin ƙunar rai ya bar gidan.

SEEYA kam ta kasa gane wannan yanayi da take ciki har sai da Inna ta yi mata bayani.
"Duk macen duniya ta na yin jinin haila,alama ce ta girma don haka ki rufe mini wannan shegen bakin naki kamar an yi Yamma da Kare" Inna ta faɗa ta na mai yi ma SEEYA ƙunzugu.

Tamkar wata marar lafiya haka ta koma,sam ta kasa walwala ga shi kuma sam Mustapha bai nan.
"Ki haɗa kayanta yanzu za mu wuce" cewar Baba Malam.
Inna ta fiddo jakar kayan SEEYA ,wani bayanin ta sake yi mata "in kin ga ƙunzugun ya ɓace ki wanke shi sai ki saka wani " SEEYA ta gyaɗa kai ta na shafar hawaye.
Ita da Baba Malam suka shiga mota har G/R , wannan ne karon farko da ta je gun dangin mahaifinta sam ba ta san kowa ba.

Hajiya Habsu wacce ta kasance Kakarta ce ta zo ta ja hannunta,SEEYA ta kalli Baba Malam da ke yi mata murmushi.
"Ki saki jikin ki nan gidan ku ne" cewar Hajiyar kafin mutanen gidan su fara yi mata magana su ma.
Lokacin da Baba Malam zai tafi kuka wiwi SEEYA ta ɗora masu,Abdul wanda ya kasance shi ma jikan Hajiya ne shi ya daka mata wata tsawa wacce ta sa hanjin cikinta juyawa.

"In na sake jin kukan wlh sai na yanke miki halshe,baƙauya kawai .Yanka ki za a yi ko kuma dukan ki aka yi da za ki ɗora mana koke-koken banza" magana yake ya na juya jajayen idonsa na tantiri.
SEEYA ta shiga hankalinta don ba ta hango sassauci a tattare da shi ba, musamman da ta lura kusan kowa na gidan shakkar shi yake saboda dabancin shi.

"Abdul mine ne haka? Kar ka firgita mini jika" cewar Hajiya Habsu,shi kuma babu ta ido ya maida mata martani "wa ya sani ko jinin ki ce,ƙila ma bare ce"
"Ko ma dai mice ce babu ruwan ka mai mugun hali! Halin ka halin mahaifiyar ka ai ko ma mine ne ita ta yi maƙasundi raba auren wanda a ƙarshe na rasa Ɗana" Hajiya Habsu ta faɗa cikin ɗaga murya.
Abdul ya sheƙe da dariya ya ce "ƴar tsohuwa ki iya bakin ki kar ki sake ambaton sunan mahaifiyata"

Rahamu wacce ta kasance Yayar Lawali,uwa ga Abdul ta yi saurin fitowa ta na tsawatar mishi.
"Abdul kar na sake jin muryar ka,babu ruwan ka da ita " ta faɗa ta na hararen SEEYA wacce tun lokacin da aka shaida zuwanta Rahamu ta bar tsakar gidan.

Abdul ya bar gidan ya na zage-zage,yayin da Hajiya Habsu ta ja SEEYA izuwa ɗakinta.
"Kar ki damu da abin da su ke cewa,su ɗin mahassadan mahaifin ki.Ita wannan uwar Abdul ɗin ba mutumniyar kirki ba ce,ita ta yi asirin raba iyayen ki .Baƙin halinta ya saka mijinta rabuwa da ita shi ne ta dawo ta tare ita da shegen ɗan ta"

SEEYA ta ce "Ni dai tsoron shi nake!"
"Kar ki damu babu abin da zai yi miki,zo ki ci abinci ki kwanta ki huta in kin tashi sai ki bani labarin makaranta" Hajiya ta faɗa ta na jawo kwanon abinci.
Chapter 8 · 0% Book details