← Book details Matar Mustapha Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 28

Sashe 12

Matar Mustapha Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

MUSTAPHA
Lokacin da ya ɗauki waya ya ga saƙonnin SEEYA ji ya yi kamar zai mutu tsabar daɗi,karanta su yake ya na sake maimaita wa a ƙarshe ya danna mata kira ta ɗauka ta na cewa "my dear Yayana" ya lumshe ido ya ce "na ga saƙonni na gode my Baby Allah bar mini ke! " Wata kunya ta ji ta rufe ido har da rufe ido kamar ya na ganinta ta ce "babu komi Yayana,ya shirye-shiryen tafiyar ?" Ya ce "sai nan da 2week fa,kafin mu tafi zan zo Gidan Rumji na gan ki ko na minti biyu ne" da sauri ta ce "da gaske Yayana?" Ya bata amsa da "sosai ki shirya tarbe na" "ka rantse da Allah za ka zo" ta yi maganar cike da ƙurciya har sai da Mustapha ya saki murmushi mai sauti ya ce "na rantse da Allah Baby zan zo" sam ta kasa ɓoye farin cikinta,duk da a waya ne bai hana Mustapha fahimtar haka ba.
Hira suka ɗan taɓa ta na bashi labarin makaranta wanda rabinsa duk na Maimunatu ne,shi kuma ya na sauraren ta bisanin su yi sallama.

SEEYA ta fito tsakar gida jin ihun yara ,tsaye ta yi ta na kallon yadda Abdul ke rarraba masu kayan daɗi irin su Chocolat, biscuits da dai sauransu.
Ya na son baiwa SEEYA sai dai yadda ya ga Ummarsa ta na hararanta yasa ya ƙi kiranta,"Umma zan yi wanka ungo kuɗin da za ki yi sayayyar kayan abinci na wata guda"
"Abdul ka sawo shinkafa da macaroni fa kuɗin kamar sun yi yawa" ta faɗa cikin so da ƙaunar Ɗa ɗaya tilo a gunta.
"Ke dai kawai ki yi amfani da shi" ya na gama faɗa ya nufi banɗaki.

SEEYA ta koma ɗaki ta na gaya ma Hajiya abin da ya faru "hum! Shashashar Uwa gare shi maimakon ta tambaye shi ina ya samo kuɗin a'a murna ma take taya shi,ko shi Kawun naku ba wani son shi yake ba kawai dai don ya na yi masu hidima"
"Ni fa bai bani komi ba" cewar SEEYA,Hajiya ta ce "bari na baki ki je ki sayo dama ɗazu aka kawo mini kuɗin haya ina son na je kasuwa na sayo abubuwan da za mu buƙata"
Su na tsaka da hira Kawu Aminu ya shigo ɗakin a hasale kamar zai bi takan SEEYA,ko gaishe da Hajiya bai yi ba ya ce "aka ce kin sayar da gonarmu ta gado ina kuɗin suke? Mi ki ka yi dasu?"
A mamakance Hajiya ta dube shi sai kuma ta mayar da dubanta ga SEEYA wacce tuni ta fara kyarma.
"Hajiya tambaya nake ina kuɗin suke?"
"Ban sani ba! Shi wanda ya faɗa ma na sayar da gonar ya zo ya shaƙe ni sai in faɗi inda kuɗin suke"
"Amma ai dai kin san gonarmu ce ta gado ko? Ya zama doli a shawarce mu kafin ayi komi"
"Ina ce shi ma Lawalin ba shege ba ne ya na da haƙi akai,to kason shi na ɗiba na yi ma ƴarsa gata"

Kawu Aminu ya waro ido,har zai yi magana kuma sai ya fita ya na ƙyaci.Ko minti biyu ba a yi ba da fitar shi ita ma Ummar Abdul ta fara masifa tsakar gida,a ƙarshe dai suka yanke shawarar sayar da sauran gonakin da suka yi saura ba tare da Hajiya ta san wainar da suke toyawa ba.

"Wannan banzan tsoron naki ina son ki mayar da shi gefe,ita duniya ba ta son matsoraci doli ki jajirce akan komi.Daga lokacin da mutane suka fahimci raunin ki shikenan za su yi ta cutar da ke ne" Hajiya ke faɗa ma SEEYA bayan fitar Abdul,kai kawai ta gyaɗa ta na ɗan jin ƙwarin gwiwa.

★A sannu a hankali jikin SEEYA ya fara canzawa ta na murmurewa tare da zama luluta ta gaske,sam ba ta san gumbar da take sha ba don haɓaka jikinta ba ne.Hankalinta a kwance yake musamman da suke waya da Inna ga kuma Mustapha kullum cikin hirar soyayya suke duk dai ba ta ida fahimtar ta ba.
Tun da sahiya ta waye Mustapha ya shaida mata nan da kwana biyu zai zo take farin ciki.
Ta yi wanka ta na tsaka da shafa mai ta fara jin hayaniya,da sauri ta gyara ɗaurin ƙirjinta saboda yanzu albarkatun fulaninta sun tsiro sosai.
Labule ta ɗaga ta na leƙo kanta,sojoji ta gani haɗi da ƴan sanda da kuma ɗaiɗaikun mutanen unguwa.
Can kuma ta ga an tiso ƙewar Abdul hannunsa sanye da Ankwa yayin da kuma aka ɗora bindiga a gefen wuyansa,da sauri SEEYA ta fito babu shiri ta na furta "innalillahi wa'inna ileyhi raji'un!" Da ƙarfi wanda har sai da ta jawo hankulan mutane,ciki kuwa har da Abdul.

Lafiyayyar fatar jikinta kawai da ya kalla ta mantar da shi tsaka mai wuyar da yake ciki,bai farga ba ya shagala da kallonta ya ji an buga masa kan bindiga ga hanci ya saki ƙara tuni kuma ji ya fara zuba.
Aka wuce da Abdul nan ƴan gulma suka fara tsiyar gumi,Hajiya ta yi saurin isowa gun SEEYA ta ja ta zuwa ɗaki.

"Mine ne na fitowa haka babu hijabi sai ɗaurin ƙirji?" Hajiya ta tambayeta a hasale.
"Hajiya na rikice ne,wai mi Ya Abdul ɗin ya yi?"
Hajiya ta ja baki " hum! Bank suka fasa suka sato kuɗi, binciken da aka yi ta yi aka gano ɗaya daga cikinsu shikenan ya tona asirin kowa" SEEYA ta waro ido "duk facakar da ya yi ta yi da kuɗi ashe na sata ne? Tabbb! Allah ya taimake ni bai bani komi ba da yanzu har da ni za a kama"
"Yi sauri ki shirya ki tafi makaranta da wannan sakalcin" SEEYA ta turo baki,ta buɗe kayanta breziya ta ɗauko wacce Maimunatu ta saya mata.
Mi Hajiya za ta yi in banda dariya "SEEYA yaushe ne breast ɗin suka fito da har aka fara saka masu breziya?" Ba ta bata amsa ba sai kukan sangarta da ta saka.

Masu son ci gaban labari za su biya only 500 via 2670215530
ZULFAU YAHAYA
Ecobank DM +22795045822
[10/11 19:28] MRS SADAUKI: *MATAR MUSTAPHA*
LOVE STORY

```MRS SADAUKI```💫 ✍️

DEDICATED to MY SADAUKI🫡

FCWA ☀️
_________

11

"Wayyo Allah ni na ga baƙar rana ,wane irin bala'i ne wannan? Na shiga ukuna ina aka tafiyar mi da Abdul?" Kukanta ne haɗi da sabatu ya cika gidan, kasancewar ba ta nan lokacin da aka kama Abdul ta na can mayanka sayen nama.
Hajiya ta fito ,"wannan kukan da ki ke ba shine mafita ba,yo ai dama kin san da zuwan wannan ranar tun da har ki ka zura masa ido ya na yin abin da ya ga dama.Lokacin da ya kawo maki maƙudan kuɗi mi yasa ba ki bincike daga ina ya tawo da su ba?"
Ande ta buɗe ido kukan nata ya tsaya cak,sam ba ta san sata ce Abdul ya yi ba.Ƴan gulma sun dai ce sojoji sun kama Abdul sun tafi da shi.
Ɗakinta ta shige ta ci gaba da kuka Hajiya ta girgiza kai kawai,yayin da SEEYA ta fita sakamakon ganin Maimunatu wacce ta biyo mata kamar kullum.

"SEEYA mi yake faruwa na ga duk mutane a ƙofar gidan ku?" Maimunatu ta tambayeta.
Ta ja baki ta ce "Ya Abdul ya yi sata yanzu ƴan sanda da sojoji suka tafi da shi" Maimunatu ta waro ido can ta ce "kuma wani ɓangare abun murna ne musamman a gare ki shikenan kin huta da tsangwamar shi na kwana biyu"

SEEYA ta yi dariya ta ce "wane irin kwana biyu? Hum! Bank fa ne suka yi fashin ai sai zancen watanni" da sauri Maimunatu ta ce "a'a wannan sai shekara ma.Ya ne ya shirye-shiryen tarben soja?" Ta canza zancen.
"To shirin mi zan yi? Ina nan ina jiransa dai" Maimunatu ta ɗan bugi bayanta ta ce "baƙauya kawai! Yau in mun sauka daga makaranta za mu je wajen mai lalle ta yi miki,gobe kuma mu je salon ayi miki gyaran gashi"
"Ni fa ban taɓa yin lalle ba,Inna ta hana "
"Mtsw! Ke komi Inna ! To ai yanzu ba gidanta ki ke ba"
"To mu fara zuwa gyaran gashin dai" cewar SEEYA,nan suka ci gaba da tattaunawa har suka isa école.
Duk cours ɗin da ake SEEYA ba ta wani fahimta sakamakon hankalinta da ya rabu gida biyu, Mustapha kawai ta ke tunani ta matsu su ga juna.
"Shamseeya fita ki bani aji" Mr ɗin su ya faɗa wanda yake lura da ita sai murmushi ta ke saki.

SEEYA ta dawo hayyacinta ta fara wiƙi-wiƙi da ido ya ce "ko ba ki ji abin da na ce ba?" A tsawace ya yi maganar wanda ya saka SEEYA fashewa da kuka ta na cewa "don Allah Mr ka yi haƙuri" ransa ne ya kuma ɓacewa ya zo da ƙarfi ya jawo hijabinta har sai da kanta ya bugu ga table ,ya yarɓa ta waje da sauri Maimunatu ita ma ta ɗauki kayanta ta bi bayan Seeyar.

"Ke dallah Malama bari kuka,yo ai mu gaba ta kaimu gobarar Titi! Zo mu tafi salon " cewar Maimunatu, SEEYA ta bi bayanta kawai ta na sharar ƙwalla.

Goshin SEEYA tuni ya yi ɗan kumburi sai da Maimunatu ta taimaka ta murje ƙululun.
Manyan kitson kanta aka fara kwancewa bisanin a shafa mata apple,kamar minti ashirin aka wanke.Gashin SEEYA ya yi wani mugun sulɓi da baƙi sai kuma ya ƙara tsawo.

Bayan an tsane gashin mai salon ɗin ta gyagyara shi sannan ta shiga casque,irin iskan nan mai zafi da ke fitowa ya saka SEEYA fara ɓata rai.Duk yadda ta so ta fito Maimunatu ta hana har sai da gashin ya bushe ringis,da ta fito ta na ta hararen Maimunatun yayin da mai salon ta shafa mata mai da turare.
Chapter 12 · 0% Book details