← Book details Matar Mustapha Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 28

Sashe 10

Matar Mustapha Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

" Har kin je gidansu kenan?"
"A'a tukunna dai"
"Ya aka yi to ki ka san da nan Layin take?"
"Ita ta faɗa mini mana,ina abincina?" SEEYA ta tambaya ta na mai sauya zancen.
"Yau ban yi girki ba,ina jira masifafiyar can ta aiko nata amma kin ga shiru har yanzu ta ƙi kawowa kamar da gayya" Hajiya ta bata amsa.
"Ni taliya da wake na yi marmari ki bani kuɗi na sayo" SEEYA ta faɗa ta na mai zowa kusa da Hajiya ta zauna daɓass ta na turo baki.

"To ki cire uniforme ɗin ki sauya kaya,Allah ta gama taliyar" Hajiya ta faɗa ta na mai kwance haɓar zanenta don kwance kuɗi.Da murna SEEYA ta tashi ta cire uniforme ɗin ta sauya zuwa riga da zane haɗi da ɗaura kallabi.

"Ke ina za ki je?" Ta ji muryarsa a bayanta,tsabar tsoro ta razana murfin kwanon hannunta ya faɗi ƙasa.
Baki na ɗan rawa ta ce "abinci zan sayo"
"Duk abincin da aka girka bai ishe ki ba sai kin fita? To babu inda za ki je koma" Abdul ya faɗa cikin game fuska.

SEEYA uwar tsoro ko murfin kwanon ba ta ɗauka ba ta yi gaba tare da shiga ɗaki ta na sharar ƙwalla.
"Lafiya? Ba ki samo taliyar ba? "Hajiya ta tambayeta.
"Ba Abdul ne ya ce babu inda zan je ba" ta faɗa cikin kuka,Hajiya ta miƙe cikin masifa ta na cewa "akan mi ba za ki sayo ba? Mu je" ta tisa ƙeyarta suka fito.

Abdul na zauna kan wani ƙaton icce ya na faman busa sigari Hajiya ta fito "nace a wane dalili a ba za ta tafi ta sayo taliya ba?"
"Saboda ba na so!" Ya bata amsa kai tsaye,Hajiya ta waro ido ta ce "kai wa?"
"Ni Yayanta ! Ina ce dai ƙanwa ta ce ko ba komi zan kula da tarbiyyar ta na hanata fita yawo"
"Sayen abincin ne yawo? Wai ma yaushe ta zama ƙanwar ka?"
Bai ba Hajiya amsa ba sai SEEYA yake kallo wacce ta zuro masa ƙwalaƙwalan idonta ta na kallon shi,alamu jira take ya bada yardar shi ita kuma ta tafi.

"Wuce ki tafi ki sayo kin wani yi tsaye " cewar Hajiya , SEEYA ta yi saurin ficewa da sauri.Abdul ya yi ƙyaci wanda ya sa Hajiya yin tsaye har sai Seeyar ta dawo suka shige ɗaki.

"Allah sarki Yayana yau ga shi zan ci wake ba tare da kai ba" SEEYA ta faɗa ta na murmushi tuna babu abin da Mustapha ya fi so kamar wake.
Hajiya ta ce "au! Na manta ban faɗa miki ba,ɗazu an kawo waya har da layi aka ce wai a baki kafin na kai ga tambayar wanda ya aiko kuma da aiken ya yi tafiyar shi" Hajiya ta faɗa ta na buɗe kwalla ta fiddo ƴar ƙaramar waya itel sabuwa dal da ita.

SEEYA ta karɓa ta jujuyata gabanin ta kunna,hoton Mustapha ta gani kan screen ɗin ya na sayen da kakin soja.Nan take wani sanyi ya mamaye ta ,annurin fuskarta kuma sam bai misaltuwa.
"Yau na ga shirme! Ke ɗaya ki ke murmushi ki na kallon waya?" Cewar Hajiya , SEEYA na shirin gwada mata hoton kira ya shigo.

```ANGON SEEYA``` shine sunan da ya fito,ta saki murmushi ta na ɗaukar kiran "Yayana!" Ta furta,daga can ɓangaren Mustapha ya ja numfashi haɗi da sauke wata wasiyyar ajiyar zuciya kafin ya ce "umhum!" Ta turo baki kamar ya na ganinta ta ce "ka manta da ni" ido ya sake lumshewa ya na mai cewa "ban kai wannan matsayin ba! "
"Hum! Ba wani!"
"Allah kuwa Baby! In na mance da ke to mine ne amfanina kenan? In babu ke babu ni !" Ta saki murmushi sosai wanda wushiryarta ta fito ,har cikin ƙawon zuciyarsa ya ji daɗin sautin murmushinta.

"Ya ki ke Baby? Ya Hajiya ? Fatan komi lafiya?"
"Eh lafiya lau,Hajiya ga ta nan zaune bari na baka ita" ba tare da ta jira abin da zai ce ba ta miƙa ma Hajiya wayar,nan suka gaisa ita Mustaphan kafin ta mayar ma da SEEYA wayar.

"Baby ki tashi daga gaban Hajiya kin ji!" Mustapha ya faɗa cikin sanyin murya, SEEYA ta dubi Hajiya sai ta ga ashe ita ma kallonta take.
Mustapha ya ce "ko ba ki ji ba ne?" Ta ce "umhum?"
"Nace ki tashi daga gabanta" ya sake faɗa,shiru SEEYA ta yi ta kasa tashi sam.

"To sai an jima tunda ba za ki tashi ba" ya faɗa kamar zai kashe wayar,da sauri ta miƙe ta nufi ƙurya ta na cewa "don Allah Yayana kar ka kashe, na tashi" Mustapha ya ja ajiyar zuciya kafin ya ɗora da "ba ki yi kewata ba?"
Ta bashi amsa da "na yi"
"Wajen mi ki ka yi kewata? Sannan mi ki ke tunawa game da ni ?" Shiru ta yi don ba ta san takamaimai abin da yake nufi ba.

Fahimtar haka ya sa Mustapha cewa "kin ga ni na yi kewar laɓan ki,ina son sake sumbatar su na rungume ki a jikina" wani abun mamaki ya faru ga SEEYA,jikinta ya ɗan fara rawa jin furucin shi yayin da kuma ta fara jin wani yanayi da ba ta san na mine ne ba ko kuma mi ke kawo hakan.

"Allah Baby na yi kewar ki sosai ko aiki nake tunanin ki nake! Jiya fa saura ƙiris na saɓa saiti da mu ka je horon halbi"
"Ni ma na yi kewar ka sosai Yayana!" Shi kawai ta iya furtawa.
"Baby ki kula mini da kan ki banda wasa da mazan makaranta,sannan in ki na da damuwa ni za ki faɗa ma ko kuma haka wata ƙawar ki da ki ka yarda da ita"
SEEYA ta saki murmushi ta ce "Yayana na kuwa yi Ƙawa yau da na tafi makaranta" nan fa ta fara bashi labarin Maimunatu wacce ba ta sani ba tuni shi Mustaphan ya san da zamanta har ma sun tsara wani plan a kai.

"In sha Allah nan da wata huɗu zan zo don fara shirye-shiryen bikinmu"
"A'a Yayana ka bari har wata shekara"
Ya waro ido ya ce "Baby ba ki tausayina? Wace irin shekara kuma ana zaman lafiya?" Ta turo baki ta ce "Ni fa ban so na bar Maimunatu"
"Au ! Maimunatu ta fi ni kenan?" Ba ta kai ga bashi amsa ba ƙittt ya kashe kiran.

SEEYA ta dubi screen ɗin wayar ,ta ga kiran ya yanke.Za ta fito suka ci karo ita da Hajiya wacce ta yi masu laɓe.
"Har kun gama wayar?" Hajiya ta tambaya, SEEYA ta gyaɗa kai kawai.

Hajiya tunanin mafita kawai take,don a yadda ta ji muryar Mustapha ma kawai ya tabbatar mata halin da yake ciki,uwa uba kuma yanzu da ta saurari wayar su.
A ƙarshe ta yanke shawarar da ta ga ita ce mafita a gare ta da kuma Jikarta.

★Haka kawai Mustapha ya ji kishin Maimunatu ya kama shi, Umar da ke gefen shi ya na ƙumshe dariya ya kalla "lafiya mine ne na kallona?" Mustapha ya tambaya ya na haɗe rai.

Umar ya sheƙe da dariya ya ce "ah to ba doli ba na ga ƴar ƙwaila ta na gigita abokina,dube ka fa yadda hankalin ka ya tashi wai ma a waya ne to ina ta na gaban ka? Hum! Malam gaskiya ina goyon bayan Inna da ta hana ka SEEYA,don wlh inda ta baka ita ba ƙaramin kuskure ta tabka ba"
Mustapha ya kai masa duka a baya ya ce "duk baƙin cikin ku dai Baby matata ce kuma doli a bani abata"
"A'a ba dai ta na ƙwailarta ba,yo wannan tashin hankali da mi ya yi kama? Hhhh! Ai wlh abokina ina gaya ma ko budurwa ƴar shekaru ashirin ta haɗu da gamu da kai to sunanta sorry!"

"Mtsw! Ɗan iska banda lokacin ka" Mustapha ya faɗa tare da shiga toilet,Umar ya ce "ai gwara ka yi wankan ko ka samu sa'ida" .

★SEEYA

Sam ba ta yi tunanin fushi Mustapha ya yi ba,sai dai ba ta ji daɗin ƙin sake kiranta da bai yi ba ga shi har dare ya yi.Sam ba ta san takan waya ba sosai,amma ta san yadda ake aika kira.
Lambar shi ta kira har ta gama ruri bai ɗauka ba,a haka ta yi ta jera mishi kira ya fi goma amma shiru.Zuciyarta ce ta karaya,tuni hawaye suka fara yi mata zuba su na ɓata pilow ɗin da ta tada kai da shi.
Zuwa yanzu ta fahimci fushi ya yi 'saboda kawai nace a bar bikin sai nan da shekara shine ka share ni? Yayana mi yasa za ka mini haka? Ko dai na shirya na tafi Tilliya ba tare da sanin kowa ba?' da wannan tunanin bacci ɓarawo ya ɗauketa.

★MUSTAPHA

Tun da aka laƙa takarda uwanda za su je mission akan allon sanarwa yake cikin ƙunci.Bai taɓa tsanar mission ba sai wannan karon,duk abokan aikinsa sosai suka yi mamakin fushinsa maimakon murna zai tafi Yaƙi.Umar kawai ya san dalili,gefe guda ya na murna yayin da kuma ɗayan ɓangaren ya na tausayin abokin shi.

"Oga mission babu sanarwa kawai sai dai mu gani" Mustapha ya faɗa ya na ɗan sunne kai,Ogansu ya ci gaba da aikin gaban shi ba tare da ya ɗago ba ya ce "Mustapha sanin kan ka ne haka tsarin soja yake,kullum cikin zuwan abubuwa na ba zata ! Wannan ba shine karon farko da za ka tafi mission to mine ne na tada hankali? Ko ko saboda ta ƙetaran Ƙasa ce? Tsoro ka ke ji?"

Kalmar tsoro ya saka zuciyar Mustapha yin baƙi ƙirin a ɗan zafafe ya ce "tsoro? Tsoro kuma Oga? Ni Mustapha? In ji tsoro? "
Oga ya saki murmushi ya ce "saboda wannan karkashin naka ne yasa na ɗora ka a matsayin jagaba,kai ne za ka jagorance su na tsawon shekara ɗaya da wata biyu.Na san sosai Ƙasar Mali za ta ji daɗin aikin gwarzon soja kamar ka" da irin wannan kalaman na ƙarfafa gwiwa Oga ya samu Mustapha ya ɗan rage haushin da yake ji.

Duka sojojin da sunan su ya fito a mission ɗin murna suke,saboda ana samun millioyoyin kuɗi a can.Sannan irin wannan mission ɗin sukan ce sai mai sa'a.
Chapter 10 · 0% Book details