← Book details Matar Mustapha Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 28

Sashe 5

Matar Mustapha Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ɓangaren Inna ganin ya ƙi buɗewa ta koma ɗaki sai sababi take, Baba Malam ya girgiza kai ya koma kwanciyar shi dama ita tashe shi.
"Saboda Allah ina Shamseeya ina kwana da miji a shekarunta? Kai ma Malam ka san ba ka kyauta ba,yadda ya yi shirun can Allah kawai ya san tsiyar da yake shubkawa" Inna ke faɗa ta na kallon Baba Malam da ya bata baya.
Can kuma ta ci gaba da cewa" hum ! Ai doli ka bashi ita tun da dama abun YI WA KAI (Ladingo) ne kai ma haka ka ke tun ka na ɗan saurayin ka wa ya sani ma kai ya gado" Baba Malam ya juyo ya ce "kin ga don Allah bacci nake ji in surutun ki za ki yi to ki koma daga waje,haba! An yi tsohuwa da shegen jinini ina ce dai matar shi ce,ke ma ba ga ki kusa da mijin ki ba?"

Inna ta waro ido ta ce "au ni ce tsohuwar? To wa ya tsufar da ni ? Hum! Wai miji bayan bacci mi ka ke yi?" Baba Malam ya yi dariya kawai ya barta don ya ga alamu ƴan rigimar ne suka motsa.

Washegari
Asubahin farko Mustapha ya tashi daga bacci duk ya ɓata jikinsa.
Lokacin sanyi ne duk da bai wani tsananta ba sosai,amma wanka lokacin doli mutum ya ji jiki.Kasancewar shi soja bai wani damu ba haka ya fita ya cika bokiti da ruwa ya yi wanka gami da alwala.
Ya na fitowa ya hangi Inna ta na shiga ɗakin shi,dama da kayan da zai saka ya shiga banɗaki wannan ya saka shi shanya wandonsa kafin ya wuce masjid .

Inna ta tafki SEEYA a cinya ta ce "tashi mu tafi kin wani lafe ki na bacci ke munafuka,zamaninmu in aka ce za a yi ma aure kuka ka ke.Amma ke murna ma ki ke an gama ki da murjejen ƙato tsabar jaraba ta yaran zamani" SEEYA ta fashe da kuka saboda a ba zata bugun ya zo mata.

Haka Inna ta tisa ƙeyarta gaba suka koma ɗakinta bayan sun yi alwala domin yin sallah.
"Ba zan sake barin ki ba! Wato har da wankan asubah kamar wani sabon ango,uwar mi ya yi miki?" Maimakon SEEYA ta bata amsa sai ta ɓingire bacci,Inna ta yi ƙyaci ta ci gaba da lazimi.

Mustapha bai dawo ba sai da rana ta fito tarrr,ya na shigowa gidan ya tarar babu gajeren wandon shi da ya shanya.
Kafin ya kai ga tambaya ya ji muryar Inna " na mayar da shi can ɗakin ka,in kai ba ka jin ta ido mu muna jin ta.Wato kai ga fitsararre don a san ka na buƙatar matar ka ,ko ko ma don a san mi ka yi shi ne ka shanya mana ɗan iskan wando ? Wlh Mutapha ni gwara ka tattara ka koma can zai fi mini nutsuwa"

Furucin Inna ba wani sabon abu ba ne a gun shi,ya saba jin su musamman in ta na yi ma mahaifinsa balbalin bala'i akan Mace ta shanye shi ta hana shi ƙara aure.
Sannan ko can dama Inna irin matan nan ne wanda tun ƙurciya suke da jinini da kafiya,ga baki babu burki.
"Inna wai don Allah mine ne laifina a nan? Kawai na gane yanzu kin bar sona.Allah sarki Momy da Daddyna " ya yi maganar kamar zai yi kuka,nan kuma jikin Inna ya yi sanyi ta fara marmar da ido kamar za ta yi kuka.

"Ina abincin karina?" Ya yi tambayar don kawar da zancen,ta ce "ga shi can kunnu da ƙosai ne in ka sha ka rage ma Baby" Mustapha ya ɗan murmusa kafin ya shiga ɗakin.

Har zai fara ci sai ga SEEYA ta shigo,gefensa ta zauna ta na turo baki.
"Lafiya Babyna mine ne?" Cikin shagwaɓa ta ce "ba Inna ce ba,wai in zo mu ci abinci da kai amma kar in yarda ka yi mini iskanci" Mustapha ya girgiza kai ya na tunanin ' Inna ko wace iri ce? Yanzu ya dace ta gaya ma SEEYA wannan kalmar?' sai kuma ya share ya fara baiwa SEEYA a baki har sai da ta ƙoshi sannan ya fara ciyar da kan shi.

"Yayana yau ina za mu je?" Ta tambaye shi ta na kafe shi da ido,ya ce "a'a babu inda za mu je,Inna faɗa za ta yi ki bari duk ranar da mu ka je Tilliya zan rinƙa kai ki yawon zaga gari"
Da murna ta sake tambayar shi "wai yaushe ne za mu tafi?" "Sai an yi bikinmu"
"Bikinmu kuma? Kamar wasu Amare?"
"Eh mana Amare ne mu!" Ya bata amsa,SEEYA ta ɓata rai ta ce "ka taɓa ganin inda Magaji ya auri ƙanwarsa?" Shiru ya yi bai san mi zai ce mata don gudun kar ya je ya tayar mata da hankali.
"Yayana ko ni ba Inna ta haife ni ba?" Ta sake jefo wata tambayar.
Mustapha ya ce "da aka yi mi ?" Ta turo baki sannan ta ce "eh ba kullum sai ta ce kar ka sabanta ɗiyar mutane ɗiyar amana" murmushi ya saki ' ashe ta na da ɗan wayo,hum! Ita nan tunanin ta ni Ɗan Inna ne'

"Wace ce Mamata? Don Allah ka gaya mini" ta faɗa ta na matsowa sosai har ta na dafa cinyar shi.
Mustapha ya lumshe ido ya ce "Babyna duk da kin ƙaramta sosai amma yau zan baki labarin Iyayenmu kamar yadda Inna ke yawan bani wasu labaran da suka shuɗe kafin wanzuwata a duniya"

LABARIN....

Usman da Zeinab ƙanwa da Magaji ne ,su biyu kawai Allah ya baiwa Inna da Baba Malam.
Akwai tazara sosai a tsakanin Usman da ita, wannan ya saka ma ya ke ɗaukarta tamkar wata Ƴar shi.
Lokacin da Usman ya yi aure fafur Zeinab ta ƙi zama gun ina ta koma gidan shi da zama.Matar Usman Hajara matar kirki haka ta zauna da ita lafiya babu tsangwama,ita ma Zeinab ɗin ta na bata girmanta don da Matar Yaya ma take kiranta.

A kwana a tashi babu wuya gun Allah Hajara ta samu ciki mai shegen laulayi,Zeinab ke kula da komi na gidan ba tare da ta gaji ba duk da ta na zuwa makaranta.A haka har Allah ya sauki Hajara lafiya ta samu Ɗa namiji.

"Ƙanwata ke za ki zaɓi sunan Ɗan ki da kan ki!" Usman ya faɗa ya na kallon Zeinab wacce ta ke ta faman washe baki ta na rungume da yaron.
"A cikin sunayen Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama sunan Mustapha na bala'in burge ni don haka shi za a saka mishi" ta faɗa tare da sumbatar shi,Usman ya karɓi yaron ya yi mishi huɗuna da Mustapha.

Zeinab ta kasance uwar rainon Mustapha yayin da Hajara ta zama uwa silar zuwansa duniya.Abun mamaki sai ya zamana Mustapha ya fi shaƙuwa da Zeinab fiye da mahaifiyar shi, wannan kuma ya taso tun ya na jariri har izuwa yanzu da ya yi wayo.

"Alhamdullah Allah ya nufa Zeinab ke ma za ki tafi ɗakin ki" Usman ya faɗa,ita kuma ta sunne kai ta na hawaye.
Mustapha wanda dawowar shi kenan daga makaranta ya faɗa jikinta shi ma ya na kukan,ta kuwa rungume shi ƙam.

Usman ya yi dariya don ya san duk wannan kukan bai wuce na rabuwa da Ɗanta Mustapha ba ne.Amma babu yadda ta iya ko wacce mace fatan ta shi ne aure ,a haka aka yi biki aka kaita Gidan Rumji can garin mijinta.

Shekaru biyar currr da auren Zeinab amma shiru ka ke ji ko ɓatan wata,sam Lawali mijinta bai damu ba saboda ya na son matar shi dangin shi dai ne su ka fara tsiyar gumi tare da yaɓa mata magana.
A haka take shanye cin kashin su ta mayar da komi ba komi ba.
An yi hutun shekara,kamar kullum Mustapha ya zo hutu gidanta.Tamkar wani yaro hala ta ke bashi abinci a baki wanda dama alƙawali muddin ta na ga wuri to Mustapha ba zai yi aikin komi ba wani irin mugun so ta ke yi mishi.

"Zeinab lafiyar ki kuwa? Innalillahi wa'inna ileyhi raji'un! Yanzu duk da ya girma ba za ki barin wannan banzar tabi'ar ba? Wannan yasa a kullum ina ki ka ce ki na son ya dawo gidan mu da zama nake hanawa,shi ne ke shahasha da ba ki san ciwon kan ki ba ki ka zauna ki na ba ƙato abinci a baki" Lawali ke faɗa cikin masifa da balbalin bala'i kamar yau ne farkon ganin Zeinab na kula da Mustapha.

A yadda ta fahimci mijinta tamkar dama ya gaji da zama da ita ne ko kuma ya na jiran kuskure kaɗan.
"Ka yi haƙuri Mustapha Ɗana ne bai girma a idona kamar jariri haka nake jin shi" wani gigitacen mari ya ɗauke ta da shi ya na mata tsawa, Mustapha ya miƙe a zuciye ya na huci Lawali na shirin sake kai hannu gare ta ya tare.

"Au! Tare mata ne ka yi ? Yau ga isasshe? "
Mustapha ya girgiza kai ya ce "ka yi haƙuri Abba"
"Ban haife ka ba don haka kira ni da suna" ya yi maganar ya na ture Mustapha,kamar abun tsautsayi Mustapha ya faɗi kansa ya bugu ga table na madubi nan jini ya fara zuba.

Ido rufe Zeinab ta fara maida martani akan ba za ta lamunce duk abin da zai taɓa lafiyar Mustapha ba.Ashe Yayarsa na waje nan ta shigo,da tirje da tuggu Lawali ya saki Zeinab saki.

Jungum haka suka yi zaune babu mai magana.
"Sai ka zuba ruwa a ƙasa ka sha tunda ka kashe auren Uwarka "cewar hajara ta na hararen Mustapha,Inna ta yi saurin katse da "ai gwara shi kashe auren ya yi ke kuma kin yi ma Ɗana asiri ya ƙi ƙara aure,ke ba ki haihu ba amma ki na baƙin cikin ya ƙaro aure"
"Inna!" Usman ya kira sunanta kafin ya ci gaba da cewa" mu nemi mafita don Allah!" Cikin zafi Inna ta ce "har abada Zeinabu ba za ta koma gidan Lawali ba,in kuma ta koma ban yafe ba duniya da lahira.Ta zauna nan gidan ka in ta gama idda ta samu miji ta yi wani auren"
Chapter 5 · 0% Book details