← Book details Matar Mustapha Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 28

Sashe 28

Matar Mustapha Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

Ba tare da ta ce komai ba ta miƙe za ta nufar waje,na dakatar da ita na ce “ki je can ɗakina” ta yo baya tare da nufar bedroom.Ta kai kamar minti biyar da tafiya kafin na take mata sawu,tsaye na yi ina jin motsin ruwa kafin na ƙarasa a bakin ƙofar zuciyata na ɗan dokawa.

A hankali na duƙa na soma leƙa ƴar hudar jikin handle,kusan suman tsaye na yi ganin baiwa Izzatu a tsaye gaban madubi daga ita sai pant ko bra babu amma ta juya wa ƙofa baya.

Das ! Das! Das! Haka bugun zuciyata ke tafiya ina Allah-Allah ta juyo don in ga abin da nake kwaɗayin ganin.Sai dai da dukkan alamu ciwon goshinta take ƙoƙarin rufewa,ƙugunta na duba wanda ya sha duwatsu ƙananu masu masifar kyau sai wani walwali suke yi.

Kamar wacce ke yi da gayya haka take ɗan motsawa sai ta yi kamar za ta juyo sai kuma ta koma daidai,a haka na shiririce ina kallonta ina haɗiyar yawu ina jin kamar na shiga ciki na same ta.

Yadda ƙafafuwana suka yi mini mugun sanyi yasa na lalaɓa na jawo blanket tare da kwanciya kan doguwar kujera na yi wa ƙofar toilet ƙuri da ido.Har sai da na fidda tsammani sannan ta fito da jiƙaƙun kaya,amma da dukkan alamu ma ba ta ankare da ni ba.
Fanka ta kunna ta yi tsaye daidai saitinta,ɗan juyawa ta soma yi tana yarfa ɗan maidaicin hijabinta ruwan ne suka soma feso mini a fuska,na lumshe ido ina jin ƙamshin turarenta na ƙara saukar mini da kasala.Ina cikin wannan hali sai ji na yi an faɗo mini ana kiran sunan.

“Wai Allah jiri nake gani!” ta furta tare da ƙanƙame ni,yadda ni da ita ɗin duk jikinmu bai da ƙwari yasa muka mirgino muka faɗo ita ke ƙasa ni kuma a kanta.Kusan a tare muka buɗe ido da ita sai dai ta yi saurin mayar da nata ta rufe ƙila ko jirin take ji,yayin da ni kuma muradina ya fi ƙarfin nagartata kawai na sauke bakina kan nata.

Yau ne karon farko da na taɓa jin son sumbatar mace,kuma yau ne farko da na fara.Babu wani tunani a cikin kwanyata banda na gusar da ƙishin da nake ji, wannan yasa kamar mayunwacin zaki haka nake kissing nata.Sam banda wata saurar nutsuwar da za ta sa na farga halin da take ciki, burina kawai na sani.Ina dab da cire mata sutura na ji wani masifaffen zafi ya ratsa gefen wuyana,babu shiri na mirgina gefe na dafe wurin da ke yi mini zugi.

Sinadarin ganina yana daf da rufewa na ga baiwa Izzatu ta kwasa a guje ta fita.Cikin dauriya da kuma jarumta na soma motsa bakina ina karanto ɗalasiman tsafi nan take na yi balaguron ruhi,na fitar da ruhina na bar gangar jikin nan kwance yayin da kuma na yi azamar tare baiwa Izzatu da ke dab da ta fita da katafaren sashena.Daidai nan free page ta ida duk mai son ci gaba zai biya 500 via 2670215530
ZULFAU YAHAYA
Ecobank DM +22795045822 ko kuma a turo katin mtn na 500.Don Allah duk wacce ke buƙata ga detail nan kawai ta tura sai ta bani shaidar biya.

*NB:* yanzu nake rubuta shi ,da zarar kuma ya zama complete 1k ne farashinsa.
Chapter 28 · 0% Book details