← Book details Matar Mustapha Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 28

Sashe 16

Matar Mustapha Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kan shimfiɗata na kwanta na shiga yin wasiƙar jaki,ƴan magana na cewa bacci ɓarawo ne to shi ne yayi nasara sace ni a karo na biyu sai dai sam ban yi mugayen mafarkai ba a wannan karon.
Ina tsaka da yin baccin da ban samu na yi ba na ji muryar Abba kaina yana kuma jijiga ni alamun na tashi,ina buɗe ido na ga sai yaƙar haƙora yake kamar gonar auduga.

“David tashi! Tashi ka ga waɗanda suka zo gidanmu.Taso suna son ganinka” Abba ya faɗa cikin murna,yadda ya riƙe mini hannu gam shi ya sa na tashi don dole na biyo bayansa.A cikin rumfarmu ta kara na hangi dattawan garinmu a zaune ko wannensu ya ƙure ƙofar ɗakina da kallo,cike da mamakin abin da ya kawo su na ƙarasa na gaishe su.Bakunansu har rawa suke wurin amsawa kafin ɗaya daga cikinsu ya ce “Jakob ka ɗan bamu wuri muna son yin magana da ɗanmu” Abba ya washe baki yana kallona kafin ya ce “David wannan shi ne pasto ɗin Cochinmu ka saurare shi da kyau,su kuma waɗannan ai ka san su tun da kana shiga gari” yana gama faɗa ya tafi.

Tambayoyi ne suka fara yi mini waɗanda sam ban san mene ne alaƙata da su ba,amma da na ajiye hankali sai nake ganin kamar sun san na taɓa littafin nan na sirri.Shiru kawai na yi ban iya ce musu komai ba,da suka gaji don kansu suka yi wa Abba sallama suka yi tafiyarsu.

Ina shirin shiga ɗaki Ummah ta fito kamar wata munafuka ta ce “Davido wacce maganar ce waɗan can mutanen suka yi da kai?” kallonta na yi da kyau,sai na ga duk wasu alamomin rashin gaskiya sun bayyana a fuskarta.

“Babu komai Ummah” na bata amsa tare da yin gaba.A tsakiyar ɗakina na yi tsaye ina kallon akwatin kayana ina son ɗauko littafin sirri ina kuma jin tsoron kar wani ya shigo ya ganni da shi.
Daga nan inda nake a tsaye na soma jin wani irin yanayi kamar kasala kamar gajiya,idona na ɗan rufewa na soma jan ƙafata na je na kwanta kan shimfiɗata.Ba bacci nake ba kuma ba idona biyu ba,ina cikin wani lamari ne mai wuyar fassarawa.Adaidai nan wata kyakkyawar mace ta bayyana a gare ni cikin shigar fararen kaya,tsawon lokaci tana yi mini wani kallo kafin ta zumbule suturarta nan siffar jikinta ta bayyana a gare ni,haka na ci gaba da kallonta kafin ta tako zuwa gare ni.Abubuwan da suka faru a tsakaninmu,ba zan iya furta su ba saboda yadda ta shagaltar da ni ta saka ni cikin wani hali da babu shi a duniyata ta zahiri.Sai bayan ta gama mu'amalantata sannan ta bi ta jikin bango ta fice daidai nan kuma control ɗin kaina ya dawo.Yadda na samu duk na ɓata jikina shi ya tursasa mini zuwa na cika bokiti na yi wanka,bayan na fito na ɗauki tsintsiya na share ɗakina wanda kuma hakan sam ba tabi'ata ba ce Jowel ce ke yi mini gyaran ɗaki amma yau dai haka na ji ina ra'ayin yin kayana.

Ba tare da na yi wa kowa sallama ba na fice,wurin da muke haɗuwa na je a yau ni ne na zauna domin jiransu.Ina nan zaune sai ga wata tsohuwa ta zo wucewa,sunana ta ambata wanda kuma ba iyayena ne suka raɗa mini shi ba a'a hasali ma ba na wannan duniyar ne ba amma a hakan na fahimci sunana ne.

“Mikiya!” ta sake furtawa a karo na biyu,sai a lokacin kuma na saka idona cikin nata wanda hakan ya bani damar yin kutse a cikin ruhinta.Babbar matsafiya ce wacce ta laƙanci aikinta na bokanci da tsafi,ta kwashe kusan ƙarni biyu a doron duniya tana rayuwa ta hanyar fatalwar ruhinta.

“Ba sunana Mikiya ba! David ne sunana” na faɗa murya a ɗan dake.Ta yi wani murmushi wanda ya ida fito da sauran muguntarta ta ce “sai yaushe ne za ka yarda? Sai zuwa yaushe ne za ka ɗauki ƙaddararka a hannu? Kai Mikiya ce mai yi wa dukkan abin da ya tunkaro ka dirar sauri,kar ka hana ikonka yin aiki akan nauyin da ke kanka” ba tare da na fahimci abin da take nufi ba na ce “na ji na yarda! Za ki iya tafiya”

“Wannan salo naka ya burge ni sak irin jarumtar mahaifinka sarki Alfanso”tana gama faɗar haka ta ɓace cikin iska, maimakon na ɗauki ƙarshen furicinta da muhimmanci sai na watsar.Ina nan zaune sai abokaina suka zo a tare lokaci guda,yanayinsu kawai na duba na fahimci yau ba su fito da niyyar yin dako ba.

“Ina za ku je haka?” na tambaye su ba tare da na yi nauyin baki ba.

Isa ya bani amsa da “za mu je mu kai takardunmu ne ko Allah zai sa mu dace a ɗauke mu aiki ka ga shikenan sai mu huta da yin dako”

“Yaushe aka yanke wannan shawarar ba tare da sanina ba?” na faɗa ina jin wani iri alamun babu daɗi don duk abin da ɗaya zai yi to dole ya shawarci sauran.

“Saboda mun ga ba ka yi wani dogon karatu ba ne shi yasa,amma ba wai da wata manufa ba” Abdul ya faɗa .

“Okay!” shi ne abin da na faɗa kafin na miƙe na kama hanyar kasuwa,tafiya nake cike da ɓacin rai ina jin ya zama dole ma na yi karatun boko tun da har an fara yi mini gori sai dai ta ina zan fara ? Ban sani ba.Da isata kasuwa na soma yin dako cikin zafin rai,wanda sam ban san na yi aikin mai yawa ba da Alhajin ya zo biyana sai ya bani kuɗi na ban mamaki.Cike da murna na koma gida,sai kuma ta koma ciki tarar da mutane da na yi a tsakar gidanmu fuskokinsu cike da alhini haka na ratsa na isa gaban Ummah wacce ke ta gumurzun kuka.

“Ummah?” shi ne kawai abin da na iya cewa,ta ɗago kanta ta dube ni da idonta da suka yi mugun ja kafin kuma ta sake rushewa da wani kukan.

“Meke faruwa ne wai?” na sake tambaya,da hannu ta yi mini nuni da ɗaki haka na tunkari ɗakin zuciyata na yi mini matsanancin bugawa.Cak na yi tsaye ina kallon tashin hankalin da na ci karo da shi,gangar jikin Joy ce a kwance cikin ɗaki babu numfashi .Fuskarsa babu ido an cire su haka ma daidai wuyansa an yi masa wani rame da dukkan alamu wani abu aka cire daga jikinsa.

Ta maza na yi na ƙarasa na zube gwiwaina ƙasa tare da tallabo kansa,wani abu na ji ya caki idona mai bala'in zafi da raɗaɗi a dole ban shirya ba na rumtse ido gam.Kamar magiji haka aka nuno mini ta yadda aka yi abin ya faru da shi.Yana zaune cikin ajinsu aka aiko kiransa,bayan ya fito sai ya ga su Isa ne da Abdul.A mutumce suka gaisa kafin su ja hankalinsa sosai ta hanyar yi masa ƙaryar cewa ya zo ni ne ke nemansa cikin gaggawa .Suna fitowa daga cikin makaranta wata mota suka shiga da shi suka saka shi a tsakiya,suna tsaka da yin gudu suka shaƙa masa hodar bacci a haka suka isa wani gida inda suka yi masa kisan gilla,da farko wuyansa suka caka da wuƙa wanda zafi da raɗaɗi yasa ya dawo hayyacinsa kafin kuma su cire masa idanuwa duka biyun. Daidai nan kuma wasu mutane masu baƙaƙen kaya suka shigo suka zagaye Joy,wata hoda ce ɗaya daga cikinsu ya zuba a jikin Joy ɗin yana yin wasu kalamai waɗanda ba na wannan duniyar ba ne amma sarai na fahimce su.Nan take gawar Joy ta ɓata ta zo nan inda yake kwance a tsakiyar ɗaki,sai kuma na ga lokacin da Ummah ta shigo ɗakin da kuma yadda ta tsorata saboda cin karo da ta yi da wannan lukutar masifar.

Idona na buɗe waɗanda nake jin sun yi mini wani mugun nauyi da zafi,har wani yaji nake ji suna yi mini feshi. Jiki na ɗan rawa na miƙe tsaye da niyyar fita sai dai wani jiri ne na ji ya soma kwasa ta,da sauri na dafa bango ina jan numfashina da ke barazanar ɗaukewa gaba ɗaya.Amma da yake ina da ƙarfin hali haka na ƙoƙarta na fito ina rangaji,wata irin runguma Ummah ta zo ta yi mini tana mai kiran sunana tashin hankalin da nake tsinkayowa a cikin amonta kamar ma ya fi na mutuwar Joy.

Damtsena na ji shigar wani abu kamar mashi,amma ba shi ne ba yatsan Ummah ne.Wani furici take yi mai shige da wancan ɗin wanda ya kasance na ƙarnin baya sai dai wannan sam ban fahimta.Kamar yadda in an zuba wa wuta ruwa take mutuwa murus,to haka na ji duk zafin kaina da ɓacin raina sun sauka.Baya na ɗan yi ina kallon Ummah wacce take yi mini wani kallo ita ma,kafin cikin ɓacin rai ta ce “mene ne wannan Davido? Ina za ka je da wannan ɓacin ran? Wuce ka tafi ɗakinka,yanzun nan Abbanku zai zo”

‘Wace ce ke?’ ita ce tambayar da zuciyata ke son yi mata amma kamar wanda aka tsafe na kasa furtawa,ɗakina na koma na yi tsaye ina kallon akwatin kayana inda na ajiye littafin sirri.Ina son yin bincike a cikinsa sai dai shock ɗin mutuwar Joy ya ƙi barina dole na haƙura,babu jimawa kuwa Abba ya shigo ya kira ni da kansa.Gawar Joy muka ɗauka muka kai can gidan gawa kafin mu fara shirya yadda jana'izar za ta kasance don sai an yi bikin binne shi,domin yin haka kuma muna buƙatar kuɗi masu ɗan yawa .Na sayen akwatin gawa,da kuma abincin da mutane za su ci da kuma kuɗin da za a bai wa makaɗa da pastocin da za su yi masa addu'o'i.

Tun a hanyar komawa gida Abba ya ce mini “ David ya kake gani game da bikin binne Joy? Ka ga dai ni banda kuɗi kai ne za ka yi komai,kana ganin sai mun yi gayyata dayawa ko kuwa?”

Na dubi Abba cike da takaici na ce “kai ba ka damu da irin yadda ka samu gawar ɗanka ba a'a ta yadda za a rufe shi kake ? Abba ka cire ran zan bari a rufe Joy ba tare da na binciko su wane ne suka yi masa wannan kisan gillar ba suka raba shi da sassan gangar jikinsa”
Chapter 16 · 0% Book details