← Book details Matar Mustapha Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 28

Sashe 14

Matar Mustapha Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A shagwaɓe ta ce "don Allah Yayana ka bari" kai ya girgiza mata,sam ya kasa yin ma magana tuni idonsa sun fara yi masa dishi-dishi kamar wani mai jin bacci haka suke lumshewa.
Wata kujera ya jawo ya zauna sannan ya ɗora SEEYA kan cinyar shi kafin ya matso fuskarta kusa da tashi ya fara sumbatar wuyanta sannan ya dire bakinsa cikin nata ya na shan yawunta.
Da tsiya da mugun abu ya zura hannunsa ta ƙarƙashin rigarta,da sauri ta haɗe cinyoyinta amma abun ka da soja ya ware su ya na mai sake shigar da hannun.
Lafiyayyar fatar jikinta ya fara shafawa ya na kuma jin wani mugun daɗi na ratsa shi, SEEYA ta ƙwace bakinta Mustapha ya tsaya da abin da yake ya na kallonta da idonsa masu cike da jaraba.
"Mu je ka ci abinci" ta faɗa ta na turo baki,ya haɗiye wasu yawu ya ce "ke ce abincina! Ƙishin ki kawai nake da!" Ta yunƙura za ta tashi da sauri Mustapha ya kama rigarta ya yi sama da ita duk yadda ta so ta ƙwace kasawa ta yi.

Ya cire rigar gaba ɗaya ya ɗora kan kujerar da ya tashi, SEEYA ta yi saurin kai hannu ta rufe ƙirjinta Mustapha bai damu ba sai ma ƙoƙarin fidda kayansa yake, SEEYA ta nufi ƙofa za ta fita da sauri ya riga ta isa ya danna ma ƙofar key......

Free page ya ida mai son ci gaba zai biya 500 ta wannan account ɗin 2670215530
ZULFAU YAHAYA
Ecobank sai ki turo da shaidar biya ta WhatsApp +22795045822 ko kuma katin mtn na 500,ƴan Niger carte airtel ta 500f

❌Duk wacce ta san ba ta shirya saya ba kar ta min magana,na faɗi yadda za ayi payment kawai ki turo da evidence ko kuma hoton katin in na zo zan saka ki a group.

Ga masu son littataina na kuɗi akwai rahusa da duk wanda ya sayi biyu lokaci guda.
[10/11 19:33] MRS SADAUKI: *INUWAR ALJAN*👻

```LoVe aNd HoRrOr story```👽

By
Chamsiya Laouali Rabo
{MRS SADAUKI💫✍️}

*SADAUKARWA:* Ga Rachida Mamar ƴan biyu, alherin Allah ya luluɓe ki . Ubangijin rahama ya kula da lamurranki👏🏻

*FCWA*☀️

________________________

01

Sakacin iyaye na ɗaya daga cikin abin da ke jefa rayuwar yara yin mu'amala da aljanu tun suna ƙananu ba tare da an ankara cewa wannan illa ne ba.
Sunana David,ɗan farko gun wasu shagalalun iyaye waɗanda suka mayar da sa'insa abin ado,cin amanar juna ruwan sha,wasa da tarbiyyar ƴaƴansu tabi'arsu.Shekaruna ashirin da biyar kacal a duniya amma in aka ganni za a iya bani shekaru talatin saboda yadda ƙwanjina ya buɗe silar aikin wahala.Tun ina ɗan yaro mahaifiyata ta rataya mini nauyin kula da ƙannaina,tun daga yi musu tsarki,wanka da kuma basu abinci a baki madadin ita ta yi.Komai tsawon dare in ƙanena yayi bahaya ni ne ke zuwa na wanke masa na kuma kai banɗaki na zubar,babu wata addu'ar neman kariya ko wani furici da zan furta domin gusar da wani abin cutar wa a irin haka ne na haɗu da wata baƙar siffa wacce duk da ƙanƙantar shekaruna bai hana na fahimci wannan ba bil'adama ba ce.

A tsaye nake tsakiyar banɗaki hannuna riƙe da fo ,yayin da kuma siffar ke tsugunne kan inda mutum ke hawa don yin buƙatarsa.A lokacin wani irin tsoro ya ziyarce ni,sai dai tamkar itaciya haka na kasa motsi sai ma ido da na ƙanƙance ina ƙarewa siffar kallo.Mace ce a zubin halitta don ga dogon gashinta nan ya zubo har yana jan ƙasa,fuskarta baƙa ƙirin ce mai ɗauke da wasu ƴan ƙananun ƙahonni daidai gefe da gefen hanci,bakinta a buɗe yake wanda hakan zai iya baka damar ganin dogayen haƙoranta biyu da suka zarce sauran.Duk a cikin duhun daren idanuwana suka bani ikon ganin wannan ikon Allahn,a hankali na ga ta taso ta zo gare ni ba tare da ta ce komai ba ta karɓi fo ɗin hannuna sai ta ɗora babban yatsanta a tsakiyar goshina wani irin abu na ji mai mugun zafi ya ratsa ni wanda yasa na fita hayyacina.Ko da na farka Ummah na gani gefena tana jiƙa wani zane a ruwa tana ɗora mini yayin da kuma idonta suka yi ja alamun ta yi kuka.Muna haɗa ido da ita ta ce “Davido?” a cikin muryarta na tsinto tsantsar tausayina,a bakinta kuma na ji cewa an same ni a yashe ga ƙasa daidai ƙofar banɗaki .

Mahaifina ya matso yana cewa “har yanzu jikin nasa da zafi?”

“Eh kamar gawarshi har wani tiriri ke tashi,dubi hatta ruwan da nake tsoma zanen sun ɗauki gumi” Ummah ta faɗa tana matsar ƙwalla.

Abba ya ce “ki goya Joy mu tafi mu kai shi gidan mai magani” ba ta ce komai ba haka ta ɗauki ƙanena Joy wanda bai rufe murfin shekara biyu ba,ni kuma Abba ne ya saɓe ni zuwa gidan mai magani.

Tun da muka shigo farfajiyar gidan idona suka soma yi mini gane-gane.Abin da ido bai kamata ya gani ba ni ras nake ganinsa,duk mutanen da suka zo babu lafiya kallo ɗaya na yi wa kowanne daga ciki na hango matsalarsa.A bisa bangunan gidan mai magani kuwa kamar yadda ƙadangaru ke yawo haka ko ta ina aljanu ne ƙanana da manyansu.Lokacin da muka shiga cikin ƴar bukarsa kuwa muna haɗa ido da shi na ga ya ɗan tsorata,amma sai ya ɓoye tsoron tare da bada umarnin a kwantar da ni kan tabarmar da ake shimfiɗe majinyata.A ido tabarma ce,amma a baɗini bijinmi wani dodo ne,bai tambayi iyayena abin da ya faru ba amma sai ni ya tambaya shi ɗin ma ba ta baki ba a'a ta ido.

“Wane ne kai? Me kake so a gare ni har ka bari aka kawo ka wurina alhalin ka fi ƙarfina?” su ne tambayoyin da idonsa suka watso mini amma ni sam ban basa amsa ba,kuma ban san dalilina na yin haka ba.Ƙila shi kuma ya fahimci har zuwa lokacin ƙarfin ikon da ke jikina ban fara yin aiki da shi ba ne ko kuwa tasirinsa bai bi jikina ba ne oho,sai ya ɗauko wata ƙatuwar laya ya ɗaura ta a damtsena tare da cewa “zuwa saukowar zazzaɓin rana duk wannan zafin jikin nasa zai sauka zai kuma samu lafiya” Abba ya basa kuɗi amma ya ƙi karɓa a haka muka dawo gida.Kamar yadda ya faɗa ɗin kuwa haka ta faru,ina warware wa kawai sai na fara walwala tare da mantawa da wannan siffar da na gani .Yayin da kuma Abba da Ummah suka dasa rashin mutumcinsu daga inda suka tsaya,dama iya na ɗaya rana ne ba su yi masifar da suka saba ba da yi wa juna gori wasu kalaman sam ba su dace ba.

A lokacin da na shiga zangon shekara goma sha biyar a duniya na soma yin aikin ƙarfi don ciyar da ƙannaina biyu Joy da kuma Joyel wacce ta kasance autarmu.Tamkar mahaifi haka suka ɗauke ni,da zarar na shigo haka suke zuwa da gudu su tarbe ni da murna iya wannan annushuwar da nake gani a tattare da su shi ke wanzar da nawa farin cikin har izuwa yanzu da nake ganiyar shekara ashirin da biyar.

“Ba ka da aikin yi kullum sai shan giya da bin mata a hakan wai kai miji ne”

“In ba miji ba ne ni ai ba zan baki yara har uku ba”

“Uwar me kake yi wa yaran ? ”

“In ban yi musu komai ke da ke uwarsu ai ina yi miki wata tsiyar da har ta sa kika kasa barina kika manne mini”

“Zancen banza yo kar ka sake yi,ka zata kai kaɗai ne namiji a duniya?”

“Kenan dama abin da nake zargi gaskiya ne kina cin amanata?”

Wannan ita ce sa'insar da iyayenmu suka tashi da ita a safiyar yau duk sun cika mana gida da surutunsu da babu daɗin ji.Cike da ɓacin rai na tashi daga kwancen da nake ,tun ina haƙurin saurarensu har na kasa jura na tunkari ɗakinsu.Ban ɗaga labule ba,a bakin ƙofa na ce “don Allah ko za ku iya yi mana shiru ko mun samu mu yi bacci cikin salama?”

Daga can cikin ɗaki Ummah ta ce “kan ubanka! Haifarmu ka yi da za ka bamu umarni?”

Shi kuwa Abba wata irin dariya ya yi kafin ya ce “ai shi ne daidai ke tun da ke ma ɗin ba mutumci ne da ke ba ga shi nan kin haifi ɗan daba ”

“Ko ma dai mene ne babu ruwanka da ɗana ”

“Ni ma ai nawa ne ina ce ni ne ubansa ko?”

“Wa ya sani abu cikin duhu!” Ummah na faɗar haka na gusa daga gurin.Ƙofar gida na fita na zauna kan dakali ina jin zuciyata duk babu daɗi.

Wani irin yammm! Yammm! Na soma jin ƙafata na yi mini ko da na duba sai na ga tururuwa ce duk ta yaɓe mini ƙafa kamar ta samu wani suga.Girgiza ƙafar na yi amma ko ɗaya ba ta faɗi ba kamar ma an sa super glue ne a manne su.Da sauri na kai hannu don kakaɓe su sai dai wani abun mamaki bayan na shafa ƙafata sai na ga wayam babu komai kuma ba su zuba a ƙasa ba.Wani irin matsanancin ciwon kai ne ya ziyarce ni,dole na miƙe na koma cikin gida na cika bokiti da ruwa na kai banɗaki .Ina tsaka da yin wanka na soma jin wani irin yanayi wanda tun da nake zan iya cewa sau ɗaya tak na taɓa samun kaina a cikinsa shi ɗin ma a mafarki a lokacin da na shiga zangon balaga.

Idona a rufe suke na goga sabulu ban wanke ba,yayin da kuma nake jin tamkar ana shafar duk illahirin jikina ana yi mini abin da ban taɓa jin makamancinsa ba.A wannan lokaci ba zan iya tantance ina cikin hayyacina ne ba ko kuwa ya gushe,abu ɗaya zan tuna shi ne na samu kaina a matsayin namiji har na samu nutsuwa,sai dai da wa? Ban sani ba.Ina dawowa cikin tunanina na ida yin wanka,na fito na je ɗakina na shirya .Ciwon kan da ya sauko mini tuni na neme shi na rasa,na fito kenan zan fita neman kuɗi sai ga su Joy sun fito su ma cikin shirin zuwa makaranta.
Chapter 14 · 0% Book details