← Book details Matar Mustapha Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 28

Sashe 3

Matar Mustapha Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Allah sa a kira ka kafin gobe" Umar ya faɗa ya na dariya.
"Kai ma ka na iya sawa a kira ni ɗin ɗan baƙin ciki,ai wlh yanzu zan kashe wayata ba zan kunnata ba sai ina gobe komawa" da sauri Umar ya ce "yi haƙuri don Allah abokina wasa nake ma,ɗazu ma Oga ai ya zo nan har yake tambayar ka nace ka tafi tun jiya"

Mustapha ya ce "ƙyale ɗan banza mai kai kamar faranti,bai fa so na zo ba"Mustapha ya faɗa cikin haushi .
"Hhh! Ogan ne mai kan faranti? Zan kuwa faɗa masa ka san makullenmu na buɗe juna"

"Eh tunda shi ma ma'abocin neman mata ne ai hikenan !"

Umar ya yi dariya ya na mai yi masa sallama.
"Da wa ka ke waya?" Inna ta tambaye shi ta na mai yin tsaye ƙiƙam.
Mustapha ya shafi gefen wuyansa ya ce "wani abokina ne!"
"Mazinacin ka ke abota da shi?" Inna ta tambayq cike da kulawa .
Mustapha ya fahimci ta ji hirar su ,sam bai so haka ba!
"Inna ba wai abota muke ba ,wajen aiki muka haɗa kuma kin san aikin soja yadda yake ba wai lalle doli kai ne za ka zaɓi inda ka ke so ba" ya yi maganar ya na mai latsa waya.
"To Allah kyauta,kai dai ka ji tsoron Allah a duk inda ka ke ya na kallon ka!" Ta na gama faɗa ta fita cike da zullumi.

★Da dare bayan sun gama cin abinci Baba Malam ya koya masu karatu su duka ukun.
Duk da Mustapha nada Alƙur'ani a kai bai hanasa zaunawa Baba na sake yi masa wani karatun ba, Shamsiyya ta kafe shi da ido ta na kallon yadda yake motsa baki sai kwararo ƙira'a yake.
Ta saki murmushi ta ce "Yayana ashe har yanzu ba ka mance karatun ba?" Dariya maganarta ya bashi,ya tsaya ya na cewa "ta ya zan manta ko a can ni nake koyar da sojawa dayawa karatu kuma ni nake basu sallah"
"To amma mi yasa ka ke koya yanzu?"
"Saboda ilimi Kogi ne Baby! Oyaaa je ki yi naki karatun gobe zan yi miki tambaya akai" sai ta ɗauki littafinta ta ci gaba da yin karatu,kafin wani lokaci bacci ya ɗauke ta ita gefe littafin gefe.

"Shamseeya tashi ki koma ɗaki,ke Shamseeya keee!" Inna ke faɗa bayan ta gama gyara shimfiɗa.
"Ki bar ta zan kaita da kaina" cewar Mustapha,Inna ta wurga masa wani mugun kallo na ba ka da hankali kafin ta tafki Shamsiyya a cinya da kuka ta tashi ta na sosa gun.

"Je ki can ɗaki ki kwanta ga shimfiɗa can " Inna ta faɗa cikin tsawa,ita kuwa ta nufi ɗakin Mustapha cikin hargowa Inna ta fara tsayar da ita "keee! Uban mi za ki yi can? Maza wuce mu tafi" ta dungure kanta haɗi da tisa ƙeyarta gaba.

Mustapha tuni zuciyarsa ta fara tururi ,tsabar haushi da takaici kasa ci gaba ya yi da karatun.
Baba Malam da ke kallon komi a nutse sai murmushi yake gabanin ya ce "Soja tashi ka kwanta na san da gajiya a tattare da kai"

Mustapha ya tashi ya shiga ɗakinsa wanda yake ciki guda ne tal,ko bai nan sai an share shi don nan su Inna ke zama da rana a cewarsu ya fi sanyi.
Tun rasuwar iyayensu bai taɓa jin makamancin baƙin ciki ba sai yau,sam ya rasa mi yasa Inna ke kwabsa misa.
Wayarsa ya ɗauko ya kunna,layin Umar ya kira har ta katse bai ɗaga ba sai a na biyu.
"Ya dai abokina ka huce?" Umar ya tambaya ya na dariya ƙasa-ƙasa.
Mustapha ya ja gwabron numfashi ya ce "abokina ina cikin matsala" da sauri Umar ya bar dariyar da yake yi ya nutsu ya ce "mi ke damun ka?" Mustapha ya basa labarin duk abin da ke faruwa bai ɓoye masa komi ba.

Umar ya ja ajiyar zuciya ya ce "abokina Inna ta fi ka gaskiya,saboda a yadda na fahimta ni kaina sam ba za ka iya jure zaman Shamsiyya kusa da kai ba" Mustapha ya katse shi da "dallah can malam! Duk shekarun da na ɗauka babu mace sai a wannan yarinyar zan sauke maitata? Hum! Ni fa kawai ina buƙatar na rinƙa jinta a jikina ne ba wai don wani abu ba"

"Ba za ka fahimta ba ne sai ranar da ka yi aika-aika,wa ya taɓa gaya ma ana keɓewa da matar da ake so? Hum! Ai wlh kwanyar ka raya ma za ta yi ƙatuwar budurwa ce sai ka gama komi ka farga kamar yadda Abdallah ya yi ma Maryam hhhh"

"Mtswww matsalata da kai kenan ana hira sai ka kawo min shirme,waye kuma Abdallah?"Mustapha ya tambaya.
"Wani jarumi ne na cikin ƁOYAYYEN SIRRI (MRS SADAUKI ga masu buƙatar book ɗin za su iya tuntuɓata ta WhatsApp kai tsaye +22795045822) yadda dai ka gan ka da Shamsiyya haka ya yi ma Maryam..." Da sauri ya katse shi ya ce "ban son ji don Allah kawai salon ka tayar min da hankali "

Umar ya sheƙe da dariya ya ce "mutane manya ne! Inda ace nan ni ne na yi maganar sai ka ga laifina,ashe dai abokina lafiyarsa lau shi ma namiji ne hhhh! " Jin kamar Umar na son juye zancen ya saka Mustapha kashe wayar kwata-kwata.
Rub da ciki ya yi ya na mai lumshe ido,abubuwa dayawa su ka fara yi masa yawo a kwanya.

Washegari
Masjid Mustapha ya yi zamansa tun bayan da ya yi sallah asubahi,karatun Alkur'ani yake rerawa tamkar Balarabe.
Tun da ta fito take jin sautin muryarsa kasancewar masjid ɗin kusan gidansu yake.Ta na nan tsaye ta ga ya fito,da sauri ta nufo shi ta na cewa "ina kwana malam Mustapha ashe ka zo?" Cak ya tsaya ya na kallonta,duk zaman da suka yi nan unguwar babu macen da yake yi ma magana duk da su na gaida shi amma bai kula su.

Kamar zai shareta sai kuma ya ce "alhamdullah!" Ya na mai yin gaba,ta bi bayan shi da kallo ta na kisisina abubuwa da yawa a ranta.
Daga bayanta ta ji an ce "Farida ba ki tafi ba tun ɗazu?" Da sauri ta juyo ta ce "Maman yanzu zan tafi" ta na gama faɗa ta kama hanyar kasuwa babba.
Mankani/gwaza ta sayo,ta na tafe ta na kankare shi a hanya don ta yi sauri. Ta na shirin shiga gida su ka haɗa ido da Mustapha wanda ya fito hannunsa riƙe da na Shamsiyya ,ya kawar da kai gefe yayinda kuma Farida ta ji wata matsanciyar kunya........
[07/11 11:44] MRS SADAUKI: *MATAR MUSTAPHA*
LOVE STORY

```MRS SADAUKI```💫 ✍️

DEDICATED to MY SADAUKI🫡

FCWA ☀️
_________

4

Mustapha ya ja hannun Shamseeya suka wuce ba tare da ya ƙara kallon Farida ba wacce kunya ta dagaskarar da ita.
Sai da ya tsayar da adaidaita har sun shiga sannan ya ke tambayarta "Baby faɗa mini ya aka yi Inna ta bari ki ka fito? Ba ta ce ba ta yarda mu je ko ina ba?" Cikin kunne ya yi mata raɗar,ta ɗago ta kalle shi tana murmushi sannan ta ce "ai wayo na yi mata na ce zan shiga banɗaki" Mustapha ya waro ido ya na mamakinta amma ko ba komi ya ji daɗi.

Gidan wasar yara suka je Fara'ah wanda ke nan garin Maraɗi.Tamkar ƙwai haka Mustapha ke kula da ita,kan shillo ya ɗorata ya tsaya daga bayanta ya na ɗan turata ita kuma sai dariya take wacce a wajensa ta fiye masa komi don ita ke wanzar da na shi farin cikin.

Ya tsaya da shillata ya dawo gabanta ya tsugunna ya na mai ɗora dukan tafukan hannuwansa kan cibiyoyinta .
Ido cikin ido suke kallon Juna,a tattare da ita ya na hango fuskar mahaifiyarta mace mafi karamci a duniya.
"Baby ki na sona?" Ya tambaye ta yana haɗiye wasu yawu,ba tare da shakka ko wani tunani ba ta bashi amsa da "sosai Yayana,zo ka shilla niiii!" Ta ƙarashe maganar cikin shagwaɓa ta na mai ɗan jijiga cibiyoyinta .

Mustapha ya lumshe ido ya na jin zuciyarsa na halbawa,wannan ihun nata tamkar ganga ko kuma sarewa mai saka mutum ya taka rawa bai shirya ba,to shi ma hakan ta haifar masa da motsawar jikinsa.
Dakyar ya tashi ya koma bayanta, maimakon ya shillata ɗin kamar yadda ta buƙata sai ya kwanto kansa gun wuyanta ya na sauke wani numfashi.

"Yayana ina son tsire dubi ga shi can ana ba wasu" ta faɗa ba tare da ta yi la'akari da halin da yake ciki ba.
Mustapha ya yi ta maza ya saita kansa,cikin tafiyar nan ta jarumai ya je ya sayo mata tsiren.Kan banci ya zauna ya na kallon yadda take ci cikin sauri kamar wani zai ƙwace mata,ya saki murmushi haɗi da shafar sumar kansa.

Ta na gamawa suka fito,sai da ya ƙara saya mata kayan motsa baki a hanya kafin su wuce gida .
A tsaye suka tarar da Inna ta riƙe ƙugu kamar wata ƴar dambe,ta na ganinsu ta ce "yanzu Mutapha duk gargaɗin da na yi maka akan Shamseeya ba ka ji ba? Ina ce dai na hana wannan fita unguwar,shi ne da ka ga na yi bacci ka ja ta kuka silale ko? Ke kuma mai shegen baki kamar an yi Yamma da Kare shi ne ki ka bisa ke uwar kwaɗayi ko?" Ta na maganar ne tare da damƙar hannun SEEYA ,ba ta ɗauki lokaci ba kuma ta kifa mata mari,ta fashe da kuka ta na kiran sunan Yayanta.

Mustapha ya rumtse ido,so yake ya yi magana sai dai ya na tsoron Inna ta tsananta hukuncin."Yi haƙuri in sha Allah ba zan sake ba Inna,kuma gobe ma zan koma" ya na gama faɗa ya nufi ɗakinsa a sanyaye.
Ita kanta Inna sai ta ji duk babu daɗi,ta bi bayansa.Kan bed ta gansa zaune dafe da zuciya,ta fi kowa sanin waye Mustapha don ko Kuturu bai gwada masa zuciya saboda lokacin da ya ce zai aikin soji ma babu yadda ba ta yi ba don kar ya je ya ƙaro wani zafin.
Chapter 3 · 0% Book details