← Book details Matar Abbana Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 24

Sashe 9

Matar Abbana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hafeeza yanaganki hannu Rabbana? babu abinda yabaki?"
tun kafin Hafeeza tace wani abu Inna Ta Rasulu ta kwashe da wata irin dariya harda tafa hannayenta biyu tafara rera waqa tace"munaji muna gani muna kuma saurare...."
*** *** ***
Washegari sauka,tun qarfe hudu na dare Hafeeza tatashi tayi nafila bata koma bacci ba tana zaune tanata tulawar karatun Alqur'ani,har aka idar da sallar asuba sannan tafuto tafara gyara gidan nasu, bayan tagama gyaran gidan ta zauna a tsakar gida tayi tagumi hannu bibbiyu tana kallon malkaden waken dake gabanta, shawarar da Maman Fadila tabata akan rashin son yin suyar qosai shi take tuna wa, wannan qosan da batason zuwa ta siyar shine yarufa musu asiri itada Inna, dashi sukeci dashi suke sha, tun tasowar ta bata ta6a ganin wani daga unguwa yakawo musu tallafin ko fallen zani ba, haka tataso acikin gwagwarmayar rayuwa harta kawo yanzu.

Ahankali tasaki ajiyar zuciya tasake jin wani qwarin gwiwar yashige ta akan sana'ar tasu, cikin hanzari tatashi ta shirya tsaf, cikin dogon hijabin ta, tahada kayanta tafice wajan sana'ar su, abinda tasa aranta shine koda qosan be qare da wuri ba zatayi haquri harya qare sannan tazo ta shirya tatafi wajan saukar tasu, saboda inda ace ba suyi qosan ba kuma babu Kawu Hamza to babu yanda za'ai tasamu damar shiga cikin sauran dalibai da za'ayi saukar dasu
*** *** ***
Tunda sukai sallar asuba basu koma bacci ba, gaba d'ayansu su ukun suka shiga kitchen suna yin donut da cake dakuma sauran kayan rabo da zasu rabawa jama'arsu bayan angama sauka, hakan yasa suka zama busy kowa da aikin da yake a kitchen din, suna aikinsu cikin sauri saboda kada lokaci ya qure musu.

Cikin hanzari yafuto daga cikin dakinsa yana Sanye da baqaqen kaya riga da wando,kayan nasa sunada laushi sosai kuma roba ne, hakan yasa wandon ya d'an kamashi wanda tsawon sa bai sauko har can qasa ba, da kad'an ya wuce gwiwar sa,rigar kuma tana hade da hula daga Qasan hular akwai zare guda biyu wanda mutum zai iya daure hular a kansa da wannan zaren,kayan sunyi mutuqar yimasa kyau kamar ka saceshi,saurin dayake yasa yafuto yana qoqarin daura agogo a tsintsiyar hannunsa me cikeda gargasa.

Kallon gefen kitchen din nasu yayi, kafin yayi magana 'yanbiyu suka gaidashi, Kaka ta kalleshi taga kamar sauri yake, cikin hanzari tace"ina zakaje haka da sassafe Hafeezu?"
Saida ya runtse idonsa cikin taqaici saboda yanda ta furta sunan nasa,bayason wannan Hafeezun datake fada, idon nasa ya bude sannan ya amsa mata cikin daure fuska kamar kullum yace"yanzu zan dawo Kaka,akwai abinda zan gani ne me muhinmanci"
Kafin Kaka tabashi amsa yayi wuf yafice daga falon nasu cikin sauri, yana futowa compound bai saurari kowa ba yashiga motar da kansa sannan yafice cikin sauri, tuqi yake yana jin wani irin nishadi acikin zuciyarsa wanda yarasa meyasa yakejin hakan,agefe guda kuma ya kunna waqa acikin motar tasa sautin waqar yana tashi kad'an-kad'an.

Bai zame ko'inaba sai wajan da Hafeeza take suyar qosai, daga nesa da'ita yayi parking motarsa, sannan yakashe motar yana kallonta tacikin tinted glass din motar, wata irin wawiyar ajiyar zuciya ya sauke da idonsa ya sauka akan kyakykywar fuskarta, duk da fuskar tasa babu walwala akanta, ahankali can qasan maqoshin sa ya furta " had'addiya ce"
Yasake gyara zamansa acikin motar tareda harde hannunsa akan qirjinsa yana faman kallonta,ya dade yana nazari akanta, haka kuma baibar wajanba har saida yaga tagama saida qosan tas, sannan ahankali yaja motarsa yabar wajan batare dayaje inda take ba.

Inna tayi mamakin yanda Hafeeza tafita suya bayan tasan cewa yau ce ranar saukar su,abun yabata mamaki sosai kuma taji dadi aranta, tasan cewa haqiqa ita aka haifawa Hafeeza tunda gashi yarinyar kullum cikin fafutukar nema musu na abinci take, cikin sauri tatashi ta kar6i kayan hannunta tafara wanke wa ita kuma Hafeeza da gudu tashiga wanka saboda kada lokaci ya qure, garin gudu gefen zanin nata ya kunce kafin ta farga ta gyara har tsayaiyan nashanunta guda d'aya yafuto waje, cikin sauri ta zaro idonta waje tana kai dubanta wajan Inna, aikuwa komai daya faru akan idon Inna ne, cikin sauri Hafeeza ta runtse idonta, Inna ta dauraye babbar robar dasuke had'a wake aciki sannan ta girgiza kanta tace"ainace dama mijinki saura zaigani inde bazaki hankali ba Hafeeza,menene abun gudu a shiga wanka in banda sakarci? inda baqi mukai ma haka zaki kama gudu kwankwaso yana miki rawa kedama abu ba kad'an ba, kici gaba Allah yabaki sa'ah"
Hafeeza de tana jinta tayi shiru batace komai ba tashige cikin bandakin nasu, agurguje tayi wankan ta tafuto tashirya cikin material d'in da Maman Fadila ta dinka mata,duk da Rigar tanada fad'i ba qaramin kyau tayi mata ba,riga ce me fad'i doguwa dakuma zare agaban rigar wanda zata kama ta daure acikinta, kamar yanda taga zaren agefen rigar itama ta kama ta daure shafaffen cikinta dashi, yanda ta daure rigar hakan yasa Hips dinta yasake futowa duk da Rigar tanada fad'i, dogon gashinta dayake daure tayi sauri ta kunce tashafa masa Vaseline sannan tasa mataji ta tajeshi daqyar, lokaci daya ya dauki wani irin sheqi kasancewar a wanke yake fes.

Dogon hijabin saukar su gogegge ta dauka ta saka,lokaci daya zahirin kyawun ta yafuto acikin hijabin,tayi mutuqar kyau duk da ba kwalliya tayiba kawai gashin girarta ta taje saikuma dan lipstick data saka shima d'an kad'an.

Maman Fadila ce ta shigo gidan itama tana jiranta, daga nan suka dunguma suka tafi.

Duk yanda take komai cikin sauri saida ta makara,tana zuwa makarantar shugaban makaranta yafara yimata fada kasancewar ita kadai ce bata zo dawuri ba, bayan dogon bayani da yayi musu kai tsaye suka qarasa wajan da aka tanada domin yin taron,gaba dayan su daliban rumfa daya aka ware musu da kujerun da kowacce zata zauna, banda sauran mutane suma dasuke cikin tasu Rumfar, wajan yacika sosai kamar me, manya-manyan baqi sun samu halartar taron saukar kasancewar islamiyar tasu babbar makaranta ce.

Malaman makarantar aka bawa dama daya daga cikinsu yayi bayanin muhinmancin ilmi dakuma muhinmancin karatun Alqur'ani, yayi da larabci sannan ya fassara da hausa.
daga nan aka kira Sunanta amatsayin daliba ta farko dazata fara karatu.

Tunda suka zauna awajan kanta yake qasa tana karanta (Bismillahirrahmanir-Rahim) acikin zuciyar ta,saboda gabanta banda fad'uwa babu abinda yake,bata ta6a shiga cikin babban taro kamar wannan ba,taso ace had'a baki zasuyi gaba dayansu daliban malami guda daya ya karanta suma su karanta kamar yanda wasu makarantun sukeyi, to saide tasu makarantar tazo musu ta daban, hakan yasa take karanta Basmala kasancewar duk wanda yakejin fad'uwar gaba kokuma yakejin tsoron tunkarar wani abu kamar jarabawa ko wani abu daban, to muddin yakama Basmala yana maimaitawa acikin zuciyar sa insha Allahu zaiyi komai nasa cikin nutsuwa kuma zaiji fad'uwar gaban ta ragu.
kasancewar tariga tasan itace zata fara karatun hakan yasa gabanta yaketa faduwa, kokadan bata fahimtar jawabin da'ake awajan, saide ta tsinkayi me jawabi yana kiran HAFEEZA KHALID USMAN amatsayin dalibar farko dazata fara karatun Alqur'ani.

Wata daliba dake gefenta tace"Hafeeza kitashi"
Ahankali ta miqe da Bismillah abakinta, tafara tafiya cikin nutsuwa kanta aqasa harta qarasa inda aka tanada domin tsayawar dalibai masu sauka.

Tunda tataso idonsa yake kanta,yana zaune akan akujerun da'aka tanada domin baqi na musanman, gabansa ne yayi wata irin faduwa ganinta awajan,cikin tsananin mamaki yasake kallon ta yana gyara zamansa aransa yace dama itace?, ahankali ya maimaita sunan nata acan qasan maqoshin sa HAFEEZA....

Cikin nutsuwa tafara rera karatun Alqur'ani cikin zazzaqar muryar ta, lokaci daya wajan yayi tsit kowa yana sauraron karatun nata, Alhaji ISAH YUNUSA babban dan majalissar yankin daya halarci wajan saukar, tun taso war yarinyar yaji ta birgeshi, da alama tanada nutsuwa sosai, lokaci daya ransa ya kwadaitu da aurenta.

Hafeeza kuwa cikin fitar da makaarij take rera karatun ta kamar karta daina,zaqin muryar tata yasa Hafeez dake zaune agefen Kaka acikin Rumfar da aka sauki manyan baqi ya lumshe idonsa yana sauraron karatun nata, a tarihin rayuwar sa zai iya cewa bai ta6a jin karatun wata mace dayayi masa dadi kamar nata ba.

Hajiya Kaka dake zaune agefe tajuya ta kalli Hafeez taga idonsa a lumshe, ta dauke kanta tana girgiza kai, tayi tunanin yanda yarinyar take karatu hakan zai dauki hankalin sa ta yanda zai zuba mata ido yana kallonta ko Allah zaisa adace, saide abun mamakin saita ga kamar ma yarinyar bata birgeshi ba.

Har Hafeeza tagama karatu taje ta zauna mutane basu daina kallonta ba, Ta Rasulu da Kawu Hamza da matar kawu Hamza da yaransa da kuma maman Fadila duk suna waje daya basu samu wajan zama ba, daga tsaye suke hango komai (
Gaddafi kuwa sai washe baki yake yanajin wani irin dadi aransa yana Alfahri kasancewar sa saurayi awajan Hafeeza.

Kasancewar daliban basu da yawa mutum biyu ne sukai karatun, daga Hafeeza sai wani namiji guda daya daga cikin dalibai maza guda biyar da'akai saukar dasu.
daga nan aka bawa shugaban makaranta dama yafuto yayi Nasa jawabin, yabada tarihin makarantar kanta.

Sannan aka bawa wani Babban malami shima yayi fadakarwa sosai akan amfanin ilmi, sannan matemakin shugaban makaranta yafara kiran dalibai daya bayan daya ko wacce ana bata allon sauka dakuma certificate.

Bayan angama basu ko wacce takoma ta zauna, Babban limamin unguwar yazo gabansu ya zauna yafara karantawa suma suna biyawa, masu camera kuwa sai zagayasu suke suna daukar su.
daga qarshe kuma baqin da aka gayyata suka fara bawa Dalibai gudunmawa ta kyauta,cikin daliban da suka samu babbar kyauta harda Hafeeza, wadda Alhaji Isah Yunusa dan majalissa yabata kyautar zunzurutun kudi har naira million biyu tareda kujerar Umarah.

Inna tanajin kud'in tayi Suman tsaye har saida Maman Fadila datake yiwa Hafeeza video ta taro ta saboda qiris yarage tafad'i qasa.(
daga nan manyan baqi suka fara sanarwa kowa da irin kyautar dayake yiwa makaranta, wannan yace yabada sadakar dubu Hamsin, wasu dubu goma, wasu dubu dari biyu, wasu dubu biyar, harda Mata masu bada dubu daya, wannan duka kyautar makaranta ce.
ma'ajin makaranta ne yatashi yafara rabawa manyan baki wasu fararen takardu masu dauke da number account din makaranta ajiki, idan da wanda zasuyi transfer saisu tura, cikin wanda aka bawa paper harda Hajiya Kaka data hakimce akujera.
Chapter 9 · 0% Book details