← Book details Matar Abbana Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 24

Sashe 14

Matar Abbana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hafeez, Koda kayi niyar 6oyemin abinda yake damunka kariga kasan cewa nasanka fiyeda kowa,idan ma ka 6oyemin zan gane"
Cikin damuwa Hafeez yace"akwai wata yarinya da al'amuranta suke damuna,Bansan dalili ba, amma naji ina damuwa da al'amuran yarinyar,kowacce safiya ina ganinta awajan sana'ar ta,ban ta6a yin magana da'ita ba,but I think tanada aure, kokuma tata6a yin auren"
Ib ya gyara zamansa yace"baka ta6a magana da'ita ba? how kagane cewa tanada aure?"
Hafeez yayi shiru yakasa yiwa Ib maganar yaganta tana bawa Baby Nono,saiya kawar da maganar yana fadin" tanamin kwarjini sosai Ib, koda nayi niyyar tunkararta inajin gabana yana faduwa,sai in kasa yimata magana"
Ib yasake yin murmushi yace"kaifa haka kake, narasa yaushe ne zaka dena tsoron yiwa mata magana Hafeez, ka tunkareta kuyi magana, idan ma tanada aure kana yimata magana zata fadama"
Kafin Hafeez yayi magana Ma'aruf yakira wayar Hafeez, cikin nutsuwa yadauki wayar yace"ma'aruf"
Daga d'ayan 6angaren Ma'aruf yace"Hafeez kana gida ne?

Inaso inzo akwai maganar da zamuyi"
Cikin aji yace"no naje Niger State, what happen?"
Ma'aruf yace" wallahi akwai wani bawan Allah dayamin maganar ka, so naso inzo muyi maganar kuma bamu hadu ba tunda nadawo, to dazu ma yasake zuwamin da maganar, yacemin akwai yarsa da yakeson baka aurenta idan babu damuwa, sannan a yanda na fahimta da gaske yake, kuma yana yabon halayenka dana yarinyar yana fadamin cewa idan ka aureta zata yima ka biyaiya yanda yakamata,ina ganin da zaka samu dama da munje munga yarinyar idan kaji kana sont...."
Tun kafin Ma'aruf yagama cewa in kaji kana sonta, Hafeez ya katse shi da sauri yace" idan naji inason wa? kai kata6a ganin mahaifin dayake neman kai da 'yarsa? kaga Ma'aruf mubar wannan maganar haka,bana sonta,ba kuma zan ta6a sonta ba, saboda haka ka dakatar dashi da wannan shirman dan Allah"(
Ma'aruf yace"Amma Hafeez....."
Kafin yagama magana Hafeez yakashe wayar sa tareda dafe kansa, Ib daya gama jin komai yace" to kagani, na tabbatar acan qasar da kake aiki ma bazaka rasa yanmatan dasuke sonka ba, gashi yanzu iyaye sun fara kawo ma yaransu,ina ganin kawai kacire shakka ka tunkari wannan yarinyar kuyi magana inde har kanajin ta aranka"
Hafeez ya girgiza kansa alamun amsawa, daga nan sukai sallama, Danladi yaja motar suka dauki hanya.
*** *** ***
Saida ya sauka agida sannan yake sanarwa Kaka cewa Niger State yaje,taso ta tambayeshi mutanan gidan Wato su MAMA, amma shakkar sa dakuma shakkar abinda zai iya biyo baya yasa tafasa tambayar.
ko abinci baici ba yayi wanka yashirya yatafi masallaci saboda anfara kiran sallah, bayan an idar da sallah yafuto zai tafi gida daga bayansa yaji ana masa sallama.

Zuciyarsa d'aya yajuya yaga wani magidanci,yabashi hannu suka gaisa.

Kawu Hamza yayi murmushi yace"yaro ashe kadawo, ai dazu da rana nasamu abokinka nayi masa maganarka"
Hafeez yanajin haka yadauki Haske, yanajin haka yagane cewa wato shine mutumin dayake neman kai da 'yarsa, ahankali yasaki ajiyar zuciya sannan yace" Bande gane abinda kakeson cewa ba"
Kawu Hamza yayi murmushi yace"to ga wajan zama can mu qarasa zaifi kyau muyi maganar a zaune"
Babu musu Hafeez ya bishi suka zauna, kawu Hamza yace"Yaro ina yawan ganinka a unguwar nan, sannan ina yawan ganinka a masallaci,ina yin nazari akan halaiyar ka har naji cewa zan'iya daukan auren yata nabaka, idan babu damuwa inaso nabaka auren yata,tanada nutsuwa sosai, ina yima sha'awar ta, sannan kaima ina yimata sha'awar ka, nasan cewa zamanku zaiyi kyau idan ka amince da'ita, amatsayina na uba awajanta inada haqqin dazan nema mata mijin aure, nikuma hankali na yafi kwanciya dakai"
Hafeez ya kalli Kawu Hamza yace"kayi haquri, amma hakan bazai iyu ba"
Kawu Hamza yayi murmushi yace"kada kace haka yaro,idan ma akwai yarinyar dakake so, ai ba laifi zaka iya auren yata amatsayin ta biyu, kokuma kafara auren yata daga baya saika auri wacce kakeso, na tabbatar bazakai dana sani akan zama da yarinya ta ba"
Hafeez ya Sosa girarsa guda daya sannan ya kalli Kawu Hamza yace"to amma ita yarinyar taka batada manema ne?"
Kawu Hamza yace"tanada manema, ni dinne de naga dacewar ace ka sameta, saboda shi abu me tsada wajen da akasan za'a adana shi dakyau nan ake ajiyeshi"
Hafeez yayi wani miskilin murmushi sannan yace"to ina ganin kawai acikin maneman nata ka nemi wani ka hada ta dashi" (
Jikin Kawu Hamza yayi sanyi kalau, be ta6a tunanin cewa akwai namijin da zaiyi wa tayin auren HAFEEZA yayi rejecting ba, yasa yaqini sosai akan yaron, bai tsammaci haka daga gareshi ba,ahankali ya kalli Hafeez sannan yayi murmushin yaqe, yace"Yaro haka kace?"
Babu tantama Hafeez yace"ina ganin hakan zaifi"
Cikin sanyin jiki Kawu Hamza yace"to madallah"
aradu Hafeezu yakira wa kansa ruwa
(Nima de Ta Rasulu banida ta cewa saide ince TO MADALLA
Complete document 1k
8621296018
Amina Muhammad
fcmb
kokuma Katin Mtn ta wannan number 08033300034, tareda shedar biya ta wannan number 08033300034
Amnah El Yaqoub
[5/28, 12:53 PM] El Yaqoub:
MATAR ABBANA
(Luv Story)
Writing By Amnah El Yaqoub
Kuyi following WhatsApp Channel dina domin samun sababbin update
https://whatsapp.com/channel/0029VbBR7naJ93wTuOypQV45
Daga nan kawu Hamza yamiqe, Hafeez yamiqa masa hannu da nufin musabaha, kawu Hamza bai bashi hannu ba yajuya yatafi, Hafeez ya kalleshi tareda dage kafadunsa alamun abun be dameshi ba.

Kawu Hamza kuwa jiyayi gaba daya qafafunsa sun saki sunyi sanyi,be yi tunanin haka daga wajan Hafeez dinba, qaran shigowar saqo yaji, yaduba wayarsa anan yaga alert ne na kudin Hafeeza wanda tasamu ranar saukar su, lokaci daya fuskarsa ta washe da annuri, kai tsaye yajuya yanufi gidan Inna Ta Rasulu.

Bayan sun gaisa Hafeeza takawo masa ruwa, sannan ta nemi waje ta zauna adan gefe dasu.

Kawu Hamza ya kalli Inna sannan yace"Ta Rasulu kudin Hafeeza yashigo, amma naga sun rufemin account dina saboda qaramin account ne, kuma bai saba daukar kudi masu yawan wannan ba, zan samu lokaci naje banki saisu bude min shi"
Inna tasaki wata Uwar guda tana sake godia ga Allah, kawu Hamza yace"sannan munyi magana da shugaban makarantar tasu yacemin sunata shirye-shiryen tafiyar ta saudia, yanzu Yaya za'ai da wannan kudin?"
Inna tace" eh ai naga wani malami yazo ya dauketa wai zasuje ayi mata fasfo(passport), Hamza ina ganin kawai karaba wannan kudin agyara mana gidan nan, inda muke yoyo da damuna duk agyara mana, sannan asiya mata kayan dakin, duk dade bamu San yaushe ne auren zaizo ba"
Kawu Hamza ya sunkuyar da kansa cikin damuwa sannan ya dago yace"da nayi tunanin in hadata dawani yaro, da farko na yaba da hankalin yaron, to dana sameshi da maganar saiyace min bayaso"
Inna ta gyara zama tace"dan waye?"
Kawu Hamza yace" acan layin suke, bansani ba ko zaki San kakar yaron, gidan Hajiya Rabi'atu, na yiwa Hafeeza sha'awar yaron saboda naga bashida hayaniya kamar de ita,sannan itama Hafeeza zataji dadin zama dashi, amma yaron nan yadubi idona yace bai amince ba,anawa tunanin duk wanda ya dauki kyautar 'yarsa yabaka ai yayima komai arayuwa"
Inna tace"wai gidan Matar da ake cewa Hajiya Kaka?, gidan ta kake nufi?"
Kawu Hamza yace" eh gidan ne"
Inna tace"ai Hajiya Kaka yayanta manya ne,gaskiya ba yaronta bane inaga jikanta ne, amma kuma Hamza, wani hanzari ba gudu ba gara fa da ba'a yi wannan hadin ba, saboda inajin rade-radin cewa Hajiya Kaka tanada wani jikanta Babba, kuma iyayen yaron suna nan araye,amma baya Shiri dasu, wanne da ne zaiyi watsi da iyayensa ya wanye lafiya aduniyar nan Hamza? to ai har gara Gaddafin data liqewa"(
Kawu Hamza yayi murmushi yace"Ta Rasulu wannan duk zancen mutane ne,sanin gaskiyar al'amari sai Allah sai kuma tsatstsauran bincike,babu damuwa Allah yasa hakane yafi Alkhairi, Allah yabata nagari, idan kuma Gaddafin ne Allah yabasu Zaman lafiya"
Inna tace"Amin"
Hafeeza datake zaune agefe tana jinsu, saide tunda suka fara maganar gabanta yake faduwa,batasan wacece Hajiya Kaka ba, bata gane akan waye suke magana ba, amma koma wanene shi ta tabbatar bazata juyawa Gaddafi baya saboda shi ba.

Da daddare suna kwance a gidan sauro Hafeeza tana tattara tilun gashin kanta tana daure shi, Inna ta kalleta tace"jiya na kwanta da safa a qafata gaba daya sai naji ni adaure"
Hafeeza tace"to Inna ai gara haka, ko sauro yashigo bazai cijeki ba, kinyi maganin sauro"
Inna tasake gyara kwanciyar ta tace"ba saboda sauro nasaka ba, abinda yasa nasaka qafata ce take kama gidan sauron saboda kaushi"(
Hafeeza tayi murmushi batare da tace komai ba.

Inna tace"Hafeeza gobe da sassafe kije wajanda kike soya qosai, kitafi da Almajirai kisa su tone duk wannan baqar qasar da muka tarawa Alhaji na sidi a qofar gidansa, naje har gida nayi masa godia nace to mungode shekara da shekaru muna sana'ah a qofar gidan duk mun baqanta masa qasar qofar gida yace babu komai, wannan bulon damuke amfani kisa Almajiran su debesu gaba daya"
Hafeeza tace"uhm..."
batare data tanka ba, saboda tafara karanta addu'ar bacci acikin zuciyar ta.
*** *** ***
Cikin dare yana bacci wani irin masifaffan ciwon ciki ya ta dashi, mararsa ta riqe yarasa yanda zaiyi sai hada gumi yake.

Cikin tsananin tashin hankali ya janyo wayarsa ya dokawa Kaka kira.

Kaka tana bacci taji qaran waya, tamiqe ta zauna tana fadin "la'ila ha illallahu,Muhammadur rasu lullah"
Ta juya gefenta ba taga Hassana ba, da alama yau ta gudu wajan Hussaina acan dakinsu zata kwana,tayi sauri ta dauki wayar ta Kara a kunne, daga nasa 6angaren yace"Kaka zan mutu"
Gabanta ya yanke yafadi tace"Hafeezu!, gani nan zuwa"
Cikin azama tatashi tafuto daga nata dakin tashiga nasa,ta kunna wutar dakin anan tayi tozali da abun Hafeez ya miqe qyam, gabanta yasake faduwa kanta ya Sara, ta kalli Hafeez din taga yana runtse idonsa ga gumi ya jiqe masa fuska sharkaf kamar an watsa masa ruwa, cikin sauri ta qarasa taja bargo ta rufe masa jikinsa duk da akwai jallabiya ajikinsa, sannan ta dauki wayarsa tace"nemo min lambar Jamilu in kirashi"
Kansa ya girgiza alamun bazai iyaba.
Chapter 14 · 0% Book details