← Book details Matar Abbana Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 24

Sashe 11

Matar Abbana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hafeeza tarufe fuskarta cikin kunya sannan tace"akwai Kawu"
Ta Rasulu ta ta6e baki tace"wannan saurayin naki Hafeeza dashi ai gara babu, saurayi kullum sai shegiyar fira yakasa tsinana miki komai, kuma shi yaqi yaturo iyayensa ayi magana, kullum de gashinan sai aukin zuwa zance, shekaran jiya yazo ta kashe kudi ta tar6eshi, ya cinye komai bai bata ko kwabo ba, yanzu yauma dazun nan yazo be tsinana Mata komai ba sai alewa daya kawo Mata itama ba tafi ta dari biyu ba, nakusa nahana ki fita zancen ma,idan zai turo iyayensa yaturo ayi maganar aure,tun shekarar dakikai candy aketa soyaiyar nan,shi idan sallah tazo ko lallen sallah uwarsa ba kawo miki take ba, Shima bazakici sisin kwabonsa ba, to gara ayi daya, kode ki sallameshi kokuma yafuto yadaukeki ku tafi can gidansa saiku qarata da mammaqonsa tunda ahaka kikeson abinki"
Kawu Hamza yayi murmushi yatashi tsaye yana yimusu sallama, dama abinda yakeson ji Kenan, kuma yasamu amsar tambayar sa.

Kawu Hamza yana fita maman Fadila tashigo gidan, Inna ta kalleta tace"Sa'adatu ina ki kabar mijin naki da wannan daren kika futo?"
Maman Fadila tayi murmushi tana zama akan tabarma tace"Inna wallahi harna kwanta Baban Fadila yashigo, kaji ne yashigo mana dasu shine na dauko muku kuma kuta6a"
Inna takai hannu ta dauki cinyar kaza takai bakinta sannan tace"haba Maman Fadila aida kinbari sai ahadu zuwa safiya"
Maman Fadila da Hafeeza sukai dariya,ganin yanda Inna tafara cin naman kaza amma tana cewa da an barshi zuwa safe.

Maman Fadila ta kalli Hafeeza tace"Hafeeza gobe akwai abinda zakiyi ne? inba abinda zakiyi kikai min Fadila asbiti mana,za'a mata allura"
Inna tace" ina zataje kuwa? ba inda zataje, saita shirya takai miki ita"
Maman Fadila tace" Nima wanki zanyi da safen,kinga idan takai min ita kafin su dawo nagama wankin na rage wani aikin"
Hafeeza tace"to Allah yakaimu"
*** *** ***
Washegari takama litinin, tunda aka idar da sallar asuba Hafeez bekoma bacci ba,sosai yayi nisa cikin tunanin ta,so yake yaje wajanda take saida qosai ko Allah zaisa yasake ganinta, yarasa meyasa yakejin idan beyi magana da'ita ba kamar zai iya Samun matsala, wannan dalilin ne yasa ya gagara komawa bacci bayan yadawo daga sallar asuba, saboda bayaso yakoma bacci daga qarshe kuma ya makara yarasa damar dazai ganta a wannan ranar.
baya cikakken minti goma beduba agogon dake hannunsa ba, qarfe bakwai da rabi tanayi yafuto daga wanka,kamar kullum yauma haka yafuto babu kaya ajikinsa, agaban madubi ya tsaya yana qarewa jikinsa kallo yanda fatar sa take shining kamar mace,cikin sauri yafara shiryawa, daga can falo yake jiyo muryar Aunty Sadiya itada Kaka suna magana da d'an qarfi hakan yasa har yake iya jiyo zancen nasu.
ahankali yasaka hannunsa ya shafo gadon bayansa lokaci daya ya lumshe idonsa cikin damuwa sakamakon tabon bulala dayake kwance abayan nasa, cikin damuwa ya shirya cikin qananun kaya riga da wando, yafeshe jikinsa da turare sannan yafuto daga dakin nasa cikin sauri.

Yana zuwa falo Hajiya Kaka kadai yagani, hakan saiya yi masa dadi saboda dama kokadan bayason ganin fuskar qanwar Mahaifiyar tasa, wato Aunty Sadiya.

Kaka ta kalleshi taga yaci uban gayu da qananun kaya, kuma tasan cewa inde yazo qasar baya ma futowa daga dakinsa sai wajan shadaya na safe, saboda yana komawa bacci bayan sallar asuba.

Cikin mamaki tace"wai Hafeezu ina kake zuwa ne kullum dasafe a cikin kwana biyun nan?"
Hafeez yadan shafa sumar kansa sannan yace" Kaka yanzun nan zan dawo"
Yafadi hakan hankalinsa yana kan agogon hannunsa saboda kada lokaci ya qure baije wajan ba, domin kuwa yayi alqawarin yau sai yayi magana da'ita.

Ajiyar zuciya tasaki batace masa komai ba,hakan yasa shima yadan kalleta yaga de idonta a kansa yake,Kaka kuwa gaban wandonsa ta kalla taga ya d'an taso kad'an, ga abu ana ganinsa taru guda kamar ansa wani abu aciki.
cikin sauri ta janye idonta, shima daga nasa 6angaren bai gane abinda take kalla ba hakan yasa cikin sauri Yajuya yafice daga falo.

Kaka ta girgiza kanta tace"uhm....

Wannan yaro Hafeezu ina tausayin matarsa"
Husna da Hassana dasuka futo daga kitchen suna qoqarin jera break fast, suka kalli Kaka, Hassana tace"Kaka magana kike?"
Kaka tace" yaron nan ne Hafeezu nake magana dashi, kullum haka yake abubuwan sa abun tausayi,ko kad'an bashida shauqi....,narasa yarinyar dazan samu na hadasu wacce zata fahimce shi, mu kanmu damuke ahalinsa mun kasa fahimtar abinda yakeso"
Husna ta zauna akusa da'ita tace"Kaka ni abinda nake gani kicire maganar auren Yaya aranki, shi aure lokaci ne Kaka"
Cikin sauri Kaka tace"haka de!, kullum haka kika iya Husna, kokadan bakyason ganin laifin Hafeezu, to idan Hafeezu beyi aure ba a shekaru irin nasa sai yaushe zaiyi? bakuda hankali ne shiyasa kuke ganin kamar ina takura masa akan batun auren, ni nasan menake hangowa, amma nariga nagama yanke hukunci zanyi magana da Alhaji Abdullahi idan beyiwa yarsa miji ba sai ahadasu ayi aurensu"
Hassana ta jinjina kanta tana murmushin jin dadi, dama kullum so take ayi aure a gidansu, shikuma Yaya Hafeez yayi biris da maganar aure.
*** *** ***
Kawu Hamza yasaki fuskar sa bayan Ma'aruf yafuto daga gida, yabashi hannu suka gaisa cikin farinciki, kawu Hamza yace"yaro Kaine Ma'aruf ko?"
Cikin mamaki Ma'aruf ya gyada kansa yace" nine Baba, meyake faruwa?"
Kawu Hamza yayi murmushi yace"wata magana ce take tafe dani mai girma, idan babu damuwa inaso mu zauna saimu tattauna akan maganar"
Ma'aruf yanuna get din gidansu da hannu yace"Bissmillah to shigo"
Cikin nutsuwa suka qarasa cikin gida, Ma'aruf yakawo masa farar kujera ta roba suka zauna can nesa da megadi, kawu Hamza ya kalli Ma'aruf yace"Magana nazo da'ita akan abokinka HAFEEZ"
Cikin sauri Ma'aruf yace"Hafeez kuma? meyafaru dashi?

Yanzun nan shigowa ta kenan bana qasar naje Ghana, ko haduwa banyi dashi ba, wani abu yafaru dashi ne?"
Kawu Hamza yayi murmushi yace" ko d'aya, babu abinda yafaru dashi sai Alkhairi dayake son faruwa dashi, wato Ma'aruf, haqiqa na yaba da hankalin abokinka, na yaba da nutsuwar sa dakuma kyawun halayensa, hakan yasa natako qafa da qafa, inaso kayi masa magana kafada masa cewa idan babu damuwa zan bashi auren 'yata"
Cikin sauri Ma'aruf yadago kansa yana kallon Kawu Hamza.

Kawu Hamza yace"ko akwai alqawarin wata yarinyar a kansa?"
Ma'aruf ya girgiza kansa yace" ko kad'an,saide nasan halin Hafeez yanada wani irin ra'ayi nasa wanda bayason sauraren mace duk yanda take,amma insha Allah zan sameshi inyi masa maganar"
Kawu Hamza yasaki murmushi yace"hakane, amma nasan cewa Babu yaron da zanyi masa tayin auren yata yaqi kar6a, saboda yarinya ce me hankali da nutsuwa,amma ka sameshi kuyi maganar, ina sauraron ku duk yanda kukayi "
Ma'aruf yabashi hannu suka sake gaisawa, sannan kawu Hamza yayi masa sallama shima yatafi.
*** *** ***
Yana qarasawa wajan daga nesa ya ajiye motarsa yafuto kai tsaye yanufi inda take saida qosan, zuciyarsa banda fad'uwa babu abinda takeyi, saide yayi alqawarin yau kam saiyayi magana da'ita baki-da baki.

Abun mamakin yana qarasawa wajan yaga waje wayam!, babu ita babu dalilin kayanta, ganin wasu samari a zaune agefe yasa yaja ya tsaya daga gefensu tareda dauko wayarsa yana duba lokaci, yayi mamakin yanda akai bata futo ba,wata zuciyar tace to ko tadena futowa saboda kyautar data samu awajan sauka?

Maganar matasan dake gefe ne tadawo dashi daga duniyar tunanin daya tafi, daya daga cikinsu yace"yarinyar nan saboda ita nake zuwa wajannan kullum, naso ace kudi ne dani da aurenta zanyi in huta da zuwa wannan wajan,amma babu yanda na'iya, saide kuma haqiqa duk wanda ya aure ta zai kwashi kaya wallahi"
Dayan abokin nasa yayi dariya yace"ashe kagane, ai Hafeeza ta hadu ba qarya, gashi kamewarta tayi yawa, maza dayawa suna son yimata magana amma suna shakkar ta"
Wani irin baqin ciki ne yazo ya tsaya a wuyan Hafeez, yaji kamar yaje ya shaqe su, wato masu zuwa kallon nata sunada yawa kenan?

Haka ya juyo yadawo gida jikinsa amace, ransa a6ace komai ya dagule masa saboda wannan furucin na kwasar kaya da wannan samarin sukai akan Hafeeza.

Ransa a 6ace yafuto daga motar sai sakin tsaki yake.

Tafiya yake yana shawara da zuciyarsa shi kadai, yakamata yayi magana da'ita, idan tasan zataci gaba da wannan sana'ar to karta sake futowa, tafada masa ko nawa take kashewa kullum saiya turo mata, amma bazai juri kullum tana fita samari suna kallonta suna maganar banza akanta ba.

Ko inda dining yake bai nufa ba, ransa babu dadi ya kwanta akan doguwar kujerar dake falon.

Wayarsa ce tafara qara,yanajin wayar ya qyaleta tayi tagama kukan ta, akaro nabiyu ma aka sake kira, cikin damuwa ya dauki wayar yakara a kunnansa batare dayayi magana ba.

Daga d'ayan 6angaren I.B yace"Hafeez nakira baka kusa,dama zance ma ne na kaiwa Yaya Jabir kud'in, kuma yace ayima godia, yasan idan yakira ka ma bazaka dauka ba, sannan naga kamar Baba yana cikin yanayin damuwa,idan babu damuwa ya kamata kazo kagana da MAHAIFINKA, sannan AUNTY UMMI...."
Sai kuma yayi shiru, Hafeez dake kwance cikin sauri yatashi daga kan kujera ya zauna yace" meyake faruwa da Aunty Ummi? meyake damunta I.b ka fadamin"
I.B yace" Aunty batada lafiya Hafeez, kuskure nane daban sanar dakai dawuri ba, nayi tunanin rashin lafiyar tata zata warware cikin sauri,amma yanzu jikin nata ya matsa, ya kamata kazo ka ganta"
Lokaci d'aya kansa yasara,wannan rashin lafiyar ta Aunty da'aka fada masa ta dakeshi, saboda Aunty tanada muhinmanci acikin rayuwar sa, Aunty mutum ce, kuma Aunty 'yar halak ce da bashida kamarta.

Baisan lokacin da wayar hannunsa tafadi ba, abinda yasani shine kansa ya daure, gaba daya ciwo kan nasa yake masa, yanason zuwa yaga Aunty da kuma mahaifinsa, amma bayason ganin MAMA, yarasa yanda zaiyi da wannan damuwar, baison ganin Mama koda wasa.

Ahankali yasaka hannayen sa ya tallafe kansa dasu, yanajin wani irin zazza6i yana neman rufe shi, cikin damuwa yadauki wayarsa yakira Dr.

Jamil, abokinsa ne sosai, sannan idan rashin lafiya takama wani daga cikinsu ko 'yanbiyu ko Kaka, kawai waya yake masa yazo har gida ya duba su.

Dr.

Jamil yana dauka Hafeez yace"Dr.

Ina cikin damuwa,ina buqatar ka"
Dr.

Jamil yayi murmushi yace"to Abokina, nabaka shawara kaqi, yanzu menene matsalar?"
Hafeez ya lumshe idonsa yace" I'm serious Jamil, ina buqatar ka"
Cikin sauri Dr.
Chapter 11 · 0% Book details