Sashe 10
Matar Abbana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Anbawa shugaban makaranta damar jawabi dakuma godia ga baqin dasuka samu zuwa, wani kudin yasake shigowa cikin asusun makarantar, ma'aji ya matso kusa da me gabatarwa yayi masa bayani, me gabatarwa yace"to Alhamdulillah masha Allah, muna kan rufe babin godia ga manyan mutanan dasuka yimana kyautar girmamawa dakuma kyautar kudi, sai kuma gashi wani bawan Allah wanda ya nemi a 6oye sunansa yaturo wa wannan makaranta tamu kudi har naira million goma Sha biyar, million goma na makaranta, sannan dalibar data fara karatun Alqur'ani wato Hafeeza Khalid yace abata million biyar sadaka fisabilillah"
Lokaci daya waje ya kaure da ihun murna kowa sai kabbara yakeyi.
Hafeez yayi sauri yamaida wayarsa cikin aljihun wandon sa ganin kaka ta zubawa wayar tasa ido tana kallo kamar tana so ta gano cewa shine yayi wannan kyautar, shikuma ba komai ne yasa yayiwa yarinyar kyautar ba saboda yaga kamar tanada karancin hijabai, kud'in zai Isa tasake dinka wasu hijaban.(
Ta Rasulu tanajin wannan kyauta tafashe da kuka wiwi.(
Yayinda Hafeeza ta sunkuyar da kanta qasa tana goge hawayen idonta.
Bayan angama karbar kyautar kudade daga nan aka fara saida calendar mai dauke da photon dalibai ajiki.
Hafeez ya kalli Hajiya Kaka yace"kin riqe takardar account, ki basu takardar su tunda bazaki iya tura musu ba"
Hajiya Kaka ta harareshi tace"saikace kai?"
daga nan ta daga murya ta Kira me gabatarwa, Yana zuwa wajanta tace"bawan Allah ka daga murya kafada a speaker cewa Hajiya Rabi'atu kakar Hassana da Hussaina wadda akafi sani da Hajiya Kaka, ta sai calendar naira dubu Dari"
Aikuwa ya karbi kudi Yakoma tsakiyar taro yafada kamar yanda Hajiya Kaka takeso, su Hassana suna zance qasa qasa saiji sukai sunansu yafado cikin kwatancen Kaka.
me gabatarwa yadawo yakawo wa Hajiya Kaka Calendar ta, Hajiya Kaka ta kar6a sannan tayi wa Hafeez wani kallo me alamun nafi qarfin raini ta kauda kai, shi kuwa dariya ma ta bashi, amma kasancewar miskilin mutum ne saiya yi dan murmushi kadan ya basar.
daga nan akayi Addu'ar tashi daga taro, aka sallami dalibai kowa ya nufi wajan 'yan'uwansa.
Hafeeza tafuto zata nemi su Inna, 'yanbiyu suka tareta Husna tace"Hafeeza tsaya ki mana photo"
Tafadi haka tana miqa mata wayar hannunta iPhone me camera uku, Hafeeza ta kar6i wayar tana murmushi har dimples dinta suna lotsawa.
Hassana ta rungume Husna sannan itama tace"kuma ki tabbatar munyi kyau sosai ehe, idan bamuyi kyau ba saikin sake mana sabo"
Hafeeza ta girgiza kanta tana murmushi sannan tafara qoqarin yimusu photon da qyar kasancewar bata ta6a riqe babbar waya irin wannan ba, tarasa yanda zatayi ta dauki photon, batasan yanda ake photon ba.
Su Husna suka sauya style, Hassana tace"kin dauka?"
Hafeeza tace"A a ban dauka ba"
Husna tace"har yanzu de baki dauka ba?"(
Lokaci d'aya Hafeeza duk ta rikice, tarasa yanda zatayi, yanda ta rikice din saita sake yiwa Hafeez kyau wanda yake tsaye ajikin motarsu yana kallonta,mayan kayan dake jikinsa sun sake qawata kyansa,sosai ya shagala wajan kallonta saide miskilancin sa ba zaisa ka gane cewa kallon arziqi yake mata ba.
Cikin zazzaqar muryar ta tace"narasa yanda zanyi ne, ku sake matsawa kusa"
Cikin sauri 'yanbiyu suka matsa suka sake rungume juna.
Hafeeza ta qoqarta ta dauke su, sannan cikin zazzaqar muryar ta, tasake cewa "kuyi murmushi to,kekuma Husna gyara tsayuwarki"
Duk abinda take fada musu haka sukayi, sannan ta dauka tabasu wayar domin su gani, kokadan bata lura da Hafeez dake tsaye agefe ba,shima Koda wasa baiyi gigin yimata magana ba,gaba daya ya shagala a kallonta, wani side na zuciyarsa yanajin tausayin yarinyar,dazu da safe yaganta tana suyar qosai, sannan yanzu gata awajan sauka, hakan yana nufin saida tagama yin sana'ar tasu sannan tataho wajan saukar.
Idonsa ya lumshe kad'an yana tuno shekarun baya yanda rayuwa ta kasance masa,yatuna yanda yake daukar qosai a kansa yana yawo
dashi waje-waje.
Cikin sauri yadawo daga tunanin daya tafi kasancewar yaji zuciyar sa tafara tafarfasa akan rayuwar daya tuno, fuskarsa babu yabo babu fallasa yakai dubansa zuwa ga 'yanbiyu anan yaga suna yin selfie tareda Hafeeza, murmushin daya gani kwance akan fuskarta shine yasa haka nan ya tsinci kansa cikin farinciki.
Maman Fadila ce tazo ta janye ta suka nufi wajansu Inna, har zuwa wannan lokacin Ta Rasulu kuka take, kawu Hamza dake tsaye a gefenta shida matarsa Maryama sai baki suke bata akan tayi haquri tadena kuka, daqyar aka samu tayi shiru sannan suka had'u waje daya gaba dayansu, Hafeeza tashiga Tsakiyar su, Maman Fadila kuma tafara yimusu photuna.
*** *** ***
Da daddare suna zaune afalo gaba d'ayansu, kayan shan'iska ne ajikin 'yanbiyu, Kaka kuwa Hijabi ne ajikinta tana jan carbi.
'yanbiyu ne suke zancen taron saukar su ta dazu.
Hafeez yana zaune agefe wando ne ajikinsa three quarter da wata riga wadda batada maraba da singlet saboda yanda dantsan hannunsa yake abude, hatta nipples dinsa kana ganin tsininsu ta cikin rigar saboda yanda rigar take ba kauri.
Jarida ce a hannunsa yana dubawa amma gaba daya idonsa ne akan takardar, tunanin sa dakuma jinsa yana wajan 'yanbiyu saboda yanaso yasake jin sunyi zancen Hafeeza ko zaiji wani abu daga cikin halayen yarinyar.
Kaka ta ajiye carbin hannunta ta shafa Addu'ah sannan tacire Hijabin jikinta ta kalli 'yanbiyu tace"Allah de kuma yakawo muku mazaje nagari, wannan yarinya data fara karatu dazu da zafe awajan sauka, haqiqa wannan kyautar data samu nasan ba saboda karatun ne kadai ba, harda masu sonta"(
Hassana tace"ai Hafeeza tasamu kudi gaskiya,Kaka itace fa wannan wadda muke fada miki ta'iya karatun Alqur'ani, kuma suma malaman namu sai nan-nan suke da'ita daga gani sonta suke"
Gaban Hafeez yayi wata irin muguwar faduwa, yasaki dan qaramin tsaki sannan yasake bude wani shafin jaridar.
Kaka tace"Allah sarki ashe itace, amma daga gani tanada nutsuwa yarinyar,kuma kana kallonta zaka tabbatar ba asalin yar qasar nan bace gaskiya,kode ruwa biyu ce kokuma daga wata qasar sukazo, ni naso inji wanda yabata million biyar dinnan,ai kyautar farko ance d'an majalissa ne yabata"
Hafeez ya d'an kalli Kaka sannan ya dauke kansa.
Kafin 'yanbiyu su sake magana wayar Hafeez dake gefe tafara ringing, cikin nutsuwa da aji irin nasa yadauki wayar tareda fadin "I.B kaga saqon dana turo mane?"
Daga d'aya 6angaren I.B yace"nagani, naje nakai masa, na sameshi cikin aminci, yana lafiya babu wata matsala"
Ahankali ya lumshe idonsa yana sakin wata irin ajiyar zuciya, batare dayace komai ba yakashe wayar.
Kafin wani daga cikinsu yayi magana wata Babbar mata tashigo falon, zata iya kaiwa kimanin shekara Arba'in dawani abu, Hafeez yanajin muryar ta yagane ta,ko a mafarki bazai ta6a mantawa da muryar taba, lokaci daya fuskarsa ta sauya ya runtse idonsa, kokadan bayason ganinta.
Matar taqaraso cikin falon, tana qoqarin zama akan kujera shikuma Hafeez yana qoqarin tashi,yanajin yanda 'yanbiyu suke qoqarin gaida matar, wadda ta kasance qanwar mahaifiyar su ce uwa d'aya uba d'aya,amma Hafeez ko kad'an baima nuna yasan taba, maganar fatar baki bata hadashi da itaba yabar jaridar dayake karantawa awajan yashige cikin dakinsa.
Kaka tabi bayan sa da kallo harya rufe qofar dakinsa.
Cikin sanyin jiki tadawo da dubanta zuwa wajan 'yartata cikin tsananin damuwa dakuma sanyin jiki take duban ta, ta rasa yanda zatai ta gyara baya, tarasa yanda zatai ta dedeta kan ahalinta yazama daya,kuskure an riga anyi, saide ayi haquri a fuskanci gaba,inda ace zata iya maida hannun Agogo baya, to haqiqa da zata dawo da nasu agogon qaddarar baya domin ta gyara matsalolin cikin ahalinta.
(meyake faruwa da ahalin Hafeezu ne?
(Jama'ah wa zai turamin 5 million Nima in sake hijabai
Complete document 1k
8621296018
Amina Muhammad
fcmb
Kokuma Katin Mtn ta wannan number 08033300034, tareda shedar biya ta wannan number 08033300034
Amnah El Yaqoub
[5/26, 1:59 PM] El Yaqoub:
MATAR ABBANA
(Luv Story)
Writing By Amnah El Yaqoub
Kuyi following WhatsApp Channel dina domin samun sababbin update
https://whatsapp.com/channel/0029VbBR7naJ93wTuOypQV45
Matar data shigo falon tayi murmushin yaqe ta kalli Kaka tace"Ummah ashe Hafeez yazo qasar"
Kaka tace"Hafeezu yazo SADIYA, su Hassana ne sukai masa magana nayi tunanin ma bazai samu zuwa ba, kuma sai gashi yazo"
Cikin Sanyin jiki Wadda aka kira da Sadiya tace" Allah sarki, nima tun safen naso zuwa kuma saboda yanayin abun hawa yayi qaranci yanzu, ba'a samun fasinjoji masu yawa atasha, shiyasa na makara, Allah ya sanya Alkhairi"
Kaka tace"Amin Sadiya, amma ai zaki zauna damu muyi kwana biyu ko?"
Cikin sauri Sadiya tace" a a Ummah,gobe zan tafi insha Allah"
Jikin kaka yasake yin sanyi kalau,tasan cewa ganin Hafeez yana gida ne shiyasa tace bazata zauna ba.
Kafin tasake wata maganar 'yanbiyu suka kawowa Aunty Sadiya abinci da abun Sha.
Aunty Sadiya ta kallesu tana murmushi tace "Husna da Hassana yanzu kuma an sauke,saura rubutawa kuma"
Kaka tayi murmushi tace"sa rubuta adakin mazajensu, aurensu zanyi, danma Husna babu mashinshini aida tuni anyi auren"
Kaka ta qarasa maganar cikin tsokana.
Husna ta harari Kaka sannan tace"ko lokacin dakike yanmatanci Kaka baki kaini samari ba,samari suna nan dayawa sai wanda nazaba"
Aunty Sadiya tayi dariya tace"Allah Husna, wato kema yanzu kinbi sahun Hassanarki bakinki yafara budewa...."
Gaba dayansu sukasa dariya kamar basuda wata matsala agabansu.
*** *** ***
Suma su Hafeeza suna zaune a tsakar gidansu akan wata babbar tabarma, kasancewar kawu Hamza yasan cewa gidan nasu zai tara jama'ah hakan yasa bai samu zuwa ba sai wajan qarfe goma na dare mutane sun tafi gida sai Inna da Hafeeza kawai.
Kawu Hamza ya kalli Inna yace"Yanzu Ta Rasulu Yaya kike ganin za'ayi da wannan kudin da Hafeeza tasamu idan ankawo mana?"
Inna tace" Haba Hamza,ai Kaine uba, Kaine zakasan abinda za'a yi dashi, nide fatana asamu adan gyara mana gidan nan, saboda da damuna munayin yoyo sosai, wani lokacin Hafeeza a zaune take kwana"
Kawu Hamza yayi murmushi yace"to dama munyi magana da shugaban makarantar tasu, yacemin nasamo account number da za'a tura mana kudin, ni ina ganin idan kudin sun shigo, kuyi tunanin wata sana'ar daban kufara, saiku ajiye wannan sana'ar qosan agefe, saikuma kayan dakinta da nakeso asiya a ajiye, kokuma abawa masu saida kayan kudin, idan aurenta yatashi kinga zuwa zamuyi mu dauka, duk da made bansani ba ko 'yartawa tanada saurayi"
Ya qarasa maganar tasa cikin salon shan ciki yana kallon wajanda Hafeeza take zaune.