← Book details Matar Abbana Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 24

Sashe 1

Matar Abbana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Root Entry
WordDocument
0Table
Data
[5/20, 7:29 PM] El Yaqoub:
MATAR ABBANA
(Luv Story)
Writing By Amnah El Yaqoub
Kuyi following Channel dina domin samun zafafan labarai
https://whatsapp.com/channel/0029VbBR7naJ93wTuOypQV45
Duk yanda yaso motar tatashi, abun yaci tura, badon yaso ba, haka yajuyo cikin ladabi da girmamawa yadubi Hajiya Kaka yace"Hajiya inaga saide natare muku abun hawa ku qarasa gida,zan kira me gyara yaduba motar,bansan meyasa ta tsaya ba"
Hajiya Kaka tasaki ajiyar zuciya sannan ta dubi kyakykywar jikarta, wadda hankalinta kacokam yake kan wayar hannunta qirar IPhone,tace"to hamshaqiya muje, kin hard'e kina danna waya kamar 'yar sarki,mota ta lalace mu sauka munemi abun hawa"
Yarinyar da batafi shekara goma Sha takwas ba,daga ganinta kasan surutu bai dameta ba, batace uffan ba, sai baki data ta6e tafara qoqarin bude motar, saide kafin takaiga budewa direban ya zagayo da sauri yabude musu, sannan yazaro wayarsa daga cikin aljihun wandon sa yafara kiran me gyara, yayinda hannunsa na hagu yake d'agashi sama yana qoqarin tare musu Keke napep.

Ba'a bar Hajiya Kaka abaya ba, itama hannu tasa tana qoqarin tare musu abun hawan har Allah yakawo wani ya dakata,kafin direban yayi magana Hajiya Kaka tace"tsaya,tsaya,d'an sahu,tsaya ka kwashemu "
Dan adede ta ya kalli motar dake gefensu fara tas,qirar Lexus Rs 350 motar sai shining take tana daukar ido,da alama sabuwa ce,nan take yasan cewa yayi babban kamu.

Hajiya Kaka tashige, sannan itama jikarta tashiga, direban ya d'an rissina dede wajan da d'an sahu yake zaune sannan yace"G.R.A zaka kaisu"
Dan sahu ya kalli Hajiya Kaka yace"Hajiya kudinku dubu uku"
Hajiya Kaka tace"muje Allah ya saukemu lafiya"
Direban nasu yafara qoqarin dauko kudin zai bayar, Hajiya Kaka tace" 'Dan Ladi barshi zan bashi kudin"
'Dan Ladi ya maida kudinsa cikin aljihunsa sannan yace"to Hajiya Kaka saina qaraso,Allah Yakiyaye hanya"
Hajiya Kaka tace"A a 'Dan Ladi, zoka kar6i dubu daya kasayi ruwa kasha"
'Dan Ladi direba yayi murmushi yace"A a Hajiya Kaka ki barshi"
Hajiya Kaka tace"to kanaji ko 'Dan Ladi?,idan angama gyara motar, kana shigowa layin farko kafin kaje gidan Alhaji Biniya,anayin qosai awajan kasiyo min kataho min dashi"
Kafin 'Dan Ladi yayi magana d'an sahu yace"Hajiya baku gama bane?"
Hajiya Kaka tace"mungama, sarkin azalzala muje,ni Allahn dayayi ni banason kad'ar hankali a rayuwata,ita rayuwa dakake bahaka ake tafiyar da'itaba "
Jikarta dake gefe ta dafe kanta da hannunta sannan ta kalli Hajiya Kaka tace" yanzu de tunda yaja mun tafi Kaka kiyi shiru mana,sai mita kike tun dazu haba!"
Hajiya Kaka tayi shiru,saide bakin nan nata ta cuno shi gaba alamun fad'an da jikar tata tayi mata baiyi mata dad'i ba.

Sun d'auki lokaci suna tafiya wani mutum daga gefen titi yataresu yace"Kabuga"
'Dan sahu yace"Drop suka dauka"
Sannan yafara qoqarin cigaba da tafiya, Hajiya Kaka tace"ai kasan drop d'in muka dauka amma daya tareka ka tsaya, tunda ka tsaya Yaya na'iya dakai? daukeshi kawai,shi musulmi ai d'an uwan musulmi ne"
Dan sahu yace"to nagode"
Ya kalli fasinjan dake tsaye yanajin duk abinda yake faruwa, sannan yace"nawane dakai?"
Fasinja yace" d'ari biyar ce"
Dan sahu yace"gaskiya banida canji yanzu nafuto"
Yana fad'ar haka yafara qoqarin tada napep dinsa, cikin sauri Hajiya Kaka tace"dakata d'an sahu,bari in duba muku canji, banaso naga abokin kasuwanci na yana Neman canji"
Cikin sauri jikarta dake gefe ta kalleta tace"Abokin kasuwancinki?, Kaka yaushe kika fara Jan adedeta bamu sani ba?"
Kota kanta bata biba, tabude hand back din dake kan cinyarta tabasu canjin, sannan ta matsa masa shima yashigo cikin adeden,basu dade da daukan hanya ba, sukasha kwana cikin wani gidan mai, Hajiya Kaka tana ganin haka tace"uhm za'a bata abinci"
Babu wanda ya tanka mata acikin adedetan har suka tsaya aka fara zuba musu mai, daga gefe guda akwai wasu samari su uku kowa yana kan Abun hawa suna jira layi yazo kansu,zancen Sojojin qasar suke,d'aya daga cikin matasan yace"ainaji dad'in yanda shugaban Sojojin nan ya tunkari kidnappers d'in nan yayi futo nafuto dasu "
Kafin wani daga cikinsu yabashi amsa Hajiya Kaka ta leqo kanta daga cikin adede tace"shi kwamandon Sojojin ne ya tunkari masu Garkuwa da mutane?

Kuma baya jin tsoro?"
Wani daga cikinsu yayi murmushi yace"Haba Mama, wanne tsoro kuma? ai bayajin tsoro"
Hajiya Kaka ta jinjina kanta sannan tace" wataran zaici gidansu kuwa"
Babu wanda bata bawa dariya ba,ciki harda jikarta wadda hankalinta yake kan wayarta tana shafawa.

Suna barin gidan man gaba kad'an sukaga dalibai masu yawa 'yan makarantar secondary suna tsaye agefen titi kasancewar safiyace kowa yana fafutukar neman abun hawa domin tafiya makaranta.

Hajiya Kaka ta kalli wannan uban dalibai wanda dayawa daga cikinsu duk Yan mata ne,kuma dukkaninsu babu me aure, ahakan burin ko wacce uwa shine ta aurar da diyarta, tasaki ajiyar zuciya ta kalli jikarta tanayi mata nuni da wannan daliban tace"kinga duk jiran abun hawa suke"
Jikar tata ta kalli daliban sannan ta maida hankalin ta kan waya batare data tanka ba,basu dade da barin wajanba suka sake ganin wasu tarin daliban, nanma Hajiya Kaka ta gagara yin shiru saida ta tanka, tasake kallon Jikar tata akaro na biyu tace"suma wannan jiran motar suke,uhm...,Allah de yabaku nagari"
Wannan Karon ma Jikar bata tanka mata ba, haushi yakama Hajiya Kaka,cikin 6acin rai tace"nifa arayuwata natsani baqin miskilancin nan naki Husna,shiyasa banason tafiya dake nafiso nayi tafiya da Hassana, muna tafe munata zancen mu,amma ke sai kiyi gum da baki kamar Yayanku HAFEEZU, gaba daya kin kwaso baqin miskilancin sa kin dorawa kanki"
Husna ta girgiza kanta tace"yanzu Kaka me kikeso nace miki? ni wallahi surutun naki ma ya isheni,qiris yarage kaina yafashe,shiyasa nayi miki shiru amma ke ban hanaki ba kiyi abunki ke kadai"
Hajiya Kaka ta jinjina kanta sannan tace"gaskiya ne,ga Rabi'atu uwar ta6a66u ai dole nayi surutu ni kadai,ato duk wanda yake surutu shi kad'ai kam menene marabar sa da ta6a66e?"(
Dan sahu yana jinsu yana dariya shi kadai,Shima d'aya matashin dayake zaune agefen Hajiya Kaka saida ya murmusa, yayinda Husna tayi shiru bata tankaba kamar bada ita ake maganar ba.

Hajiya Kaka kuwa ta cuno baki gaba tace"Gaskiya ne"
Da'aka sake jimawa ita kadai de tasake cewa "Gaskiya ne"
Itade Husna batace komai ba, har Allah yakawo su gida lafiya,d'an sahu ya ajiyesu a bakin get din wani danqararen gida,kallo d'aya zaka yiwa hadaddan gidan ka tabbatar nera tayi kuka.

Me gadi ya bude masu qaramar qofa yana sake gaida Hajiya Kaka cikin girmamawa, suna shiga compound din gidan Hajiya Kaka tacire Mayafin jikinta tad'aga qafa tayi gaba tabar Husna abaya,yayinda wayar Husna tayi qara alamar kira yashigo, ta amsa kiran tana magana yayinda idonta yake kan parking lot din gidan wanda wasu manya-mayan motoci guda hudu suke adane aciki sai daukan ido motocin suke, saide akwai yar qura ajikinsu kad'an kasancewar ba'a cika hawansu ba.

Hajiya Kaka tana shiga falonsu wani sanyin esi ya daketa, tayi wulli da Mayafin hannunta akan kujera sannan ta zauna tana fad'in "banda zuwa ta'aziyyar nan tazamemin dole, da babu abinda zaisa nafita daga gida sassafen nan"
Hassana dake jera abun break fast akan dining taqaraso falon tana fad'in "Kaka kun dawo?, ina kika bar Husna?"
Hajiya Kaka ta kalleta, 'yanbiyun jikokin nata basu da banbanci ta 6angaren kamanni,idan baka sansu ba babu yanda za'ai ka'iya banbance su saboda yanda suke tsananin kama da juna,saide halaiyar su ta banbanta data juna, Husna miskila ce taqin qarawa kamar Babban Yayansu HAFEEZ ,yayinda Hassana take faram-faram kowa nata ne.

Saida tagama tunanin sannan tace"naje na siyar da'ita nadawo, kudin kuma qarfi ya cinye"
Hassana tanajin haka tayi murmushi, lokaci daya tagano cewa da alama sunyi abunda suka saba, wato fada.

Kafin tayi magana Husna tashigo falon, suna ganin juna itada Hassana suka saki murmushi, daga nan Hassana tawuce tahado tea, ta kunna Kallo takamo musu tashar Bollywood, tana shan tea suna kallo, yayinda Husna take danna wayarta gefe guda kuma tana kallon itama, basu dade da fara kallon ba suka fara musu da juna, inda Husna take ganin Tauraruwa Rashmika tafi Dipika, Hajiya Kaka ta kallesu ta girgiza kai sannan ta miqe tawuce Dining domin cin abinci, dan kwata-kwata bata fahimci akan me suke musun ba.
*** *** ***
Sassafe tatashi daga baccin datake me mutuqar dad'i,kasancewar ta kwanta jikinta cike da gajiya hakan yasa baccin yayi mata mugun dadi sosai,daqyar tatashi ta zauna tayi wata irin miqa tana banqaro qirji,hakan yasa fararen nashanunta suka banqaro kamar zasu futo daga saman rigar jikinta, wadda kallo d'aya zaka yiwa doguwar rigar jikin nata ka tabbatar cewa rigar taji jiki, hamma tasaki wadda tayi sanadiyar lo6awar kumatun ta duka biyun (dimples), tajuya manyan idanuwanta wadda qwayar cikinsu ta kasance ruwan toka,ta kalli inda INNA TA RASULU datake kwance tana baccin ta cikin kwanciyar hankali,ta rafka wani irin tagumi hannu bibbiyu tana alhinin rayuwarta, Koda yaushe aikinta Kenan tashi sassafe tatafi wajan sana'ah,kuma Koda wasa Inna bata taimaka mata da aiki ko tsinke bazata dauke mata acikin ayyukan datake ba.

Tasaki ajiyar zuciya tana girgiza kanta cikin alhinin MATAR ABBAN NATA,yanda ta girgiza kan nata ne yayi sanadiyar kuncewar dogon gashinta harya sauko yazubo mata zuwa gadon bayanta, ahankali tasaka hannu ta tattare dogon gashin nata me mutuqar santsi, sannan tajuya ta nemi d'an kwalin rigar tata wanda yayi gefensa saboda dad'in bacci, ta daure kanta tafuto daga cikin gidan sauron datake ciki, kai tsaye bandaki ta shiga ta tsaftace jikinta kasancewar tana hutun sallah.

Tsakar gidan su ta futo wanda yake cikeda rairayin qasa ta zubawa dan qaramin tsakar gidan nasu ido tana kallo tana tunanin da wanne aiki zata fara?

Fara ce tas! cikakkiyar bafulatar qasar Mali, farar fuskar ta tana d'aukeda manyan idanuwa,qwayar idonta ruwan toka ne,tanada d'an qaramin baki siriri,ko kad'an batada qiba, Siririya ce kamar ka hureta tafad'i,abinda yakeda auki ajikinta shine hips,tanada bajajjan hips Allah yabata daidai gwargwado,yayinda nashanunta suka kasance madedeta kuma a tsaye car kamar zasu tsonewa mutum ido.

Allah yayi mata baiwar zaqin murya mai daukar hankali,muryarta tanada zaqi sosai musanman idan tana rera karatun Alqur'ani, abinda take mutuqar so arayuwa shine karatun Alqur'ani, ta qulla qawance dashi kullum tana karanta shi a fili ko a zuci,bata wasa da hadda akoda yaushe.
Chapter 1 · 0% Book details