← Book details Matar Abbana Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 24

Sashe 18

Matar Abbana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Adede lokacin wayar sa ta dauki qara,cikin sauri su Hafeeza suka juya suna kallon wajan, saide dayake ala6e yake, basu ganshi ba saide qarar wayar kawai.

Cikin taqaicin shigowar kiran Hafeez ya runtse idonsa,ya daidaita Kansa fuskar nan tasa ya daure ta kamar bashi ba,kawai yayi shahada yafuto daga dakin yana d'an danna waya.

Yana dan dago Kansa daga danna wayar dayake,idonsa ya fada cikin na Hafeeza,gabanta yayi wata irin faduwa sakamakon kayan data ga yana sanye dashi,kwata kwata wandon iyakar sa gwiwa,ga wannan Riga gaba daya dantsan sa awaje suke anyi masa zanen tattoo ajikin hannayen nasa,ga dan kunne amaqale a kunnansa na hagu, bata ta6a ganin namiji haka azahiri ba, hakan yasa cikin sauri ta sunkuyar da kanta qasa,gabanta banda faduwa babu abinda yake tana Addu'ah cikin ranta Allah yasa baiji abinda ta gama fadaba.

Complete document 1k
Amnah El Yaqoub
[6/14, 2:25 PM] El Yaqoub:
Koda wasa bai nuna wata magana tata6a had'ashi da'ita ba,d'auke Kansa yayi fuskar sa ahad'e kamar koda yaushe.

Hassana da Husna atare suka had'a baki wajan gaidashi tunma kafin ya zauna.

Furucin YAYA da Hafeeza taji 'yanbiyun sun fada hakan yasa tagane cewa kenan shid'in Yayan sune, tsananin mamaki yagama kamata,kuma har zuwa wannan lokacin gabanta banda faduwa babu abinda yake, kanta aqasa tana tuna abubuwan da suka faru tsakanin su ita dashi, yanzu fa kamar fanko yake ganinta tunda yariga yaga qirjinta,wani irin baqin cikin abinda ta aikata na bawa Fadila nono ya kamata,mema yakai ta ne? meyasa tayi hakan?

Kowa yana ganinta da daraja, amma ban dashi, shi din kallon da zai dinga yimata daban.

Tunanin tane ya tsinke,taji kamar wani abu ya fada cikin qirjinta sakamakon Zaman da Hafeez yayi dab da'ita,saide akwai 'yar tazara atsakanin Zaman nasu, amma duk da hakan, awajan Hafeeza kusancin yayi kusanci sakamakon bata sababa.

Kanta aqasa yake har lokacin,gade esi iya esi afalon amma fuskarta harta fara hada gumi,cikin rawar murya tadan kalli gefensa kadan sannan tace"Ina kwana''
Agajarce ya amsa da "Lafiya"
Yadan kalli gefenta yaga abinda yake nema Wato remote,hakan yasa yakai hannun sa ya dauki remote din sannan yafaki idon qannan nasa, yayi sauri Yadan sake matsawa kusa da Hafeeza,itade Hafeeza kanta yana qasa,gabanta sai faman faduwa yake,Sarai taga lokacin daya sake matsowa kusa da'ita.

Hafeez ya kalli Hassana yace"Ke kawo min Coffee"
Cikin sauri Hassana ta miqe tashige kitchen.

Ahankali Hafeeza ta dan dago kanta, adede lokacin Hafeez ya kalleta afakaice,idonsu yana haduwa tayi sauri tasake yin qasa da kanta.

Hajiya Kaka tashigo falon taga yanayin Zaman Hafeez da Hafeeza yayi d'an kusanci,mamaki ya kamata ganin yanda Hafeez din ba mai sakewa da mutane bane, musanman yanmata, amma gashi a zaune dab da yarinyar kuma ko a jikinsa.

Ta kalli Hafeeza taga kamar atakure take da Zaman, ta zauna tareda fadin" 'yar nan cire hijabin naki mana kisha is'ka"
Hafeeza tatuno maganar Maman Fadila da take cewa abinda yagani ne ya dawo yaqarasa gani, Wato ta cire hijabi yanzu ma yasake kallon qirjinta, ahankali ta danyi murmushi tace" a a babu damuwa Kaka"
Hajiya Kaka tace"tokici abinda qawayen naki suka kawo miki mana,ko adafa miki wani abincin?"
Cikin sauri Hafeeza ta Girgiza kanta, batare da tayi magana ba.

Hajiya Kaka tayi murmushi, gaba daya tagama karantar yarinyar a firgice take, ta kuma tabbatar saboda Zaman Hafeez Akusa da'ita ne, cikin son Jan magana tace" ni qosai Naso ci kuma sunje nemomin basu samu ba"
Hassana ta kawo wa Hafeez Coffee ta'ajiye agaban sa.

Ahankali yasaka hannu ya dauki coffee din sannan ya kalli Kaka cikin maganar sa me aji yace"Aina fada miki tadena,ba zatayi ba"
Gaban Hafeeza ya Yanke ya fadi ganin akanta ake maganar.

Hajiya Kaka tace" ko zatayi ma abaqin miskilancin ka ai zaka min baki taqiyi, kaide Matarka ta shiga ukunta da baqin miskilanci"
Hafeez yayi sipping Coffee din hannun sa sannan yajuyo yana satar kallon Hafeeza,duk da cewa ta kasance tana masa kwarjini yarinyar Gara yayi kokari ya kawar da hakan aransa kada yan maza suji kunya.

Wannan Karon ma sun sake hada ido shida ita,hakan yasa cikin ranta ta Yanke shawarar tafiya gida, kafin ta miqe Hassana tace" Hafeeza yaushe ne tafiyar ki Saudia?"
Cikin murmushi ta Kallesu tace"bazan wuce sati biyu ba"
Hafeez yajuyo Kansa tsaye ya kalleta, sannan ya ajiye Coffee din ya tashi yafice daga falon.

Yanajiyo Hajiya Kaka tana cewa "to nide Abayar da Zaki siya kiyiwa saurayin ki ado da'ita, Nima irin ta Zaki siyo min"
Hafeeza tayi murmushi ta miqe tsaye tace"Kaka duk abinda nasiyo kema naki daban zan siyo miki"
Hajiya Kaka tace" to Allah yayi muku albarka, Allah yabaku mazaje nagari"
Hafeeza tace"Amin Kaka,zan tafi gida kada anemeni"
Su Husna suka kwashe duk kayan snack din da suka kawo Mata da lemuka suka zuba Mata aleda, sannan suka rakota bakin get sunata tsokanar ta,daga bakin get din ta dakatar dasu saboda babu Nisa sosai tayi musu godia bayan sunsha Fama da'ita kafin ta karbi snack din da suka biyota dashi.

Zuciyarta daya ta futo daga gidan ta dauki hanyar gida tareda ajiyar zuciya tanajin wani irin dadi saboda cikin gidan atakure take kasancewar Hafeez yana wajan.

Ba tayi nisa sosai ba kawai taga mutum agaban ta,qiris ya rage su hadu da juna hakan yasa tayi saurin yin baya,hannunsa ya harde a faffadan qirjinsa ya zuba Mata narkakkun idanunsa, gabanta ne ya fadi ganin irin kallon dayake Mata,ahankali ta matsa zata wuce ta gefensa cikin sauri yasake shan gabanta, Hafeeza ta kalli ko'ina taga layi shiru babu mutane, gashi tana tsoro kada yayi mata wani abu,kuma dama Maman Fadila tafada mata cewa idan zatazo wajan sa kada tatafi ita kadai, to dawa zatazo bayan ita ba wasu qawaye ne da'ita ba?

Cikin dauriya ta dago kanta ta Kalle shi tace" kabani kudin Inna zan kai Mata"
Haka nan Hafeez ya tsinci Kansa dajin dadin yanda suke maganar su biyu,cikin wani irin nishadi yace"wanne kudi?"
Hafeeza ta lumshe idonta cike da damuwa sannan ta bude shi akansa,Hafeez yazubawa qwayar idonta kallo me kama data mage,cikin sauri dakuma qaguwa da tsaiwar ta awajan tace" Kabani"
Wani miskilin murmushi yasa ki,yanayin yanda tayi maganar cikin fishi sai hakan yasake birgeshi, duk da gabansa yana dan faduwa sakamakon rashin Sabo, hakan ya daure yajefo Mata tambaya, yace"Babyn wa kika kai asbiti rannan?"
Gabanta ya Yanke ya fadi,cikin taqaici ta runtse idonta sannan ta bude tace"Malam Kadena min wannan maganar,bana so!!"
Ta qarasa maganar cikin tsananin 6acin rai dakuma quluwa.

Hafeez yadan shafa sumar Kansa sannan ya kalli layin dasuke tsaye yace"gidannan akwai qaran Gen. , kina min bayanin Babyn dana ganku tare,sai naji kamar kince narabu dake"
Cikin 6acin rai Hafeeza tace"malam cewa nayi Kadena min wannan maganar, kabani kudina natafi "
Hafeez yace" waye zai baki kudi?"
Cikin sauri tace" waye zai bani idan bakai ba?

"
"an rad'awa kudin cewa nine kawai mai ba dashi? nabaki kudin ki mana, kiduba nabaki"
"yaushe kabani?"
Cewar Hafeeza.

Hafeez yasaki ajiyar zuciya yace"kiduba rigar ki yana ciki,kokuma nina duba"
Ran Hafeeza yasake 6aci ganin irin rainin hankalin da Hafeez din yazo Mata dashi,yaushe yabata kudi? yaushe yasaka mata kudi arigar ta?

Cikin 6acin rai tace"Malam bazan duba ba kawai kabani natafi"
Cikin dakiya dakuma aji yasake matsowa dab da'ita, gabanta yasake tsananta faduwa har tana iya juyo numfashinsa akan fuskarta,cikin wata irin muryar rad'a yace"tsaya na dauko miki"
Bai saurari amsar ta ba yakai hannun sa cikin aljihun doguwar rigar da take jikinta,Hafeeza tanajin haka ta zaro idonta,cikin hanzari tafara kiciniyar qwacewa, nan da nan kokawa ta 6arke a tsakanin su, shi yana kokarin dauko Mata kudin daya Riga yasan cewa yasaka Mata kudin a jikinta, ita kuma tana kokarin qwace kanta tana so taraba kanta dashi,cikin azama tayi kokarin ruqo hannun sa mai cike da gashi,tayi Sama da hannun nasa zata bige hannun,Shikuma Hafeez a maimakon dawo da hannun sa cikin aljihun rigarta by mistek hannun sa yadan bige boob's dinta, laushin da yaji ne yasa yakai idonsa kan hannun sa,adede lokacin itama takai idonta kan abinda ko a mafarki bata ta6a tunanin kafin tayi aure wani namiji zai iya kai hannunsa wajan ba, atare suka zaro idonsu, cikin sauri Hafeez ya janye hannunsa, wata irin kunya ta kamashi,yakasa hada ido da'ita,hakan yasa Kansa aqasa yace mata" I'm sorry,pls I'm sorry"
Cikin sauri yabar wajan yajuya zuwa gida,ko takan motarsa da take ajiye agefe baibi ba.

Cikin tsananin baqin ciki Hafeeza ta tsugunna awajan ta fashe da wani irin kuka.

Lokaci daya,maganar Maman Fadila ta fad'o Mata, cewa idan zatazo wajan sa karta kuskura tazo ita kadai, sosai take kuka kamar anyi mata mutuwa, saida ta gama shan kukan ta kafin tamiqe cikin baqin ciki tanufi gida,kana ganin yanayin tafiyar ta dakuma fuskarta zaka tabbatar da cewa ranta a6ace yake.

Tana zuwa gida kai tsaye tanufi daki ko kallon Inna da take zaune cikin rumfa ba tayi ba.

Ta Rasulu ta kalleta tace"kin kar6o kudin ne?"
Ataqaice Hafeeza tace"A a"
Ajiyar zuciya Ta Rasulu tayi, sannan tace"dama bakida niyya"
Hafeeza tayi shiru batace uffan ba.

Ta Rasulu tasake kallon ta tace"kin zauna kinyi shiru sai zun6urawa mutane baki kike, kinyi waya da saurayin naki yau kuwa?"
Yanzunma a taqaice Hafeeza tace"A a"
Inna ta jinjina kanta tace"zan baki shawara Hafeeza,wannan saurayin naki dakika dora ranki akansa batake yakeba, duk lokacin da kikaje Saudia kawai kiyi Addu'ah Allah yabaki wani"(
Cikin sauri Hafeeza ta kalleta,ta rasa me Gaddafi yayi mata bata sonsa,bawani saurayi da zata roqa face tayi Addu'ah Allah ya tabbatar Mata da Alkhairi ita da Gaddafi.

Tana gama yanke wannan tunanin ta tashi tashige cikin daki tafara qoqarin cire kayanta domin shiga wanka, tana cire rigar jikinta taga wata takarda ta fad'o daga aljihun rigarta,cikin tsananin mamaki ta tsugunna ta dauka, tana budewa taga dala dari, gabanta yayi mugun faduwa, idan bata manta ba kwana ki anta6a fada musu cewa duk dala d'aya ta haura dubu da dari biyar, wannan mutumin Kansa daya kuwa?

Meyake damunsa? mezatai da wannan kudin?
Chapter 18 · 0% Book details