← Book details Matar Abbana Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 24

Sashe 2

Matar Abbana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wanke-wanke tafara yi, sannan tayi sauri ta share gidan nasu tas,ta dauki niqan wake tafice tabar gidan,kai tsaye gidan da'ake musu niqa tawuce,matar ta niqa mata waken sannan tadawo gida tasake shiryawa ta dauki abinda zata dauka tayi shirin ficewa qofar gida inda suke sana'ar soya qosai, har zuwa wannan lokacin Inna tana bacci bata tashi ba.

Idan akwai mutanan da ake kira expert to wannan yarinyar tana cikinsu,domin kuwa yanda take soya qosan kadai zai tabbatar Maka da cewa 'yar na gada ce ba 'yar na koya ba,kan kace me, samari da yara da masu abun hawa suka yanyameta suna siya, saide dayawa daga cikin samarin ba qosan ne yakawo su ba,yarinyar datake qosan ce takawo su wajan.(
Cikin qanqanin lokaci tagama saida wa ta kashe wutar ta tattaro kayanta tayi gida,tana zuwa gida taga Inna a zaune cikin 'yar qaramar rumfar dake tsakar gidan nasu, kai tsaye wajanda suke wanke-wanke ta wuce ta wanke kwanukan data dawo dasu,tasake diban ruwa mai yawa taje ta zubawa shukar na'a na'arta, kasancewar kullum cikin karatun Alqur'ani take hakan yasa ta nemi na'a na'a ta shuka,kullum zata siyo shayi ruwan bunu tasaka aciki tasha,kokuma ta dafa shayin da Na'a-Na'ar,duk lokacin datasha tana ganin amfanin ta sosai wajan daidaita mata fitar da makarujul huruf.

Saida tagama jiqe na'a na'ar da ruwa sannan ta qarasa wajanda Inna take tace" Inna ga kud'in"
Wadda aka kira da Inna tasa hannu ta kar6i kudin ta qirga ko sannu batayi mataba.

Daga nata 6angaren itama bokiti ta dauka ta wuce ta debo ruwa tanaso tasake watsa ruwa kasancewar tanajin zafi,uwa uba kuma dama daga gaban wuta take,jikinta banda gumi babu abinda yake.

Inna ta kalleta tana daga cikin rumfa sannan tace "HAFEEZA zoki dauki wayata ki kamomin lambar Mariya ki kiramin ita"
Abinda take tabari, tazo ta dauki wayar tata,takira taji ba Kati, ta kalleta cikin zazzaqar muryar ta tace"Inna bakida kati yaqare"
"Flashing zaki mata" cewar Inna.

Sake gwada kiran tayi akaro na biyu sannan tace"bazai fita ba, nima kuma wayata ba Kati dana kira miki ita"
"saurayin naki be saka miki Kati ba?"
Cikin sanyin hali Hafeeza tace"besan banida kati ba Inna"
Wadda aka kira da Inna ta numfasa tareda girgiza kanta sannan tace"oh ni Aminatu,narasa wacce irin sokuwar yarinya ce ke Hafeeza,kwata-kwata baki iya dabarar kar6ar kud'in samari ba,irin haka ai saiki masa flashing idan yakiraki sai kice karkaji shiru yau ban kiraka ba banida kati ne shiyasa"(
Kafin Hafeeza tayi magana Mariya tashigo gidan, mace me kimanin shekaru arba'in da wani abu,ganin mariya ta shigo gidan hakan yasa Hafeeza tayi hamdala aranta tayi wuf tashige bandaki domin watsa ruwa.

Tana shiga cikin bandakin nasu ta zare kayan jikinta gaba daya, lokaci d'aya farar fatar jikinta ta bayyana,cikin nutsuwa tafara wankan ta harta gama wanke jikinta gaba d'aya,tazo wanke fuskarta tasaka sabulu a fuskar tana wanke wa kamar wasa taji qaran abu asama, cikin sauri tafara qoqarin wanke idonta da farin ruwa,saide kafin tagama wanke fuskar wata uwar gafiya tafad'o jikin Hafeeza kasancewar langa langan da'aka rufe saman bandakin dashi duka yamutu, rana ta riga ta kashe shi, hakan yasa gafiyar tasamu damar fadowa jikinta, Hafeeza tana had'a ido da wannan gafiya tasaki wani uban ihu tana Salati, aguje ta fizgi zanin wankan ta tafuto daga bandakin fuskarta duk kumfa, yayinda rabin nonuwan ta suke awaje kasancewar daurin zanin bana nutsuwa bane.

A tsakar gida tayi turus tana maida numfashi, yayinda fatar jikinta inda gafiyar ta fad'o wajan ya qwarzane yafara jini kad'an saboda 'yan yatsun gafiyar ya karceta awajan.

Mariya ta kalleta tace"Hafeeza lafiya kike ihu ke kadai?"
Hafeeza bata iya bata amsa ba,sai numfashi datake maidawa jikinta banda rawar tsoro babu abinda yake.

Inna Aminatu ta kalleta taga yanda tabar nonuwan nata awaje, kuma ana tambayarta tayi shiru,baqin ciki ya kamata, tasaki ajiyar zuciya tace"wannan Nono de angama nunawa duniya,saura za'a kai gidan miji"
Hafeeza tanajin wannan furucin ta runtse idonta, tadawo cikin hayyacinta tasaka hannu ta gyara daurin zaninta,tasan cewa dede gwargwado tana yiwa Inna biyaiya,batasan meyake damunta ba tsufa ne kokuma haka nan take mata wasu abubuwan?tarasa meyasa wani lokacin furucin arziqi baya futowa daga bakin innar tata kuma MATAR ABBANTA.
(Fan's ya kwana biyu zance ko shekara da watanni
littafin kudine, Complete document 1k
8621296018
Amina Muhammad
Fcmb
Amnah El Yaqoub
[5/21, 12:38 PM] El Yaqoub:
MATAR ABBANA
(Luv Story)
Writing By Amnah El Yaqoub
Kuyi following WhatsApp Channel dina domin samun sababbin update
https://whatsapp.com/channel/0029VbBR7naJ93wTuOypQV45
Mariya tayi murmushi tana duban Inna sannan tace"haba Ta Rasulu, wanne irin saura kuma? gani aiba ta6awa bane"(
Bata saurari amsar Inna ba tajuya ta kalli Hafeeza sannan tace"Hafeeza meyafaru haka?"
Saida tagama maida numfashi sannan tace"Inna Mariya Gafiya ce tafad'o jikina ina wanka"
Mariya tace"Subhanallah, Allah Yakiyaye gaba,qarasa Randa ki wanke fuskarki ki kawomin ruwa abuta"
Kanta da gyada babu musu ta wuce ta Debi ruwa abuta ta wanke kyakykywar fuskarta kasancewar dama tagama wankan,sannan ta debowa Inna Mariya wani ruwan takawo mata.

Inna Mariya ta kar6a tace"nagode,Allah yabaki miji nagari, mijin kirki muje gidanki musha kunun tsamiya"
Ta Rasulu kalli Mariya tace"kunun tsamiya kuma ina kanta? kiyi mata fatan wani kunun de"
Inna Mariya tayi murmushi taqarasa alwala tatada kabbarar sallar Walaha, kasancewar tsohon ciki gareta hakan yasa da qyar take iya yin sallar,bayan ta idar Ta Rasulu takalleta tace"Mariya Kirage wannan haihuwar wallahi,inba hakaba mahaifarki fashewa zatayi"
Inna Mariya ta cire Mayafin jikinta tana firfita dashi sannan tace"shikkenan ma idan ta fashe nahuta,Innar Hafeeza bazaki gane Jarabar Baban Mas'uda ba,bashida aiki sai Jaraba kullum ana abu d'aya, har so nake yaqara aure nima inhuta Amarya kuma saitaci gaba da haifa"
Ta Rasulu ta jinjina kanta sannan tasaki numfashi tace"gani yayi kina haifar su lafiya-lafiya shiyasa baya d'aga miki qafa,kekuma dakika fishi Jaraba Mariya kin kai shekara Arba'in da biyar amma kullum idan ya debo jiki yazo saiki bud'e masa qafa"(
Mariya tayi murmushi tana d'an leqen cikin daki inda Hafeeza take tana fatan ace Allah yasa de yarinyar bata fahimci akan me suke magana ba.(
Ta Rasulu kuwa ko akanta, saboda tariga tasan halin Hafeeza bazata kasa kunne tanajin zancen su ba, ta kalli Mariya tace"Haka wasu mata suke fama anan layin mu,duk shekara saisun haihu itada kishiyar ta, mijin baya daga musu qafa saboda tsabar tsohuwar jaraba,acikin su biyun d'aya mata take haifa duk shekara, d'ayar kuma maza take haifa, kusan kullum sai sunyi fada suna yiwa juna gori, ita me haifar mata so take ta haifi namiji Koda sau daya ne,itama me haifar maza so take ta haifi yar budurwa, ita me haifar mazan tsabar yanda takeso ta haifi mace tana haihuwa tun kafin mabiyya ta futo take leqawa tace mena haifa?

Amma kullum amsar itace namiji ne ba mace ba"
Mariya tasaki wata irin ajiyar zuciya tace"tabdi kaji jaruma,ni ai bana tambaya kuma bana dubawa kodan mix nake maza da mata? wahala ma bata bari na induba"
Ta Rasulu ta d'aga murya tace"Hafeeza futo kici abinci,banason mutum ya zauna da yunwa"
Hafeeza datake zaune adaki idonta a lumshe tana tulawar karatun Alqur'ani ko zuciyar ta zatayi sanyi akan furucin Inna na cewa tagama nunawa duniya nononta, saura zata kai gidan miji,maganar har yanzu taqi barin zuciyar ta, hakan yasa ta nutsu take tulawar karatun Alqur'ani har saida takai ayar datake karantawa sannan tace"Bazanci ba Azumi nake"(
Cikin d'aga murya Ta Rasulu tace"kina al'ada ni zaki cewa azumi kike? kar Allah yasa kici, ni har a fadamin azumi? acikin tsakiyar azumi aka haifi mahaifina,Asalin Sunana shine Aminatu d'an Azumi,kara ce tasa ake kirana Aminatu Mamman"
Mariya tace"Ta Rasulu ai kina qoqari ma,tunda kishiyarki ta mutu tabar miki Hafeeza kike fama,Shima mijin naku rai yazo yayi halinsa, inda take birgeni de yanda ta dage take muku sana'ah, gashi kamar tana fita da sunan Allah tana fara suyar qosai sai kiga ansiye kodan mahaddaciyar Al-Qur'ani ce inajin akwai karatun datake na kiran kasuwa kafin tafice daga gida"(
Inna tace"yo in bamuyi sana'ah ba me zamuci Mariya? sana'ah ai tazame mana dole"
*** *** ***
Hajiya Kaka tayi shiru ta zubawa abincin dake gabanta ido ta gagaraci,ko kad'an hankalinta baya jikinta,tariga tayi nisa wajan tunani,idan bata manta ba yau Babban jikanta mafi soyuwa acikin zuciyar ta yacika shekaru ashirin da takwas,babu abinda ya rasa na rayuwa, amma koda wasa babu tunanin aure agabansa,abun yana mutuqar damunta musanman idan tatuno shekarun baya kafin yazama cikakken saurayi yanda yake fama da matsala ta tsananin sha'awa.

Husna ta kalleta tace"Kaka bakici abinci ba"
Cikin damuwa Hajiya Kaka tasaki ajiyar zuciya,fuskarta cikeda tsantsar damuwa tace"qyaleni Husna bata abinci nake ba, ta rashin auren yayanku nake"
Hassana dake zaune agefe ta kalleta tace"Kaka da kinyi haquri da batun auren nan, shi Yaya miskiline, ko yanmatan layin nan baya kulawa, bare su sasanta da wata ayi maganar aure"
Kaka ta kalli Hassana tace"ke rabu dashi da Allah, miskilancin banza, to ai irinsu sune 'yan'iskan"(
Husna dake kusa da Kaka tasaki murmushi.

Hajiya Kaka tabawa Hassana wayarta tace"ungo kiramin shi awaya"
Hassana taduba number Yayansu ta doka masa kira, saida ya dauka sannan tabawa Kaka wayar.

Hajiya Kaka ta kara waya a kunnanta tace"Hafeezu ya aiki?"
Cikin damuwa ya runtse idonsa,bayason wannan Hafeezun datake fada,gaba daya lalata masa suna take,saida ya saita kansa kafin Ataqaice yace"Alhamdulillah"
Hajiya Kaka tace"Hafeezu ita Rayuwa dakake gani,bahaka ake tafiyar da'ita ba,tsakani da Allah shekara da shekaru Hafeezu kana zaune babu aure,ka girma harka riqa kana zaune a tuzuru,shine nace Hassana ta kiramin kai nace konaje nayi magana ne a had'a ka da yarinyar nan Hafsa 'yar wajan Alhaji Qani nakan layin mu?"
Ajiya zuciya yasaki daga cikin wayar,tsawon lokaci ya dauka batare dayayi magana ba harta cire rai zaiyi magana sannan yabude baki cikin tsantsar aji da tsananin miskilanci yafara magana a rarrabe kamar bayaso "Koda yaushe Kaka...,bakida aiki sai zancen had'a aure....,kina daga zaune,kin zama me dalilin aure" (
Cikin sauri Hajiya Kaka tace"yaushe nata6a had'a aure Hafeezu? yaushe akai haka? banta6a jiba"
Tana fada masa haka ta dauke wayar daga kan kunnanta ta miqawa Hassana tace"ungo kashemin wayata"
Hassana ta kalli wayar sannan ta kalli Hajiya Kaka tace"Kaka yana magana fa"
Cikin 6acin rai Hajiya Kaka tace"Kashemin waya nace!!"
Babu yanda ta'iya dan dole ta kashe wayar.
Chapter 2 · 0% Book details