← Book details Matar Abbana Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 24

Sashe 22

Matar Abbana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan kawu Hamza yatafi Ta Rasulu tabi bayan Hafeeza ta ganta a zaune agefen d'an qaramin gadon su tayi shiru, zama tayi Akusa da'ita sannan tace"yanzu Hafeeza 'yar Habujar damuke kwadayin zuwa Zaki mana manaqisa?,banda abun ki abinda Hamza yakeyi akanki aiko wadda ya Haifa acikinsa sai haka, Hamza ko wuta yace ki shiga Hafeeza banajin kinada za6i, bare ma shi wannan sanata kina gani de qoqarin da yayi miki, kika bibiya ma wannan miliyan biyar din da'aka rasa wanda yabaki nasan shine zai bayar saboda Kar talakawa Irina mu dinga tsine masa muna cewa kudin mu ne shiyasa ya6oye sunansa, kiyi haquri mana Hafeeza"
Hafeeza tace" to ni Inna menace? wallahi na amince dashi har raina"
Cikin farinciki Ta Rasulu tace"yauwa, Allah yayi miki albarka"
*** *** ***
washegari da yamma Ta Rasulu tana zaune daga falo tana ganin yanda Hafeeza take aiki kamar bataso, ta daga murya tace"Hafeeza kiyi da jikinki mana Kar yazo baki gama girkin ba, Babban Mutum irin wannan yaushe zaizo ki barshi yana jira, nida kinji tawa ma dafadukan taliya zakiyi masa kisa masa dan kifi aciki, amma kin tsiri dafa masa Shinkafa"
Hafeeza ta kalli Inna tace"to Inna yanzu ai Shinkafar tafi tsada, muma ita mukeci, shima idan yazo saiyaci"
Inna tace"ai shikkenan"
sosai Hafeeza ta nutsu tadafawa baqon nata Shinkafa da miyar qwai, sai lemuka data siyo masa dakuma ruwan gora.
saide baisamu damar zuwa ba sai bayan magrib, baqar Abaya ta saka me kyau irin wanda ta siyo a Saudia,sosai rigar tayi mata kyau, sai zuba qamshi take kamar amarya, ta juya zata tafi Ta Rasulu ta tsayar da'ita tasake fesheta da turaruka,sannan tatafi.
tana futowa qofar gida taga wata hamshaqiyar Mota aqofar gidan,daga jikin motar ta tsaya tareda qwanqwasawa, shima daga cikin yabude Mata tareda fadin"qaraso mana"
mamaki ya kama Hafeeza, tayi tunanin zai futo ne su qarasa cikin gidan, duk da haka batayi qasa a gwiwa ba, tashiga cikin motar, tana shiga ya rufe motar tareda kallon ta cikin murmushi yace"kinsan ba kowane yasan nazo garin ba, ina buqatar privacy"
Hafeeza ta Kalleshi, Babban Mutum ne sosai,shi kadai ma yacika kujerar dayake zaune,cikinsa kuwa qwarya guda kamar me shirin haihuwa, kanta aqasa batare data Kalle shi ba tace"ina wuni?"
Cikin wani irin Jin dadi sanata yagama qarewa jikinta kallo sannan yakai hannunsa ya ruqo ha6arta yace"dago ki Kalle ni mana Baby"
Wata irin faduwa gabanta yayi, ganin yanda ya Kamo ha6ar tata batare da wata damuwa ba, ahankali takawar da fuskar ta gefe, hakan yasa hannun nasa ya zame daga kan ha6ar tata, saide maimakon ya janye hannunsa saiya saukeshi kai tsaye akan nashanunta, cikin sauri ta Kalleshi, jikinta yafara rawa, shi kuwa hankalinsa kwance yake kallonta saima murmushi dayake zubawa yanajin dadin yanda yaga ta tsorata saboda yanda yad'ora hannun nasa akan nashanunta hakan ne yasake tabbatar masa da cewa shine zai koya Mata harkar,da alama bata ta6a aikata hakan da wani ba.

Cikin 6acin rai Hafeeza ta Dora hannunta akan nasa tafara qoqarin janye masa hannunsa akan nonuwanta, murmushi ya saki maimakon ya dauke hannun nasa saida ya matsa Mata da qarfi, sannan ya saki.
baqin ciki ne yasata fashewa da kuka.

Cikin tashin hankali ya gyara zamansa,sannan ya sassauta murya yace"Haba Baby, menene abun kuka kuma? to kiyi haquri kiyi shiru kinji Baby na, hakan bazata sake faruwa ba kinji?"
ahankali ta gyada kanta alamun amsawa, saide gaba daya jikinta rawa yake, ta sare da al'amarin sa.
ganin ta daina kukan hakan yasa yace"to goge hawayen ko?"
ahankali tasa gefen mayafin Abayar jikinta ta goge hawayen, sannan ta Kalleshi tace"nayi tunanin zaka shiga gida ne, meyasa kakeso ka koya min abinda kai kanka kasani Allah subhanahu...."
Cikin sauri ya dakatar da'ita yace"Dakata Hafeeza, ya kike wani abu kamar baki wayeba? duk Yara sa'anninki yanzu sun San haka rayuwar takoma, menene aciki? bafa komai bane dan romance ne kawai,ki kwantar da hankalin ki, Zaki samu kudi sosai, ki saki jiki musha soyaiya kafin a daura auren, ni mutum ne Maison soyaiya a aikace, banason nuqu-nuqu naku irinna malamai, saboda haka karki fara yimin wa'azi, yawwa ki saki jiki ki kwashi kudi iya rabonki, inaso ana daure aure mubar qasar muje qasar waje nasake bude miki ido akan harkar kingane?"
Hafeeza da jikinta yake rawa cikin sauri ta gyada kanta, jitake kamar ta zura da gudu zuwa gida, Babban Mutum da yayi jika da'ita shine yake fada Mata haka.
ganin ta amince da maganar tasa hakan yasa yace" yaushe zakuyi musabuqa ta jiha? ko bakyason musabuqa?"
muryar tace tafara rawa,ahankali tace"ba'a fara maganar musabuqa ba, idan anfara idan na cancanta makaranta zata dauka dani"
Cikin sauri yace"wanne irin cancanta kuma? tunda kina dani ai kin gama cancanta Baby, zakiyi musabuqa kuma zakici saboda zan tsaya miki,bayan ta jiha ma harta qasa saikin je, kinji?"
Cikin nutsuwarta ta gyada masa kai, sannan ta Kalleshi tace" nagode, ni zan shiga gida"
Hannunsa yasaka a aljihunsa ya dauko damin kudi Yan dubu daya, kimanin dubu dari, sannan ya miqa Mata yace"Gashi Kisha Chocolate ko?"
Cikin sauri Hafeeza tafara Girgiza kanta, gefe daya kuma tana qoqarin bude Motar.

Cikin sauri yace" ki kar6a mana, yanzun nan fa nagama cewa ki saki jikinki kisamu kudi,inaso na maidake babbar yarinya,very soon zan siya miki Mota, Zaki kai iyayen ki dukansu makkah keda kanki, sannan duk lokacin dakike buqatar kudi kawai kimin magana kinji?"
Hannu biyu tasa ta kar6i kudin sannan tace" nagode, Allah yaqara budi"
Cikin Jin dadi yace"Amin ya Allah Baby,dadi na da malamai akwai Addu'ah"
Dan murmushin yaqe tayi sannan ta bude motar, cikin Jin dadi ya kalleta yace"kinga"
ahankali ta juyo, aikuwa ya huro Mata kiss, sannan yace"idan kinje gida kidan turomin photon wannan abun dakikai min rowa kika hanani matsawa dakyau"
gabanta ne yasake faduwa,wanne irin mutum Allah ya hadata dashi? cikin sauri ta gyada masa kai, sannan tafi ce tareda rufo masa motar.
tana shiga gida Ta Rasulu data kafa ta tsare a tsakar gida ta kalleta tace"ke yana ganki kamar bakya cikin hayyaci?

Ina baqon naki yake?"
Kudin hannunta ta bata sannan tace" yatafi Inna, kuma gaskiya ni bazan aureshi ba, bazan iyaba,wallahi dan'iska ne, kwarto ne"
Ta Rasulu ta kamota ganin kamar bata cikin hayyacinta,tace" Hafeeza Kalleni nan, meya miki? yayi miki wani abu ne?"
Hafeeza ta dafe kanta da hannunta ta rasa me zata fadawa Inna,to me zata ce? cemata zatai yata6a Mata nono ya huro Mata kiss sannan yace taturo masa photon nono?, cikin tashin hankali ta Girgiza kanta sannan tace"nide dabi'unsa basu min ba,bana son sa kawai"
tana fadar haka ta wuce daki, ta Rasulu ta kalli dubu Darin datake hannunta sannan ta daga murya tace"shashancin banza, to tunda ba jikinki ya ta6a ba, menene zaisa kiqi aurensa? aikuwa aure dole"
Hafeeza de tana jiyota daga daki,kanta har wani sarawa yake saboda damuwa, bata taba ganin tashin hankali irin wannan ba, iskanci qiri-qiri azahiri?,da farko tayi tunanin zai dauki nasiha da wa'azi shiyasa tafara qoqarin tunatar dashi, ashe yariga yayi nisa, hannunta ta kai kan breast dinta taji yanayi Mata wani irin ciwo sakamakon matsawar da akamai yanzu bata hankali bace, tashi Tayi tagabatar da sallah ta kwanta sakamakon wani zazza6i daya rufeta.
washegari bayan tayi sallar asuba bacci takoma, sosai take bacci sama-sama taji Inna tana kiran ta, ahankali tatashi zaune, Ta Rasulu tace"kizo Hamza yana jiranki, kin kwanta kina faman bacci har qarfe Tara tayi"
ahankali Hafeeza tatashi,tana futowa tsakar gida ta tsugunna ta gaida shi ya amsa, sannan tatashi ta Debi ruwa tashiga bayan gida,tafuto daga ciki bayan ta wanke bakinta, ta zauna agabansa tace"gani kawu"
Kawu Hamza yace"Hafeeza, jiya Alhaji Isah yazo,munyi magana dashi yacemin kun gama daidaitawa,yanzu kuma na shigo sai Ta Rasulu take min wata magana cewa kince ke bakya sonsa, bayan kuma jiya ba haka mukai dake ba,menene yake faruwa?"
Hafeeza tayi shiru ta rasa abun cewa,tariga tasan cewa haqqin uba ne akan ya nemawa yayansa uwa ta gari, haka itama yanzu haqqin tane ta nemawa yaran ta uba nagari, kuma abinda yafaru tsakanin ta da wannan bawan Allah bai kamata ta sanar dasu ba, saboda duk wanda ka rufawa asiri kaima Allah zai rufama, wannan bawan Allah bai dace daya zama uban 'ya'yanta ba, domin kuwa duk abinda ya aikata da'ita dole sai anyiwa yayansa,ba wannan bama, kafin ita tasan adadin yaran mutane nawa yagama lalatawa? inda ace bashida wannan halin haqiqa zata yiwa kawu biyaiya ta aureshi, to amma wannan dabi'ar tasa bata sababa, bazata iyaba.

Kawu Hamza ya katse Mata tunani yace"kinyi shiru Hafeeza,meyake faruwa ne?"
Ta Rasulu tace" ta fadi dalili kam muji, nan ta shigo min gida kamar mahaukaciya tana cewa ita bata sonsa, to ai kinji yanda akai da iyayen Gaddafi, ba aure zaiyi yanzu ba saboda bashida ko sisi saide qarya kawai, Shikuma wannan ai ba zamu hanashi ba kuma musaki agaba mu dinga kallonki bayan ba wani ne dake ba, Habuja de kike mana manaqisa ko? to kije kin kyauta"
Kawu Hamza yace"Ta Rasulu ya'isa, kibarta tafadi dalilinta na cewa tafasa"
Hafeeza tasake sunkuyar da kanta qasa sannan cikin nutsuwa tace"kawu munyi magana dashi sosai, shide ya fahimce ni, amma maganar gaskiya kawu nide ban fahimce shi ba, dabi'unsa basuyi daidai da nawaba"
"nide gaskiya dabi'unsa basuyi daidai da nawaba, yen yen yen kaji ta sai kace yar gidan shugaban qasa, nan kuwa ubanki Haladu ko dangi bai hada da Kansila ba" (
cewar Ta Rasulu.

Kawu Hamza yace"ya'isa mana Ta Rasulu"
Ta Rasulu tace"nayi shiru Hamza,Abun ne yake qonamin rai wallahi,ga arziqi yana kiran ta amma tana neman liqewa Gaddafi, kuma bazata watsa mana qasa a'idoba, dole ta aureshi"
Hafeeza tana Jin furucin Inna ta fashe da kuka tace"Allah kawu nide bana sonsa,kabani koma waye nayarda"
Ta Rasulu tafara tafa hannaye cikin mamaki.
Chapter 22 · 0% Book details