← Book details Matar Abbana Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 24

Sashe 19

Matar Abbana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Idan Inna tasani aita shiga ukunta, yaushe ma yasaka Mata kudin? tunani tatafi, ta tuna yanda yasake matsowa jikinta afalon gidan su, babu makawa a wannan Zaman yasaka Mata, shiyasa bayan tafuto yace yariga ya bata taduba jikinta, lokaci daya hannun ta ya dauki rawa, ta tashi ta saka dalar acikin kayanta, sannan tashige wanka.
*** *** ***
Acikin satin Hafeeza tatafi Saudia, gida ya rage daga Inna sai masu dan leqo mata suna dan tayata fira, sai kuma Maman Fadila tadake yawan shigowa tana kawo Mata Fadila duk da suna fafatawa kafin Inna ta kar6eta.

Duk wani motsin Hafeeza dayake Saudia Hafeez yana sani, satinta daya da tafiya da daddare yana kwance adakinsa bayan yagama shirin bacci yadokawa Ma'aruf waya.

Daga can 6angaren Ma'aruf ya kalli wayar sa cikin tsananin mamaki ganin shabiyu saura, cikin sauri ya dauki wayar, Yace"Hafeez lafiya kake kuwa?"
Murmushi Hafeez yayi yace" lafiya ta kalau Ma'aruf ,inaso muyi sallama ne gobe zan tafi Saudia"
"zakaje Umarah ne?"
Cikin aji yace"zanje Umarah da neman iri,akwai yarinyar da take hargitsa min lissafi Ma'aruf,inajin abubuwa dayawa akanta"
Ma'aruf dayake kwance agadonsa ya tashi zaune tareda dora fillo akan cinyarsa cikin tsananin murna yace"wow,wacce me sa'ar ce wannan?"
Hafeez yasake juyi akan gadonsa cikin jin dadi,wannan firar dasuke ta Hafeeza tafi masa komai dadi, cikin wani irin Nishadi yace" ina yawan Jin faduwar gaba duk lokacin dana tun kare ta, tanada kwarjini sosai,ina yawan Jin feeling akanta, Ma'aruf rana daidai ne banayin mafarki da'ita wallahi"(
Ma'aruf ya kwashe da wata irin dariya yace"Abokina kakamu wallahi, please kayi Mata magana mana,meyasa zaka tafi Saudia? ka tsaya ku fuskanci juna tukunna,but Wai Kaka ma tasani kuwa?"
Hafeez yayi ajiyar zuciya yace" idan Kaka tasani ai tun kafin na fadawa yarinyar zataje ta nema min auren ta,gaskiya bata sani ba, inaso ne nafara tunkarar yarinyar dakaina, naga ita din ustaziya ce, kullum tana cikin hijabi, yanzu taje Saudia,inaso nasameta acan muyi magana,daga nan zanyi Addu'ah saina dawo."
Ma'aruf yasa ki ajiyar zuciya yace"harna matsu ayi abunnan wallahi Hafeez,kuma kayi sa'ah mutumina, kasan ustazan yaran nan komai kaine zaka koya musu,babu damuwa saika dawo,Allah yasa muji alkhairi,amma ka kawar da wannan kwarjinin dakace tana ma kuyi magana"
Hafeez yace"ok"
Daga nan sukai sallama fuskar Ma'aruf cike da farinciki.

Bayan kwana hudu acan Saudia Hafeeza tabar harami tana zaune awani wajan shan shayi tana jiran akawo mata,sanye take cikin baqar abaya me adon stone baqi da kuma fari,saide baqin stone din yafi farin yawa, tasake yin fari tayi Shar abun ta bazaka taba cewa bahaushiya ceba musanman yanda tayi rolling da mayafin abayar akanta, daga Saman goshinta kana iya hango yanda gashinta ya kwanta luf.

Waya ce a hannun ta babba tana dannawa hankalin ta kacokam yana kan wayar, tana so tasan abubuwan dayake kan wayar kasancewar ba iya wayar tayi ba, har yanzu tana so tasan waye yake aiko Mata abubuwa na more rayuwa tunda tazo qasar, hakan yasa tayi wa Kawunta Hamza magana ganin yanda data bar harami idan takoma masauqin ta zata ga an ajiye Mata abubuwa naci da Sha masu kyau, kuma kawun nata ya tabbatar Mata cewa dan majalissa ne, Wato wanda yabiyamata kujerar zuwa Saudia, bata kawo komai aranta ba, hankalin ta kwance take ibadarta, tana yiwa kanta Addu'ah da qasa da kuma Sauran musulmi, saide rabi Addu'ar tata tafi yawa ne ga iyayen ta dasukabar duniya.

Wannan hutu da sauyin Cima data samu shine yasa tasake yin wani fresh,tayi fari sosai hatta nashanunta sun sake cika sosai.

Wani irin daddan qamshin daya daki hancin ta, shine yasa ta dago kanta da sauri, dede lokacin shima ya zauna hakan yasa idonta ya fada cikin na Hafeez, yayi masifar kyau cikin qananun Kaya,farar rika sai kuma baqin wando, yasaka glass Jan duhu wanda yasake qawata fuskar sa.

Cikin sauri ta janye idonta daga Kansa,duk da gabanta yana faduwa haka ta maze taci gaba da danna wayarta.

Adede lokacin aka kawo Mata shayin, wanda yakawo Mata yayi magana da larabci taba shi amsa, sannan yajuya, hakan ba qaramin dadi yayiwa Hafeez ba, sosai ta birgeshi.

Cikin dakewa yadan motsa lips dinsa sannan yace Mata "Sunana HAFEEZ"
Ataqaice tace"HAFEEZA"
Murmushi yasa ki yace"nasani"
Kallonsa tayi ta dauke kanta, sannan ta dauki cup din shayin tafara Sha, Adede lokacin shima aka ajiye masa wani, ya dauka yafara Sha idonsa akanta, sosai yake kallon dan mitsitsin bakinta yanda take shan shayin kamar yakai bakinsa ya lashe lips din nata.

Hafeeza tafara tsarguwa da kallon dayake Mata, ahankali itama ta dago kanta ta Kalleshi ko zai janye idonsa daga kanta,tana kallon sa idonta ya sauka akan faffadan qirjinsa har tana hango gashi a kwance akan qirjin nasa kasancewar bai gama rufe botir din gaban rigar ba, saide kuma abun mamaki data kalleshin ma ko alamun janye idonsa baiyi ba, sai ma wani murmushi dayake binta dashi wanda yasake qawata kyakykywar fuskar sa.

Adede lokacin Kira yashigo wayar sa, kasancewar wayar tasa a ajiye take agaban su akan table din dake gabansu hakan yasa Hafeeza taga sunan MAMA 6aro-6aro akan fuskar wayar, wata irin ajiyar zuciya ta saki tana hamdala aranta, ko banza dole ya dauki wayar, hakan zaisa ya dauke idonsa daga kanta.

Amma abun mamaki saitaga kallo daya yayiwa wayar yanayin fuskar sa ya sauya, kuma be dauki wayar ba harta gama ringing,kiran yana yankewa wani yasake shigowa saide wannan Karon cikin sauri ya kashe wayar gaba daya.

Kan Hafeeza ya daure, Mama tagani a fuskar wayar, meyasa hakan? mahaifiyar sa na Kira meyasa bazai daukaba?

Maganar sa ce ta dawo da'ita daga tunanin data Lula,duk da shima daga nasa 6angaren gabansa faduwa yake haka ya daure ya dauki tissue ya goge kyakykywan sajen daya sake qawata fuskar sa, sannan ya fuskanceta cikin wata irin murya mai aji yace"nasha wahala awasu shekaru can baya arayuwata,hakan yanada nasaba da quncin danake ciki a koda yaushe har zuwa yanzu, tunda nahadu dake nakejin sauyi acikin zuciyata,inajin nishadi dakuma walwala aduk lokacin dana ke6e dake azahiri dakuma cikin mafarkina,inason inci gaba jin wannan farincikin,but nasan cewa hakan bazai samu ba dole saikin zama tawa,kafin nasamu hakan dole saikin fara bani dama nashiga cikin jerin manema auren ki..."
Hafeeza ta zuba masa ido tanajin yanda yake zuba Mata zance, bazaka taba tunanin shine yake zancen ba.

Hafeez yasaki ajiyar zuciya sannan yaci gaba da fadin"na fuskanci qalubalen rayuwa kafin na kawo matsayin da nake a yanzu,ki bani dama inaso na qarar da Rayuwata tare dake,zan baki lokaci kiyi shawara da mahaifiyar ki"
Kafin Hafeeza tayi magana ruwa yafara saukowa,kasancewar Abaya ce a jikinta shiyasa nan take ruwan yajiqata jalaf,shima anasa 6angaren rigar jikinsa tafara jiqewa,ya kalleta zaiyi magana idonsa ya sauka a qirjinta ga shatin bra duk ya futo, cikin sauri ya nuna Mata wani waje da hannun sa, cikin sauri suka qarasa wajan suka tsaya saide gaba daya ya daburce itama daga nata bangaren haka, duka su biyun kowa yakasa kallon kowa, hannun sa yazuba cikin aljihun wandonsa, ya dauko katinsa yabata yace"gashi"
Kanta aqasa batare data dago ba tasa hannu ta karbi katin, saide jikinta yayi sanyi sosai dajin kalaman sa,duk yanda akai ya fuskanci abubuwa dayawa acikin rayuwar sa, amma abunda yafi daure mata kai meyasa be dauki wayar Mamansa ba? meyasa dataje gidansu iya shida qannansa da Kakarsa ne kawai agidan?

Ina mahaifiyar sa?, ina mahaifinsa? meyasa Basa tare gida daya?

Sun dade awajan har saida ruwa ya tsaya, babu mai magana acikin su face satar kallon juna dasuke.

Bayan ruwan ya tsaya ya nuna Mata hanya yace"muje ko?"
Kanta ta gyada masa,suka fara takawa ahankali, ita kanta ba tasan ina zasuje ba,babu wanda zai kallesu baiji sun birgeshi ba, sosai suka dace da juna.

Kai tsaye wani super market suka shiga,qa'idar super market din sai ma'aurata ne kawai suke shiga, amma ganinsu tare yasa babu wanda yamusu magana kai tsaye zakace su din ma'aurata ne, bayan sun shiga saida yayi mata siyaiyar Kaya kamar hauka, Hafeeza kawai Kallonsa take, saida yajido Mata Kaya masu shegen kyau da tsada sannan suka futo,bayan sun futo ma saida Yakoma wani shagon yasiyo Mata sabuwar waya dalleliya babbar ta hannun ta, sannan ya dauki kayan suka wuce masauqinta, har zuwa lokacin babu wanda ya cewa dan'uwansa uffan.

Saida ya ajiye mata kayan sannan yazuba hannun sa cikin aljihun wandonsa ya kalleta yace"zan tafi"
Ba tayi kuskuren Kallonsa ba tace"nagode"
"saina jiki"
Abinda yace kenan yajuya ya tafi, harya 6acewa ganinta batabar wajanba, ahankali ta sunkuya ta dauki kayan, taji nauyi sosai, hakan yasa takai wani, tasake dawowa ta dauki Sauran, bayan ta shiga dakin ta tabude kayan gaba dayan su, ta rafka uban tagumi tana tunanin yanda zatai da wannan bawan Allah, kokadan baza tace ga abinda takeji akansa ba.

Ga kuma Gaddafi agefe, ajiyar zuciya ta saki,ta dauki wayarta ta dokawa abokiyar shawarar ta kira, Wato Maman Fadila.

Ta dade tana kiran wayar amma kwata-kwata wayar taqi shiga.

Tagumi tayi tareda zubawa kayan ido,har yanzu ba zata ce ga abinda takeji akansa ba,abinda tasani kawai shine Gaddafi shine acikin zuciyar ta,harga Allah tana son mutum mahaddacin Alqur'ani,Shikuma wannan babu alamar ma yasan addinin bare ayi maganar karatun Alqur'ani.

Ajiyar zuciya ta saki tamiqe ta cire Abayar jikinta ta shiga toilet domin watsa ruwa.

Ko kwana uku Hafeeza bata qara a Saudia ba ta kammala duk wata ibadar ta,tayi shirin dawowa Nigeria, har zuwa wannan lokacin bata sake ganin Hafeez ba, haka katin daya bata me dauke da numbers dinsa ajiki shima ba tayi kuskuren saka number ta kirashi ba.

Suna sauka a Airport taga kawu Hamza da wasu daga cikin malaman makarantar su, acikin wata hadaddiyar Mota suka tafi gida, itade Hafeeza tunda suka fara tafiya zuciyarta cike da mamakin motar,tarin tambayoyi fal ranta saide babu me bata amsa,kawu Hamza kuwa sai janta yake da zance ahaka har suka qarasa gida.

Anan taci Karo da gyare-gyaren da'ake yi musu agidan, sosai gidan ya sauya yayi kyau sai son barka.

Tundaga qofar gida Inna da Maman Fadila da Sauran maqota suka tarota kowa yana murna har suna neman kada ta aqasa, daga nan suka dunguma zuwa gida aka baje kolin fira, gida yacika da Jama'ah kowa yana yi Mata sannu da zuwa.
Chapter 19 · 0% Book details