← Book details Matar Abbana Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 24

Sashe 4

Matar Abbana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Husna tace"wai Kaka a'ina ake siyo miki wannan qosan ne me dad'in tsiya?"
Kaka tasake jefa qosai a bakinta tace"can ne layin can na baya d
ede gidan Alhaji Munzali"
Husna tatafi tunani tana fadin"Alhaji Munzali,Alhaji Munzali...."
Sannan tadawo da duban ta wajan Hassana tace"bangane shiba, ke kin ganeshi?"
Hassana ta girgiza kanta alamun itama bata gane ba,Kaka ta kallesu tace"bakusan Alhaji Munzali ba?

Alhaji Munzalin? saina d'ura muku zagi"(
Husna ta hada ido da Hassana sukai murmushi, sannan suka juya suna kallon Kaka.

Hajiya Kaka tace"Alhaji Munzali fa,wanda matarsa tayi hatsarin mota ta rasu,har mukaje daku gaisuwa 'yan'uwan matar sai faduwa suke suna aljannu"
Cikin sauri Hassana tad'an bugi kafadar Husna tace"ke natuna,kusa da gidan wannan 'yar ajin namu HAFEEZA KHALEED"
Husna tace"ok dama adede nan gidansu Hafeeza yake? kai wannan ai aitaci Sunanta Hafeeza din,akwai karatun Alqur'ani kamar ruwa,ga muryar ta dad'i idan tana karatu,but in hakane meyasa tana kusa da islamiya amma kusan kullum saita makara inde haddar safe zamu bayar?"
Hassan ta dangwali yajin qosai, takai bakinta tacinye, sannan tace"gaskiya de inde haddar safe zamu bayar zakiga amakare take zuwa,amma idan da yamma ne kinga bata makara,gata kyakykywa kamar aljana,suma malaman namu naga sai nan-nan suke da'ita kamar ma sonta suke"
Husna tace"su sukasan me suka gani,ai rannan kafin kidawo daga toilet tashigo late, tana sauri zata shigo ajin ashe qusa ta riqe mata gefen hijabinta ita kuma dayake sauri take bata sani ba, aikuwa Hijabin nata yad'age sama, karkiga uban qugun wannan yarinyar, shi kansa malam Sabo bakiga idonsa ba kamar zai fado, ya qwarawa guqun baiwar Allah ido,kuma ahakan kullum tana cikin Hijabi, gashi batada qawaye kullum ita kadai zaki ganta, to dan Allah tanasa Hijabi ma malamai suna mata haka idan wataran tasa mayafi tafita gari ai baza'a rasa samari masu kawo mata Hari ba"
Kaka dake sauraron firar su tace"ikon Allah, aikuwa taji dad'in ta,Hijabi ai shine cikamakon mace mai hankali da tarbiya"
*** *** ***
Da yamma tana zaune tana wanke musu kayan su itada Inna sai Yatsina fuska take tana runtse idonta saboda yanda marar ta take murd'awa, tun safe take jin ciwon marar har zuwa yanzu,kuma maganin ta ya qare gashi aiki yahanata fita ta siyo wani maganin.

Inna dake zaune daga cikin Rumfa tana jin Radio a wayar Hafeeza, wayar ma har tayi ja babu caji, tana qoqarin kashe Radion aka sako wa'azin wani malami,bata fasa ba ta kashe tana fadin''aikuwa bawan Allah saide kayi haquri baqin wa'azin naka nayi ba,caji saura yanka d'aya"(
Maqociyar suce tayi sallama ta shigo gidan, Wato Maman Fadila, mace me kimanin shekaru 35, tana dauke da Fadila a kafadarta, adede lokacin Hafeeza tadena wanki ta sunkuyar da kanta qasa tana tauna siraran lips dinta.

Maman Fadila tace"Subhanallah,Auntyn Fadila meyake damunki naga kina runtse ido?"
Inna Ta Rasulu tace" wankin ne bataso,tun dazu taketa faman yatsina fuska ina kallonta"
Maman Fadila tayi murmushi tace"haba Inna ita ta'isa tace haka?"
Tajuya wajan Hafeeza tace" ko cikin ki ne yake ciwo?"
Cikin sauri ta girgiza mata kai tace" marata ce take ciwo tun safe,kuma yaune ranar dazan gama hutun sallah ta,bansan meyasa takemin ciwo ba,qila wannan aikin ne wallahi,kullum mutum bashida aiki daga wannan sai wannan"
Inna tanajin haka tace"Hafeeza ki kiyaye ni, karki sani abakin duniya,yanzu inda wasu baqi ne agidan Namu kika fadi haka ai sai azata naman jikinki nake yanka saboda azaba,wani ma cewa zaiyi azaba na ganawa uwarki harta mutu, nan kuwa ciwon naqudarki ne ya kashe ta,Shima Babanki majanunin Laila bata dade da mutuwa ba shima yabita,idan baki mana wanki ba wanne kaya zamu sa?, Ya zakiyi? haka zaki daure ki qarasa wankin, ni wallahi badan wannan ciwon qafar tawa ba ni Ta Rasulu har a fadamin aiki?"(
Maman Fadila tayi murmushi tace"Inna da Hafeeza drama, kinga riqe min Fadila inje gida in kawo miki magani,nida nakawo raino Uwar raino ba lafiya ai banga ta zama ba"
Daqyar Hafeeza ta kar6i yarinyar ganin idon yarinyar akanta ko qyaftawa batayi, sai taji tausayin yarinyar, ta kar6eta ta goya ta, sannan ta dauraye kayan tafara shanya wa.

Bayan tagama shanya kayan tadawo cikin Rumfar ta zauna akan kujera.

Daga qofar gida Inna tajiyo wani dan gwangwan yana cewa"tsohon kwano mataccen kaya akawo mu siya..."
Daga inda suke zaune Ta Rasulu tace" me za'a kawo ku siya? asato kusiya de, nan almajiri yashigo da sassafe muna baccin asara, ya sace min sabon bokiti na yakawo muku kuka siya, kwana ki dana fita Unguwa wata tukunya dana gani awajansa sabuwa dal nace a'ina kasamu wannan tukunyar yace siya nayi, nace a a, aka sato kuka siya dai, kudena siyan kaya awajan yara yawanci duk na sata ne, nayi masa nasiha de yace yadauka, shine dan tsaurin ido yanzu ma kinji ya dawo"
Dataji Hafeeza shiru bata tanka mata ba, saita kalleta tace"Hafeeza kinyi waya da saurayin ki yau kuwa?"(
Hafeeza ta dago kanta da qyar tace" Inna ba kincinye cajin wayar kinajin radio ba?"
Inna tace"Af....haka akayi fa, na manta, sannu Hafeeza, Allah de yabaki lafiya"
Kafin Hafeeza tayi magana Maman Fadila tashigo takawo mata magani tasha, sannan ta shinfida mata tabarma ta kwanta, ta dauki Fadila zasu tafi, Hafeeza ta meqa mata hannu daga kwancen tace "Bani ita"
Babu musu Maman Fadila ta miqa mata yarinyar tanajin dadin yanda Hafeeza take dawainiya da Fadila,duk maqota kowa yasan yanda Hafeeza take son Fadila,hatta shima Baban Fadila kasancewar yasan Hafeezan tanada hankali da nutsuwa uwa uba duk unguwar kowa yasan cewa Hafeeza ta amsa Sunanta, mahaddaciyar Alqur'ani ce, hakan yasa shida kansa Baban Fadilan wani lokacin yake cewa akai Fadila raino wajan Hafeeza.

Hafeeza ta kar6i Fadila ta d'orata akan ruwan cikinta, tadora mata kanta akan tudun tsayaiyun nashanunta, yarinyar kuwa tayi luf kamar ta tada kai da nonon uwarta.(
Cikin sati biyu su Hafeeza suka gama bitar tilawar su gaba daya,har makaranta ta saka musu ranar da za'a yayesu tareda bikin saukar su,acikin sati biyun nan bata zama, kullum tana cikin neman kudi ta hanyar qosai, da daddare bata baccin kirki saboda yanda take raba dare tana tulawar Alqur'ani kasancewar an riga an tantance su itace daliba ta farko dazata fara karatun Alqur'ani aranar saukar tasu, hakan yasa takowanne 6angare take shirye-shirye cikin farinciki.

Yau bayan tadawo daga wajan suyar qosai tabawa Inna kudin kamar yanda tasaba, zata wuce tashiga wanka Inna tace"zo muyi lissafi Hafeeza"
Cikin nutsuwa ta dawo ta zauna,Inna ta janyo asusun dasuke tara ribar su ta fasashi, tahada da kud'in cinikin ranar suka qirgasu,Inna tace"to Islamiyar taku nawa sukace zaku bayar kudin saukar?"
Hafeeza tace"Dubu hamsin ne Inna,kuma tun ranar da suka fada mana nabiya gidan Kawu Hamza nafada masa"
Inna tace"toga ribar mu kinga munsamu kusan dubu saba'in da shida,kidauki dubu hamsin din kikai musu,kuma naga man suyar tamu ma yaqare,ki biya ki siyo mana, ki auno wake, sannan kitahomin da irin naman nan dakika siyomin rannan, dan qafar nan tawa har yanzu jinta nake"(
Lokaci d'aya farinciki ya kama Hafeeza, saboda bata ta6a zaton Inna zata bata kudin ba,shiyasa ma kai tsaye tawuce gidan Kawu Hamza tafada masa,tace"to Inna zan siyo insha Allah,bari nayi wanka"
Tafadi hakan bakinta a washe da tsantsar walwala dimples d'in nan nata kuwa sai lotsawa sukeyi.

Tana miqewa zata shiga bandaki Kawu Hamza yayi sallama yashigo gidan,hakan yasa ta fasa shiga wankan ta dawo ta Shimfida masa tabarma takawo masa ruwa a kofin silba, bayan sun gaisa yadubi Hafeeza yace"Hafeeza ya shirye shiryen saukar?"
Cikin farinciki tace"Alhamdulillah kawu"
Yayi ajiyar zuciya sannan yace"to masha Allah,Allah yatemaka, ubangiji Allah yayi miki Albarka"
Cikin nutsuwa tace"Amin Kawu"
Kawu Hamza yadubi Inna yace" Ta Rasulu Hafeeza taje gida tayi min maganar kud'in saukarsu, to nayi niyar zuwa tun ranar in kawo mata kudin dasuke hannu na to kuma sai wani uzurin yashigo, yanzu de ga dubu Hamsin d'in nan tasamu takai musu kafin muga abinda za'a yi kuma"
Inna ta washe bakinta tace" to madalla,Allah yasaka da Alkhairi"
Saikuma ta fashe da kuka tace"Allah yabar zumunci Hamza, Allah yajiqan Haladu,addu'ar Haladu a kullum itace yanda yasawa wannan yarinya suna Hafeeza Allah yasa sunan yabita, kuma gashinan Hafeeza ta tabbata Hafeeza saide baya raye,sun tafi sun barmu nida Hafeeza"
Kawu Hamza yace"Haba Ta Rasulu,menene abun kuka kuma,insha Allahu daga Yaya har Mahaifiyar Hafeeza suna Aljanna, Allah ya musu Rahma ni zan tafi"
Inna ta goge hawayen idonta tace"to Hamza mungode,agaida mutanan gida"
Bayan yafita Hafeeza tamiqe zata shiga wankan ta, Inna tace"ina zaki Hafeeza, zoki dauki kud'in mana"
Hafeeza ta dawo ta zauna tace"Inna ai kin riga kin bani,basai mu ajiye wannan dinba?"
Inna tace" A a, wancen dana baki dama ai kece me wahalar nemowa, wannan kuma kyauta yabaki, ki ware dubu ashirin ki siyo mana taliya da macaroni tunda munada sauran shinkafa, dubu talatin din kije dashi gidan Maman Fadila saiku tsara abubuwan da zakuyi na rabo, ranar saukar "
Hafeeza tace"to Inna baza'a sake siyo miki wani abun ba? kodan lemo haka?"
Inna Ta Rasulu ta yatsina fuska tace"barshi Hafeeza, karki siyo min lemon komai,banajin d'and'ano abakina Hamza yatuno min da mutuwar mijina data mahaifiyar ki,gaba daya naji komai yafita akaina,tsiren de damukai magana dake d'azu shi kawai zaki siyo min" (
Hafeeza tayi murmushi tace"to Inna"
Bayan tafuto daga wanka kai tsaye gidan Maman Fadila ta wuce, tabata dubu talatin din tafada mata kayan rabo zasu siya dashi, maman Fadila tayi lissafi zasuyi cin-cin da meat pie da dublan, ragowar kudin kuma tace sai Hafeeza tasai kayan kwalliya dashi.

Bayan sungama tsara komai Maman Fadila ta dauko Alqur'anin ta dakuma littafin Akhdari Hafeeza tayi mata qarin karatun.

Sannan tayi mata sallama tatafi, kai tsaye tawuce ta siyo kayaiyakin da sukai lissafi itada Inna, bata fasa ba saida ta siyo mata lemon gora guda biyu samfirin Limca ,sannan tadawo gida.
Chapter 4 · 0% Book details