Sashe 6
Matar Abbana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kallan fuskarsa tayi tasaki murmushin jin dadi,da alama yau ranar sa'ah ce awajan ta, yanda taga idonsa a lumshe yana sakin numfashi hakan yasa ta daina shafa masa abun,kai tsaye tafara matsa masa shi tana addu'ar Allah yasa ya amince da buqatar ta,inde tasamu nasarar samun wannan abun toda Hafeez yagama mata komai aduniya.
ahankali tadena tsotsar kunnansa tafara yimasa rada cikin wasu irin kalamai wanda dolen dolema hankalin namiji yatashi idan yajisu, lokacin daya kuwa qasan mararsa tafara tashi, cikin qarfin hali yasamu yadawo hayyacinsa, hannunsa daya yasaka ya doketa, bata zame ko'inaba sai kan kujerun da'aka tanada domin zaman baqi,cikin sauri tafara gyara daurin dankwalinta daya fadi gefe tana kallonsa cikin tashin hankali.
Hafeez kuwa kasa dagowa yayi,yana sunkuye yayinda hannayen sa suke kan table din dake gabansa,muddin yace zai miqe to gaban wandon sa zai iya tona masa asirin halin dayake ciki.
Ahankali tataso tadawo gabansa tace"meyake damunka?"
Cikin tsananin damuwa yace"leave me alone please!,ki fice daga office dina, ki fice daga cikin rayuwata!!!"
Cikin sauri ta kalleshi, tunda take dashi bata taba ganinsa cikin wannan yanayin na 6acin rai ba,haqiqa ransa a6ace yake ta yanda jijiyoyin kansa duk sun futo har zuwa kan goshin sa.
Wani irin hawaye yazubo daga idonta tace"Hafeez ni kake kora acikin rayuwarka? saboda kaga na damu dakai inason kasancewa dakai? wacce mace ce zata iya sadaukar ma da jikinta saboda soyaiyar datake ma?
Amma ni nakawo kaina gareka shine kakemin abinda ranka yakeso,babu damuwa, dama zuwa nayi inyi ma sallama, nasamu canjin wajan aiki zuwa Germany,nayi tunanin zamuyi sallama cikin annushuwa da kewar juna,ashe bahaka bane,zanjiraka har zuwa lokacin da zaka amince da buqata ta...."
Tana fadin haka tajuya tafice daga office din, ahankali yasaki ajiyar zuciya sannan yakai hannunsa zuwa kan mararsa yaji abun yariqe babu alamun sauka,cikin tsananin damuwa ya runtse idonsa yana tunanin mafita, yariga yasan cewa tun kafin yakai shekarun balaga yake buqatar mace,amma bayajin akwai yarinyar da zatayi nasarar sace zuciyar sa saboda mata yawancin su halinsu daya ne,wani lokacin basu da Imani ko kad'an,yanajin dadin yanda suke tafiyar da rayuwar su cikin kwanciyar hankali iya su hudu, shi da Kaka dakuma qannan sa yanbiyu, bayason sanadin mace wannan walwalar data dawo cikin gidansu ta rushe irin wasu shekaru abaya wanda baya qaunar tunawa dasu.
Cikin sauri yabude wata locker yadauki wani magani yasha, sannan yasamu ya zauna yariqe kansa da hannunsa bibbiyu, ba'a ta6a masa wannan wajan bama kullum yana cikin sha'awa to inaga anzo an ta6o masa shi, ahankali yagama yanke wa kansa shawara gara ya tattara yabar qasar,taron saukar 'yanbiyu da yayi niyar qin zuwa gara yaje ko zai samu ya Kaucewa matan dasuke kawo masa Hari, idan baiyi da gaske ba dole watarana zasu maidashi dis virgin, wanda shi kuma bayason hakan,dalilin dayasa kenan duk sati yana cikin yin azumin litinin da alhamis.
*** *** ***
Ta Rasulu tasake karyar dubulan din dake hannunta sannan ta kalli Hafeeza tace"Abun naku yayi dadi kuwa,ga zaqi kamar sikarin"
Hafeeza tace"Maman Fadila ce tayi,kowa cewa yake yayi dad'i, nima tanayi ina ganin yanda takeyi yanzu harna koya"
Inna tace"dama mezai hana ki koya,aigara dakika zuba mata ido kikaga yanda takeyi, kinga idan Allah yasa kikai aure saiki dingayin na siyarwa akai miki shago, idan Allah yakawo kasuwa sai kiga kin samu sana'ah, wai saurayin naki kuna waya kuwa kwana biyun nan?"(
Hafeeza ta girgiza kanta sannan tace"a a bamuyi waya ba"
Cikin mamaki Inna tace"A a, to besan zakiyi sauka bane ko Yaya?"
Hafeeza tasaki murmushi wanda yakawo lotsawar dimples dinta, tace" Yasani Inna, Nafada masa, kuma yacemin insha Allah zaije wajan sassafe,zaiyi min vedio a wayarsa idan ina karatun qur'ani"
Inna tasaki baki galala tana kallon Hafeeza sannan tace"narasa wacce irin yarinya ce ke Hafeeza, waishi haka ake soyaiya ne kwandalar sa bazatai ciwo a wajanki ba? kekuma sakarya wato za'a miki vedio har wani washe baki kike,Allah yaji qan ubanki Haladu kullum idan zaizo wajena zance da baqar Leda yake zuwa, yasan zakiyi saukar amma be baki ko taro ba?"
Hafeeza tace"Inna cemin yayi nayi haquri rannan yasamu dubu d'ari amma ya kyautar dasu atake"
Inna ta kalli Hafeeza tace"Yakyautar da dubu d'ari?
Kud'i har dubu d'ari kuma duka ya kyautar dasu 'yarnan?"(
Hafeeza tayi shiru takasa magana, Inna taci gaba da fadin" ke Hafeeza wannan saurayin naki maqaryaci ne"(
Hafeeza tace"Inna ba qarya yake ba, nasan Gaddafi bazai min qarya ba"
Inna tace"Hafeeza zaki rufemin baki kokuwa saina doke miki bakin? tayaya ne zai dauki dubu d'ari kacokam yayi kyautar ta? awannan yanayin?
Kuma kika yarda? dayayi kyautar meyasa ke ya manta dake bai baki ba amma yasan yazo yabaki labari?"
Hafeeza tace" Inna in zaka so mutum kasoshi dan Allah,kiyarda nasan bazai min qarya ba"
Inna tace"yo tayaya zan yarda Hafeeza? bama wani sashe na kudin ba ace dubu d'ari ka kyautar da'ita atake su waye iyayenka?
Shiyasa kusan kullum yake miki qaryar yana Abuja, saide in da dubu darin daya samu yake zaryar kudin mota zuwa Abujan, shiyasa yanzu ya tsugunna tunda kud'in yaqare"(
Hafeeza de tayi shiru batace komai ba,duk wannan fadan da Inna takeyi ko kad'an ba taga laifin Gaddafi ba, asali ma abun hannunsa baya birgeta, yanda ya'iya karatun Alqur'ani yafi komai daukar hankalin ta, shiyasa take mutuwar son sa ta gagara sauraron kowa.
Inna tace"ga kudi can ki dauka kije kisiyo wake ki gyara"
Hafeeza taturo d'an qanqanin siririn bakinta gaba tace"Inna wake kuma?"
Inna tace" gashi kuwa kinbawa kanki amsa?"
"Inna jibi fa Saukarmu kuma yanzu goben ma sai munyi qosai?"
"idan bamuyi sana'ah ba dame zamu rufawa kanmu asiri? kitashi kije kisiyo nace"
Cikin fishi ta dauki kud'in tafice daga gidan, bata zame ko'ina ba sai gidan Maqociyar su Maman Fadila.
Maman Fadila tana ganinta tace"Alhamdulillah dama gidanku zanje yanzu,Baban Fadila ne ya siyo miki takalmi, Nima ga material na dinka miki,kinga material din yayi Kala da hijabin da'aka raba muku a islamiya wanda zaku saka awajan sauka,kinga saiki saka material d'in naki"
Lokaci d'aya farinciki ya mamayeta, ta daka tsalle ta rungume Maman Fadila tana zuba mata godia, Maman Fadila tayi murmushi tace"ni ki daina yimin godia Hafeeza kamar qanwata haka nake jinki,yanzu de meyafaru kika shigo da 6acin rai?"
Hafeeza ta Yatsina fuskarta tace" Wai Inna ce tace naje nasiyo wake gobe zamuyi qosai, shine nazo in fada miki ko zaki mata magana,jibi fa saukar mu, kuma dan Allah kamar mu mukafi kowa neman kudi kwana biyun ma ba zamuyi haquri ba?"
Maman Fadila tayi murmushi tace"Haba Hafeeza,yanzu idan badan kuna wannan sana'ar ba tayaya zaki kai kud'in saukar ki makaranta?
Nan jiya Baban Fadila ya zauna yana yabonki yana cewa bakida girman kai kina kokarin nema muku abinda zaku rufawa kanku asiri to yanzu kuma karki bani kunya mana,Inna kamar mahaifiyar ki ce,duk abinda tafada miki me dadi da marar dadi kiyi haquri wataran sai labari,idan Gaddafi ya shirya ma rana daya zamu dauke ki mu kaiki can gidansa saide kizowa Inna ziyara"
Hafeeza tanajin wannan maganar kunya ta kamata,ta kalli Maman Fadila tace" Maman Fadila nawane Sauran kudin dakika ragemin wanda zan sai kayan kwalliya dashi?"
Maman Fadila tace" Dubu uku da dari takwas ne, kona dauko miki Zaki biya ta shagon ki siyo?"
Hafeeza ta Girgiza kanta tace"a a, kawai ni abar kayan kwalliyar, kibawa yaro ya siyo nama kiyi wa Gaddafi Farfesu anjima zaizo da daddare, kinga saina hada da kayan rabon nabashi nasa tun yau ko?"
Maman Fadila tace"haba Hafeeza,kayan kwalliyar ma idan kin siya ai shi zakiyi wa kwalliyar,ki bar kudinki kisai kayan kwalliya irin na yanmata, Shikuma idan yazo saiki zo ki dauki qullin kayan rabon ki bashi"
Lokaci daya Hafeeza ta sauya,cikin damuwa tace"Maman Fadila idan na kashewa Gaddafi kudi ban fadi ba, Dan Allah ki barni ayi masa Farfesun tunda ni kwalliya ba damuna tayi ba"
Maman Fadila ta saki Ajiyar zuciya tace"eto hakane, shima kuma tunda saukar taku tazo ai nasan zai bada contribution dinsa kinga sai mu sai lemon talakawa dashi"
Cikin murna Hafeeza tace"niko be bani komai bama babu komai"
Maman Fadila tace"um su Hafeeza masoya, irin wannan soyaiya haka"
kunya ta kama Hafeeza, cikin sauri tafice daga gidan tatafi wajan siyo wake tana dariya.
*** *** ***
Da yamma suna zaune afalo duka su ukun,Kaka ta zubawa tv ido tana kallo, Husna ta ajiye wayar hannunta wadda tagama karanta azkar din yamma, ta kalli Hassana tace"Sister kitashi muje mu gyara wa Yaya dakinsa,kinga baya raina datti ko Ya yake,karyazo gobe yace bamu gyara masa dakin sa da kyau ba, kekuma kin zauna sai faman karatu kike, jibi de zamuyi saukar nan kowa ya huta"
Kaka ta kallesu tace"gyaran dakin me? har wani gyaran daki zaku masa? meya hana yayi aure matarsa ta masa? babu wanda zai gyara masa daki"(
Husna ta kalleta tace"Kaka an dade ba'a gyara masa dakin bafa"
Kaka tace"wanne irin dadewa?
Naga ga dakin nasa nan ko giftawa kazo yi ta wajan qamshi ne yake tashi"
Hassana ta ajiye Alqur'anin hannunta tace"muje driver yakaimu supermarket muyi cefane nasan yanason farfesun kaza sai muyi masa mai dad'i dan yasan cewa muma yanzu mun qware a girki"
Kaka ta kalli Hassana tace"wacce irin kaza kuma ana zaune lafiya? ku kuwa kuhuta mana, kullum kuna cikin girki ku rabu dashi goben kafin jirgin su ya sauka sai muyi order ko Fizza ce"
Hassana da Husna suka kalli Kaka,zasu gyara masa daki tahana su tace idan yanaso yayi aure matarsa ta gyara masa, yanzu suna qoqarin siyo abun cefane suyi masa girki shima ta hana, basusan me Kaka tataka ba.
Husna tasaki murmushi takoma cikin kujera tayi kwanciyar ta,cikin zuciyarta kuwa Allah-Allah take gobe tayi domin taga yanda Kaka zata qare tsakanin ta da Yaya Hafeez.
*** *** ***
Kamar yanda tasaba sassafe tafita wajan suyar qosanta, kamar kullum yauma Hijabi ne ajikinta dogo har qasa,hijabin yayi wa farar fatar ta kyau sosai mai launin ruwan toka me duhu,kyakykywar doguwar fuskar ta tayi kyau sosai acikin hijabin,mutane ne zagaye da'ita tana zuba musu qosai akan takarda sannan tasaka acikin Leda tabasu, yayinda wasu samari agefe suke tsaye suna jiranta wasu a mashin wasu kuma zaune suke daga gefe suna jira tasaka musu suci abunsu anan.