Sashe 21
Matar Abbana Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Qafafun nata ya dauka yad'ora akan cinyoyinsa yafara matsawa,sannan yadago Kansa ya kalleta yace"Kaka na tambayi yaran nan sunce min kina kwance adaki, nace me kika tara har Zaki shige daki ki kwanta?"
Hajiya Kaka ta Kalleshi tace" Bar batun na ajiye ko ban ajiyeba,tunda na ajiye wadda ta haifeka ai kasan nayi ajiya"(
dan yamutsa fuskarsa yayi sannan yace"naji... naji,ni wasa nake miki Kaka"
Hajiya Kaka tace"inma da gaske kake kar nake kallonka Hafeezu,daidai nake daku agidan nan,fadamin meya kawoka? dan nasan wannan zuwan naka akwai dalili"
farincikin sane yasake qaruwa yace"yawwa Kaka dama... am dama zan fada miki ne nasamu wata yarinya"
Cikin sauri Hajiya Kaka ta Kalle shi, sannan ta saka tafukan hannunta ta murtsika idonta ta tabbatar ba bacci take ba, ahankali ta yunqura tatashi zaune, sannan ta Kalle shi tace"Hafeezu mafarki nake koda gaske ne?"
hannayenta yakamo ya mintsineta, cikin sauri takai masa duka abayansa yakauce yana sakin dariya.
Hajiya Kaka ta daga hannayenta sama tace"Ya ubangiji nagode ma, Allah Abun godia ashe zanga wannan ranar ni Rabi'atu, Allah na gode ma"
Ta shafa Addu'ah sannan ta fuskanceshi da kyau tace"ka tabbata da gaske kake Hafeezu?"
Kansa ya gyada Mata, sannan yace" da gaske nake Kaka, ina sonta sosai"
"gaskiya na yarda kana sonta tunda harka iya bude baki da kanka ka fadamin, yau wacce rana, Alhamdulillah, amma 'yar waye? inane gidansu?"
Cikin kunya yadan shafa sumar Kansa yace"Kaka aikin santa ma, qawar yarannan ce, yarinyar da tazo wajan su kwana ki, Hafeeza"
Cikin tsananin mamaki Hajiya Kaka ta rufe bakinta da hannayenta sannan ta bude tace"Almiri,ni nasan awajan saukar nan Kaine katura Mata wannan kudin ko?"
Cikin salon shagwa6a yace" Kakaaa"
Kaka tayi murmushi sannan tace" to shikkenan naji, aiba laifi bane hakan Hafeezu,ladanka yana wajan Allah"
Ajiyar zuciya ya sauke, sannan yasake matsa hannayenta dasuke cikin nasa yace"tun ranar da nazo na ganta, ina yawan bibibyar ta,itace take saida qosan da'ake siyo miki, tana cikin halin rashi Kaka, sannan sana'ar datakeyi itace tasake jefa min tausayin ta araina, da wannan hannayen nawa nayi irin wannan sana'ar datakeyi, waje-waje nake yawo da qosai akaina...
"
ya qarasa maganar yanayin sa yana sauyawa, yayinda ya zubawa tafukan hannunsa ido yana kallonsu.
jikin Hajiya Kaka yayi sanyi,tasaki Ajiyar zuciya sannan tace"kadena tuna baya, ka fuskanci gaba, nasan cewa idan mukaje nema maka auren ta akwai qalubalen da zamu fuskanta,nariga nasan rade-radin da'ake agari a kanmu"
maimakon yabata amsa saiya sauya akalar maganar tasa zuwa wani abun daban, ya kalleta yace"amma Kaka ai kin yaba da hankalinta ko?"
Cikin gamsuwa Hajiya Kaka tace"sosai, ai naga tanada nutsuwa babu laifi,amma de abunda yake damuna daya ne, naji yaran nan su Hassana suna cewa tanada kwankwaso yarinyar, inji de ba abinda yakaika kenan ba ko?" (
Wani irin kallo yayi mata ya Girgiza kansa,sannan yace"saida safe"
Hajiya Kaka tasaki dariya ita kadai,tana sake daga hannu tana godewa Allah.
Kawu Hamza ya kalli Malam Usman bayan sun gama gaisawa dashi yace"Maganar yarinyar nan marainiya yar wajan Yayanah haladu marigayi ce ta kawo ni, to kasan yaron wajanka Gaddafi yana zuwa wajanta zance, to abinda yake faruwa shine, akwai manemi da yarinyar tasamu, na zauna da'ita nayi Mata maganar sa, amma ta nunamin batason shi wanda yafuto din, yaron wajanka Gaddafi takeso, to shine nazo dakaina, kasancewar yanzu ita amana ce awajena, koda mahaifinta yana raye, ni zai wakilta wajan wannan al'amarin, banaso manemin nata yazo ya da maganar turo wa gida kuma mu ce munyi Mata miji alhalin kuma babu wata tsaiyayar magana daga wajan ku, saboda haka idan da gaske yaron wajan naka yake nabashi dama yafuto"
Malam Usman yayi Ajiyar zuciya yace"wallahi Malam Hamza tunda naji labarin Gaddafi yana zuwa wajan Hafeeza awajan qannansa,nake cikin farinciki da wannan alaqa saboda nasan cewa Gaddafi yaza6i yarinya gidan tarbiya uwa uba kowa kwatance yake da Hafeeza musanman a makarantun Islamia,Hafeeza babu ruwan ta kowa yana yabon halayen ta, saide wani hanzari ba gudu ba, inda ace inada wani yaron Babba toda nida kaina zan bashi Umarni yaje ya auri Hafeeza amma ba Gaddafi ba, saboda yanzu haka maganar danake ma Gaddafi sonake yakama hanya yatafi kudu neman kudi,shi kuma bayaso yafi so ya zauna yana bibibyar wadannan Yan siyasa yau wannan yabasu dubu Ashirin wannan yabasu dubu biyar dubu goma, ina rayuwa zata iyu dahaka Malam Hamza?"
Kawu Hamza ya jinjina Kansa sannan ya dago ya kalli Mahaifin Gaddafi yace" to ita de Wannan yarinya Hafeeza ta nuna shi takeso, kuma kasan su Mata da kunya amma yarinyar nan haka ta ajiye kunya ta bude baki tacemin ita sai Gaddafi, yanzu babu wata sana'ah dayake yine ko min qanqantarta wadda zai iya riqe yarinyar?"
Malam Usman yace" Bashida sana'ah,kaga saboda shi bai kamata a dakatar da wanda yafuto yanzu ya shirya ba, tunda kun tabbatar wanda yafuto din da gaske yake to ita mace ce, wanda yafuto ai dashi za'a yi, ba za'a jira Wanda ko muhalli bashi dashi bare sana'ah ba"
Kawu Hamza yace"hakane, toba damuwa Malam Usman godia nake"
Malam Usman yabashi hannu suka sake gaisawa sannan ya juya yatafi.
*** *** ***
Hajiya Kaka ce ta shigo falon ta zauna tareda fadin "wash Allah, wannan qafafu nawa sun riqe kamar wanda nayi doguwar tafiya"
Husna datake cin abinci ahankali kamar bataso ta kalli Hajiya Kaka tace"harna gama girki kina maqota a kwance"
Hajiya Kaka ta kalleta a sheqe, cikin gatse itama tace" eh wallahi bacci nake sai yanzu nafarka"(
Husna tata6e baki taci gaba da cin abincin ta.
Hassana datake danna waya tatashi ta zauna tace"Hajiya Kaka har kin dawo?"
"nadawo Hassana, ina can muna tattauna wa da Alhaji Ali, akan maganar neman auren yayanku"
Cikin sauri Husna ta ajiye spoon din hannunta, yayinda Hassana ta ajiye wayarta har hada baki suke suna tambayar "wanne yaya?"
Kaka tace"Hafeezu mana,yazo ya sameni yace yana son wannan qawar taku Hafeeza,shine naje gidan Alhaji Ali nafada masa, ko zai tambayo mana idan ba'a yi Mata miji ba"
ihu suka saki gaba dayan su,sannan suka hada hannu suka tafa, Hassana tace"Yaya zai huta wallahi"(
Hajiya Kaka tayi Mata daquwa tace"Hassana gidanku,Allah yasa yajiki keda shine"
Husna ta jinjina kanta tace" tabdi, lalle Yaya, kiga ranar da tazo gidannan yawani basar kamar baisan taba?"
Hassana tace" to Husna ai bakisan wani abuba, inaga fa sun dade da shirya wa, damukace tafada mana irin mijin datake so ai gaba daya suffar Yaya Hafeez ta zayyano mana"
Husna tace"wallahi hakane,ko tayaya suke zance?"
suka sake kwashewa da dariya.
Hajiya Kaka tace"Allah ya shirye ku"
*** *** ***
Kawu Hamza ya kalli Hafeeza, bayan yagama kwashe labarin abinda yafaru tsakaninsa da mahaifin Gaddafi ya fada Mata, sannan yaqara da fadin"saikiyi haquri ki kar6i shi Alhaji Isah da hannu bibbiyu, ke malama ce,kinsan ayar datake magana akan mafi yawan abinda mukeso yana iya zama sharri agaremu, wanda bama so kuma sai ya zama alkhairi agaremu, nayi magana dashi yace zaizo yaganki kuyi magana ku fahimci juna idan kunyi maganar saiya turo magabatan sa"
tunda kawu Hamza yafara wannan maganar Hafeeza kanta yake qasa,jikinta ne yayi sanyi bayan kawun yagama tunatar da'ita ayar da itace ya kamata ace tafada masa ita.
Cikin biyaiya tace"to kawu, Allah yasa hakane yafi Alkhairi"
Complete document 1k
8621296018
Amina Muhammad
fcmb.
kokuma Katin Mtn ta wannan number 08033300034, tareda shedar biya ta wannan number 08033300034
Amnah El Yaqoub
[6/14, 2:26 PM] El Yaqoub:
Kawu Hamza yace"Amin ya Allah, Allah yayi miki albarka, idan yazo din duk yanda ku kayi dashi zanzo sai inji me kuka tattauna"
Hafeeza ta amsa Masa cikin ladabi, sannan ta shige daki.