Sashe 3
Matar Abbana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kaka ta saki tsaki tace" abinda yasa kukaga na damu da aurensa bafa komai bane, sonake muma mu dinga ganin qananun yara acikin gidanmu, bamuda kowa, 'yar'uwa ta qwalli d'aya data ragemin ta mutu,Zaman lafiya suke itada kishiyarta na innaa-naha, da kishiyar tata ta mutu damuwa tasa ta susuce daga baya itama ta mutu, zamansu lafiya kalau duk inda zasuje suna tare, ko girki daya zatayi to tare sukeyi kokuma d'aya tayiwa d'aya,komai nasu tare sukeyi, to yanzu shi ban'isa nayi masa maganar aure ba saiya fututtuke fuska dama shi fuska kullum a d'aure, kuma tausayi yake bani wallahi, wannan rashin auren nasa yasa duk ya sauya, gaba d'aya a firgice yake"(
*** *** ***
Kamar kullum yauma sassafe tatashi takama aikin da tariga tasan cewa nata ne,kasancewar bata kwanta da wuri ba sakamakon hadda datayi daren jiya, hakan yasa idonta yake cikeda bacci, aikin take amma tanayi tana Hamma tana murza idonta dake cikeda jin bacci,yau Inna Ta Rasulu idonta biyu, tana ganin duk yanda Hafeeza take ayyukan ta cikin sanyin jiki saboda rashin samun isasshan bacci yasa gaba daya kasala ta lullu6eta, ganin gari yana sake wayewa ko niqan wake bata kai musu ba hakan yasa Inna ta miqe da azama ta nufi Hafeeza tana fad'in "ke da Allah bani wankin waken nan na qarasa, kina abu kamar sauna"
Tafadi hakan tana qoqarin meqa hannu zata kar6i robar da waken yake ciki, tana sako qafarta santsin ruwan da Hafeeza ta zubar awajan ya kwashe ta saiji kake timm....,Inna Ta Rasulu tazame tafadi. (
Sai akai sa'ah fad'uwar tahadu da raki,lokaci d'aya Inna tasaka wani uban ihu tana fad'in "Wayyo Allah ni Tarasulu na mutu na lalace!!!"
Cikin sauri Hafeeza tayi kanta tana dora hannunta akan qafar tana fad'in "Inna kinji ciwo aqafar ne?"
Cikin azaba Inna tace"qaniyar ciwo naji Hafeeza,cire hannunki daga wajan kiyi sauri ki kiramin Bala mad'ori "
Cikin sauri Hafeeza tazari hijabin ta tafice daga gidan, kasancewar safiya ce sosai hakan yasa babu mutane awaje, uwa uba unguwar tasu ta manyan mutane ce kowa yana gida, shiyasa kanta tsaye ta kwasa da gudu tayi gidan Bala Mad'ori, bata juyo tadawo gida ba sai tare dashi, daqyar da kururuwa da rakin kuka aka samu aka gyara wa Inna Ta Rasulu targaden da taji qafarta, Hafeeza ta taimaka mata tadawo cikin Rumfa, sannan ta dauki niqan tafice daga gidan.
A wannan rana de Hafeeza bata samu tafita suyar qosai dawuri ba,amma dayake ita kasuwa ta Allah ce babu abinda tarage saida ta saida qosan tas sannan tadawo gida.
Bata dawo gida ba saida ta siyowa Inna Robb, tana shigowa gidan kuwa ta shafa mata awajan, sannan taci abinci tasha shayi ruwan bunu me cikeda ganyen na'a na'a, sannan tayi sauri tafice makaranta dayake yau sunada bada haddar tulawar da'aka basu, bata dawo dawuri ba kasancewar itace qarshen biyawa, hakan yasa tabiya wajan wani me saida tsire ta siyo wa Inna, daga nan tataho gida,tabude mata tsiren tanaci ita kuma tawuce wajan wanke-wanke tafara wanke kwanukan data dawo dasu daga wajan suyar qosai.
Wata mata ce tayi sallama tashigo gidan tana yiwa Inna jaje, Inna ta dauki tsokar tsire ta danna a bakinta sannan ta kalli matar tace"wallahi Lami kingani de yanda tsautsayi ya sameni, yarinyar nan tana aikinta ka'in da na'in, da shegen iyayi na nace tabani aikin zanyi, kuma fa dama can bani nake aikin ba, ko tsinke bana daukewa agidan nan komai itace takeyi, to yau d'in tsautsayi ya debeni,qasar wajan ta jiqe, zuciya ta d'aya ina meqa qafa, naji an sureni anyi sama dani, to kinga de naji targade a qafar,Allah yaso aikin na kar6a ba suyar qosan na kar6a ba, yo inda ace suyar qosan takeyi na kar6a nace zanyi kinga aida tuni akan tanadar mai zan fada,saide ayi kama-kama akawo ni gida"(
Lami ta girgiza kanta cikin alhini tace" Allah mungode maka,Allah yaso agida abun yafaru"
Ta Rasulu tasake kai tsire cikin bakinta tareda yatsina fuska sannan tace"kede bari Lami"
Lami ta kalli yanda Inna take cin nama tana yatsina fuska,hakan yasa tace"Ta Rasulu kode naman baya miki dad'i ne naga kina yatsina fuska?"
Cikin sauri Inna tace" a a nama da dadinsa,jikin ne de babu dad'i"(
Lami ta juya ta kalli tsakar gidan nasu sannan ta maido da kallonta wajan Inna tace"Ta Rasulu ashe kunada zogale agidan naku, aida nasani da nazo nacira nayi dambu"
Inna tace"Um muna dashi zoki tsigeshi gaba daya munbaki, dama a wannan yanayin ma waye yakeda kud'in dazai sai kayan had'in zogalen?"
Kafin Lami tace wani abu, Inna ta kalli Hafeeza datake wanke-wanke tace"Hafeeza zoki dauko min wannan sauran garin kwakin namu ki jiqamin Nasha"
Hafeeza ta wanke dogoyen yatsun hannunta sirara,sannan ta taso tawuce daki ta dauko mata ledar gaarin tace"gashi Inna"
Inna tace"bude ki zuba a Kofi saiki jiqo"
Hafeeza tace"A a Inna debi da kanki"
Inna tace"ki zuba nace"
Hafeeza ta bude ledar tafara zuba mata gaarin a Kofi, Inna taga Hafeeza tana zuba gaari kamar bata so, tasa hannu ta qwace ledar tace"bani ni"
Tasake bude kan Leda tana zubawa dayawa, Hafeeza ta kalleta tace"ya kike qoqarin juyeshi duka muda muke lalla6ashi Inna?"
Inna tace" naki ko nawa? bataki d'aya tame garin jamaga, zubo min ruwa aciki kigani"
Hafeeza ta jiqo mata gaarin takawo mata, Inna tana gani tace"qara masa ruwa ki barshi ya juqu karnaje yajuqu aciki na, tayaya zansa wannan abu aciki na? ai juquwa zaiyi acikina, kar6o min aron cokali awajan Maman Fadila,duk Cokulan nawa babu kin kwashe kin zubar, lokacin da muke zuwa legas, haka nake kar6ar Cokula bashi, dozin d'aya nera dari"
Lami tayi murmushi bayan tagama bin bayan Hafeeza da kallo, sannan tadawo da kallonta wajan Inna tace"Ta Rasulu Hafeezan taki tagama zama budurwa sai had'a uban qugu take kamar babbar mace,gata kyakykywa kamar bafulatana"
Inna tayi dariya tace" tabdi toko zo in kasheki da fullanci bata sani ba"(
Lami tayi murmushi tace"ikon Allah amma tana kama dasu sosai"
Adede lokacin Hafeeza tadawo gidan,da goyon Fadila abayan ta,yarinya yar sati biyar da haihuwa, tabawa Inna cokali sannan taje tana share wajan datayi wanke-wanke.
Inna tasaka cokali acikin kofin garin kwakinta tafara Sha, ta d'ago kanta ta kalli Lami tace" mahaifiyar Hafeeza ba bafulatana bace,ita tasan yaren mecece, yaqi akayi a qasar su suka dawo Nigeria itada iyayenta, iyayen nata suka rasu, sai mijina ya auro ta,lokacin da'aka kawo ta gidan nan karkiga yanda nacika nayi fam ina Kishi da'ita kamar zan fashe, saboda kyau ne da'ita kamar aljana,ga uban gashi kamar 'yar ruwa,yanda kikaga sadaka yalla yan Niger, haka uwarta take, mijina yaje ya auro min ita saboda bana haihuwa,tana zuwa Allah da ikonsa ko shekara ba'a rufa ba ta haifi Hafeeza,ashe ni aka haifa wa, uwar ta mutu, Shima mijin Namu ba'a dade ba yarasu"
Lami tace" Allah sarki,ashe Zaman bane dorewa bane"
Inna tace"to ya za'ai, kwana yaqare, yanzu duk babu kowa dagani sai Hafeeza sai Qanin Babanta dayake qoqarin yimana hidima lokaci zuwa lokaci"
Hafeeza ta qaraso cikin Rumfar ta Shimfida Sallaya ta kwantar da Fadila,yarinyar kyakykywa da'ita fara.
Lami tayi musu sallama tatafi.
Inna ta kalli Hafeeza tace"Hafeeza banji kinyi waya da saurayin kiba yau, ko kunyi wayar nice bansaniba?"
Hafeeza tace" A a bamuyi waya ba Inna"
Ta Rasulu tace"to saboda me? ki kirashi mana Kiji Yaya yake,sai kice masa dama kira nayi mu gaisa,ina laifi mai sonka ai yafi me qinka"
"Inna idan nakira ba lalle ya dauka ba,jiya da mukai waya dashi ya fadamin yanada uzururruka dayawa,baya zama agida suna asbiti an yiwa qanwar sa aiki a qirjinta,wannan shine karo na uku ana yi mata aikin"
Ta Rasulu tace"Subhanallah,Allah yabata lafiya,inajin qari ne da'ita, a qirji yace anyi mata aikin ko a Nono?"(
Cikin sauri Hafeeza ta zaro idonta tana kallonta sannan tace"nashiga uku na, a a Inna bankai nan ba, ban tambayeshi nan ba"(
littafin kudi ne, Complete document 1k
8621296018
Amina Muhammad
fcmb
tareda shedar biya ta wannan number 08033300034
Amnah El Yaqoub
[5/22, 9:20 AM] El Yaqoub:
MATAR ABBANA
(Luv Story)
Writing By Amnah El Yaqoub
Kuyi following WhatsApp Channel dina domin samun sababbin update
https://whatsapp.com/channel/0029VbBR7naJ93wTuOypQV45
Washegari sassafe suka tashi sukai aikin komai suka gyara gidan sannan suka zauna suna break fast saboda yau sunada gyaran tulawa da safe, Husna de fruit takesha, yayinda Hassana take shan tea mai kauri idonta yana kan d'an qaramin Alqur'anin dake hannunta tana dubawa.
Hajiya Kaka tafuto daga dakinta taga har sun gyara gida, hadaddan falon nasu sai qamshi yake,ta zauna akan kujera tana fadin" Allah de yamuku albarka yaran nan,Allah yakawo muku mazaje nagari,ni bansan meyasa nasa goro a bakina ba, yau Alhamis da yanzu nawuce da azumi na kuma wai sainasa goro,kunga kuwa ai babu Azumi"
Husna ta ajiye Bananar dake hannunta ta kalli kaka tace"Dama fa Kaka ba niyya,inaji lokacin da Hassana ta tasheki Sahur tace ko zakiyi Azumi kikace Anya kuwa?"
Kaka tace" Au haba?, yaushe akai hakan? to bansan anyi ba"(
Husna tace"dama ai bazaki sani ba"
'Dan ladi direba ne yayi sallama falon yakawo wa Kaka qosai kamar yanda yasaba siyo mata duk lokacin datake so,bayan yafita Kaka taja hadaddiyar food flask din tasu ta zamani, tafara qoqarin budewa da qarfinta amma taqi buduwa,ahankali tasaki d'an qaramin tsaki tace" wataran zan 6alla kwano kuwa, haba gaba daya kwanukan mu na arziqi tunna da can kunsa anbayar ankawo mana na zamani gashinan kanaso ka bude kwano amma kayi-kayi abu yaqi budewa me ake da irin wannan rayuwar?"
Hassana tace"qarfi kika Sawa flask din,ana bude abu ahankali amma Kaka ke kullum kin kasa zama 'yar gayu saiki sawa flask qarfi"
Husna tace"kuma fa ba qarfin ne da'ita ba, ko ina abun yake oho"
Kaka ta kallesu kawai ta girgiza kai sannan tabude ahankali, aikuwa flask ya budu,qamshin Qosai da zafinsa ya bugi hancinta, ta dauki guda daya ta saka abakinta tace"dan masifa qosai yakoma uku nera hamsin,kayi magana ace wake yatashi"
Daga Hassana har Husna suna jin qamshin qosan suka matso suma suka saka hannu,qosan yanada dad'i sosai ga wani yaji aqefe me shegen dad'i.