Sashe 15
Matar Abbana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Cikin sauri tafuto daga dakin tashiga dakinsu Hassana, tatashi Hussaina cikin magagin bacci Hussaina ta kamo mata number, sannan Kaka tafuto daga dakin ta zauna afalo da wayar a kunnanta, harta kusa katsewa sannan jamilu ya dauka, cikin muryar sa me yanayin bacci yace"gaye ya ne?"
Kaka tace" Jamilu ba Gayen bane kakar Gayen ce da kanta"(
Jamilu yayi sauri yabude idonsa, yace"Kaka meyafaru? lafiya kuwa?"
Kaka tace"abokinka yana nan rai a hannun Allah, inaga de lalurar sa dayake fama da'ita ne tadawo masa,dan naga yanayin jikin nasa sai ahankali,idan zai iyu de kazo"
Jamilu yace"to gani nan zuwa"
Yakashe wayar yasauko daga gadonsa ya zura jallabiya, yadauki abubuwan da yasan cewa zasu iya buqata, sannan yafuto acikin wannan dare, yanufo gidansu.
Kaka kuwa shayi ta hado masa da lemon tsami aciki, takoma dakin, anan ta ganshi ya kifa cikinsa ya kwanta akan abun nasa, yayinda kansa yake cikin fillo yana yamutsa fuskarsa cikin azaba.
Zama tayi akusa dashi tace"Hafeezu tashi kasha wannan shayin"
Cikin dauriya yace"Kaka mutuwa zanyi bazan iya shaba"
Kaka ta ajiye shayin tace"ni fa duk yanda nake dakai banason ka dinga kawo min zancen mutuwa Hafeezu,gaba dayanku kaida qanannka kuna nan tare dani babu inda zaku tafi ku barni, Hafeezu idan nace kayi aure bakason maganar,yanzu wannan abun dame yayi kama Hafeezu?"
Suna cikin wannan magana Jamilu yashigo, yadora hannunsa awuyan Hafeez yaji babu zazza6i sosai, ya yaye bargon anan yayi tozali da abu me girma, cikin nutsuwa ya maida bargon ya rufe, sannan yahada allura yayi masa, yana tunanin da alamun maganin da Hafeez din yakesha ne yaqare shiyasa har akazo kan wannan ga6ar, kuma rannan yaje asbiti kafin yadawo ya nemi Hafeez yarasa, yabude brief case dinsa yabawa Kaka wasu magunguna yace"gashi, dasafe a bashi wannan yasha, insha Allah zai samu sauqi, yanzu ma idan allurar ta sakeshi zaiji sauqi insha Allah"
Kaka tace"to shi wannan ciwo na Hafeezu babu makari ne Jamilu?"
Dr.
Jamil yayi murmushi yace" Kaka ki masa aure kawai,shine abun nasa zai rissina insha Allah"
Cikin damuwa Kaka tace"to Jamilu mun gode, muje na rakaka qofar gida"
Cikin sauri yace"Haba Kaka, kiyi zamanki tareda driver nafuto, Allah yabashi lafiya"
Kaka ta yiwa jamilu godia sannan tasake gyara wa Hafeez bargon jikinsa, tasake qara masa qarfin esi, sannan tafuto daga dakin, bayan taga bacci me nauyi ya daukeshi.
Cikin ikon Allah zuwa asuba yaji shi kalau yadawo normal babu ciwon cikin ko kad'an,saide kafin yayi sallar asuba saida yayi wanka, bayan ya idar da sallah zama yayi a daki dayake agida yayi sallah ba'a masallaci ba,gari yanayin Haske, yafuto daga dakin kai tsaye yashiga mota yafice daga gidan.
Su Hassana da suke gyaran gidan Kaka tafuto daga dakin Hafeez tana sallallami, Hussaina tace"Kaka me aka miki?"
Hajiya Kaka tace" ku taimakeni jama'ah, ina Hafeezu yashiga ne?"
Hussaina tace" kamarya? haba Kaka kamar wani yaro, may be yafita wani waje"
Kaka ta zauna agefen hannun kujera tace"bazaki gane ba,bashida lafiya jiya kwana mukai bamu runtsa ba"(
Hassana dake goge dining table tace"Kaka yanzu fa kika tashi, na tabbatar sallar asuba ma kin makara, kuma kince kwana kukai baku runtsa ba"
Kaka tace"keni banason jarabar musun tsiya,kiramin shi a wayarki inji ina yake"
*** *** ***
Yana futowa daga gida kai tsaye inda yasaba ganinta yawuce,yau akusa da inda take soya qosai ya faka motarsa, ya zauna acikin motar yana Addu'ah Allah yasa tafuto,yau sosai yakejin qwarin gwiwar yimata magana kamar yanda Babban abokinsa Ib yabashi shawara.
Wayarsa dake gefe tafara qara, yaduba yaga Hassana ce,yasa hannu yakashe wayar baki daya.
Kasancewar hankalinsa yana kan wayarsa yana kasheta,hakan yasa dagowar da zaiyi yaganta awajan tareda wasu Almajirai su biyu, akan idonsa Almajiran suka fara tone duk wata baqar qasa me maiqo data dade awajan, sannan suka debe qasar suka tafi zasu zubar, ita kuma tafara qoqarin motsa manyan dutsinan datake amfani dasu wajan dora abun soya, gabansa ne yafara wani irin fad'uwa, ya lumshe idonsa yana karanta duk addu'ar da tazo bakinsa,fuskarsa babu alamun dariya kokuma sakewa kamar de yanda take kullum, haka yabude motar yafuto,hannunsa zube cikin aljihun wandon sa,kai tsaye wajanda take tsugunne ya tunkara,saida yaje gab da ita sannan yaja ya tsaya yazuba mata ido yana kallonta,fuskarta kamar kullum babu kwalliya ko daya, amma tayi kyau cikin hijabin dayake jikinta.
Jin takun mutum daga gefenta yasa ta dago fararen manyan idonta ta kalleshi,idonsu ya sarqe dana juna, lokaci daya ta tuna haduwarta dashi a asbiti, kuma agabansa ne tabawa Fadila nono,nan da nan tashin hankali ya wanzu a fuskarta, gabanta yafara fadawa,wani irin tsoro ya kamata tanajin tsoron karfa ace mutumin nan ya santa.
Wata tsohuwa ce tazo wucewa ta hanyar,ta kalli Uwar motar datake adane agefe, sannan ta kalli Hafeeza da Hafeez tayi murmushi sannan tace"masha Allah kun dace kuwa"
Cikin sauri suka juya suka kalleta gaba dayansu, ganin yanda suke kallonta yasa tasake magana tayi tunanin Hafeeza suyar qosai tafuto kamar kullum, hakan yasa tace"inma ba saurayin ki bane to me irin wannan motar tunda ya tsaya awannan wajan to yau zakiyi ciniki"
Hafeeza ta kawar da kanta gefe tareda daure fuskarta, ta d'an dage Hijabin ta kad'an tafara qoqarin ture dutsin datake suya zuwa gefe, lokaci daya idon Hafeez ya sauka akan bajajjan hips dinta sakamakon dan janye hijabin datayi, sosai yake kallon qugun nata yakasa dauke idonsa akanta.
Hafeeza ta juyo ta kalleshi nan take ta kamashi yana kallon qugunta,cikin sauri ta saki hijabin nata sannan cikin zazzaqar muryar ta tace"miye hakan?"
Hafeez ya d'an gyara tsayuwar sa sannan yayi gyaran murya, duk da gabansa yana fad'uwa haka ya dake yace"Normal"
Hafeeza tasaki ajiyar zuciya sannan ta dauke idonta daga kansa, tarasa tsaiwar meyake mata awajan,gashi yazuba mata ido sai kallonta yake, gaba daya saita jita wani iri atakure,kafin tagama tunanin datake sai taji Hafeez yace"Dama nace a asbiti....."
Iya abinda yafada kenan,gabanta yayi wani irin luguden faduwa,ta zaro idonta, sannan ta juya ta kalleshi tareda dora d'an yatsanta akan pink lips dinta tace" Kamin shiru"(
Mamaki da wata irin dariya ta kama Hafeez,ya d'an dage girarsa guda daya,yaga alama kamar batason yayi mata maganar asbitin,duba da yanda gaba daya ta rikice sai zare ido take.
Ahankali yatako yaqaraso wajanta ya tsugunna dab da ita kamar jikinsu zai hadu dana juna,har yanzu fuskarsa a daure take babu walwala saide shi a hakan fuskar asake take,hannunsa ya dora akan dutsin da hannunta yake kai,da hannu daya ya juyo da dutsin bai damu da baqin dayake jikin dutsin ba,cikin dakewa dakuma saka qwarin gwiwa yace"ina zankai miki?"
Cikin sauri ta girgiza kanta gabanta yana fad'uwa,kusancin nasu yasake takura ta,bata ta6a kusanci da namiji har hakaba,ahankali tadan ja baya ta matsa daga kusa dashi,gashi taga layin nasu shiru kamar an hana kowa wucewa,Hafeez ya kalleta yaga yanda gumi yake yanke mata agaban goshinta,yazubawa d'an qaramin bakinta ido yana kallo,sannan ya maida idonsa kan gashin idonta masu ban sha'awa, yaga yanda take matsawa daga kusa dashi,ya d'an ta6e bakinsa, cikin wata irin muryar rada wadda sai iya su biyu shida ita ne zasu iya jin abinda suke fada yace"ina son qosai,dayawa nakeso kiyi,sannan kiyimin sadaka dashi, but... wannan yarinyar ta hannunki a asbiti...."
Gaban Hafeeza yasake faduwa,taga alamun mutumin nan tona mata asiri yakeson yi,cikin sauri tafara kad'e hannunta zata tashi tabar masa wajan.
Hafeez yaga alama kamar so take ta gudu tabar wajan,gashi yanason suci gaba da magana, bayason tatafi batare daya sake jin zazzaqar muryar ta ba, hakan yasa cikin sauri yaciro dala dari daga aljihun wandon sa yabata tare da fadin "gashi, kiyimin qosai, kuma kibani canji"
Bata kalli kudin dayake bata ba,so take kawai su rabu ko zata samu yadena tuna mata zancen asbitin nan,cikin sauri ta bude yar qaramar fos din dake cinyarta,Hafeez yana kallonta yaga akwai sababbin kudi acikin fos din miqaqqu.
sai lokacin ta dago kanta ta kalli kudin dayake bata,taga dala ce, kuma tasan cewa dala dari de ba qaramin kudi bane, cikin sauri ta girgiza kanta tace"ni banda canji"
Hafeez ya kalli d'an qaramin bakinta sannan yace"kamarya? baga kud'i nan ina gani ba?"
Hafeeza ta daure fuska sannan ta kawar da kanta gefe tace" sababbin kudi ne,tarasu nake saboda bikin wani yayana"
Cikin dabara yace"inane gidanku sai inzo in kar6i canjina?"
Ahankali tajuya ta masa wani kallo sannan tace" kaga riqe kudin ka kawai,zanyi ma sadakar kyauta"
Cikin sauri shima yace"bangane ba? ni banason kyautar ki,kawai ki riqe kudin nan kiyi qosai kiyimin sadaka kuma ni inason canji na, canji na kawai zaki bani"
Hafeeza tasaki ajiyar zuciya sannan ta lumshe idonta tabude su tareda juya idanuwan nata cikin wani irin salo, hakan datayi ba qaramin tafiya da imanin Hafeez tayi ba, ta matsu yatafi, hakan yasa tace"ka riqe kudin ka,zanyi qosan da kudi na, nikuma zanzo na kar6a awajanka"
Cikin wani irin jin dadi yace"Really?"
Cikin zaquwa yatafi tagyada masa kanta,ahankali yajuya cikin motarsa yadauko mata wani Kati wanda address din gidan yake jiki ya ajiye mata agabanta, daga haka bai sake cemata komai ba yajuya yashiga motarsa yatafi, sai alokacin tasaki wata irin ajiyar zuciya, tadafe kanta daya fara yimata ciwo,sai yanzu tayi dana sanin abinda ta aikata a asbiti,gashi yanzu wannan bawan Allah yana bibiyarta,kuma duk yanda akai da alama yasanta, idan be santa ba tayaya zai zo har inda take sana'ah?
Cikin tashin hankali tatashi tabar wajan ko ta kan dutsin datakeson janye wa bata biba,kai tsaye ta nufi gidan Maman Fadila, adede lokacin Baban Fadila yafita kasuwa , ita kuma Maman Fadila tana zaune tana karyawa da taliya da Manja.
Hafeeza tana qarasowa ta zauna awajan tare fashewa da wani irin kuka,sosai take kuka harda shashsheka.
Maman Fadila tafara Salati sannan tatashi ta wanko hannunta ta zauna agefen Hafeeza tace"Hafeeza keda waye? menene ya hadaki da Inna yau kuma?"
Hafeeza tayi shiru taci gaba da kuka.