Sashe 17
Matar Abbana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Awajan ta tsugunna tana dana sani meyasa ma tace masa zatazo ta kar6i kudin awajansa? kawai sai taje wajansa tace kudin nazo kabani? to ai kuma dama ta fada masa cewa zatazo dinne kawai dan ya rabu da'ita.
Gabanta banda faduwa babu abinda yake, haka ta dauki hanya tafara tafiya tana tunanin haduwa dashi, saida tayi Nisa sosai sannan ta tuna takardar address din gidan daya bata tana gida, haka ta juya tasake komawa gida har lokacin kawu Hamza yana nan Suna tattauna yanda za'a fara yi musu gyaran gidan shida Inna, cikin kayanta ta duba ta dauko takardar sannan tasake ficewa,kai tsaye tanufi hanyar gidan tana Addu'ah cikin ranta, saide idan ta tuna shawarar Maman Fadila saita danji sauqi aranta.
Tunda ta shiga layin unguwar gabanta yasake tsananta faduwa ganin manya manyan gidajen dasuke layin,number gidan tasake dubawa a katin dake hannunta ahankali taci gaba da takawa har tazo gaban wani hadadden gida,gabanta yasake yankewa ya fadi cikin sauri taja da baya saboda gidan ya bata tsoro sosai, can gefe ta matsa jikin wani gida ta tsaya tana jira ko Allah zaisa yafuto su hadu, batare data shiga gidan ba.
Kusan minti ashirin tana tsaye,gashi unguwa shiru tsaf za'a sace mutum batare da an sani ba,hakan yasa takoma bakin get din gidan, hannunta yana rawa tafara nocking get din gidan.
Babu 6ata lokaci taga anbude qofa,danladi direba ya kalleta, saiya ga kamar ya santa, amma kuma ya manta inda yasanta, cikin rashin sani yace"daga ina?"
Cikin zazzaqar muryarta tace"wajan...wajan...."
Gaba daya saita rikice tarasa sunan wa zata kama,Shikuma danladi ganin tarasa abun fada yasa ya rufe qofar Yakoma ciki.
Cikin damuwa tadafe goshinta,tasake kallon get din gidan, har zata sake nocking saita dakata tafara tambayar kanta idan yasake budewa to wajan wa zatace tazo?
Hakan yasa ta Yanke shawarar juyawa takoma gidan Maman Fadila idan Allah yasa ta dawo saita ari kudi awajan ta tabawa Inna, Shikuma idan suka hadu saiya bawa Maman Fadilan.
Cikin kwanciyar hankali ta juya tatafi, bayan zuciyarta ta gama nutsuwa da shawarar data yanke.
Acikin gidan kuwa Hafeez yana zaune shida Hajiya Kaka afalo,sanye yake da wando three quarter iya gwiwar sa, sai Riga marar hannu hakan yasa murdaddan dantsan sa yasake bayyana, waya yake qasa qasa,yayinda Hajiya Kaka ta kasa kunne tana so taji dawa yake wannan wayar qasa qasa kamar yana magana da mace, juyowa yayi ya kalleta tareda kashe wayar yace"tona kashe,saiki dena meqomin kunne"
Hajiya Kaka ta harare shi,ko kunya kuma saita matsar da kunnen ta daga kusa dashi din.(
Ajiyar zuciya ya sauke yace "ina yaran nan suke?"
Kai tsaye Hajiya Kaka tace"na aikesu suje su nemo min qosai,dan ladi Naso intura saboda dama shine yake siyo min, kuma baya nan"
Hafeez ko tanka mata baiyi ba ya tashi yafuto daga falon, kai tsaye wajan me gadi yanufa yace"Baba yauma wata yarinya 'yar buzuwa haka ba tazo nemana ba?"
Baba Megadi yace" ito,gaskiya yanzu de babu, amma danladi yafuta yanzun nan,kafin ya tafi yacemin in sake kula da qofa sosai saboda dazu wata yarinya tazo yana tunanin irin larabawan nan ne Yan gudun hijira suka shigo gari"
Tun kafin yagama magana Hafeez ya runtse idonsa, baqin ciki ya kamashi, cikin 6acin rai ya kalli Megadi yace"kace danladi driver ya koreta?"
Baba Megadi yace" tabbas haka akayi ranka ya dade,tuba nake yalla6ai wallahi na zaga toilet ne alokacin"
Cikin damuwa Hafeez yace"amma ba danladi ba ko dan litinin ne aibe kamata ku koreta ba ko?"
Baba Megadi yayi shiru,tabbas duk yanda akayi Hafeez din yana cikin damuwa akan rashin haduwar sa da yarinyar duba da yanda tun jiya yake faman tambaya ko tazo.
Cikin bacin rai Hafeez ya buga qafarsa aqasa tareda juyawa ciki kamar zai fashe da kuka.
Kai tsaye dakinsa yashiga zai dauko car key yafita ko Allah zaisa ya ganta.
Hafeeza kuwa tana cikin tafiya taji anja hijab dinta tabaya,tana juyawa taga hassana da Hussaina Yan ajinsu, lokaci daya ta saki murmushi har dimples dinta suna futowa, Husna tace"Hafeeza dama ana ganinki?"
Kafin tayi magana hassana tace"aikuwa tunda kikazo layin mu dole kizo muje gidanmu ku gaisa da Kaka"
Hafeeza tace"zan dawo daga baya yanzun ne...."
Tun kafin ta qarasa magana Husna tace"yanzun me? gaskiya ki juya muje inba haka ba da daddare zakiga kunama"
Hafeeza tayi murmushi tajuyo suka taho tare dasu hannun ta yana cikin na Husna.
Tunaninta begama tsinkewa ba saida taga gadan-gadan sun nufi gidan da wannan mutumin yabata address, lokaci daya kanta ya kulle,me hakan yake nufi? dama gidansu Husna ne nan? menene hadinsa dasu? tana cikin wannan tunani taga anbude musu gidan cikin girmamawa saide wani ne daban yabude musu yanzu, ba wanda yabude Mata bane dazu.
Gabanta ne yasake tsinkewa bayan sun shigo cikin harabar gidan, ba qaramin tsorata tayi da gidan ba, saboda a tarihin rayuwar ta bata ta6a shiga gida mai kyan wannan ba,su Husna sai tsokanar ta suke suna mata magana amma hankalin ta begama kwanciya da gidan ba, kokadan bazaka ce gidan hausa wa bane saide turawa.
Suna shiga falon wani irin qamshi me sanyi ya daki hancin Hafeeza,ga sanyin esi, ta nutsa qafarta cikin capet tana jinjina irin wannan daula dasu Hassana suke ciki amma koda wasa basuda girman kai da dagawa irinna wasu daga cikin Yayan masu kudi.
Hajiya Kaka tana ganinsu tace"yana ganku hannu wayam"
Hassana taja hannun Hafeeza suka qarasa wajan Kaka tareda fadin" Kaka ga qawarmu Hafeeza, wadda ta samu kyaututtuka ranar da mukai sauka? kin tuna?"
Hajiya Kaka tayi shiru tatafi tunani sai can tace" natuna mana,ba itace me zaqin muryar nanba? wacce kwana ki kuke cewa dinki ya muku yawa saide qugun Hafeeza?"(
Cikin sauri dakuma son basarwa Husna tace"Haba Kaka, yaushe akai hakan?"
Cikin tantama Hajiya Kaka tace"au to kode ba'ita bace? tonima de bansan anyi hakan ba"(
Hafeeza tayi murmushi ta kalli Hajiya Kaka sannan tace"kuma kika fada?"
Hassana tayi dariya tace" bakisan Kaka ba kenan"
Tajuya ta maida kallon ta zuwa wajan Kaka sannan tace"Kaka bamu Samo miki qosan ba, ance wacce takeyi din waita daina"
Gaban Hafeeza daya Yanke ya fadi ba tasan lokacin data zura hannun ta cikin hijabi ta dafe qirjinta ba, wajan ta sukaje neman qosai kenan?
Bata gama tunanin da take ba taji Kaka tana cewa"ai tunda wancen baqin miskilin yace ta daina nasan za'a Rina, bari yafuto yau duk inda qosai yake saiya nemomin shi"
Hafeeza ta danyi murmushi sannan tace"ina kwana Kaka?"
Cikin Jin dadi dakuma yaba hankalin yarinyar Kaka tace" lafiya kalau Hafeeza,kinada hankali da nutsuwa Allah yasa kina jin magana ba kamar takwaranki ba"
Kan Hafeeza ya daure tarasa gane waye takwaranta, sai tayi murmushi kawai ba tace komai ba.
Husna ta kawo lemuka da ruwa da meat pie ta ajiye agaban Hafeeza sannan ta bawa Kaka wayarta tana cewa "Kaka kinga dinkin da telan mu yayi mana, ankon gidan Uncle Shu'aibu,ni kwata kwata dinkin bemin ba"
Hajiya Kaka tayi zooming photon dinkin tagani sannan tabata wayar tace"ai anko ne, koma Yaya ne kunde saka,kada yan'uba suce baku saba"
Tajuya ta kalli Hafeeza cikin salon jan magana tace"koba haka ba Hafeeza?"
Hafeeza tayi murmushi tace"hakane kam"
Hajiya Kaka tasake cewa"ko kin iya dinki su dinga kawowa kinayi musu?"
Hafeeza tayi murmushi tace"A a Kaka ban'iya ba"
Hajiya Kaka tace"Au to! jinake kin iya,Nima da sai in dinga bawa HAFEEZU nawa yana kawo miki, amma gaskiya ni in dinkin Zaki min ma saide kimin irin wanda kike sakawa,koba haka ba? saboda Idan zanzo gidanki inci kwalliya ta dashi inzo ko Allah zaisa mijin ki ya yaba"(
Hafeeza tayi murmushi,ta lura matar tanada barkwanci sosai dakuma iya zama da mutane,cikin murmushi tace"Kaka ai abunda zan d'inga mikin ma shine zai siyo miki da kudinsa"
Hassana ta bude lemon da Husna ta kawowa Hafeeza ta zuba Mata a cup sannan ta tura Mata gabanta tana cewa "inde Kaka ce to zata qwace miki miji kuwa"
Hajiya Kaka ta miqe zata shiga kitchen ta kalli Hafeeza tace"kici dan abun ta6awar 'yar nan,bari na baku waje ku danyi gulmar samarin ku"
Gaba dayan su dariya suka saki,Husna ta gyara zama tace"Hafeeza bakici komai ba"
Sai alokacin ta dauki meat pie din taci dan kadan, ta ajiye sauran.
Cikin nutsuwarta ta kallesu tace"bari in tafi gida,kada a nemeni"
Husna ta Harare ta tace"har wani? daga zuwan naki? gaskiya ki tsaya muyi fira tukunna"
Hassana tace"Hafeeza ya samari? nasan suna nan lodi-lodi yaushe zamusha biki?"
Hafeeza tayi murmushi tace"wa? a a wallahi nima bansani ba"
Hassana tace" mukam wallahi Gara ayi mana auren mu,mazaje suna futowa zamuyi wuf, mu shige"
Hafeeza tayi murmushi tadan saki jikinta ganin Kaka bata wajan, tace"to wanne irin mazaje kuke so? ance yawanci yanbiyu sunfi son su auri mazaje suma Yan biyu"
Husna tace"hakan ma yanada dadi,ko banza kasan cewa kana tareda yar'uwarka, amma kinga ai abun dace ne, nide gaskiya inason namiji mai irin halin Yaya HAFEEZ, bana son hayaniya"
Hafeeza tanajin sunan gabanta ya fadi, tun kafin tayi magana Hassana tace"maganar gaskiya nide duk wanda nasamu banda za6i, kefa Hafeeza?"
Tafadi maganar tana kallon Hafeeza.
Adede lokacin Hafeez yabude qofar d'akinsa zai futo fuskar nan tasa ahade kamar hadari,har yanzu taqaicin rashin haduwarsa da'ita yake, saide sako kan da zaiyi zuwa falon idonsa ya sauka a kanta, gabansa yayi wata irin faduwa, cikin sauri yajuya da baya, ganin babu wacce ta lura da budewar qofar dakin nasa acikin su,saide bai maida qofar ya rufeta duka ba, yana iya hangosu, sannan kuma yana iya jiyo abinda suke magana akai.
Hafeeza kuwa zuciyarta daya tadan juya fararen idonta sannan tatafi duniyar tunani tana hango siffar saurayin ta Gaddafi acikin idon zuciyar ta sannan tace" inason namiji hafizin Alqur'ani,ban damu da rashin kudinsa ba,saide inaso ya kasance me qirar jarumai,me murdadden dantsan hannu"
Cikin sauri Hafeez dayake Jin firar ya kalli dantsan hannun sa,mamaki yagama kashe shi dama tana magana haka? hakan yana nufin batada aure kenan.
Hafeeza taci gaba da fadin"miskili wanda baya son hayaniya,kuma kyakykywan gaske"
Wannan Karon ma cikin sauri ya kalli fuskar sa ta screen din wayar sa dake hannun sa,har wani gyara sumar Kansa yake,gaba daya hankalin sa ya tafi zuwa gareta,besan ma yana wannan dube duben ba.