Sashe 13
Matar Abbana Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Washegari yashirya tsaf,cikin shigar manyan kaya, shadda yasaka milk color tareda babbar riga yayi bala'in yin kyau, idonsa akan madubin dakinsa yana kallon yanayin fuskarsa datake cikeda miskilanci dakuma rashin fara'ah,Agogo ya daura a hannunsa me cikeda gargasa sannan ya sake gyara zaman hularsa yafuto daga dakin, ko Kaka bai fadawa inda zaije ba, yade yimusu sallama yafita, yana zuwa compound Danladi driver ya daukeshi kai tsaye suka nufi Niger State, jihar data kasance asalin sa, sannan kuma tushensa.
sai wajan sha biyun rana suka qarasa,tunda suka shigo layin gidansu gabansa ya tsananta faduwa,kansa yafara sarawa, ko kad'an bayason kallon unguwar saboda tana tuno masa da abubuwa marasa dadi dasuka faru dashi shekarun baya,hakan yasa ya lumshe idonsa har saida yaji motarsu ta tsaya alamun sunzo inda ya kamata su tsaya.
Ajiyar zuciya ya sauke, yayinda ya bude idonsa akan wani madedecin gida me qatuwar rumfa wadda take cikeda Almajirai kowa da allo a hannunsa sunata faman karatu, daga can gefe guda akwai wani babban mutum a zaune kansa da nadin rawani irinna malamai yana karanta Alqur'ani, da alama shine Malamin wannan Almajiran.
Doguwar Rumfar dasuke zaune acikinta tana malale da lailayar siminti, saide kana ganin yanayin ginin gidan zaka tabbatar cewa gida ne irin na da can, babu abinda aka sauya na gidan saide yar kwaskwarima da'ake yiwa gidan akai-akai, sa6anin gidan da yake zaune akano shida kaka da 'yanbiyu bazaka ce ma gidan acikin Nigeria yake ba saboda tsabar tsaruwar gidan.
Danladi ne yayi sauri yazo ya budewa Hafeez motar, ahankali yazuro qafafunsa yafuto, gabansa banda fad'uwa babu abinda yake ta faman yi, yana futowa idon Almajiran dasuke karatu yakoma kansa, kowa ya bishi da kallo, har zuwa wannan lokacin wannan malamin dayake zaune agefe bai dago idonsa ya kalli motar data tsaya a qofar gidan saba,asalima hankalinsa yana kan paper datake hannunsa yana karantawa cikin kwanciyar hankali, adede lokacin daddadan qamshin turaren Hafeez yacika wajan, cikin nutsuwa yasamu waje gefen malamin ya zauna sannan ya sunkuyar da kansa qasa, malamin bai kalleshi ba har saida ya kammala karanta paper Alqur'anin datake hannunsa, yadago idonsa ya kalleshi, karaf idonsa ya sauka agefen wuyan Hafeez, inda ya hango zanen tattoo daga gefen wuyan nasa, ahankali ya girgiza kansa batare da yace uffan ba, Hafeez yadago idonsa shima ya kalli Malamin, har kullum fuskarsa tana nan yanda take cikeda haiba da kamala irinta malinta, idonsa ya sauke qasa sannan yace "Barka da wannan lokaci BABA"
Malamin da Hafeez yakira da Baba yayi ajiyar zuciya sannan yace"Kana lafiya?"
Ahankali Hafeez ya gyada kansa, sannan yace"Alhamdulillah"
Daga haka babu wanda yasake magana a cikinsu, ko baqo ne yazo wajan, nan take zaisan cewa ko kad'an babu jituwa,fahimtar juna,soyaiyar d'a da uba atsakanin su.
Awannna halin Danladi ya qaraso ya tsugunna awajan tareda kallon malamin wanda ya maida hankalinsa kan karatun dayake, yace"Malam ina wuni,mun sameku lafiya?"
Malam ya gyada kansa ba tareda ya amsa ba, saida yasake kammala paper hannunsa sannan ya amsa gaisuwar Danladi.
Hafeez ya qarewa Almajiran dasuke karatu kallo,yatuna shekarun baya lokacin da shima yake shiga cikinsu suyi karatu tare, cikin nutsuwa yadawo da kansa qasa yana tunanin ko Malam zai tambayeshi Hassana da Hussaina,saide har yayi yagama zamansa uffan malam bai sake cewa ba, bai tambayi Kaka ba, haka suma su Hassana dasuke tsatsonsa ko harafin H bai kamaba bare ya tambayi lafiyar yaran.
Ahankali Hafeez ya sauke ajiyar zuciya sannan yasaka hannunsa acikin aljihun Babbar rigar sa ya dauko kudi yan dubu-dubu dami uku,ya ajiye agaban malam sannan ya kalleshi yace"zan koma"
Malam baice dashi uffan ba, saide ya gyada masa kansa alamun amsawa,amma ko addu'ar Allah Yakiyaye hanya bata futo daga bakinsa ba,Shima Hafeez bai sake magana ba yamiqe yanufi motarsa ya tsaya yana jiran Danladi dayake jibge kayan abinci da su katan katan din taliya a qofar gidan, saida yagama jibge uban kayan abincin sannan yaciro kudi a aljihun sa dami daya na yan dubu daya yafara bin Almajiran yana raba musu, wanda hakan umarni ne daga Hafeez tun suna hanya yabashi kudin yace yaraba wa yaran sadaka.
Ahankali malam yadago kansa ya kalli Hafeez dayake tsaye can ajikin Mota, suka hada ido, saide kuma cikin sauri kowa ya janye idonsa, Hafeez yayi sauri yabude mota yashige ko kallon hanyar dazata kaishi cikin gidan beyi ba, daga 6angaren malam shima yana tunanin Hafeez din zai shiga cikin gidan su gaisa da mutanan ciki dakuma MAMA, amma saiya ga sa6anin haka, domin kuwa Hafeez kam yana shiga motar ya lumshe idonsa, hanyar cikin gidan ma baisan gani bare yakai kansa ciki har su had'u da MAMA.
Bayan Danladi yagama rabar da kudin ya qarasa yayiwa malam sallama sannan yashiga yaja motar suka bar qofar gidan.
Kai tsaye gidan Aunty suka nufa, yana qoqarin shiga gidan yana turawa abokinsa I.b saqo ta waya, gidan nata shiru alamun babu kowa yaran sun tafi makaranta, kansa tsaye yashige har cikin falo kamar yanda bashida shamaki da gidansa na kano,wata mata ce a tsaye afalon tana qoqarin ajiye magungunan akan wata loka, aqalla zatayi shekaru Arba'in, qamshin turaren da ta riga tasan na waye shita shaqa, cikin sauri ta juyo idonta ya sauka a cikin na Hafeez, lokaci daya fuskar ta ta washe bakinta yabude, cikin tsananin farinciki tace"Hafeez!"
Shima daga nasa 6angaren murmushin sa mai aji yasaki,tareda bude mata hannayen sa, cikin sauri ta qaraso ta shige qirjinsa, lokaci daya suka saki ajiyar zuciya, daga nata 6angar
en hawaye takeyi na farincikin ganinsa, yayinda shikuma ya lumshe idonsa yanajin kamar wata damuwar sa zata ragu sakamakon ganin Auntyn nasa, sun jima ahaka kafin su koma kan kujera su zauna, hannunsa cikin nata ya kalleta da kyau yace"idan zan koma wajan aiki ya kamata ki shirya mutafi, likita saiya dubaki acan"
Cikin jin dadi tace"haba Hafeez, likitocin nan ma suna iyaka kokarin su,kuma ina shan magani, yanzu ma abinda yasa jikin nawa yatashi, gurasa ce nagani tabani sha'awa sainaci, daga nan naji yanayin jikin nawa yana sauya wa"
Cikin sanyin jiki yace"Aunty nifa ciwon suger dinnan yana tsorata ni gaskiya, dan Allah kubar garin nan keda mijinki mu koma Kano zanfi kulawa dake yanda yakamata,yanzu kinga bansan bakyajin dadi ba, Shima kuma Ib ya 6oyemin,hankalina yatashi akan hakan,shiyasa yau nashigo"
Murmushin qarfin hali tayi sannan tace"naji sauqi Hafeez,ka kwantar da hankalin ka,cuta aiba mutuwa bace, kaje gida ne?"
Ahankali ya gyada mata kansa, daga haka bata sake yimasa tambaya akan yashiga cikin gidan ko be shiga ba, saboda tariga tasan cewa abu ne me mutuqar wahala Hafeez yasa qafarsa acikin gidan.
Cikin jin dadi ta tashi takawo masa fruit, sannan ta zauna tasake kama hannayen sa ta riqe, tace"Hafeez ina yanmata? kana zaune kaqi kayi aure ko?"
Ahankali ya zame yadora kansa akan cinyarta tareda lumshe idonsa, maganar yanmata datayi masa tasa ya tuno Hafeeza,yanaso yafada mata damuwar sa amma yakasa, yanaso yayi mata batun Hafeeza amma yarasa qwarin gwiwar hakan.
*** *** ***
Bayan an idar da sallar azahar Kawu Hamza yanufi gidansu Ma'aruf akaro na biyu, bayan megadi yayi masa sallama da Ma'aruf yabashi hannu suka gaisa,kunya ta kama Ma'aruf saboda bai yiwa Hafeez maganar da sukayi shida kawu Hamza ba, daga gefe guda kuma yana mamakin yanda kawu Hamzan yadawo, yana mamakin yanda uba zai dage yana nemawa yarsa miji kamar mazaje sun qare,saide a yanda yaga kawu Hamzan ya dage ya tabbatar da cewa lalle da gaske yakeson hadin.
Kawu Hamza ya kalli Ma'aruf yace"kaga nadawo ko?, dama zan tambayeka ne inji Yaya kukai kaida abokin naka? ya amince da maganar da nazo da'ita kuwa?"
Ma'aruf yayi murmushi yace" wallahi Baba nayi laifi,saboda har yanzu banyi masa maganar ba, ni a yanda nakeso inaso ne in sameshi fuska-da fuska muyi maganar, amma insha Allah yau zanyi masa maganar"
Kawu Hamza yayi murmushi yace"to ba laifi, ka sameshi kuyi maganar, saboda harga Allah ni hankali na ya kwanta da yaron,naga yanada nutsuwa sannan babu ruwansa da samari masu rawar kai, sannan nima nasan halin yata zatayi masa biyaiya yanda yakeso"
Ma'aruf yayi ajiyar zuciya yace" insha Allah zanyi masa maganar,duk yanda mukai zakaji"
Kawu Hamza yabashi hannu suka sake gaisawa sannan yayi masa sallama yatafi.
*** *** ***
Agidan Aunty suka wuni,shida kansa yashiga kitchen dinta yayi musu girki, yaranta suna dawowa daga makaranta gida ya kacame da hayaniyar su, shida yaran nata kana gani zakasan cewa ba qaramin sabo sukai dashi ba, tare sukaci abincin cikin jin dadi da walwala, rabon sa da yaji nutsuwa irinta yau harya manta, daga qarshe Danladi ya dauki yaran sukaje shopping kowa taza6i abinda takeso,bayan sallar azahar yayi sallama da Auntyn bayan yagama jiqata da kudad'e dakuma jan kunnanta akan ta kiyaye abubuwan da zata dinga ci, ta kuma dage akan shan magungunan ta.
Daga nan gidansu Ib sukaje, inda ya gaida mahaifin Ibrahim din, sannan yayi musu ihsani, yafuto, shida Ib suna zaune abayan motar, yayinda Danladi yake tuqi ahankali ganin sun kusa zuwa inda zasu sauke Ib din, sukuma su dauki hanyar kano, saida sukaje inda Ib zai sauka sannan Danladi yafice daga motar ya barsu su kadai ko zasuyi wata maganar.
Yana fita kuwa Ib ya kalli abokin nasa yace"meyake damunka ne?
Naga kasake zama silent ko da wata damuwar?"
Dan qaramin tsaki yayi sannan yace"rashin lafiyar nan ta Aunty UMMI tana damuna, inaso in dauketa but naga kamar tana son zama agarin nan,Bansan Yaya zanyi ba wallahi "
Ib yayi murmushi yace" banda abunka Hafeez Yaya mata tana zaune da mijinta,sannan mijinta yana aikinsa zaka raba shi da inda yake ka maida su kano? kabarta anan tareda yaranta, kuma naga ai jikin nata ma da sauqi sosai"
Ajiyar zuciya Hafeez ya sauke yace"itama haka tace"
Ib yayi murmushi yace"bayan haka sai menene yake damunka?