← Book details Kyalkyalin Kauna Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 93

Sashe 7

Kyalkyalin Kauna Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ammi tayi tace je inada shi ki dauka saiki maza kiyi wanka Babanki ya saukeki a shagon Maman Intee kinsan yau za amai karin girma kada ku sashi latti cikeda murna Yasmeen tace karin girma Ammi ? Ammi tace ohh uwar bacci natuna jiya dayana fadi kinyi nisa a jam iyanna naki kyalkyacewa da dariya tayi kana ganin yanda yake kasan tana bala in son Mamanta hararanta Ammi tayi tace amaida Babanki CP saiki tayashi da addu a kina dariya awajen tsalle tayi tace Alhamdulillah naji dadi Allah taya Baba riko cikeda farinciki tafito daga kitchen din tawuce falon Maman su inda Baba yake zaune yana duba jarida sallaman ta yasa yadago kanshi yakalleta hakan yasa takarasa wajen kujeran dayake tsugunnawa tayi adan kunyace tace Baba Allah sanya alheri murmushi yamata tareda maida kanshi kan jaridan dayake hannunshi itakuma tawuce tadauki bread din da Ammi tasa tazo tadauka, bin bread din Baba yayi da kallo ahankali yace zai isheki ? Gyadamai kai tayi dasauri tace eh Baba wucewa tayi tafito daga dakin zuwa dakinsu inda taga Sa a da Farida nashan koko da kosai da aka soya, zama tayi gefen Sa a dake watsa mata harara saikuma kaman wacce ta tuna wani abu tace Yasmeen kinsan Fahad yace yau zamu hadu narasa a ina zance muhadu wlh tsoron Baba nake zaro idanu daga Farida har Yasmeeen sukayi suna kallonta, da sauri Yasmeen dan ita bata kaunar fada ko masifan Baba saisa har tsoro take tayi laifi tace nidai baruwana kema kinsan Baba yahana muyi tadi bayace idan wani nasonka kace yazo gida ba wani kalan mugun harara Sa a tamata tace ni saisa wlh nafison Farida dudda she s just 15 amman tafiki hankali da mutunci da rufama yar uwanta asiri, sokike Fahad yazo Baba yakoramini shi yaro dan masu kudi Baban ku daya iya firgita mutane Allah yasawake wlh ko zan bari yazo yaga su Baba saina tabbatar yagama fadawa soyayyata yanda kome Baba zaimai ba gudu baja da baya shidai yanasona tai shiru sannan takalli Farida dake kallonsu tace Farida kinji bani shawara kaman jira Farida take dan ita arayuwan ta tanason taji ana hira da zancen samari dasauri tace ba yau za ama Baba karin girma ba, bazai dawo da wuri ba, kibari yazo amman saiku tsaya tabayan layi ko Anty Yasmeen ? Dasauri Yasmeen takalli kanta saikuma ta nuna kanta ita hiran kadaima tsoro yake bata tace ? Akufule Sa a tace a bakeba da gatari ake magana, kinga Farida kada ki kara sata a zancen mu ita ta sani tsoron Baba saiyasa kin kasa auruwa saisa har yau ko me babur baitaba cewa yana sonki ba adan tsorace Farida dake kallon Yasmeen itama tace kuma Anty Yasmeen duk kin fimu kyau wlh haka har yan unguwa ke cewa, wani kalan sweet skin gareki coffee coffee, butter butter dake hararanta Yasmeen tayi ta tashi batare datace musu komiba tashiga cire kaya ta daura zani tafice wanka taje tayo sannan tadawo, gaban sip nasu taje taciro wata atampa mai kyau brown da aka mata dinkin doguwan riga saka sannan tadauki jakan zuwa aiki school nasu tadawo wajensu tazauna handout taciro tamikama Sa a tace dan Allah karanta mini page 10 Ya Sa a mutumin yace shi baya fadin ranan test kuma kinga gobe Friday zani school fizge handout din Sa a tayi tace ni kinaso na taimakeki amman ke baki taimako na dan murmushi tayi daya karamata wani kalan kyau tace to kiyakuri bazan karaba, ba Farida tace yazo bayan layi ba, ita saita miki gadi koda Baba yazo saita miki flashing koda wayan Mama ne sai alokacin Sa a tai murmushi sannan tabude page 10 din tashiga karanta mata tai shiru tana saurare anatse, daidai Sa a tazo wani gaba da sauri Yasmeen tace Ya Sa a yimin spelling phe dasauri Sa a tace peripherals wai? Gyadamata kai Yasmeen tayi da sauri tana ciro wani byro daga jakanta, Sa a tace P, e, r, i,p,h,e,r,a,l,s palm nata Yasmeen ta kalla data rubuta words din ahankali tashiga maimaitawa da baki kafin takulle idanu tana kokarin karanto spelling din. P, E R E P E ahankali Farida dake kallonta tace P, H ne Anty Yasmeen kafin E din ahankali Yasmeen tabude idanunta takalli tafin hannunta, ajiyan zuciya tasauke dayasa Farida taji idanunta sun kawo kwalla tashi tayi dasauri takwashi cups na kokon dasukasha kawai tafito daga dakin, Yasmeen nabata tausayi tun tana yarinya tana yar karama lokacin tana ganin yanda Ammi ke bugun Yasmeen idan ana koyamata homework agama fada mata ta manta har Ammi tagaji tadena dukanta, gashi Anty Yasmeen tun tana yarinya lokacin yarinya ce mai zuciyan so takoya babu wurin wanda bata zuwa agidan nan yakoya mata karatu but still, su Baba, su Baffa su yayinsu, hatta su Yaya da bama suyi makaranta ba suma sun koyar da Yasmeen ABCD but still, Yasmeen bata taba cewa sabida ta girmeta baratazo takoya mata ba, har yau so da dama zatazo tasameta tabata handout takaranta mata, yanda Yasmeen ke wahala da karatu abin na mata gwarama tadaina makarantan to dole ne karatun bayahuden gwara tacigaba da zuwa wajen Maman Intee koyan girke girke da Islamiyya abinta wannan bokon ba dole dan bakar wahala kawai Anty Yasmeen kesha. Wasu hawaye masu zafi guda biyu ta goge kafin ahankali tadauke bucket din tawuce bayi. Kusan sau uku Sa a takaranta mata page 10 din kafin tabata handout din tace to hada bakin ki karanta naji, kinga kun kusan fara first semester exam gashi bakince malamai kusan 4 ke muku course din ba kuma kowanne da nashi Yasmeen yaya zakiyi wannan na mutum dayane cikinsu yanzu kike page 10, wannan page 10 din nan kadai zai iya daukanki 10days kafin ki gama iyawa ki gama gane spelling da komi wai karatun nan dole ne, ki hakura ki barshi, karatu is not for u Allah bai baki kwakwalwan bane ba kawai, ki sami Baba ki sanar dashi kada kiji tsoro wlh mayun gray eyes nata Yasmeen tazuba ma Sa a tanajin wani abu nataso mata daurewa tayi ahankali tace nidai in karanta kiji mini ? Ijiyan zuciya Sa a tasauke zuciyanta namata badadi sabida yanda taga Yasmeen na wahala da karatu tace karanta naji to tunda ke Allah yamiki bakin zurfin ciki anatse Yasmeen tafara karatun, yanda take hada words da kyar tana fadi zaka dauka yar primary 1 ce, layi biyu tayi masu kyau takakare at the 3rd line wajen kalman Jahillya period, tashi Sa a kawai tayi tace nima zanje nai wanka inada lectures 11 gwarake Baban ki yanzu zai wuce dake ya kaiki ni saidai nahau mota, better think about abinda nafada miki and meet Baba da maganan binta da kallo Yasmeen tayi harta fice daga dakin kafin ahankali tadawo da kanta takalli littafin idanunta kan kalman data kasa fadi, yatsanta tadaura kan Ja din ahankali tace ..no ja is JAAAA tai shiru tana kallon Hi tace Hi, kaman hi din hello kenan yauwa ai nasan hi shiru tayi tana kallon LI, itafa duk words dazata gani ta iya karantawa to tazauna ta haddace spelling din ne tasan yanda ake kiran word din, irin su Apple, cup, house, happy, da sauran kalamai da makaranta yasa ta zauna ta koyi spelling din ta haddace other than that ko she yanzu karubuta mata inhar bata taba zama da takoyi kalman ta iya shi ba to kafin ta iya pronouncing she din nan aiki ne babba agareta. Labulen dakin aka daga hakan yasa tajuyo dasauri Baba ne yayi wani irin kyau yasa goggagun uniform, yana kallonta yace da hijabi mutafi gyadamai kai tayi tamike tawuce sip wani pink gogaggen hijabi tadauka tasaka dake kaimata har kasa tadauki jakan zuwa aiki da flat takalminta najiya tasaka sanan tafito, su Ammi dake tsakar gida sukace adawo lafiya gyadamusu kai tayi Nana tabiyota har gate tace Anty Yasmeen yauma ki kara kawomini tsaraba wani kalan murmushi Yasmeen tayi sannan ta duko hancinta taja tace Nanani na ta iya kwadayi ko shikenan zan kawomiki washe baki Nana tayi tana tsalle tareda mata bye bye ta kwala ihu tace Baba bye bye bye Baba yamata yana murmushi shima. Har gaban shagon Maman Intee ya ijiyeta sannan yaciro 1k a aljihun shi yabata yace gashi idan kin tashi kikaga babu keke ki koma ki zauna call me da wayan Maman Intee zanzo na daukeki kada ki kara takowa daganan har gida is risky kinji gyadamai kai tayi ahankali tace to Baba tasa hannu zata bude kofar kaman daga sama taji Baba yace me da me kuke bukata ? Dasauri tajuyo ta kalleshi tana zaro manyan fararen idanunta masu bala in kyau, maimaita tambayan Baba yayi yace medame kuke bukata keda yan uwanki ? Ahankali tace ai Baba munada komi kasaya mana last month takalmin kafanta yakalla yace baki bukatan takalmi murmushi tayi akunyace tace eh inaso Baba ahankali yace dame kuma kanta tasauke akasa cikeda ladabi tace inaso na dinga hijabi sabo wayan nan sun tsufa wasu iron ya konamin, Ya Sa a kuma ita jakane da takalmi da turare, Farida ma haka, sai Nana ita ribbon takeso da dankunne jinjina kai yayi yace shikenan tafi gyadamai kai tayi cikin cool voice nata tace Baba Allah ya tsareka yakara daukakaka Allah bada sa a yakawo rabo Mai albarka murmushi yayi yace Ameen diyar Baba kema Allah miki albarka murmushi tayi sosai tace Ameen sannan tabude kofan motan ahankali tafice tawuce ciki, saida Baba yaga shiganta sannan yajuya motan yawuce tareda ciro numbershi yay dialing number Ammi, wayan na gab da katsewa tadauka, strictly yace yaran nan sun tafi school ? Ahankali tace Farida ta tafi Nanah fa Baba yay maganan bawasa, bayabo ba fallasa Ammi tace naga yau Thursday danace ne kawai abari monday sai takoma gabaki daya tunda bataje tun ranan monday ba shiru yayi kaman bazaice komiba saikuma ahankali yace banson kina mini ganganci da karatun yarana, sabida kinga ina rigasu fita shine zaki dinga barinsu bazasu makaranta ba, Allah kaimu gobe I will personally take them to school cikin kunkuni Ammi tace kanada lokaci ne ai saisa cikin fushi Baba yace me kikace dasauri tace ni bada kai nai magana ba dan murmushi yayi, cikeda son su shirya danshi baiso yana fada da matarshi
Chapter 7 · 0% Book details