← Book details Kyalkyalin Kauna Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 93

Sashe 39

Kyalkyalin Kauna Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

yanda kafanta yayi sanyi, dawani kalan gudu Yasmeen ta taho batai wata wataba tawani kalan shige jikin Ammi tace Ammiiii kankameta Ammi tayi tace ..yarinyana kene, Yasmeen dina tafashe da kuka bude kofa Yaya tayi jin hayaniya dan gidan nasu yadawo kaman na makoki tun bayan an sace yaran, ganin Yasmeen yasa tawani kwala ihu Baffa fito Yasmeen kowa na gidan fitowa yayi hadda su Farida da Sa a haduwa sukayi dukansu suka kankame Yasmeen, kowa na gidan Hamdala yake ganin Yasmeen, sun dade ahaka sannan Ammi tasake ta hannunta takai ta daura kan goshinta inda Ya kumbura dakuma kafanta da hannunta duk tana dubawa, wani kalan murmushi Yasmeen tayi ahankali tace jiya naji ciwon da ina kokarin guduwa ta window dakin danake, don t worry Ammi lafiyana kalau Gyadamata kai Ammi tayi sai kuma tasake jawota jikinta ta kankame fincike Yasmeen Yaya tayi daga jikin Ammi tace ke Maman Nanah bakida kawaici kinsan kwana na nawa bama bacci sabida Yasmeen dina, zonan diyan kirki tarungume Yasmeen tace barka barka Allah ya fito mana dake karasowa wajen Baffa yayi ahankali ya rungumeta yama kasa fadin komi sannan yacirota daga jikinta tareda shafa mata kai hakama Baba karami da Hajjo Ammi sai bin Yasmeen din take da kallo, kafin ta tashi da sauri bucket tadauka tawuce kitchen dasauri ruwan zafi ta debo ta sirka bucket din yacika tadauko dasauri Baba yazo yasa hannu zai karbi bucket din wani kalan kallo Ammi tamai hakan yasa ahankali yacire hannunshi dagakan bucket din, wucewa Ammi tayi da bucket din dakinta dan bazama tabarta tai wanka atsakar gida ba bayinta ta ijiye tafito takalli Yasmeen din dahar ta zauna kusada su Farida da Sa a duk sun rirrike mata hannu su Baffa kuma duk sun tsaya kallonta suke Ammi tace zomuje kiyi wanka tashi tayi ahankali tabi Ammi ciki hakan yasa Baffa yakalli su Yaya da Hajjo dasukai charko charko yace aje ahada karin kumallo yakalli su Farida yace kuje ku taya iyayenku aiki a kitchen duk suka watse Baffa yawuce yashiga dakinsu hakan yasa Baba ahankali yawuce yashiga daki afalo yazauna yay shiru yanajin Ammi da Yasmeen. Zaunar da ita Ammi tayi abakin gado tana kwance mata dankwalin data daura awuya tace babu abinda suka miki girgixama Ammi kai tayi ahankali tace anatse Ammi tana kallon kwayar idanunta tace babu wanda yataba mutuncin ki na diya mace? Karki mini karya ko ki boye mini wani abu, babu wanda yamiki wani abu ? Ahankali tace anatse Ammi tace kin fara period ? Gyadama Ammi kai tayi, Ammi tace yaushe? Ahankali tace yau day 2 ijiyan zuciya Ammi tasauke tace waya baki pad ? Murya chan kasa tace nayi rashin lafiya inata amai cikina na ciwo shine aka kawo Dr yadubani ni bansani ba kaman Dr ne yagaya musu abinda ke damuna sai suka kawomini pad Dr yace na shirya zai dawo nan da 15minutes hadamin drip, bayan 15min yadawo yasamin, drip din baima kareba ganin ba kowa adakin na zare nai attempting escape ta window shine naji ciwukan nan, karnukansu suka biyoni aka maidani daki shiru Ammi tayi tana kallonta tace wani yataba dukanki ko marin ki ? Dasauri ta girgiza kai tace babu abinda aka tabamin ahankali Ammi tace kinga fuskan Ogan su shi Pablon ? dasauri ta girgizama Ammi kai tace a suna boye fuskansu hannunta Ammi takai tadaura akan cikinta tace baki wani ci abincin kirki ba ko ? Gyadama Ammi kai tayi, ahankali Ammi ta mike tsaye tareda dagata zage mata zip na riga tayi tareda bata zani karba tayi tajuya akunyace tacire rigan tadaura zani, kayan Ammi ta karba tace jeki wankan to wucewa bayin tayi Ammi takawo pad da pant dawani simple gown na bacci mai taushi ta ijiye mata kan gado sannan ta kwashe kayan data cire tafito falo zatakai waje Baba tagani zaune kallo daya tamai tadauke kai tafita tadan jima awaje dan saida ta tsaya a kitchen tahado shayi dan Yasmeen nason tea da bread tana shigowa bataga Baba afalo ba wucewa uwar daka tayi zaune taganshi abakin gado yarufama Yasmeen datai bacci bargo dan tun dazu tafito ta shirya tsaf bin Ammi yayi da kallo zuwa Ammi tayi ta ijiye tea ganin tana bacci tajuya zata fita karaf Baba yakama hannunta wani kalan kallo tamai ahankali Baba yace hit me if possible but I can t stand wannan silent treatment dakike mini dan Allah kiyakuri cikin wani kalan murya Ammi tana kallonshi tace how dare put my children at risk Ibrahim eh? How dare you kasa rayuwan yarana a hadari? Kadauka bansan meke faruwa bane? I know yanda baka basu duka abubuwan su ba dalilin dayasa suka rike Yasmeen kenan, wlh wlh ka godema Allah mutanen nan basu tabamini yarana ba, I believe everything da Yasmeen tace sabida nasan tana al ada banda wannan ni mahaifiyarta ce nasan baa tabamin yarinya ba, amman wlh wlh wlh kaji na rantse maka sau uku da mutanen nan sun tabamini yara da sai kaga complete new side of me, and bari kaji nafada maka Ammi tai maganan azafaffe but yet muryanta so soft ko Yasmeen dake dakin da idanunta biyu daba lallai tajisu ba tanuna Baba da yatsa babu tsoro ko shakka tace bazan taba hanaka aikin ka ba amman kasani don t you ever and ever put rayuwan yarana a hatsari wlh tadalilinka ko aikin ka idan wani abu yakara tabamini yara Allah saina bark hannu Baba yasa dasauri yadaura akan bakinta dan yasan duk cikin bacin rai take maganganun nan cikeda lallashi da saukan da murya dan yasan kowa shi zaiyi blaming baida option but yabasu hakuri daga ita har Baffa yace bazan kara sa rayuwan yaranmu a hatsari ba I promise, I am so sorry wife ki yakuri dan Allah I can t stand this anger, now that yaranmu duka are with us let s solve our differences mucigaba da kula da yaranmu muna basu tarbiya tare kinji, kiyakuri forgive ur husband yanda Baba ke lallashinta kaman bashiba tadade tana kallonshi tausayi ma taji yabata duk yay zuru zuru kaman bashiba shima tasan yashiga damuwa dama da itama kawai shi namiji ne dole Ya daure amman kowa yasan yanda yake son yaran nan dudda taso tai sati bata kulashi ba kasawa tayi shigewa jikinshi tayi tafashe da kuka ahankali tace hankalina gabaki daya ba akwance yakeba yanzu tayaya xan barsu suje school sucigaba da activities nasu what if sun dawo sun kara kwashemini yara dasauri Baba yace duka yaranmu will resume activities nasu babu abinda zai samesu da izinin Allah, zan zuba yan sanda a school nasu Farida, zansa Aliyu for now yadinga bin Yasmeen school, da wajen aiki yana gadinta daga nesa batare datama sani ba, so our kids are safe in sha Allah kawai kidage da musu addu a kinji gyadamai kai Ammi tayi dagota Baba yayi ya manna mata peck agoshi murya chan kasa yace I love you sosai Maman Nanah juyamai idanu tayi cikeda yanga tace shiga bayi kai wanka nidai kallon Yasmeen dake bacci sosai yayi sannan yakalleta, fari tamai da idanu tace ba saisa nace maka kasayi fili ba migina bigger house wucewa tayi tafita daga dakin shikuma Baba yawuce bayi yana sauke ijiyan zuciya hankalinshi ya kwanta saura Baffa yanzu, deep down tunani yake ta yanda zai kama Pablo dan yanda yay kidnapping yaranshi yasa Baba ya kudirci aniyan kozai mutu in the process he must bring Pablo Escobar din nan to justice but for now he will secure and safeguard family nashi tsaf tsaf dan su kadai Pablo zai taba yatabo shi harsu Baffa yanzu zai zuba undisguised yan sanda akasuwa dan baiso su Baffa su sani dan wlh bibiyan Pablo yanzu yafara he will get that boy koshi dan gidan uban waye, he will get Pablo Escobar no matter what!. M SHAKUR EPISODE 3 KUZO KUSHIGA GROUP DIN MARYAM ABAYA DAN SAYAN ABAYOYI Open this link to join my WhatsApp Group: https://chat.whatsapp.com/CPRnRPcAD5K8vEY91Ziz8V EPISODE 3 Wajajen 3:30 yatashi daga kan dadduman, laptop din Hamad yadauka yakoma kan kujera yazauna yabude yasa password yashiga ciki yashiga email yay logging account na Hamad out yasa nashi yafara aikace aikace dukdan ya manta da Yasmeen ganin yakasa yasa kawai ya ijiye laptop din yamike tsaye wucewa yayi yabude kofa yafita daga dakin tashi Hamad yayi yazauna kawai ya girgixakai yawuce bathroom. Wani dake nan kasa yabude ahankali Baba yagani zaune kan dadduma shiru yayi jin an bude kofan dan Maheer yaki magana kafin ahankali Baba yace zonan Maheer shigowa dakin Maheer yayi ya maida kofan yarufe yakarasa ahankali zuwa inda Baba yake kan dadduma yazauna tareda tankwashe kafa, murmushi Baba yayi yace yau katuna da Baban ka da sauke kanshi yayi kasa tareda shafa kan nashi ahankali yace Baba fushi kake dani? Baba yace kataba ganin uba yayi fushi da danshi? Ijiyan zuciya Baba yasauke yace bazan taba iya fushi da y ana ba har abada, ba wannan bama meya sameka kasami hatsari? Wannan bakin fushin naka kayi ko ? Shiru Maheer yayi yakasa magana hakan yasa Baba yace komi yayi zafi maganin shi Allah, ka koma ga Allah Maheer, ka kyautata tsakanin ka da ubangijin ka, salla akan lokaci, yawan istigifari da hailala zakaga komi na rayuwa yazo maka da sauki wlh kanajina, kowa da tasa kaddaran fatanmu gabaki daya shine Allah yabamu ikon jarabawan mu sannan muyi kyakkyawan karshe and kasani cewa duk runtsi duk wuya duk wahala, ni mahaifinka ne i will always be that, Maheer koyaya kake ina sonka kai d ana ne, kaida Hamad baku da banbanci awajena kaji Maheer ahankali yace naji Abba daidai lokacin aka bude kofan dakin Hamad ne yashigo kallo daya yama Maheer dake kusada Baba yace tashi muje masallaci wani kalan dan iskan kallo Maheer yamai sannan yatashi shima Baba mikewa yayi duk suka hadu suka tafi mosque ana sallamewa Maheer yatashi yafita binshi Hamad yayi da kallo koba komi yau yayi salla a jam i shi yasan inda nan yake da yafi salla akan lokaci amman mayyan chan bazata taba barinshi yaje wani wuri ba. Yana kaiwa gida dakin Hamad yakoma yawuce yazauna shi karan kanshi yarasa meke damunshi kawai bayajin dadin rayuwanshi ne tunanin Yasmeen na neman hallakashi gashi bazai taba iya fadama kowa abinda ke damunshi ba
Chapter 39 · 0% Book details