Sashe 52
Kyalkyalin Kauna Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
yakalli Ammi yace "nafita idan yaron yazo kada yawuce awa daya agidana dan haka ku kiyaye" yay maganan da kakkausan murya yawuce yafice Ammi tabishi da kallo baki sake kafin tasauke jiyan zuciya tace "kaji dashi" tadago Yasmeen tace "ke dalla chan yau saurayinki zaizo duk kinbi kin kuka jibi idanunki, tashi kije kiyi wanka kizo dakina ina jiranki" makema Ammi wuya tayi cikin muryanta dakeda gobe na kuka tace "ni bazanyi wanka ba" haba Ammi takama tace "au yau shagwaban yatashi ne ahhh lallai Aiko mangareki zanyi anan niba Babanki bane dazai tsaya lallashinki ba, tashi muje ma abayin nawa zaki wanka" badan taso ba Ammi ta tasata agaba suka tafi dakinta wanka tasata tayi sannan tafito mata dawata sabuwar atampa superwax gal wanda na salla Baba ya dinka musu dan dazaran yasami kudi yake abubuwa da wuri duk a ijiye, kayan Ammi tanuna mata tace "imaza saka kizo kigani" Ammi tasauke wani babban akwatinta tunna aure taciro wani gyale chantily milk sabo a leda tace "kinga tsaraban gyalen da makociyar mu Hajiya Mariya tabani yau ga amfaninshi" Yasmeen dake jan zip na skirt din datasaka takalli Ammi cikeda rigima tace "waye zai da gyale Ammi"? Hararanta Ammi tayi tace "wale tunda kaina nake cirowa gyalen" kaman Yasmeen zatai kuka tace "Ammi ni hiabi zan saka" akwatin Ammi tadauka tamaida sama tace "uku saura kwata fa kike shirmen nan wh Yasmeen nadade banga fitinanniyan yarinya irinki ba bari kiga naje nakira miki Sa'adatu da Farida" juyawa Ammi tayi tafita dakin Yaya tawuce Sa'adatu na zaune da Farida afalon da Yaya da Hajjo suna hira shigowa Ammi tayi ciki tace "Yaya yarinyar chan na sani ciwon kai wh, Sa'a keda Farida kuje ku mata kwalliya naciro mata gyale dan gidansu shi zata saka" tashi sukayi suka fita da sauri Yaya tace "ai Yasmeen ni bantaba gani yarinya baiwar Allah irinta ba, Allah dai ya tabbatar da Alhairi" atare duk sukace Ameen. Yasmeen duk yanda take rigima bataso bataso saida Sa'a tamata kwalliya lafiyayye mai kyau tasamata jan baki tamata dauri daya fito da jelan gashinta ta daurin yay wani kyau Sa'a ta yafamata gyalen awuya daidai nan aka sallama cewa yazo Yayacw ta leko tace "ace yashigo" tunda Yasmeen taji haka gabanta ke faduwa sosai da Sa'a da Farida suka kwashe da dariya Sa'a tace "wlh yanda kikeyi kaman wata amarya Yasmeen that means randa zaa kaiki gidan miji ba karamin kuka zakiyi ba" daidai nan Maheer yashigo cikin gidan, yana sanye dawata milk yadi anmai dinkin jumper dayamai kyau ga hula akanshi Ya Allah! Zaka dauka wani kalan angon e tundaga gate kamshin shi yacika ko'ina Farida ne tafito daga dakinsu takalleshi yana tsaye wajen gate aranta tace wow wanna kyakkyawan ne mutumin Innalillahi karasawa tayi har inda yake akunyace tace "ina yini Yayan mu" Maheer yadade yana kallon Faridan, she's just like Yasmeen amman Yasmeen tafita kyau nesa ba kusa ba, murmushi yasakin mata mai sanyaya zuciya yace "Anty Faridan mu" wani kalan kashe Farida yayi da dadi tace "zo muje na Kaika daki ance kashigo" anatse yace "ok" tana tafiya yana biveda ita abayin gidan tsaf tsaf dudda ba gidan masu kudi ba amman ko datti daya bai gani ba, dakin Ammi tashiga tajuyo takalleshi tace "bismillah" cikin dakin ya kalla kafin anatse yace "Assalamu Alaykum" yashiga ciki Farida ta amsa kuiera tanunamai tace "kazauna wata one sitter yazauna akai sannan tashiga ciki cikin whispering tace "Innalillahi Ya Sa'a kinga yanda saurayin Anty Yasmeen keda kyau kuwa kuje ku gaishe shi bari naje dakin Yaya na kwasomai ruwa" fitowa falon tayi akunyace yawuce tafita Sa'a takalli Yasmeen dava zauna tai kuri kaman jira take ace kule tafashe da kuka tace "tashi muje" makemata kafada tayi hakan yasa Sa'a tace "wh zanje nagayama Ammi" dasauri ta mike tsaye hannayenta narawa har saida Sa'a ta lura hakan yasa yakama hannunta tajawota suka fito, tunda suka fito Maheer yadaura idanunshi kan Yasmeen da kanta ke kasa har suka shigo cikin falon Sa'a ta zaunar da ita kan 1sitter dake facing Maheer sannan tajuyo takalli Maheer akunyace itama tace "ina yini" dan murmushi yamata yace "Yaya Sa'adatu ina yini" wani kalan dadi Sa'a taji akunyace tace "sannu da zuwa bari naje" Gyadamata kai yayi tajuya tafita daidai lokacin Farida na shigowa da wani hadadden tray da kayan kwalama ke kai taba zuwa wani stool tajawo tadaura akai sannan itama tafice daga dakin bayan tasaci kallon Yasmeen da kanta ke kasa sai wasa da gyalen jikinta take. Kusan 20min dukansu suna zaune adakin babu wanda yay magana acikinsu. For the first time in those 20'min yajaye idanunshi daga kanta yakalli tray da aka kawomai zobo ne mai sanyi a jug da cup sai dambun nama da cincin dago kanshi yayi yakalleta ahankali yace "zoki zubamin drink nasha" kaman bazata dago kanta ba ahankali tadago kanta takalleshi suka hada idanu for the first time tunda yazo faduwa gabanta yayi sosai so take ta dauke idanunta amman ina takasa yay locking eye contact nasu strictly yamata pointing abin gabanshi da yatsa alamun tazo ta zubamai, bataso tayi bamataso ta tashi daga inda take amman takasa musu tashi tayi ahankali tamike tsaye tana jajjan gyalen jikinta tana lullube ko'ina najikinta sabida vanda yake mata lafiyayyen kallo ko kunya bayaji saikace baitaba ganinta babu hijabi babu mayafi bama, karasowa gabanshi tayi ahankali ta tsugunna taki kallonshi jug din tadauka duk yana kallonta ta tsiyayamai zobo a glass cup sannan ta jiye juice din tadauki cup din ahankali tadan dago kanta kaman mai tsoron kallonshi tamikamai hada idanu sukayi dasauri tadauke kai murya chan kasa tace "ka amsa hannuna yagaji". Dan murmushi kadan yasaki yana kallonta kaman yau yafara ganinta he just wants to understand dalilin dayasa tunda yasan yarinyar nan yarasa peace of mind he's just chasing after her, for how many years now baitaba abandoning sana'an shi ba but sabida yarinyar nan yabar komi tsabagen yanda take kanshi yazo in disguise zai aureta, what kind of charm tamai? What kind of black magic? He just hope idan ya aureta zai dainajin abinda yakeji yacigaba da rayuwanshi. "Ni kadaina kallona" tafadi tana dauke kai tana kallon gefe, dan kunya yaji baice komi ba yasa hannunshi yadaura kan kan nata yahada hannunta da cup din tare batare dava karbi cup din ba yarike wani kalan zabura Yasmeen tayi sabida shocking din dataji dabadan yarike hannun nata da cup din da kyau ba data zubar da kofin da zobon, kallonshi tayi tana zaro idanu takalli kofa gudun kar wani yashigo kaman zatai kuka tana kallon kofa tace "ka sakeni pls kar wani yashigo dan Allah, dan Allah kaji" "to kalleni" juyoda idanunta tayi tazubamai su dasukaji kwalli dan lumshe idanu yay yabudesu murya chan kasan makoshi yace "why are you so beautiful Fateema"? Ya tambayeta cikin cool husky voice dayasa gabanta yafadi itama ta tsareshi da idanu takasa magana, murya chan kasa yace "I want u to be smiling sabida kowa yadauka kina sona and also" tasake zaro idanu tana kallonshi kara make murya yayi yace "idan an tambayeki kan aurenmu kice yes" Gyadamai kai tayi da sauri tace "toka saken mini hannun" gently yasaki hannunta tareda karbe glass cup din Gyadamai kai tayi da sauri tace "toka saken mini hannun" gently yasaki hannunta tareda karbe glass cup din dasauri tajuya takoma tazauna yabita da kallo everything about her is just too perfect, tamai kyau bana wasa ba kaman ba itaba everything about the outfit looks fabulous ajikinta, zama tayi daidai lokacin aka fara kiran sallan la'asar 3:45 dasauri takalleshi hada idanu sukayi yana rikeda cup na zobon data bashi dauke kanta tavi da sauri tareda ballamai harara tadan turo baki tace "kazo katafi Baba yace awa daya zakayi" dagakai yayi yakalli agogon dakin yace "ban cinye time dina ba" juyowa tayi dasauri takalleshi gain baya tsoron Baba kaman ma Baba baya lissafi shi daidai E3 lokacin Nanah tashigo dakin tana kallonsu faduwa gaban Yasmeen yayi kar Nana taganeshi murmushi Nana tayi tana kallon Maheer dan murmushi Maheer yasakin mata da sauri tai wajenshi zata shige jikinshi tace "Uncle" dan firgita kadan Maheer yayi dahar saida Yasmeen dake kallonsu ta lura, murmushi yama Nanah yace "how you"? Washe mai baki tayi tana kallonshi tace "Uncle kanada kyau sosai" murmushi shima yamata ganin yanda take kallonshi kaman tanaso ya dauketa ne yasa yakai hannu cikin aljihunshi yaciro dubu daya sabuwa fil yamika mata yace "gashi jeki sayi minti" dan kallon Yasmeen Nana tayi yace "karbi kayanki kada ki kalli Anty Yasmeen" Aiko dasauri Nana ta karba tana murmushi tace "Allah amfana Uncle" tajuva tafice daga dakin, mikewa tsaye yayi ahankali yakalli Yasmeen sannan yafara tafiya jin takunshi Yasmeen take har zucivanta dasauri tamike tsave tana wasa da kasan gyalenta, wuceta yayi ya tsaya waien kofa yace "jeki gayama Ammi zan tafi" gyadamai kai tayi yafita daga dakin itama tafito ko kadan batasan yana wajen kofan ba saura kadan tafadi vatareta da hannu fizge jikinta tayi da gudu tana turamai baki yay murmushi tawuce dakin Yaya su Ammi duk suna waien tace "Ammi zai tafi wai yanaso yagaidaki" kallon su Yaya Ammi tavi dasauri tace "kie ku gaisa E3 yakamata" hijabin Yaya Ammi takarba tasaka taja hannun Yasmeen din tace "muje" fita tayi waje hangota yasa Maheer dake tsaye gaban Dakinsu ya tsugunna kanshi akasa anatse yace "ina yini Ammi" cikeda kunya itama Ammi tace "dan Allah katashi Maheer, tashi tashi" girgiza kai yayi batare dayayi magana ba Yasmeen dake kallonshi tawani murguda baki, Ammi tai murmushi tace "Ya aiki Maheer? Allah yabaku sa'a, Allah kuma ya taimaka ka gaida Baban ka dan Allah" Gyadamata kai yayi yace "sai anima" cikeda murmushi Ammi tace "mujima lafiya" wucewa yayi Ammi tanunama Yasmeen gate da hannu alamun tabishi ta makema Ammi kafada, fita yayi ko 10secs baiyi da fita ba wani almajiri yay sallama dawata yar jaka mai kyau ahannunshi yace "salamu alaikum ance nabawa Fatima wannan" yay maganan yana karasowa wajen su Ammi kallon ledan Ammi tavi tace "kai maida" dasauri yaron yace "yaja mota yatafi" hannu Ammi tasa ta amsa tareda bude yar jakan kayan zakine zalla su chocolates biscuit da sauransu ajiyan zuciya tayi ganin ba kudi bane tabama Yasmeen tace "gashi jeki kaima su Yaya" daidai an bude