Sashe 23
Kyalkyalin Kauna Part 3 Complete Hausa Novel · about 3 min read
hancinta ta fyato majina, wani kalan yatsine fuska Maheer yayi shi karan kanshi baimasan yayi ba irin ewww din nan dirty girl, kaman taji ajikinta dago manyan idanunta tayi ganin yanda yayi da fuska yasa takara wankamai wani mugun harara kaman zata kasheshi da idanu dayasa ya zaro idanushi cikeda mamaki irin wat! Sake ballamai hararan tayi ciki ciki tace mara imani kawai cikin kakkausan murya yace mekika ce ? Juyowa tayi takalleshi da sauri suka hada ido cikin tsantsan dakewa dan yanzu jitake dukma abinda zai faru yafaru tace cewa nayi Allah yasa kada Babana ma yabaka abinda kakeso duk abinda zakayi kayi tsayawa yayi chak yana kallonta abin looks really strange to him, dan tunda yake babu wacce tama isa tamai wani kalan kallo balle tamai rashin kunya haka wato she s stubborn kaman babanta, kwallin taba yadauka yabude yazaro daya yakai bakinshi yadauki lighter zai kunna saikuma yakalleta anatse yace idan Babanki bai bani kayan kwayoyi na ba saina kasheshi har lahira zaro manyan idanunta dasuke jikeda ruwan hawaye tayi ta kalleshi kana ganinta kaga tsoro da fargaba dakuma shakkan shi aranta jin yanda yake kiran kisan kai kai tsaye, hakanan saiyaji yaji mugun dadin hakan, lighter yasa ya kunna taban sannan ya ijiye ya zuki taban ya fuzar ahankali yace bashi kadai zan kasheba duk wani tsatso da jininshi daya bari aduniya sainabi na kashesu daya bayan daya yakara zukan taban ya fuzar, yabita da kallo yanda yaga yan dogayen brown skin yatsunta ke rawa masu kyau dabasu da dark knuckles, gently yadauki wayanshi yabude yay dialing number Dan yasa a speaker yace bari nafara da kannenki dawani kalan sauri ta kalleshi dan bata gane takamaimen mene ze fara da kannenta ba, daukan wayan Dan yayi yace yes sir dan shiru yayi yakalleta yanda take zaro manya manyan idanunta tana kallonshi cikin wani kalan murya na asalin mugunta da isa yace shoot those children Dan, ka kwashe gawawwakin su ka bama Kikito yaci don t cut the call, execute the task ina kan wayan dasauri Dan yace Yes Sir wani kalan mikewa tsaye Yasmeen tayi kanta har juyawa yake jikinta wani kalan bari bari yafara kaman wacce takeda farfadiya tana dumfaro shi tace dan girman Allah, dan girman Allah malam kada ka kashe kannina, kill me, nika kasheni dan Allah let them be, ka kasheni, kayakuri dan Allah kaya kuri tana tafiya tana hade hannayenta biyu tana rokonshi tana karasowa wajen dayake ta zagayo ta bayan table din kusada shi tafashe da kuka sosai tahade hannayenta biyu tana kallonshi yanda yakeshan katon lukutin taban abinshi ko kallonta bayayi daidai nan taji karan bude kofa tawayan saiga kukan Nanah kaman zai tsaga wayan, Dan yace Sir gani nan na iso zaro manyan idanunta tayi kirjinta na bugawa sosai tarushe da kuka tai kneeling gefenshi takai hannunta saman hannun kujeran dayake zauna tana kallonshi tana kallon wayan tace dan Allah kada ka kashe kannina dan girman Allah dan ya Rasullullahi, bawan Allah kayakuri kada ka kashe min Farida da Nanah su kadai ne kannina dan Allah daidai lokacin taji kukan Nanah da ihun Farida tana cewa wayyo me kake nunani da bindiga Yasmeen batasan lokacin data mike daga kneeling din datayi ba hannunta har rawa yake tawani kalan daukan wayanshi garin haka hannunta ya gogi nashi wani kalan shocking Maheer yaji dasauri yakalleta, bama tasan tayiba dasauri takai wayan kunnenta kaman ba a speaker wayan yake ba tana ihu sosai tace dan Allah kada ka kashemin kan tuss tuss taji sau biyu wani kalan ware idanunta tayi kafin idanunta suwani kalan juye sama tai baya luuuuu zata zube kasa dawani kalan sauri Maheer yatarota hakan yasa tafado jikinshi a sandare. SPARKLES OF AFFECTION