Sashe 46
Kyalkyalin Kauna Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
you done to me ? Kaman ta kurma ihu takeji but sabida tasan akwai dalibai awaje yasa ta rike bakinta tareda lumshe idanu da sauri, adan zafafe Maheer yace nace ki kalleni bude idanuwan tayi dasauri ta maidasu kanshi sun cika da kwalla sosai dake gab da zubowa, babu wasa akan fuskanshi yace wani spell kikai casting akaina? Tell me! Yadanyi ihu kadan still ba irin wanda za ajisu a school ba, rawa bakinta yafara tama kasa magana kawai gabanta is hopelessly beating, fizge hannunta Maheer yayi yarike gam yakai kan kirjinshi dashima ke bugawa binbimbin yace listen to my heart beat from the day dana fara ganinki beating dinshi ya chanza to this, koda yaushe tunanin ki nake, when am awake, when am asleep, nabude ido na ganki, na rufe ido na ganki, you are in my head, my body, my eyes, my thoughts, my eyes, my everything, look at me, look at what I ve subjected myself into ni koyarwa in this I donno cottage school din naku all because of you tell me wani black magic kikamin hooon! yasake dukan bango dayasa tafashe da kuka tana girgizamai kai tama rasa mezatayi tadaura hannunta akan baki sabida kar karan kukanta yafito tsayawa she s just so scared, wannan mutumin yabiyota school yana cewa metamai, to metamai? Kuri Maheer yayi yana kallonta da tsoronta da kukanta da yanda yake goge hawayen da bayan hannu everything about her na burgeshi ji yake kaman he should hug her and tell her sorry, ahankali yasauke ijiyan zuciya yana kallonta still batare daya dauke idanunshi daga kanta ba yace i want you to become my wife!!! Dum dum dum haka gaban Yasmeen yafadi shi karan kanshi Maheer din mamakin abinda yafito daga bakinshi yayi dan wlh wlh baisan ya akayi abin yafito ba, sakin hannunta yayi da sauri yawuce yazauna kan table yay crossing kafanshi daya kan daya yana kallonta yanda take kallonshi tana kuka tana goge hawayen da bayan hannu kaman tana kokarin kara gasgasata abinda yafadi, yakai kusan 5min yana kallonta yana tunanin abinda yace sannan ahankali yace remember you are indebted to me dan haka yamike tsaye yawuce chan gaban tv office din ya tsaya tareda kulle hannunshi tabayanshi yana kallon tv yajuya mata baya awani irin hankali yace Fateema Ibrahim Ibrahim! Faduwan da gaban Yasmeen yayi this time around saida ta daura duka hannayenta kan kirjinta tana kallon bayanshi dan yabata baya, anatse Maheer yace i hate marriages but for the first time I think shine solution dina and how to end all this problems yasake shiru kafin chan yace listen and listen very well, there s an envelope akan table dina jeki dauka ki bude share fuskanta Yasmeen tayi ahankali kaman bazataba tawuce table nashi tadauko wani envelope data gani takoma inda take tsaye da, budewa tayi yawanci hotunan Baba ne dashi da wani dan saurayi daya kamo yana kalle kalle yasa a mota, sai wani gida, sai Baba da kayan yan sanda, Baba yafito daga masallaci, Baba dasu Baffan ta suna magana gaban mosque juyowa Maheer yayi yakalleta yace I know kinsan waye a hotunan nan dan mahaifinki ne d other mutumin dakika gani is one of my drivers dan murmushi kadan Maheer yayi yace Baban ki is secretly trying yakamani at all cost, all the four drivers ranan da aka sakesu suka bar garin wannan ma mamanshi ke rashin lafiya abinda yahanashi tafiya kenan but Babanki yakamoshi secretly yakaishi wanchan secret gidan yana ganamai azaba just sabida yasami information akaina wanda trust me driver chan gwara yamutu daya fadi anything yadanyi shiru yace what he don t know is babu abin Babanki da bansani ba I have men dake binshi 2,4,7 sabida I know mutum kaman mahaifinki bazai taba barina mutumin dayakama yaranshi ba that easily he will do duk abinda zai iya dan kamani, yanzu haka naso sniper na ya harbe mahaifinki 1mins is too much sosai Yasmeen ke kallonshi dan bata taba ganin cruel, ruthless dan ta adda irin mutumin nan ba, dan murmushi kadan Maheer yasakin mata yakarasa zuwa gaban table dinshi yadauki kwalin taba yazaro daya yakai bakinshi yadau lighter zai kunna yaga tadan yatsine fuska hakan yasa gently yacire daga bakinshi ya ijiye danji yayi bazai iya sha agabanta ba, yakalleta yace akwai wani al ada damu yan mafia kedashi yadanyi murmushi kadan yace idan kanada enemy daya addabeka the best way kuyi ending na kiyayyan shine ta hanyar kulla auratayya, idan akai aure kasan bazaka taba iya taba gidan wane ba dan diyarka na ciki, haka kaima baraka taba gidan wane ba dan yarsu kake aure, zan aureki for only 2 reasons Fateema! Yanuna mata yatsunshi guda biyu yace one sabida yanda nakasa cireki daga zuciyana kinyi bewitching Pablo Escobar and secondly sabida mahaifinki daya addabeni sosai take kallonshi kirjinta na faduwa, maida hannunshi kasa yayi yace idan ban aureki na tabbata zanma mahaifinki abinda bazanso namai ba tasowa yayi yazo gabanta dab da ita yana kallonta kasa jurewa tayi tasauke idanunta kasa awani kalan hankali yace I will be sending my father his friends and my brother to gidanku azo atambayi aurenki dan dukawa yayi yakai bakinshi saitin kunnenta ta saman hijab kaman mai whispering yace if you dare koda wasa kika fadi cewa nine nake neman aurenki I will first kill that little girl ta gidanku mai shegen kukan nan like you dasauri Yasmeen tajuyo da fuskanta takalleshi numfashinta dake fita fast fast na sauka kan fuskanshi hakan yasa shima yakalleta in the eyes irin tantirin nan yace followed by yayarta, then your Mom yay dan murmushi irin na mugunta dinnan yace then ur sweet caring father sannan kuma I will still marry you duk inda kika shiga kuma saikin zauna dani hawaye ne masu zafi suka zubo mata daga idanu dasauri yadauke kai yace you can go zamuzo ya nuna mata kofa da hannu. https://www.instagram.com/p/CtwFCtXITwD/?igshid=YjgzMjc4YjcwZQ== EPISODE 4 Juyawa Yasmeen tayi ahankali zata tafi saikuma ta tsaya chak kafin dasauri tajuyo takalleshi kaman yanda yake kallonta bai motsa daga inda yakeba, dakewa tayi takai bayan hannunta ta share fuskanta tace ko kaine the only namijin daya rage aduniya bazan taba aurenka ba, kuma kuma baka isa ka kashe su Baba ba sai lokacin su yay wani kalan kallo yamata dayasa maganan ya makale awuyanta ahankali yace are you underestimating me? Ni? Faduwa gabanta yayi tana kallonshi tana kara kallonshi mutumin daya sa akayi kidnapping ita da Nana da Farida babu abinda bazai iyaba, baki tabude zatai magana saikawai kuka yacita takasa magana irin kukan rasa mezakayi dinnan kariga kasan anfi karfinka, kukan tsaka mai wuya, tasowa yayi ahankali ya tsaya agabanta he feels kaman yay hugging nata, handky yaciro yamika mata makemai kafada tayi taki karba hakan yasa yakai hannunshi yakama hannunta yasa mata kafin yay folding hannunshi a kirji yace destiny family ki lies on your hand, bazaki iya sadaukar da rayu wanki ma iyayenki ba, inhar kin aureni har abada babu abinda zai sami yan uwanki da iyayenki idan bakiyi ba I will take revenge dan ayanzu Babanki ya nemi tsokanata an kashe case yakama direbana again and you know I don t forgive! Stop crying yafadi ahankali hakan yasa ta tsayar da kukan, ahankali kaman mai lallashi yace will you marry me ? Hararanshi tayi tareda turomai baki tace babu abinda zanyi da criminal irinka dan Mafia dan murmushi yayi ganin tanamai tsiwa kafin murya chan kasa kaman dan baby yana kallon fuskanta yace m hungry har cikin jikinta taji kalman saikuma tajuya tawuce tafita daga office din yabita da kallo ko kallon Dan batayi ba tawuce masallacin school nasu, zama tayi wajen alwalan mata takifa kanta a guiwa what kind of life is this? Wannan wani kalan tsaka kai wuya tashiga, wazata gayamawa, mutumin nan babu abinda bai saniba game da Baba dasu yaranshi harda su Baffa, idan yakashe Baba fa da Ammi da Nana da Farida fa dasu Baffa wazai rage mata aduniya? Amman idan ta yarda ta aureshi bazai musu komi ba kuma ta yarda bazai musu ba dan kaman yana sticking to alkawari, ijiyan zuciya tasauke ta dago tai tagumi tai shiru tana kallon waje daya all this while tanaji azuciyanta tanaso ta ganshi deep down she misses him har kuka take idan ta tunashi amman yau daga ganinishi saitaji inama bata ganshi ba, lectures din dabata koma kenan ba sai wajajen 3 ta nufi gate hakan yasa Aliyu shima yatafi ganin ta tafi dan Baba yace karyabari tasan yana binta, Keke ta tare ta shiga shagon Maman Intee tasa akaita dudda bama tasan dalilin dayasa tace chan ba. Clinic da Hamad ke aiki yasa Dan yakaishi, suna shiga parking Dan yayi saukowa yayi glasses nashi akan idanunshi babban hospital ne ahankali yake tafiya harya shiga ciki, direct wani office yawuce budewa yayi yashiga kai tsaye daidai Hamad na duba BP wani tsoho dake zaune kan kujera yana sanye da lab coat hakan yasa ya tsaya jikin kofa shiba karaso ciki ba yana kallon Hamad, dasauri Hamad yay murmushi yace Baba kaje pharmacy zan aika musu da magungunan da za a baka godiya tsohon yayi yatashi yazo yafice hakan yasa Hamad yace kaikuma meya kawoka wajen aiki na ? Maida kofan Maheer yayi yarufe bayan tsohon yafita sannan yakaraso ciki yana kallon Hamad dake kallonshi, instead of yazauna kan chair wajen observation bed na office din yayi yahau yazauna wayanshi yaciro yana dubawa Hamad duk yana kallonshi yadade baiga miskili kaman Maheer ba ganin baida niyyan magana yasa yazauna yashiga tura magungunan da za a bama tsohon daya fita to pharmacy kaman daga sama yaji Maheer yace I want to get married! Durun dum! Maganan yasauka akan Hamad dasauri yadago kanshi ya kalli Maheer din da kaman bashine yayi magana ba, karasa tura sakon Hamad yayi sannan yataso yazauna kan table yana facing Maheer tareda rungume hannunshi a kirji yace wazaka aura? Hope ba wanchan matar data haifeka kake shirin aure ba sabida dan ciwon datayi kanka shiru Maheer yayi sai danna waya yake kaman bazaiyi magana ba saikuma ahankali yace not she dasauri Hamad yace to wakake so ka aura Maheer ? Wannan karan yakai kusan 3min baice komiba kafin ahankali yace that girl which girl ? Hamad ya tambayeshi