← Book details Kyalkyalin Kauna Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 93

Sashe 24

Kyalkyalin Kauna Part 3 Complete Hausa Novel · about 10 min read

M SHAKUR
EPISODE 1
Anty kene ba warwaro, ba dan kunne ba sarka haba dan Allah, Oya Oya shiga group din nan kije ki kwashi sarkoki da dankunnaye akan kudi dan kankani.
Open this link to join my WhatsApp Group: https://chat.whatsapp.com/JGCK4a99vpjGLtepWcYwrn
Wani kalan sanyi yaji ajikinshi a asalin cikin bargon kashin jikinshi da tunda yake koda yay zaman Russian ma da Alaska baiji kalan irin sanyin nan acikin jikinshi ba, in his entire life banda Hajiya Maryam this is the second lady dayataba rikewa ko ta taba shiga jikinshi, tundaga kan guntayen hawayen dake gefen idanunta yake kallo harzuwa kan small yar doguwan fuskanta da brown skin nata kewani shinning kaman butter da aka narka, dan karamin bakinta yakara ja kaman wacce zazzabi ke shirin kamawa, goshinta da gashi yacika sun kwanta ga uban zufan daya ketomata agoshi sai sukai lub lub hakan yay mata wani kalan kyau idanunshi ya daura akan katon pimple guda daya daya fito mata a in between giranta guda biyu dayasa tai wani kalan kyau zuwa gudu ukun dasuka fito mata a kumatu dasuka mata bala
in kyau yasake maida idanunshi kan dan karamin pink lips nata dasukai so moist kaman ta shafa vaseline, wani kalan lumshe idanu yayi da bala
in sauri dan abin is somehow ko Hajiya Maryam baijin yataba tsayawa yamata wannan cikakken kallon dayama yarinyar nan ba kuma baimasan mesa yakemata kallan kallon nan ba, abu yaji yanamai yawo aciki kaman tafiyan butterfly dasauri ya runtse idanu saikuma yabude idanunshi da sauri yakai hannunshi kan goran ruwan shi dake kan table din yabude goran dasauri yakai duka ruwan saman fuskanta yana kallon fuskan yadaga goran yashiga juyemata ruwan, wani kalan nishi Yasmeen tayi dan ruwan akwai sanyi sosai hakan yasa ya tsayar da kwarara mata ruwan yamaida goran ya ijiye kan table yana kallon fuskanta still batare daya saki shoulder nata ba, ahankali take bude idanuwanta dasuka mata dishi dishi bamata gani da kyau idanunta na sauka kan wani kalan kyakkywan mutum dakenan kaman bakin balarabe ga lips dinshi jazur yana kallonta shima, cikin yanayi na asalin wacce bata gama farfadowa sosai ba tabude lips nata, saikuma kawai tafashe dawani kalan soft kuka tana karasa bude idanunta tass tana kallonshi still, yan
da take kuka kaman irin karaman yarinyar nan dabata dawani hope daya rage mata aduniya hawaye na bulbulowa ta gefen idanunta, wani abu ne yaji yatabamai zuciya ganin yanda take kukan, dawani kalan sauri yadauke kanshi cikin kakkausan murya dake nan a bit calm ba kara sosai yace
tashi daga jikina
makemai kafada Yasmeen tayi batare datayi ko motsi ba, hakan yasa dasauri yajuyo da kanshi ya kalleta kaman yanda take kallonshi shi baitaba ganin karfin hali haka ba, tana kuka sosai mara kara tana kallonshi hade giran sama da kasa yayi yakoma sak Pablo dinshi yace
tashi daga jikina
makemai kafada tayi tana kallonshi cikin idanu kyur batako kyaftawa, kwayar idanunta yakalla yanda yay gray sosai ga idanun sun jike da hawaye sosai sakejin wani abu yayi namai tafiya aciki dasauri ya dauke kai yay baya da kujeran dayake kai zai tashi hakan yasa Yasmeen tai maza cikin kuka ta yunkuro daura kanta tayi akirjinshi in so much agony cikin wani kalan kuka tace
wlh wlh nima saika kasheni, I can
t live anymore mai amfanin rayuwana kannena sun mutu? Wlh wlh saika kasheni baraka tafiba
tacigaba da bubbugamai kanta akirjinshi, baitaba ganin mutumin dabaya tsoronshi ko shakkan shi ba irin yarinyar nan, cikin kakkausan murya yace
dagani to nadauki bindiga na nakashe ki
cikin kuka ahankali ta yunkura zata tashi da jikinta daya mutu sosai karaf ta tsaya sabida yanda gashinta ya makale a boturin jikin riganshi ba karamin zafi abin yamata ba dasauri cikin kuka tace
washhhh
takai hannunta dasauri zata daura akan kirjinshi cikin dan tsawa yace
t touch me ke!
Tsayawa tayi cikeda gajiya da komi na duniya tace
to kacire mini
dan kallon kan nata dake saitin kirjinshi yayi da yanda gashin yay tangling akan boturin shi, tsaki yayi kadan tareda yatsine fuska yakai hannunshi ahankali kaman mai tsoron taba gashin nata yace
look at her dirty hair kazamiya
cikin kuka tace
eh naji amma dai inada imani kuma ban taba kashe kow
wani kalan kuka ne yaci karfinta mai bala
in kara this time tunawa da yakashe Nana da Farida yanzu, kasa taba gashin nata yayi ahankali yaduko da kanshi kasa yana kallon yanda take kuka ta runtse idanunta gam tana kuka mai taba rai har harshenta yake hangowa jajajir sabida yanda take kukan, wani abu yaji ya tsayamai arai yanda take kukan nan tausayi ne shi baitabajin tausayin wata ba baima cika jin emotions ba to meke damunshi, jitayi kaman ana kallonta hakan yasa tabude rinannun idanunta cikin kuka karaf suka hada idanu saida gabanta yafadi shima haka dasauri yadauke kai tareda kai hannunshi da sauri yana cire gashinta daga jikin riganshi da sauri yakasara cirewa cikin fushi yace
now get up
tashi tayi dasauri tana kuka, shima yamike tsaye yahade rai tareda jawo drawer yaciro bindinga yadago kanshi yakalleta, kallon bindigan tayi yay pointing bindigan saitinta yace
kince na harbeki ko
? Gyadamai kai tayi cikin kuka tace
ahankali yana kallon kwayan idanunta ya matso dab da ita tareda daura bindigan akan goshinta lumshe idanunta tayi da sauri tana wani kalan nishi hawaye na fitowa ta gefen idanunta ta sadakar kawai, pulling trigger yayi bindigan tai wani kalan kara har cikin scull nata taji karan batasan sanda ta kurma wani kalan uban ihu ba.
Wayyoo Ammi na mutu
jikinta ko
ina narawa, wani kalan murmushi ne ya kufce mai daga baki yana kallon yanda ta zare ya girgiza kai kawai yasauke bindigan kasa ahankali yace
ahaka ake mutuwa ko
? Chak ta tsaya tadan zaro idanu saikuma takalli kanta ita wlh tadauka ta mutu, hannunta takai tashafa saman goshinta inda yadaura bindigan ta lakato tadawo dashi gaban idanunta taga ko akwai jini taga bakomi hakan yasa tadago manyan idanunta ta kallai, wani kalan dan iskan kallo yamata sannan yawuce yafara tafiya zaiyi hanyar kofa kaman wanda akace dole yayi magana yace
your sisters are alive
wani kalan zaro idanunta tayi takalleshi dasauri tabi bayanshi tace
da gaske
kojuyowa baiyiba balle yakalleta but hakanan taji kawai ta yarda dashi they
re alive, ganin yakai kofa yasa dasauri tace
dan Allah ka maidani wajensu
chak ya tsaya hakan yasa itama ta tsaya dasauri batare daya juyowa cikeda gadara yace
this is your punishment
cikin wata kalan sanyin murya kaman marainiya tace
dan Allah kayakuri kayafemini
wani kalan juyowa yayi yazuba mata mayun idanunshi dasauri takoma baya tasauke kanta kasa dasauri, anatse yace
I don
t forgive mistakes
juyawa yayi zai bude kofa yafita hakan yasa dasauri Yasmeen tace
ni kuma I forgive you duka abinda kamini da kannina
haryasa kafa yafita ya tsaya chak juyoda fuskanshi yayi yakalli side nashi batare daya juyo yakalleta ba, ahankali yace
? Matsowa kusa dashi tayi kadan tace
sabida you are a good person dabai da kow
wani kalan juyowa Maheer yayi kaman zaki dayasa maganan ya makale abakinta tazaro idanu adan firgice kafin abalain tsorace tace
kayakuri I guess I misspoke
wani kalan juyawa Maheer yayi yabar dakin azuciye tareda rufo kofa.
M SHAKUR
EPISODE 2
ZAKI IYA SHIGA GROUP DIN DANAKE POSTING
KYALKYALIN KAUNA
TA HANYAR DANNA LINK DIN NAN
https://chat.whatsapp.com/HyR79BijM7XFBaNPrFcBYn
Daga Baba dake wajen aiki harsu Ammi dake gida babu wanda ya runtsa ranan, dan saida dare yayi Ammi ta birkice sosai dan all this while bata yarda anyi kidnapping yaranta ba saida dare yayi, dare yayi taga yaranta duka basa tareda ita an daukesu kenan yanda take kuka sosai saida Baffa yafita yakira wani likitan anguwansu yazo yama Ammi alluran bacci sannan suka samu tai bacci.
Shima Baba dake station baiyi bacci ba saida ya sumar da direba daya cikin direbobin har saida su Aliyu suka fito dashi daga dakin amman direbobin nan sunki magana ganin yanda ya sumar da dayansu kuma yake fushi yasa suka gane Pablo yadauki wani abu nashi that means sun kusa fita hakan yasa suka kara dake ransu sukaki bada any information dan dasuyi betraying organization din dake basu mahaukacin kudin nan dabasu taba samun irinshi arayuwan su ba gwara su mutu a police station din dasu bada information akan Pablo.
Wuraren 7:15 na safe Baba na zaune kan dogon kujeranshi ya lumshe idanu hannunshi rikeda wayan da babu abinda yake sai fatan Allah yasa Pablo yakirashi Aliyu zaune gefenshi daya damu sosai wayan hannun nashi yayi kara hakan yasa dasauri yabude wayan hannunshi har rawa yake saiga video, Yasmeen ce tafara kokarin karatu saida Farida dasuke bayanta itada Nanah sun kankameta tafito takarba tafara karanta abinda ke paper da yanda tafashe da kuka akarshe, yaran sunyi zuru zuru kaman sunyi shekara dari hannun criminals, kasan sau goma Baba yakalli video sannan yakalli Aliyu yabashi wayan yace
sake kiramin number
dialing number Aliyu yayi kaman tsafi number yayi ringing dauka akayi dasauri Baba ya karbi wayan yace
Hello Pablo
Dan ne yayi magana yace
Oga is unavailable, yariga yamaka kiran dazai maka trust me har abada Oga bazai kara kiranka ba kuma
ijiyan zuciya Baba yasauke ahankali yace
hope my children are fine
dasauri Dan yace
absolutely
ahankali Baba yace
zan saki kayanku yanzun nan bada jimawa ba amman shipment din zan fara saki sainaga yarana zan saki direbobi ku
dan murmushi kawai Dan yayi kadan yace
deal namu is direba da kayanmu, nonetheless Oga always keep promise nashi, za
a kai shipment namu trailer park a ijiye we will take it from there
Dan na maganan ya katse wayan Baba yawani kalan fuzar da ijiyan zuciya abin namai kaman bashiba baitaba sanin wani abu zai iya faruwa dazaisa yayi compromising any case ba sai yau! Bude idanunshi yayi ahankali yakalli Aliyu yace
get the boys ku dauki motocin ku kai inda sukace
dasauri Aliyu yace
direbobin fa
lumshe idanu Baba yayi yace
sainaga yarana tukunna
ijiyan zuciya Aliyu yasauke yawuce kawai yafita wato Baba akwai taurin kai shi bazai iya magana ba Ogan shine he must obey abinda yace amman har cikin ranshi yaso Baba yasaki komi nashi, samin yaranshi yayi dasuka iyajan mota aka kwashi motocin aka tafi dasu har zuwa tipa garage din akai parking tsayawa sukayi suka shige cikin mutane trying to see wanda zaizo yadauka. Baba na zaune a office wayan yayi kara dasauri yadauka cikin kakkausan murya Dan yace
call your boys kace subar wajen nan kafin Oga ya chanza mind dinshi
dip ya katse wayan dasauri Baba yakira Aliyu yace subar wajen dan dole suka tare keke suka shiga sukabar wajen.
Fitowanshi daga wanka kenan yana daure da wani short towel a waist nashi da karami a hannunshi yana tsane kanshi, knocking akayi saida yakarasa kan couch dake dakin ya zauna sannan yace
shigo
shigowa Dan yayi cikeda girmamawa yace
Sir munyi securing shipment din komi lafiya lau saidai bai saki direbobin mu ba
dan gejeren murmushi Maheer yasaki sannan yay crossing kafa daya kan daya tareda ijiye karamin towel din a gefenshi sannan yadago kai yakalli Dan yace
kasa Wike to drop the 2 kids, abar babban anan
gyadamai kai Dan yayi yace
yes sir
yajuya yafita daga dakin.
Farida da Nanah nazaune adaki kaman marayu idanunsu sun kumbura kaman babu komi Wike ya shigo da yaranshi dasuka rufe fuskokinsu yana dariya yace
hip hip hurray, time to go home children
fashewa da kuka Nana tayi Wike yamata wani mugun kallo yace
dabakin ta kaman na kifi ke dauketa kafin na bugamata bindiga tasume, mutafi
dasauri Farida dake sanye da hijabin Yasmeen ta dauketa tana leken kofa ganin bataga Yasmeen ba saikuma tai tunani kila tana mota, wani bakin yadi Wike yasamata a fuska yasama Nana sannan aka kama hannunsu aka fita dasu faduwa kawai gaban Farida yake Nanah sai kuka take tanaji aka sasu a mota bata sake sanin ina sukeba sai tafiya suke hankalinta yaki kwanciya, ita batasan iya dadewan dasukai a mota ba but akalla sunkai awa daya sannan taji motan ya tsaya awani waje aka zare hulunan kansu aka bude kofa Wike yamata wani mugun kallo yace
ku sauka
dasauri Farida ta jujjuya takalli motan ganin bataga Yasmeen ba yasa tace
ina Anty Yasmeen
? Wani mahaukacin kallo da Wike yamata yasa tasauka daga motan da gudu tana daukan Nana a hannu yace
idan kinje gida ask your Daddy
sannan sukaja motan dawani kalan bala
in gudu, bin inda suke Farida tayi da kallo sai yanzu tagane ashe agaban school nasu take, goya Nana tayi abaya tashiga tafiya dasauri sauri gudu gudu dan gani take kaman zasu kara zuwa su daukesu kuma tai gida dan basu da nisa sosai da gida, daga Baffa, Baba, da Baba Karami da Aliyu police duk suna tsaye a kofar gida dan yanzun nan Baba yadawo tareda Aliyu baima iya ya shiga cikin gidan ba, kaman daga sama yaji ance.
Babaaaa
dasauri yajuya, hango Farida yayi goye da Nana tana gudu kaman mahaukaciya dawani kalan sauri dagashi harsu Baffa sukayi kanta yana zuwa Farida batai wata wata ba tafada jikinshi sai kuka Baffa kuma ya karbe Nana daga bayanta, dago Faridan yayi daga jikinshi bakinshi har rawa yake yace
.ina
.ina Yasmeen?
KYALKYALIN KAUNA
Chapter 24 · 0% Book details