Sashe 49
Kyalkyalin Kauna Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
tsakaninka ga Allah Baba yadanyi shiru sai chan yace kanaso ka auri yarinyar nan dan kaci mata mutunci ne ka wulakantata kodan ka kara tozarta mahaifinta sabida yataba kayanka??? Kaa gayamin gaskiya Maheer shiru Maheer yayi kafin chan yace a Baba shiru Baba yayi tun yana karami Allah yabashi baiwan gane idan mutum yana karya ajikinshi kodan sabida shi makaho ne Allah yabashi baiwan oho, cikin kwantacciyan murya Baba yace sai tambaya tabiyu kanason yarinyar ne Maheer ? Hakanan Maheer jiyayi gabanshi yafadi, wannan karan yakusan kai 5min yakasa amsa maganan kafin chan cikin murya mai taushin gaske tsakanin shi ga Allah dakuma zuciya daya yace nima bansani ba Baba dan shiru Baba yayi yana kallonshi sunnar da kanshi kasa Maheer yayi kusan 10min suka bata ahaka kafin Baba yasauke ijiyan zuciya yace tashi katafi zan kira Malam Sani yau zaije yama Baban ta magana yaneman mana izini idan ya yarda cikin satin nan zamuje sai ayi magana kutashi kutafi cute smile Maheer yasaki yatashi ahankali yawuce sama shikuma Hamad ya tsaya batare daya tashi dagakan wajen ba yana kallon Baba cikeda mamaki dan baiyi tunani Baba will accept maganan nan dawuri haka ba, dan murmushi Baba yasaki dan yasan Hamad na zaune awajen har yanzu, anatse yace hanyar shiriya Maheer ya dauko Hamad I have to support him dudda nasan kalubale na gabanshi, akasin hakan zai iya jefashi yaje yayi wani babban kuskuren dayafi komi muni, tashi kaje soon u will understand abinda nayi dakuma abinda hukunci na ke nufi harya tashi Baba yadauki wayanshi yamikamai yace gashi kiramini Malam Sani, idan kaje sama ka karbi address na gidan su yarinyar saika turama Malam Sani ta wayanka ijiyan zuciya Hamad yasauke yayi ma Baba dialing number sannan yawuce yatafi sama yana tunanin kiran telanshi dan dinkama Maheer manyan kaya dan bazasu neman aure yana sanye da kananun kaya ba. As usual wuraren 6 na yamma Baba yadawo gidan saida yafara duba yaran dan yau babu islamiyya sannan yawuce daki, wanka yayi agurguje ya chanza kaya zuwa shadda yasa hula yafito dan tafiya masallaci atare suka fita da Baffa da Baba Karami dan suma sun dawo daga kasuwa. Ana idar da salla andanyi jawabi suka fito suna gangarowa Baffa namusu magana kan kayan gonna da aka samu a gonan Baban su, wani magidancin mutum suka gani akofar gidansu tsaye jikin wata yar mota corolla tsaf tsaf dashi yaci manyan kaya harda Malum malum suna karasowa cikeda girmamawa yabasu hannu yace Assalamu Alaykum barkanmu dai dasauri Baffa dan yafisu raha yace barkanmu bismillah naga kaman mu kake nema ko ? Atsanake yace kwarai kuwa nazo naganku ne gaskiya kam ni ina matsayin kaman dan aike ne, wajen Malam Ibrahim nazo Yay magana yana kallon Baffa, Baba dashi kadaine babu wata fara a akan fuskanshi bawai kuma ko wulakanci bane no he s just a serious person, sanin halin Baba yasa dasauri Baffa yace incedai bawata matsala bane, ga kanina nan shine Ibrahim Meya faru ? Dan dariyan dattawa mutumin yayi yace to dafarko dai sunana Malam Sani nine babban aminin Malam Maheer Makaho wanda a gaskiya shiya aikoni nan na nemi izini wajenku anatse Baba da sai alokacin yah magana yace izinin mene ? Ahankali yace Kunsan dayake makaho ne baya iya fita sosai ya aikoni ne nazo na nemi izini awajenku yanaso yazo axauna ya nemawa danshi Maheer izinin neman auren diyarku Fateema wani kalan gyara tsayuwa Baba yayi dan maganan ta saukanmai kaman aradu, baki yabude zaiyi magana Baffa sanin halinshi yadagamai hannu yace waye dan nashi a ina yasan Fateema? Sannan ita tasan shi ? Anatse Malam Sani yace ehh to kusan zan iya cewa Fateema tasanshi amman bawai irin sannin dakuke tunani ba dan banjin wata magana ma yataba hadasu ba danshi Maheer lecturer ne a makarantan su yana koyar da English ma duka department dake makarantan, yasami Baban shi yau kan yanaso afara sanarda iyayenta idan sun bashi izini sai afara neman aurenta gaskiya banjin suntaba magana bama kusan Baba zai iya cewa ya yarda dan wayanta akai akia yake bincika wa kuma da aka dauketa wayan all through na hannunshi ba a taba kiranta daidai da 1 miss call ba anatse Baba yace ba yanzu zan aurar d tareshi Baffa yayi da sauri ta hanyar sakin ma Malam Sani murmushi yace gobe juma a zaku iya zuwa bayan juma a dan bayan salla bama komawa kasuwa agida muke yini murmushi Malam Sani yayi yace Masha Allah to too Allah ya zabamana abinda yafi alkhairi, bari na barku ku shiga gida to saida safenku yasake babbasu hannu suka gaisa, motanshi ya shiga yaja yabar wajen Baffa yakalli Baba da bacin rai dan dama baiwani huce sosai ba dudda Baba yabashi hakuri yace kana kokarin gayamusu baka shirya aurar da Yasmeen ba kasan alamomin gidan mutunci kuwa ? Baffa yanuna motan mutumin daya wuce yace gidan mutunci ne da yaron kwarai awannan zamanin zasuzo sufara tambayan izinin iyaye kafin dansu yama yima diyarka magana, kadaisan bazan taba bayarda Yasmeen banyi bincike ba kabar ganin kanka kaine dan sanda kaine ka iya bincike kasan abubuwa nafika sanin rayuwa Ibrahim, kabari gobe suzo muga yaron idan natsuwanshi yayi zamu bashi izini ya nemi Yasmeen inyaso saina hada bikinta dana Sa a dan iyayen yaron sunzo kasuwa sun samen, kuam iyayen yaron sun damen sunaso asa rana nan da wata daya kanajina badan yasoba Baba yace Baffa yakalli Baba karami yace koba hakaba anatse yace hakan yayi Yaya, Yasmeen ta isa aure ai jinjina kai Baffa yayi jin ana kiran isha i yace mutafi muyi isha i kawai gabadaya duk suka juya suka wuce mosque, koda suka dawo sama sama Baba yaci abincin yawuce dakinsu Yasmeen dukansu na zaune adakin harda Nana suna hira suna dariya ganin Baba yasa sukai tsit, binsu yayi da kallo one bye one sannan yasaki labulen yawuce yashiga dakinsu, direct kan kujera yayi yazauna Ammi dake zaune ganinshi haka yasa tace lafiya Baban Nanah kanka ciwo yake ne ? Girgixa mata kai yayi baice komi ba yawuce yatafi uwarka da kawai. Har wajajen dayan dare Baba yakasa bacci juye juye yake hakan yasa cikeda damuwa Ammi ta kunna wutan dakin takalleshi shima kallonta yayi saikuma yatashi yazauna tareda folding hannu akirji cikeda damuwa Ammi tace wai menene Baban Nanah am getting worried? Meke troubling naka haka ka kasa bacci sai juye juye kake shiru yayi yana kallon Ammi kasa dannewa yayi yace wani mutumi dazu yazo tambayan neman Auren Yasmeen shine Baffa yace suzo gobe wani kalan murmushi Ammi tayi da abin harsaida yasa Baba sakin baki dasauri tace waye shi ? Cikeda dan bacin rai Baba yace nima bansani ba sai gobe idan sunzo amman ance yaron lecturer ne a school nasu wani kalan murmushi Ammi tayi kaman anmata albishir da kujeran makka hannu ta daga sama tace Ya Allah ka tabbatar da Alkhairi kabawa Yasmeen miji mai sonta sama da yanda Baban ta ke sona dan tsaki Baba yayi kawai yakoma ya kwanta tareda juyamata baya dariya Ammi tayi da shewa tace wlh Baffa Yamin daidai aka biyemaka bazaka taba aurar da yaran nan ba kashe wutan tayi tadawo rungume Baba tayi tace zonan wlh saikai farin ciki daganan salon labarin ya chanza. M SHAKUR EPISODE 4 EPISODE 48 To Jama a anan nakawo karshen FREE EPISODES na wannan littafin nawa Mai suna KYALKYALIN KAUNA wato SPARKLES OF AFFECTION Wannan aure zai yu kuwa?? Yaya Baba zaiyi idan yagano Maheer shine Pablo Escobar?? Kuna ganin kafin aure ko bayan aure ne Baba zai gano gaskiya??? Hajiya zata taba barin Maheer da Yasmeen suyi zaman aure??? Hmmmm!!! Kubiyoni. Idan kinason cigaba da karanta littafin nan all you have to do is pay ko 1k or 500 into 3107021073 Aisha Muhammad first bank. Zakimin magana a WhatsApp wa.me/+7012181461 sainai adding naki a paid group. Group na 1k is 2updates daily banda alhamis da juma Group na 500 is 1update daily banda alhamis da juma And inada EXCLUSIVE shi a Email nake musu update yanzu haka sun wuce ku is 5k. 4episode daily Please patronize my little work, and appreciate my talent, show me support ta hanyar subscribing ki shiga paid group. Thank you I love you all https://vm.tiktok.com/ZM2U8NPMo/ Kusan duka yaran gidan babu wanda yasan akwai wani abu dazai faru yau Baffa dai yasa Baba karami yasayo drinks harda su Maltina da ruwan gora, matan gidan kuma harda Ammi aka hau girki yaran gidan kuma duk suka tafi school, Baba sabida haushi tun 6 yatafi aiki Baffa dai saida yakirashi ya jaddadamai biyu tamai agida, Yasmeen 9 ta tafi school abinta yau har 6 takeda lectures. Ana idar da sallan juma a Baba yadawo gida gidan an gyara yay kal kal an shimfida manya manyan tabarmai a compound kasan bishiya girgixa kai kawai yayi yawuce ciki wanka yayi ya shirya cikin babban kaya harda Malum Malum da hula ya fesa turare yafito waje daidai ana sallama Baffa ya kalleshi yace muje mu shigo dasu baiyi musu ba suka fita atare, Hamad ne ke tuki sai Maheer agefenshi Maheer yasaka wata faran shadda jumper da hulan Hamad akai wlh kaga Mageer zaka dauka ango ne, Malam Sani da Baba sai limamun anguwan su wanda yake abokin Baba ne sosai, duk suna tsaitsaye Baba yafara fitowa daga gidan kallo daya Maheer yamai yasauke kanshi kasa sabida yanda Baba yamai wani kalan kwarjini a ido gaisawa su Baba sukayi dasu Malam Sani hakan yasa Hamad yataho tareda dan jan Maheer daya kasa motsi Malam Sani yace surukin naku akwai bala in kunya, wannan shine yayan shi Hamad yanuna Hamad dake bama Baffa hannu Baffa yakarba cikeda murmushi yace ina gajiya sannan yanuna Maheer da kanshi ke kasa yace wannan shine Maheer ahankali Maheer yabama Baba dake kallonshi hannu karban hannun Baba yayi mury a chan kasa Maheer yace ina yini ba yabo ba fallasa Baba yace lpy lau tareda karbe hannunshi, Baffa yace bismillan ku kushigo shiga ciki sukayi Ammi dasu Yaya ta window suke lekawa kaman yara dukansu are so excited Ammi tace waye surukin nawa naga samari biyu Yaya tai pointing Maheer dake sunnar dakai tace daga ganin mai kunyan chan shine mai neman Yasmeen wani kalan murmushi Ammi tayi tace surukina badai kyau ba kaman